Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 47

Bangaskiyarka Tana da Karfi Kuwa?

Bangaskiyarka Tana da Karfi Kuwa?

“Kada ku damu. Ku ba da gaskiya.”​—YOH. 14:1.

WAƘA TA 119 Wajibi Ne Mu Kasance da Bangaskiya

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wace tambaya ce za mu iya yi wa kanmu?

IDAN ka yi tunanin abubuwan da za su faru a nan gaba, kamar hallakar addinan ƙarya, harin da Gog na Magog zai kawo mana, da kuma yaƙin Armageddon, hakan yana sa ka damuwa? Ka taɓa tambayar kanka cewa, ‘Idan abubuwan nan suka faru, zan iya riƙe amincina?’ Idan ka taɓa yin wannan tunanin, abin da Yesu ya faɗa a ayar da aka ɗauko jigon wannan talifin zai taimaka maka. Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “Kada ku damu. Ku ba da gaskiya.” (Yoh. 14:1) Bangaskiya mai ƙarfi za ta taimaka mana mu jimre duk wata matsala da za mu fuskanta a nan gaba.

2. Ta yaya za mu ƙarfafa bangaskiyarmu kuma me za mu tattauna a wannan talifin?

2 Idan muna tunanin abin da muke yi sa’ad da muka fuskanci matsalolin da suka gwada bangaskiyarmu, za mu san abin da za mu iya yi don mu sa bangaskiyarmu ta ƙara ƙarfi. Yin wannan tunanin zai taimaka mana mu san inda za mu ƙara ƙwazo don mu ƙarfafa bangaskiyarmu. A duk lokacin da muka jimre wata jarrabawa, bangaskiyarmu za ta ƙara ƙarfi. Hakan zai taimaka mana mu jimre matsalolin da za mu fuskanta a nan gaba. A wannan talifin, za mu tattauna matsaloli huɗu da suka sa almajiran Yesu suka bukaci ƙarin bangaskiya. Sa’an nan, za mu tattauna yadda za mu iya jimre matsaloli makamancinsu a yau, da kuma yadda za mu shirya kanmu don abubuwan da za su faru a nan gaba.

MU BA DA GASKIYA CEWA JEHOBAH ZAI YI MANA TANADI

Za mu iya fama da matsalar kuɗi, amma bangaskiyarmu za ta taimaka mana mu mai da hankali ga ibadarmu (Ka duba sakin layi na 3-6)

3. Kamar yadda Matiyu 6:​30, 33 suka nuna, wane batu ne Yesu ya bayyana dalla-dalla game da bangaskiya?

3 Kowane magidanci zai so ya tanadar wa iyalinsa abinci, da sutura da wurin kwana. Hakan bai da sauƙi a wannan mawuyacin lokaci. Wasu ’yan’uwanmu sun rasa aikinsu kuma duk da cewa sun yi ƙoƙari su sami wani aiki, ba su samu ba. Wasu kuma sun daina aikin da suke yi domin aikin ya saba wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Idan irin abubuwan nan suka faru, muna bukatar mu ba da gaskiya cewa Jehobah zai tanadar mana abin da muke bukata. Yesu ya gaya wa almajiransa hakan dalla-dalla sa’ad da yake huɗuba a kan dutse. (Karanta Matiyu 6:​30, 33.) Idan muka kasance da tabbaci cewa Jehobah ba zai bar mu ba, za mu iya ci gaba da bauta masa da dukan zuciyarmu. Yayin da muke ganin yadda Jehobah yake tanada mana abin da muke bukata, za mu daɗa kusantarsa kuma bangaskiyarmu za ta daɗa ƙarfi.

4-5. Me ya taimaki wata iyali sa’ad da suke damuwa a kan abin biyan bukata?

4 Ka yi la’akari da yadda Jehobah ya taimaki wata iyali a Benezuwela sa’ad da suke damuwa a kan yadda za su sami abin biyan bukata. A dā, iyalin suna samun kuɗi daga noman da suke yi a gonarsu. Amma wasu ’yan bindiga suka kwace gonar. Mahaifin mai suna Miguel ya ce: “Yanzu muna yin noma a wata ƙaramar gona da muka ara. A kowace safiya, ina roƙon Jehobah ya ba mu abin da muke bukata a ranar.” Iyalin nan suna fama da matsaloli, amma domin sun ba da gaskiya cewa Jehobah zai ba su abin da suke bukata kullum, ba sa fasa zuwa taro da kuma yin wa’azi. Sun saka Mulkin Allah farko a rayuwarsu kuma Jehobah yana ba su abin da suke bukata.

5 A duk lokacin nan da suke shan wahala, Miguel da matarsa mai suna Yurai, sun mai da hankali ga yadda Jehobah yake kula da su. A wasu lokuta, Jehobah yakan sa ’yan’uwansu masu bi su ba su wasu abubuwa da suke bukata ko su taimaka wa Miguel ya sami aikin yi. A wasu lokuta kuma, Jehobah yakan yi musu tanadi ta wajen reshen ofishinmu da ke ƙasar. Jehobah bai taɓa barinsu ba. Hakan ya sa bangaskiyarsu ta daɗa ƙarfi. A lokacin da ’yarsu babba mai suna Yoselin take ba da labarin yadda Jehobah ya taimake su, ta ce: “Yadda Jehobah ya taimake mu ya ƙarfafa mu sosai. Ina ɗaukansa a matsayin abokina, kuma na san zai taimaka min a kullum.” Ta ƙara da cewa: “Matsalar da iyalinmu ta shiga ya taimaka mana mu shirya kanmu don matsaloli masu wuya da za su faru a gaba.”

6. Ta yaya za ka ƙarfafa bangaskiyarka idan kana fama da rashin kuɗi?

6 Shin kana fama da rashin kuɗi ne? Idan haka ne, mun san cewa ba zai yi maka sauƙi ba. Duk da haka, za ka iya yin amfani da wannan lokacin ka ƙarfafa bangaskiyarka. Ka yi addu’a kuma ka karanta abin da Yesu ya faɗa a Matiyu 6:​25-34, sa’an nan ka yi tunani a kan su. Ka yi la’akari da labaran da suka faru a zamaninmu da suka nuna cewa Jehobah yana taimaka ma waɗanda suka sa mulkinsa a gaba. (1 Kor. 15:58) Hakan zai tabbatar maka cewa kamar yadda Jehobah ya taimaki ’yan’uwanka, zai taimaka maka. Ya san abin da kake bukata da yadda zai tanadar maka abin. Yayin da kake ganin yadda Jehobah yake taimakon ka, bangaskiyarka za ta daɗa ƙarfi kuma hakan zai taimake ka ka jimre matsaloli masu wuya da za ka fuskanta a gaba.​—Hab. 3:​17, 18.

MUNA BUKATAR BANGASKIYA DON MU JIMRE WA “BABBAN HADARI”

Bangaskiya mai ƙarfi za ta taimaka mana mu jimre kowace jarrabawa (Ka duba sakin layi na 7-11)

7. Bisa ga abin da ke Matiyu 8:​23-26, ta yaya wani “babban hadari” ya gwada bangaskiyar almajiran Yesu?

7 Akwai lokaci da Yesu da almajiransa suke tafiya a teku, sai aka soma ruwa da iska. Yesu ya yi amfani da wannan lokacin don ya taimake su su gane cewa suna bukatar su ƙarfafa bangaskiyarsu. (Karanta Matiyu 8:​23-26.) Don ƙarfin iskar, ruwa ya soma cika kwalekwalen. Amma Yesu ya ci gaba da barcinsa. Sa’ad da almajiransa, cike da tsoro, suka tashe shi daga barci don ya cece su, sai Yesu ya tambaye su cewa: “Don me kuka ji tsoro haka, ya ku masu ƙaramar bangaskiya?” Ya kamata almajiran su tuna cewa Jehobah zai iya kāre Yesu har da waɗanda suke tare da shi. Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin? Bangaskiya mai ƙarfi za ta taimake mu mu jimre duk wani “babban hadari” ko matsalar da ke kama da hakan.

8-9. Mene ne ya jarraba bangaskiyar Anel, kuma me ya taimake ta?

8 Ka yi la’akari da labarin wata ’yar’uwa mai suna Anel, wadda ba ta yi aure ba, daga ƙasar Puerto Rico. Ta fuskanci wata matsala da ta sa bangaskiyarta ta daɗa ƙarfi. Matsalar da ta auko mata ‘babban hadari’ na zahiri ne. Matsalarta ta soma a 2017 a lokacin da mahaukaciyar guguwa mai suna Maria ta hallaka gidan Anel. Saboda wannan guguwar, ta rasa aikinta. Anel ta ce: “Sa’ad da abubuwan nan suke faruwa, na damu sosai. Amma na dogara ga Jehobah ta yin addu’a kuma ban bar damuwa ta hana ni yin abin da ya kamata ba.”

9 Anel ta ce yin biyayya ma ya taimaka mata ta jimre matsalarta. Ta ce: “Bin umurnin da ƙungiyarmu ta bayar ya kwantar mini da hankali. Jehobah ya taimake ni ta wajen ’yan’uwana. Sun ƙarfafa ni kuma sun ba ni abubuwan da nake bukata. Jehobah ya ba ni fiye da abin da na roƙa kuma bangaskiyata ta daɗa ƙarfi.”

10. Me za ka iya yi idan ka fuskanci wani “babban hadari?”

10 Shin kana fuskantar wani “babban hadari?” Mai yiwuwa kana shan wahala saboda wani bala’i da ya auku. Ko kuma kana fama da wani rashin lafiya mai tsanani da yake sa ka sanyin gwiwa kuma ba ka san abin da za ka yi ba. A wasu lokuta, za ka iya damuwa sosai, amma kada ka bar damuwar ta hana ka dogara ga Jehobah. Ka kusace shi ta wajen yin addu’a. Ka ƙarfafa bangaskiyarka ta yin bimbini a kan yadda Jehobah ya taimake ka a baya. (Zab. 77:​11, 12) Ka tabbata cewa har abada, Jehobah ba zai yar da kai ba.

11. Me ya sa yake da kyau mu ƙudura cewa za mu riƙa biyayya ga masu ja-goranci?

11 Me kuma zai iya taimake ka ka jimre matsaloli? Anel ta ce yin biyayya ne ya taimake ta. Ka yarda da waɗanda Jehobah da Yesu suka naɗa. A wasu lokuta, za mu iya ganin kamar umurnin da ’yan’uwa masu ja-goranci suka ba mu bai dace ba. Amma Jehobah yana yi wa masu biyayya albarka. Kalmarsa da labaran ’yan’uwa masu aminci sun nuna cewa yin biyayya yana cetan rayuka. (Fit. 14:​1-4; 2 Tar. 20:17) Ka yi bimbini a kan misalan nan. Hakan zai ba ka ƙarfin gwiwar bin umurnin ƙungiyar Jehobah yanzu da kuma a nan gaba. (Ibran. 13:17) Da haka, ba za ka ji tsoron ƙunci mai girma da ke gaba ba.​—K. Mag. 3:25.

BANGASKIYA ZA TA TAIMAKE MU MU JIMRE RASHIN ADALCI

Idan muka ci gaba da yin addu’a, bangaskiyarmu za ta daɗa ƙarfi (Ka duba sakin layi na 12)

12. Wace alaƙa ce ke tsakanin bangaskiya da jimre rashin adalci kamar yadda Luka 18:​1-8 suka nuna?

12 Yesu ya san rashin adalci zai iya jarraba almajiransa. Don haka ya ba da misali a littafin Luka don ya taimaka musu su san abin da za su yi in hakan ya faru. Yesu ya yi maganar wata gwauruwa da ta yi ta roƙan wani alƙali marar adalci don ya yi mata adalci. Ta san cewa naciyarta zai sa ya taimake ta. A ƙarshe, ya yi hakan. Wane darasi ne muka koya? Jehobah ba mai rashin adalci ba ne. Shi ya sa Yesu ya ce: “Ashe, Allah ba zai biya wa mutanen da ya zaɓa waɗanda suke masa kuka dare da rana hakkinsu ba?” (Karanta Luka 18:​1-8.) Sai Yesu ya daɗa da cewa: ‘Sa’ad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami mutum mai bangaskiya a duniyar nan kuwa?’ Idan aka yi mana rashin adalci, mu nuna cewa muna da bangaskiya ta yin haƙuri da kuma nacewa kamar yadda gwauruwar ta yi. Ta hakan, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai taimake mu. Ƙari ga haka, ya kamata mu ba da gaskiya cewa yin addu’a zai taimaka mana. A wasu lokuta, Jehobah zai iya amsa addu’o’inmu a hanyoyin da ba mu zata ba.

13. Ta yaya yin addu’a ya taimaka ma wata iyali da aka yi musu rashin adalci?

13 Ka yi la’akari da labarin wata ’yar’uwa mai suna Vero da ke Jamhuriyar Ɗimokuraɗiyyar Kwango. Vero da maigidanta da ba Mashaidi ba ne, tare da ’yarta mai shekara 15, sun gudu daga ƙauyensu sa’ad da wasu ’yan bindiga suka kai ma ƙauyensu hari. Sa’ad da suke tafiya, wasu ’yan bindiga dabam suka tare su kuma suka ce za su kashe su. Da Vero ta soma kuka, sai ’yarta ta yi ƙoƙari ta kwantar mata da hankali ta wajen yin addu’a da babbar murya da kuma amfani da sunan Jehobah a cikin addu’ar. Bayan addu’ar, sai shugaban ’yan bindigar ya ce mata: “Yarinya, wa ya koya miki yin addu’a?” Sai yarinyar ta ce: “Mamata ce ta koya min ta wajen yin amfani da addu’ar Ubangiji da ke Matiyu 6:​9-13.” Sai shugaban ya ce, “Yarinya, da ke da iyayenki ku sauka lafiya kuma bari Allahnki Jehobah ya kāre ku!”

14. Me zai iya jarraba bangaskiyarmu, kuma me zai taimake mu mu jimre?

14 Irin misalan nan suna nuna mana amfanin yin addu’a. Amma idan Allah bai amsa addu’arka da sauri ko a gagarumar hanya ba fa? Kamar gwauruwa da ke misalin Yesu, ka ci gaba da addu’a kuma ka tabbata cewa Allah ba zai bar ka ba. A kwana a tashi zai amsa addu’arka. Ka ci gaba da roƙan Jehobah don ruhunsa. (Filib. 4:​13, Littafi Mai Tsarki) Ka tuna cewa nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai yi maka albarka sosai har ka manta da duk matsalar da ka fuskanta. Yayin da kake jimrewa da taimakon Jehobah, bangaskiyarka za ta daɗa ƙarfi kuma za ka iya jimre matsalolin da za su zo a gaba.​—1 Bit. 1:​6, 7.

BANGASKIYA ZA TA SA MU CI GABA DA BAUTA WA JEHOBAH

15. Wace matsala ce almajiran Yesu suka fuskanta kamar yadda aka rubuta a Matiyu 17:​19, 20?

15 Yesu ya ce wa almajiransa bangaskiya za ta sa su ci gaba da bauta wa Allah duk da matsaloli. (Karanta Matiyu 17:​19, 20.) Akwai lokacin da almajiran Yesu suka kasa fid da aljanu duk da cewa sun taɓa yin hakan. Me ya sa? Yesu ya ce musu suna bukatar ƙarin bangaskiya. Isasshen bangaskiya za ta sa su iya ci gaba da bauta ma Jehobah duk da matsaloli masu girma kamar tuddai! A yau, mu ma za mu iya fuskantar matsalolin da za su iya sa ya yi mana wuya mu ci gaba da bauta wa Allah.

Za mu iya yin baƙin ciki sosai, amma bangaskiya za ta taimaka mana mu mai da hankali ga ibadarmu (Ka duba sakin layi na 16)

16. Ta yaya bangaskiya ta taimaka wa Geydi ta jimre bayan an kashe maigidanta?

16 Ka yi la’akari da misalin Geydi wata ’yar’uwa daga Guatemala. An kashe maigidanta mai suna Edi sa’ad da suke komawa gida daga taron ikilisiya. Ta yaya bangaskiyar Geydi ta taimaka mata ta jimre baƙin cikin? Ta ce: “Addu’a tana taimaka min in danƙa damuwata ga Jehobah kuma hakan yana sa in sami kwanciyar hankali. Jehobah yana nuna min cewa yana ƙaunata ta wurin iyalina da kuma abokaina a ikilisiya. Yin ayyukan ibada yana rage min baƙin ciki kuma yana taimaka mini in ci gaba da bauta wa Jehobah kullum ba tare da damuwa a kan abin da zai faru gobe ba. Daga abin da ya faru, na koyi cewa ko da wace irin matsala ce za mu fuskanta a nan gaba, Jehobah da ƙungiyarsa da kuma Yesu Kristi za su taimaka mana mu jimre matsalar.”

17. Me za mu iya yi idan muka fuskanci babbar matsala da take kama da tudu?

17 Shin kana baƙin ciki domin wani da kake ƙauna ya mutu? Ka karanta labaran waɗanda aka tā da su a Littafi Mai Tsarki don ka ƙarfafa bangaskiyarka cewa Allah zai tā da matattu. Kana baƙin ciki ne domin an yi ma wani a iyalinku yankan zumunci? Ka yi nazari don ka tabbatar wa kanka cewa Jehobah yana yin horo a hanyar da ta dace. Ko da wace matsala ce kake fuskanta, ka yi amfani da damar wajen ƙarfafa bangaskiyarka. Ka gaya wa Jehobah yadda kake ji. Kada ka wāre kanka. A maimakon haka, ka riƙa yin kusa da ’yan’uwanka. (K. Mag. 18:1) Ka yi abubuwa da za su taimaka maka ka jimre ko da kana kuka a duk lokacin da ka tuna abin da ya faru da kai. (Zab. 126:​5, 6) Ka ci gaba da zuwa taro da karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin wa’azi. Kuma ka ci gaba da yin tunanin abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi alkawari zai yi maka a nan gaba. Yayin da kake ganin yadda Jehobah yake taimaka maka a yanzu, bangaskiyarka za ta daɗa ƙarfi.

“KA ƘARA MANA BANGASKIYA”

18. Idan ka lura cewa bangaskiyarka ba ta da ƙarfi sosai, me ya kamata ka yi?

18 Idan matsaloli da ka fuskanta a dā ko waɗanda kake fuskanta yanzu sun nuna cewa bangaskiyarka ba ta da ƙarfi sosai, kada ka karaya. Ka ɗauke su a matsayin damar ƙarfafa bangaskiyarka. Ka roƙe Allah kamar yadda almajiran Yesu suka yi sa’ad da suka ce: “Ka ƙara mana bangaskiya.” (Luk. 17:5) Ban da haka, ka yi tunanin misalan da muka tattauna a talifin nan. Kamar yadda Miguel da Yurai suka yi, kai ma ka tuna lokutan da Jehobah ya taimaka maka. Kamar yadda ’yar Vero da kuma Anel suka yi, ka yi addu’a sosai ga Jehobah musamman idan kana cikin babbar matsala. Kuma kamar yadda Geydi ta yi, ka san cewa Jehobah zai iya taimakon ka ta wajen abokanka ko iyalinka. Idan ka bar Jehobah ya taimake ka ka jimre matsalar da kake fuskanta, hakan zai ƙara tabbatar maka cewa zai taimake ka ka jimre a nan gaba.

19. Wane tabbaci ne Yesu ya kasance da shi, kuma wane tabbaci ne kai ma za ka iya kasancewa da shi?

19 Yesu ya taimaka wa almajiransa su ga inda suke bukatar ƙarin bangaskiya, amma ya kasance da tabbaci cewa da taimakon Jehobah, za su iya jimre matsalar da za su fuskanta a gaba. (Yoh. 14:1; 16:33) Yana da tabbaci cewa taro mai girma za su tsira daga ƙunci mai girma. (R. Yar. 7:​9, 14) Za ka kasance a cikinsu? Da taimakon Jehobah za ka tsira idan ka yi iya ƙoƙarinka ka ƙarfafa bangaskiyarka yanzu.​—Ibran. 10:39.

WAƘA TA 118 Ka “Ƙara Mana Bangaskiya”

^ sakin layi na 5 Muna marmari ƙarshen wannan muguwar duniyar ta zo. Amma a wasu lokuta, za mu iya tunanin ko bangaskiyarmu za ta iya taimaka mana mu jimre idan ƙarshen ya zo. A wannan talifin, za mu tattauna misalai da kuma darussan da za su iya taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu.