Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 44

Ka Yi Godiya don Kaunar Jehobah Marar Canjawa

Ka Yi Godiya don Kaunar Jehobah Marar Canjawa

“Ƙaunar [Jehobah] marar canjawa ta har abada ce!”​—ZAB. 136:1.

WAƘA TA 108 Ƙauna ta Gaskiya Daga Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne Jehobah yake so mu yi?

ƘAUNA marar canjawa hali ne da yake da muhimmanci sosai ga Jehobah. (Hos. 6:6) Yana so bayinsa su ɗauki wannan halin da muhimmanci su ma. Ta bakin annabinsa Mika, Jehobah ya umurce mu mu “ƙaunaci yin jin ƙai,” ko kuma ƙauna marar canjawa. (Mik. 6:8) Amma kafin mu iya nuna wannan halin, dole ne mu san abin da halin yake nufi.

2. Ya ake nuna ƙauna marar canjawa?

2 Me ake nufi da ƙauna marar canjawa? An yi amfani da furucin nan “ƙauna marar canjawa” wajen sau 230 a cikin New World Translation of the Holy Scriptures. Ya ake nuna wannan halin? Mai ƙauna marar canjawa zai ci gaba da ƙaunar mutum da kuma nuna masa aminci. Jehobah ne ya fi nuna wannan halin. A wannan talifin, za mu tattauna yadda Jehobah yake nuna wa ’yan Adam ƙauna marar canjawa. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda bayin Allah a yau za su iya bin misalinsa ta wajen nuna wa juna ƙauna marar canjawa.

JEHOBAH MAI YAWAN “ƘAUNA MARAR CANJAWA” NE

3. Mene ne Jehobah ya gaya wa Musa game da kansa?

3 Ba da daɗewa ba bayan Isra’ilawa suka bar Masar, Jehobah ya gaya wa Musa sunansa da kuma halayensa. Ya ce: “Ni ne Yahweh, ni ne Yahweh! Allah mai jinƙai ne, mai alheri, marar saurin fushi, mai yawan ƙauna marar canjawa, cike da aminci kuma, mai kiyaye ƙauna marar canjawa ga ’ya’ya har zuwa tsara ta dubu, mai gafarta laifi, da zunubin ganganci, da kowane irin zunubi.” (Fit. 34:​6, 7) Da waɗannan kalmomi masu daɗin ji, Jehobah ya bayyana wa Musa wani abu na musamman game da ƙaunarsa marar canjawa. Me ke nan?

4-5. (a) Yaya Jehobah ya kwatanta kansa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

4 Jehobah bai ce shi mai ƙauna marar canjawa ba ne kawai, amma ya ce shi mai “yawan ƙauna marar canjawa” ne. An sake ambata furucin sau da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki. (L. Ƙid. 14:18; Neh. 9:17; Zab. 86:15; 103:8; Yow. 2:13; Yona 4:2) A dukan wuraren nan, an yi maganar Jehobah ne, ba ’yan Adam ba. Ba abin mamaki ba ne cewa sau da yawa Jehobah ya bayyana kansa a matsayin mai wannan halin. Hakika ƙauna marar canjawa hali ne mai muhimmanci a gare shi. Shi ya sa Sarki Dauda ya ce: “Ya Yahweh, ƙaunarka marar canjawa ta kai har sammai. . . . Ina misalin darajar ƙaunarka marar canjawa! ’Yan Adam sukan sami wurin ɓuya a ƙarƙashin inuwar fikafikanka.” (Zab. 36:​5, 7) Kana godiya don wannan halin kamar yadda Dauda ya yi?

5 Bari mu tattauna tambayoyi biyu don mu daɗa fahimtar ma’anar ƙauna marar canjawa. Tambayoyin su ne: Su waye ne Jehobah yake nuna wa ƙauna marar canjawa? Ta yaya za mu amfana daga ƙaunar Jehobah marar canjawa?

SU WAYE NE JEHOBAH YAKE NUNA WA ƘAUNA MARAR CANJAWA?

6. Ga su waye ne Jehobah yake nuna ƙauna marar canjawa?

6 Su waye ne Jehobah yake nuna wa ƙauna marar canjawa? Ga ’yan Adam ne kaɗai za a iya nuna ƙauna marar canjawa. Amma ba ga kowa ne Jehobah yake nuna ƙauna marar canjawa ba. Yana nuna wannan halin ga waɗanda suke da dangantaka mai kyau da shi ne kawai. Allahnmu yana nuna ƙauna marar canjawa ga abokansa. Yana da nufi mai kyau a gare su kuma ba zai taɓa daina ƙaunar su ba.

Jehobah yana ba ’yan Adam abubuwa masu kyau da yawa da suke bukata, har da waɗanda ba sa bauta masa (Ka duba sakin layi na 7) *

7. Ta yaya Jehobah yake nuna wa dukan ’yan Adam ƙauna?

7 Jehobah yana nuna wa dukan ’yan Adam ƙauna. Yesu ya gaya ma wani mutum mai suna Nikodimus cewa: “Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.”​—Yoh. 3:​1, 16; Mat. 5:​44, 45.

Bisa ga abin da Sarki Dauda da kuma annabi Daniyel suka faɗa, Jehobah yana nuna ƙauna marar canjawa ga waɗanda suka san shi, da suke tsoronsa, suna ƙaunarsa kuma suna bin dokokinsa (Ka duba sakin layi na 8-9)

8-9. (a) Me ya sa Jehobah yake nuna ƙauna marar canjawa ga bayinsa? (b) Me za mu tattauna yanzu?

8 Kamar yadda muka gani ɗazu, Jehobah yana nuna ƙauna marar canjawa ga bayinsa ne kaɗai. Mun ga tabbacin hakan daga abin da Sarki Dauda da kuma annabi Daniyel suka faɗa. Alal misali, Dauda ya ce: ‘Ka ci gaba da nuna ƙaunarka ga masu saninka, ci gaba da adalcinka ga masu gaskiya a zuci.’ ‘Ƙauna marar canjawa ta Yahweh marar farko marar ƙarshe ce ga masu tsoronsa.’ Annabi Daniyel ya ce Jehobah yana nuna ‘ƙauna marar canjawa ga waɗanda suke ƙaunarsa suna kuma kiyaye umurnansa.’ (Zab. 36:10; 103:17; Dan. 9:4) Bisa ga abin da mutane biyun nan suka faɗa, Jehobah yana nuna wa bayinsa ƙauna marar canjawa domin sun san shi, suna tsoronsa, suna ƙaunarsa kuma suna bin dokokinsa. Jehobah yana nuna ƙauna marar canjawa ga waɗanda suke bauta masa a hanyar da ya kamata ne kawai.

9 Kafin mu fara bauta ma Jehobah, ya nuna mana irin ƙaunar da yake nuna wa ’yan Adam gaba ɗaya. (Zab. 104:14) Amma da muka soma ƙaunar sa, sai ya fara nuna mana ƙauna marar canjawa. Hakika, Jehobah ya tabbatar ma bayinsa cewa: “Ƙaunata marar canjawa ba za ta rabu da” ku ba. (Isha. 54:10) Kamar yadda Dauda da kansa ma ya shaida, Jehobah yana “zaɓa wa kansa masu hali irin nasa” don ya nuna musu ƙauna a hanya ta musamman. (Zab. 4:3) Me ya kamata mu yi don irin wannan ƙaunar da Jehobah yake nuna mana? Wani marubucin zabura ya ce: “Bari mai hikima, ya yi tunanin abubuwan nan, ya kuma kula da ƙauna marar canjawa ta Yahweh.” (Zab. 107:43) Wannan shawara mai kyau ta fito daga wurin Jehobah ne. Saboda haka, za mu tattauna hanyoyi guda uku da Jehobah yake nuna ƙauna marar canjawa, da kuma yadda muke amfana a duk lokacin da ya nuna mana ƙauna marar canjawa.

TA YAYA ZA MU AMFANA DAGA ƘAUNAR JEHOBAH MARAR CANJAWA?

Jehobah yana ba da ƙarin abubuwa masu kyau ga waɗanda suke bauta masa (Ka duba sakin layi na 10-16) *

10. Ta yaya sanin cewa ƙaunar Jehobah marar canjawa ta har abada ce yake taimaka mana? (Zabura 31:7)

10Ƙaunar Jehobah marar canjawa ba ta ƙarewa. An ambata irin wannan ƙaunar sau 26 a littafin Zabura ta 136. Aya ta farko ta ce: “Ku yi godiya ga Yahweh, gama shi mai alheri ne, ƙaunarsa marar canjawa ta har abada ce!” (Zab. 136:1) An maimaita furucin nan “ƙaunarsa marar canjawa ta har abada ce” daga aya 2 zuwa 26. Yayin da muke karanta wannan zaburar, za mu iya yin mamakin yadda Jehobah yake nuna ƙaunarsa marar canjawa a hanyoyi dabam-dabam babu fasawa. Furucin nan da aka yi cewa “ƙaunarsa marar canjawa ta har abada ce,” ya tabbatar mana cewa ƙaunar da Jehobah yake nuna wa mutanensa ba za ta canja ba. Sanin cewa Jehobah ba ya saurin daina ƙaunar bayinsa yana ƙarfafa mu! Idan Jehobah ya soma ƙaunar bawansa, ba ya barin shi musamman a lokacin da yake cikin wahala. Yadda muke amfana: Sanin cewa Jehobah ba zai bar mu ba yana sa mu farin ciki, kuma yana ba mu ƙarfin jimre matsaloli don mu ci gaba da bauta masa.​—Karanta Zabura 31:7.

11. Bisa ga abin da ke Zabura 86:​5, me yake sa Jehobah ya gafarta mana?

11Ƙaunar Jehobah marar canjawa tana sa shi ya gafarta mana. A duk lokacin da Jehobah ya ga cewa mai zunubi ya tuba kuma ya daina yin mugayen abubuwan da yake yi, ƙaunarsa marar canjawa tana sa shi ya gafarta wa mutumin. Ga abin da Dauda marubucin zabura ya ce: “Bai yi da mu bisa ga zunubanmu ba, bai kuwa sāka mana bisa ga laifofinmu ba.” (Zab. 103:​8-11) Dauda da kansa ya san yadda mutum yake baƙin ciki idan zuciyarsa tana damun sa saboda wani zunubin da ya yi. Amma ya gano cewa Jehobah yana a shirye ya yi “gafara.” Me yake sa Jehobah ya gafarta mana? Amsar tana Zabura 86:5. (Karanta.) Kamar yadda Dauda ya faɗa, Jehobah yana gafarta ma waɗanda suka nemi gafararsa.

12-13. Idan zuciyarmu tana damun mu don wani zunubi da muka yi a dā, me zai taimaka mana?

12 Idan mun yi zunubi, yana da kyau mu yi nadama don laifin da muka yi. Hakan zai sa mu tuba kuma mu ɗauki matakan gyara halinmu. Amma wasu bayin Allah sun bar zuciyarsu ta dame su sosai don zunubin da suka yi a dā. Zuciyarsu tana gaya musu cewa Jehobah ba zai taɓa gafarta musu ba ko da sun tuba. Idan haka kake ji, sanin yadda Jehobah yake nuna ƙauna marar canjawa zai taimaka maka.

13Yadda muke amfana: Duk da ajizancinmu, za mu iya bauta ma Jehobah da zuciya mai tsabta. Hakan yana yiwuwa ne domin “jinin Yesu Ɗansa . . . yana tsabtace mu daga dukan zunubi.” (1 Yoh. 1:7) Idan ajizancinka yana sa ka sanyin gwiwa, ka tuna cewa Jehobah yana a shirye ya gafarta maka idan ka tuba. Dauda ya bayyana alaƙar da ke tsakanin ƙauna marar canjawa da kuma gafarta wa mutane. Ya ce: “Kamar yadda yawan nisan sama yake daga ƙasa, haka yawan ƙaunarsa marar canjawa take ga masu tsoronsa. Kamar yadda gabas take nesa da yamma, haka ne ya sa zunuban gangancinmu sun yi nesa da mu.” (Zab. 103:​11, 12) Hakika, Jehobah yana a shirye ya gafarta wa mutane a yalwace.​—Isha. 55:7.

14. Yaya Dauda ya bayyana yadda ƙaunar Jehobah marar canjawa take kāre mu?

14Ƙaunar Allah marar canjawa tana kāre dangantakarmu da shi. A cikin addu’ar da Dauda ya yi, Dauda ya ce wa Jehobah: “Kai ne wurin ɓuyana, za ka kiyaye ni daga masifa. Kana sa masu murnar nasarata su rufe ni da muryar waƙoƙinsu. . . . Ƙauna marar canjawa za ta kewaye masu dogara ga Yahweh.” (Zab. 32:​7, 10) A zamanin dā, katanga tana kāre mutanen birni daga maƙiyansu. Ƙaunar Jehobah marar canjawa tana kama da wannan katangar domin tana kāre mu daga duk wani abu da zai ɓata dangantakarmu da shi. Ƙari ga haka, ƙaunar Jehobah marar canjawa tana sa ya kusace mu.​—Irm. 31:3.

15. Ta yaya ƙaunar Allah marar canjawa take kama da wurin ɓuya?

15 Dauda ya sake amfani da wani kwatanci dabam don ya bayyana irin kāriyar da mutanen Allah suke samuwa. Ya ce: “Kai ne wurin ɓuyana, ya Allah, kai ne Allahna wanda yake nuna mini ƙauna marar canjawa.” Ga abin da Dauda ya ƙara faɗa kuma game da Jehobah. Ya ce: “Shi ne ƙaunata da katangata, wurin ɓuyana da mai cetona, garkuwata inda nake ɓuya.” (Zab. 59:17; 144:2) Me ya sa Dauda ya kwatanta ƙauna marar canjawa da Jehobah yake nuna wa mutane da katanga da kuma wurin ɓuya? Ko da a ina ne muke zama a duniyar nan, Jehobah zai tanada mana abubuwan da za su taimaka mana mu kāre dangantakarmu mai kyau da shi. Zabura 91 ta ƙara tabbatar mana da hakan. Ayar ta ce: “Zan ce wa Yahweh, ‘Kai ne wurin ɓuyana da katangata.’ ” (Zab. 91:​1-3, 9, 14) Musa ma ya yi amfani da wani furuci makamancin wannan. (Zab. 90:1) Ƙari ga haka, a lokacin da Musa ya kusan mutuwa, ya sake yin amfani da wani kwatanci mai kyau. Ya ce: “Allah marar farko marar ƙarshe shi ne wurin zamanka. A ƙarƙashinka hannunsa yana riƙe ka.” (M. Sha. 33:27) Mene ne wannan furucin, “a ƙarƙashinka hannunsa yana riƙe ka” ya nuna mana game da Jehobah?

16. A waɗanne hanyoyi biyu ne Jehobah yake taimaka mana? (Zabura 136:23)

16 Idan muka yi imani cewa Jehobah zai kāre mu, hakan zai iya ƙarfafa mu. Amma a wasu lokuta, mukan yi sanyin gwiwa kuma mu kasa yin farin ciki duk da ƙoƙarinmu. A irin waɗannan lokutan, mene ne Jehobah zai yi mana? (Karanta Zabura 136:23.) Zai saka hannunsa a ƙarƙashinmu, ya ɗaga mu a hankali kuma ya taimaka mana mu daina sanyin gwiwa. (Zab. 28:9; 94:18) Yadda muke amfana: Mun san cewa za mu iya dogara ga Allah a kullum. Hakan yana taimaka mana a hanyoyi biyu. Na farko, ko da a ina ne muke zama, mun san cewa Jehobah zai kāre mu a kullum. Na biyu, Ubanmu na sama da yake ƙaunar mu ya damu da mu sosai.

MUN SAN ALLAH ZAI CI GABA DA NUNA MANA ƘAUNA MARAR CANJAWA

17. Wane tabbaci ne ƙaunar Allah marar canjawa take sa mu kasance da shi? (Zabura 33:​18-22)

17 Kamar yadda muka koya, a duk lokacin da muka fuskanci matsaloli, Jehobah zai taimaka mana mu kāre dangantakarmu da shi. (2 Kor. 4:​7-9) Annabi Irmiya ya ce: “Ƙaunarka marar canjawa ba ta ƙārewa, jinƙanka ba su da iyaka, ya Yahweh.” (Mak. 3:22) Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da nuna mana ƙauna marar canjawa domin Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “idanun Yahweh suna a kan masu tsoronsa a kan masu sa zuciya ga ƙaunarsa marar canjawa.”​—Karanta Zabura 33:​18-22.

18-19. (a) Mene ne ya kamata mu tuna? (b) Me za mu tattauna a talifi na gaba?

18 Me ya kamata mu tuna? Kafin mu fara bauta ma Jehobah, Jehobah ya nuna mana irin ƙaunar da yake nuna wa ’yan Adam gaba ɗaya. Amma da muka soma bauta masa, ya soma nuna mana ƙaunarsa marar canjawa. Saboda wannan ƙaunar ce Jehobah yake kāre mu. Zai ci gaba da kusantar mu kuma zai cika alkawuran da ya yi mana. Yana so mu zama abokansa har abada! (Zab. 46:​1, 2, 7) Don haka, ko da wace matsala ce muke fuskanta, Jehobah zai ba mu ƙarfin jimrewa don mu riƙe amincinmu.

19 Mun riga mun tattauna yadda Jehobah yake nuna ƙauna marar canjawa ga bayinsa. Yana so mu nuna ƙauna marar canjawa ga ’yan’uwanmu. Ta yaya za mu yi hakan? Talifi na gaba zai tattauna wannan batu mai muhimmanci.

WAƘA TA 136 Jehobah Zai Ba Ka “Cikakkiyar Lada”

^ sakin layi na 5 Me ake nufi da ƙauna marar canjawa? Su waye ne Jehobah yake nuna wa ƙauna marar canjawa kuma ta yaya suke amfana? Za a ba da amsoshin tambayoyin nan a cikin wannan talifin. Talifin shi ne na farko a cikin talifofi biyu da za su tattauna wannan halin.

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTUNA: Jehobah yana nuna ƙauna ga dukan ’yan Adam, har da bayinsa. Alamun da ke kan mutane da ke hotunan sun nuna yadda Jehobah yake nuna ƙauna. Abu mafi muhimmanci da ya yi mana shi ne, ya ba da Ɗansa Yesu Kristi don ya mutu a madadin mu.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTUNA: Jehobah yana nuna ƙauna marar canjawa a hanya ta musamman ga waɗanda suka zama bayinsa kuma suka ba da gaskiya ga hadayar Yesu. Ƙari ga ƙauna da Jehobah yake nuna wa ’yan Adam gaba ɗaya, Jehobah yana nuna ƙauna marar canjawa ga bayinsa kaɗai. An nuna yadda yake nuna irin wannan ƙaunar a cikin hotunan.