Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Yadda Na Nemi Rayuwa Mai Ma’ana

Yadda Na Nemi Rayuwa Mai Ma’ana

SA’AD da nake tafiya da jirgin ruwa a tsakiyar Bahar Maliya, na lura cewa jirgin ruwan ya fashe kuma ruwa yana shiga cikin jirgin sosai. Sai aka soma yin iska mai ƙarfi. Tsoro ya kama ni, kuma na yi addu’a. Wannan shi ne karo na farko da na yi addu’a bayan shekaru da yawa. Ta yaya na sami kaina a wannan yanayin? Bari in soma ba ku labarin daga farko.

A lokacin da nake shekara bakwai, iyalinmu sun zauna a ƙasar Brazil

An haife ni a ƙasar Nedalan a shekara ta 1948. Bayan shekara ɗaya, iyalinmu sun ƙaura zuwa birnin São Paulo na ƙasar Brazil. Iyayena ba sa wasa da zuwa coci, kuma a iyalinmu, mukan karanta Littafi Mai Tsarki kullum bayan mun ci abincin yamma. Mun sake ƙaura a 1959, amma a wannan karon, zuwa ƙasar Amirka kuma mun zauna a jihar Massachusetts.

Mahaifinmu ya yi aiki tuƙuru don ya biya bukatun mu takwas a iyalin. Ya yi aiki a wurare dabam-dabam. Alal misali, ya yi aiki a matsayin mai sayar da abubuwa, mai gyaran hanya da kuma wakilin kamfanin jirgin sama. Kowa a iyalinmu ya yi farin ciki sa’ad da mahaifinmu ya sami aiki a kamfanin jirgin sama domin hakan zai ba mu damar yin tafiya zuwa wurare dabam-dabam.

A lokacin da nake makarantar sakandare, nakan yi tunanin abin da zan yi da rayuwata idan na girma. Wasu abokaina sun shiga makarantun jami’a, wasu kuma sun shiga aikin soja. Amma ban so in shiga aikin soja ba domin ni ba mai son cacar baki ba ne balle ma faɗa. Na yanke shawarar zuwa makarantar jami’a domin in guje wa shiga aikin soja. Amma a cikin zuciyata, na fi son in yi abin da zai taimaka ma wasu, domin a ganina hakan zai sa rayuwata ta kasance da ma’ana.

SA’AD DA NAKE JAMI’A

Na yi shekaru da yawa ina neman rayuwa mai ma’ana

Sa’ad da nake makarantar jami’a, na yi nazarin ilimin ɗan Adam domin ina so in san yadda rayuwa ta soma. An koya mana cewa ba Allah ne ya halicci abubuwa ba, kuma an bukace mu mu amince da hakan ba tare da yin tambaya ba. Amma a ganina, dalilan da suka bayar ba masu gamsarwa ba ne, kuma sun bukace ni in amince da hakan ba tare da hujja ba. Yin hakan ya saɓa wa ƙa’idodin kimiyya.

A makarantar, ba a koya mana ɗabi’u masu kyau ba, sun fi mai da hankali a kan koya mana yadda za mu yi nasara ta kowace hanya. Zuwa fati da kuma shan ƙwayoyi sun sa ni farin ciki, amma hakan na ɗan lokaci ne. Na yi ta tunanin ko hakan rayuwa mai ma’ana ce.

Sai na ƙaura zuwa birnin Boston kuma na shiga makarantar jami’a da ke wurin. Don in sami kuɗin biyan makarantar, sai na soma yin aiki a lokacin hutu, kuma a lokacin ne na soma haɗuwa da Shaidun Jehobah. Wani abokin aikina ya tattauna annabci game da “tsawon lokaci bakwai” da ke littafin Daniyel sura 4 tare da ni, kuma ya bayyana mini cewa muna rayuwa a kwanakin ƙarshe. (Dan. 4:​13-17) Nan take, sai na ga cewa idan na ci gaba da koya game da Littafi Mai Tsarki kuma na amince da abin da nake koya, dole ne in canja salon rayuwata. Don haka, sai na soma guje wa abokin aikina.

A makaranta, na yi nazarin abubuwa da za su taimaka mini in yi aikin agaji a Amirka ta Kudu. Na ɗauka cewa yin aikin agaji, zai sa rayuwata ta kasance da ma’ana. Amma sai na ga cewa yin aikin agajin ma bai sa rayuwata ta kasance da ma’ana ba. Don haka, sai na dakatar da karatu da nake yi a jami’ar.

NA CI GABA DA TUNANIN YADDA ZAN YI RAYUWA MAI MA’ANA A WATA ƘASA

A watan Mayu na 1970, na ƙaura zuwa birnin Amsterdam da ke Nedalan kuma a wurin na yi aiki da kamfanin jirgin sama da mahaifina ya yi aiki. Wannan aikin ya sa na yi tafiya zuwa wurare dabam-dabam, kamar ƙasashen Afirka da ƙasashen Turai, da ƙasashen Amirka da kuma Asiya. Na lura cewa a duk wata ƙasa da na je, mutane suna fama da matsaloli da yawa, kuma babu wanda ya iya magance matsalolin. Duk da haka, ina so in yi rayuwa mai ma’ana, sai na yanke shawarar sake komawa ƙasar Amirka kuma na sake shiga makarantar jami’a a birnin Boston.

Da na koma makarantar jami’a, bai jima ba, sai na gane cewa abubuwan da ake koya mana ba sa taimaka mini in sami amsoshi game da rayuwa. Hakan ya sa na tambayi malaminmu game da abin da zan yi. Amsarsa ta ba ni mamaki, ya ce mini: “To don me kake ci gaba da makarantar? Me ya sa ba za ka daina ba?” Na bi shawarar da ya ba ni, sai na daina zuwa makarantar.

Da yake har yanzu ina ji kamar rayuwata ba ta da amfani, na shiga ƙungiyar da suke da’awar cewa ba ruwansu da al’adu, kuma suke ƙoƙarin ɗaukaka zaman lafiya da ƙauna a cikin al’umma. Ni da wasu abokaina mun yi tafiya da ƙafa daga Amirka zuwa birnin Acapulco a ƙasar Meziko. Mun zauna tare da wasu mutane da suka yi watsi da ƙa’idodin rayuwa, kuma suna yin rayuwa kamar ba su da damuwa ko matsaloli. Amma da na ci gaba da zama da su, sai na gane cewa irin rayuwar da suke yi ba ta da ma’ana kuma ba ta kawo farin ciki. A maimakon haka, yawancin mutanen marasa gaskiya ne kuma marasa aminci.

NA YI TAFIYA DA JIRGIN RUWA DON IN NEMI RAYUWA MAI MA’ANA

Ni da abokina mun nemi wani tsibiri mai kyau

Na soma tunani a kan abubuwan da nake so in yi sa’ad da nake ƙarami. A lokacin da nake yaro, burina shi ne in zama matuƙin jirgin ruwa. Hanya ɗaya da zan iya yin hakan ita ce sayan jirgin ruwa na kaina. Da yake abin da wani abokina mai suna Tom yake so ya yi ke nan, sai muka yanke shawarar yin tafiya da jirgin ruwa zuwa wurare dabam-dabam a faɗin duniya. Burina shi ne in sami wani tsibiri mai kyau inda zan yi rayuwa dabam da wanda na saba yi.

Ni da Tom mun yi tafiya zuwa yankin Arenys de Mar da ke kusa da Barcelona a ƙasar Sifen. A wurin, mun sayi wani jirgin ruwa mai girman kafa 31 mai suna Llygra. Mun canja fasalin jirgin don mu iya yin tafiya da shi a teku. Da yake ba ma hanzarin isa wurin da za mu je, sai muka cire injin jirgin, don mu daɗa samun wurin saka ruwan sha. Don mu iya tuka jirgin a ƙananan tashar jirgin ruwa, mun sayi abin tuka kwalekwale guda biyu da tsayinsu ya kai kafa 16. A ƙarshe, sai muka nufi tsibirin Seychelles da ke tekun Indiya. Niyyarmu shi ne mu tuka jirgin ruwan zuwa gaɓar tekun da ke yammacin Afirka da kuma tsibirin Cape of Good Hope da ke Afirka ta Kudu. Mun yi amfani da taurari da taswira da littattafai da kuma wasu ƙananan na’urori don mu iya gane hanyar da za mu bi. Na yi mamaki sosai a kan yadda muka iya gane hanya.

Ba da daɗewa ba, sai muka gane cewa jirgin bai dace mu yi tafiya da shi a kan teku ba. Aƙalla ruwa galan shida ne yake shiga jirgin a cikin awa ɗaya! Kamar yadda na faɗa a gabatarwar, sa’ad da aka soma iska, na yi addu’a a karo na farko bayan na yi shekaru da yawa ban yi hakan ba, kuma na yi wa Allah alkawari cewa idan muka tsira, zan yi iya ƙoƙarina don in bauta masa. Sai aka daina iskar kuma na cika alkawarina.

Na soma karanta Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke cikin tekun. Na ji daɗin zama a cikin jirgin a Bahar Maliya kuma ina ganin kifaye iri-iri suna iyo da kuma sararin sama. Da daddare, dami-damin taurari da nakan gani a sama sun burge ni sosai kuma sun ƙara tabbatar mini da cewa akwai Mahalicci da yake ƙaunar ’yan Adam.

Bayan wasu makonni, sai muka isa tashar jirgin ruwa a Alicante da ke Sifen. A wurin, mun saka jirgin ruwanmu a kasuwa don mu sayi wani da ya fi shi kyau. Ba mu sami wanda zai sayi jirgin ba. Hakan bai ba mu mamaki ba domin jirgin ya tsufa, ba shi da inji kuma ruwa yana shiga jirgin! Amma a wurina, wannan lokaci ne mai kyau na karanta Littafi Mai Tsarki.

Da na ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki, sai na soma ɗaukan sa a matsayin littafin da zai taimaka mini in yi rayuwa mai ma’ana. Na ji daɗin yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalla-dalla yadda za mu kasance da ɗabi’u masu kyau. Kuma na yi mamakin dalilin da ya sa mutane da yawa har ma da ni, suke kiran kansu Kiristoci, amma ba sa bin waɗannan ƙa’idodin.

Na kuɗiri niyyar kyautata halayena, don haka, sai na daina shan kwayoyi. Na soma tunani cewa dole ne akwai mutane da suke bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma ina so in haɗu da su. Na yi addu’a a karo na biyu, kuma a addu’ar na roƙi Allah ya taimaka mini in haɗu da su.

YADDA NA NEMI ADDINI NA GASKIYA

A ganina, ya dace in bincika addinai ɗaya bayan ɗaya don in san wanda yake da gaskiya. Da nake tafiya a titin Alicante, na ga wuraren ibada na addinai dabam-dabam. Amma da yake yawancinsu suna amfani da siffofi a ibadarsu, sai na gane cewa su ba addinan gaskiya ba ne.

Wata ranar Lahadi da rana, ina zaune a kan tudu ina kallon tashar jirgin ruwa kuma ina karanta Yakub 2:​1-5 inda aka yi gargaɗi game da nuna son kai ga masu kuɗi. Da nake komawa inda jirgin ruwanmu yake, sai na ga wani gini da ya yi kama da wurin ibada. A ƙofar ginin, an rubuta: “Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah.”

Sai na ce, ‘Bari in gwada mutanen nan, don in ga yadda za su marabce ni.’ Sai na shiga cikin Majami’ar Mulki ba takalmi da dogon gemu kuma wandona a yage. Ɗan atenda ya ba ni wurin zama kusa da wata tsohuwa wadda ta taimaka mini in ga wurare da mai jawabin yake ambatawa a Littafi Mai Tsarki. Bayan taron, na yi mamakin yadda suka nuna mini alheri. Wani daga cikinsu ya gayyace ni zuwa gidansa don mu tattauna, amma da yake ban gama karanta Littafi Mai Tsarki ba, sai na gaya masa cewa zan sanar da shi idan na shirya. Amma na ci gaba da halartan dukan taruka.

Bayan wasu makonni, na ziyarci mutumin a gidansa, kuma ya amsa tambayoyin da nake da su daga Littafi Mai Tsarki. Bayan mako ɗaya, sai ya ba ni jaka cike da riguna masu kyau. Ya gaya mini cewa mai kayan yana kurkuku domin yana bin ƙa’idar Littafi Mai Tsarki cewa ya ƙaunaci mutane, kuma kada ya yi yaƙi. (Isha. 2:4; Yoh. 13:​34, 35) Hakan ya tabbatar mini cewa na sami abin da nake nema, wato mutanen da suke bin dokokin Littafi Mai Tsarki game da ɗabi’a! Yanzu burina shi ne in daɗa fahimtar Littafi Mai Tsarki, ba in je wani tsibiri mai kyau ba. Don haka, sai na sake koma ƙasar Nedalan kuma.

NA JE NEMAN AIKI

Na yi kwana huɗu ina tafiya da kafa kafin na isa birnin Groningen a Nedalan. Na nemi aikin yi a wurin don in sami abin biyan bukata. Da na je wani shagon kafinta neman aiki, sai aka ba ni wani fom in cika. A fom ɗin an tambaye ni addinina. Sai na rubuta cewa “Ni Mashaidin Jehobah ne.” Da mai shagon ya karanta, sai na ga cewa fuskarsa ta canja. Sai ya ce mini, “Zan kira ka.” Amma bai yi hakan ba.

Sai na je wani shagon kafinta kuma na tambaye mai shagon ko zai so in taya shi aiki. Sai ya ce in nuna masa shaidar ayyuka da na taɓa yi da wadda ta nuna cewa na je makaranta. Na bayyana masa cewa na taɓa gyara jirgin ruwa na katako. Na yi mamaki da ya ce, “Za ka iya soma aiki da ranar nan, amma da sharaɗi. Sharaɗin shi ne ba na so ka tayar mini da masifa a shagona domin ni Mashaidin Jehobah ne kuma ina bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.” Na yi mamaki sosai, sai na ce masa, “Ni ma Mashaidin Jehobah ne!” Da ya lura cewa gashin kaina da gemuna suna da tsayi sosai, sai ya ce, “To zan yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai!” Na yi farin ciki kuma na amince da hakan. Yanzu na gane dalilin da ya sa mai shago na farko bai kira ni ba. Jehobah ne ya amsa addu’ata. (Zab. 37:4) Na yi aiki a shagon ɗan’uwan na shekara ɗaya, kuma a lokacin ya yi nazari da ni. Bayan haka na yi baftisma a watan Janairu na 1974.

A ƘARSHE, NA SAMI RAYUWA MAI MA’ANA!

Bayan wata ɗaya, sai na soma hidimar majagaba, kuma hakan ya sa ni farin ciki sosai. Wata ɗaya bayan hakan, sai na koma Amsterdam domin in taimaka ma wani rukuni na yaren Sifanisanci da aka kafa. Na yi farin cikin yin nazari da mutane a yaren Sifanisanci da kuma na Portuguese! A watan Mayu na 1975, na yi farin ciki da aka naɗa ni majagaba na musamman.

Wata rana, wata majagaba na musamman mai suna Ineke ta kawo ɗalibarta ’yar Bolibiya taronmu na Sifanisanci. Ni da Ineke mun soma tura wa juna wasiƙu, kuma ta hakan muka gano cewa muna da maƙasudi ɗaya. Mun yi aure a 1976, kuma muka ci gaba da yin hidima a matsayin majagaba na musamman har zuwa 1982 a lokacin da aka gayyace mu aji na 73 na makarantar Gilead. Mun yi farin ciki da kuma mamaki sosai sa’ad da aka tura mu gabashin Afirka, kuma muka yi hidima na shekara biyar a birnin Mombasa na ƙasar Kenya! A 1987, an tura mu ƙasar Tanzaniya inda bai jima da aka cire taƙunƙumi da aka saka wa aikinmu ba. Mun yi shekaru 26 a wurin, kafin muka sake komawa Kenya.

Taimaka wa mutane a gabashin Afirka su koyi gaskiya da ke Littafi Mai Tsarki ya sa ni da matata farin ciki

Koya wa mutane masu zuciyar kirki gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki, ya sa rayuwarmu ta kasance da ma’ana. Alal misali, ɗalibina na farko a Mombasa wani mutumi ne da na haɗu da shi sa’ad da muke wa’azi. Bayan na ba shi mujallu guda biyu, sai ya ce mini, “Idan na gama karanta su me zan yi?” Bayan mako ɗaya, sai muka soma nazarin littafin nan da shi Kana Iya Rayuwa Har Abada Cikin Aljanna a Duniya kuma bai jima da aka fitar da littafin a yaren Swahili ba. Ya yi baftisma bayan shekara ɗaya kuma ya soma hidimar majagaba na kullum. Tun daga lokacin, shi da matarsa sun taimaka wa kusan mutane ɗari su yi baftisma.

Ni da Ineke mun shaida yadda Jehobah yake taimaka wa bayinsa su yi rayuwa mai ma’ana

Da na koyi dalilin da ya sa Allah ya halicce mu, sai na ji kamar ɗan kasuwar nan da ya sami dutse mai daraja kuma ba ya so ya rabu da shi. (Mat. 13:​45, 46) Niyyata tun farko ita ce in yi amfani da rayuwata don in koya wa mutane dalilin da ya sa Allah ya halicce mu. Da ni da matata, mun shaida yadda Jehobah yake taimaka wa mutane su iya yin rayuwa mai ma’ana.