Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 50

Ku Kasa Kunne ga Makiyayi Mai Kyau

Ku Kasa Kunne ga Makiyayi Mai Kyau

“Za su kuwa saurari muryata.”​—YOH. 10:16.

WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane dalili ne wataƙila ya sa Yesu ya kwatanta mabiyansa da tumaki?

YESU ya nuna cewa dangantaka da ke tsakaninsa da mabiyansa tana kama da wadda ke tsakanin makiyayi da tumakinsa. (Yoh. 10:14) Ya dace da Yesu ya yi wannan kwatancin domin tumaki sun san muryar makiyayinsu, kuma suna bin shi. Akwai wani matafiyi da ya ga gaskiyar wannan maganar. Ya ce: “Mun so mu ɗauki hoton wasu tumaki, kuma mun so su zo kusa da mu, amma sun ƙi su zo kusa da mu da yake ba su san muryarmu ba. Sai wani ɗan ƙaramin yaro makiyayinsu ya zo. Kafin ma ya gama kiran su, sai suka soma binsa.”

2-3. (a) Ta yaya mabiyan Yesu za su nuna cewa suna jin muryarsa? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin da kuma na gaba?

2 Abin da wannan matafiyin ya shaida, ya tuna mana abin da Yesu ya faɗa game da mabiyansa, ya ce: “Za su kuwa saurari muryata.” (Yoh. 10:16) Amma Yesu yana sama. Ta yaya za mu iya saurararsa? Hanya mai muhimmanci da za mu iya yin hakan ita ce ta bin koyarwarsa.​—Mat. 7:​24, 25.

3 A wannan talifin da kuma na gaba, za mu tattauna wasu daga cikin koyarwar Yesu. Za mu ga cewa Yesu ya gaya mana mu daina yin wasu abubuwa, kuma ya ce mu yi wasu abubuwa. Da farko, za mu tattauna abubuwa biyu da Yesu ya ce mu daina yi.

KU DAINA DAMUWA

4. Bisa ga Luka 12:​29, me zai iya sa mu damu?

4 Karanta Luka 12:29. Yesu ya umurci mabiyansa cewa kada su damu game da abubuwan da suke bukata. Mun san cewa shawarar Yesu daidai ne kuma tana da amfani a kullum. Muna so mu bi shawarar a kullum, amma a wasu lokuta hakan zai iya yi mana wuya. Me ya sa?

5. Me zai iya sa wasu su damu game da abin biyan bukata?

 5 Wasu za su iya damuwa a kan yadda za su sami abinci, da kayan sakawa da kuma wurin kwana. Mai yiwuwa suna zama a ƙasar da akwai talauci sosai, don haka ba sa samun isasshen kuɗi da za su yi amfani da shi su kula da iyalinsu. Ko kuma wanda yake tanada wa iyalin ya rasu, don haka iyalin ba ta samun abin biyan bukata. Wasu kuma cutar korona ta sa sun rasa aikinsu. (M. Wa. 9:11) Idan muna fama da waɗannan matsalolin ko kuma wasu matsaloli dabam, ta yaya za mu bi umurnin Yesu cewa mu daina damuwa?

A maimakon mu bar matsalolinmu su sa mu nutse a cikin damuwa a alamance, muna bukatar mu daɗa dogara ga Jehobah (Ka duba sakin layi na 6-8) *

6. Ka bayyana wani abin da ya taɓa faruwa da Bitrus.

6 Akwai wani lokaci da manzo Bitrus da kuma wasu manzannin Yesu suke tafiya a cikin jirgin ruwa a Tekun Galili, sai aka soma iska mai ƙarfi, kuma suka ga Yesu yana tafiya a kan ruwa. Bitrus ya ce: “Ubangiji, idan kai ne, ka sa in zo wurinka a kan ruwan.” Sai Yesu ya ce masa, “Zo mana.” Bayan Yesu ya gaya masa cewa ya zo, “Bitrus ya fita daga jirgin, ya fara tafiya a kan ruwa zai je wurin Yesu.” Ka yi la’akari da abin da ya faru bayan hakan. “Da ya ga iskar ta yi ƙarfi, sai ya ji tsoro ya fara nutsewa. Sai ya yi ihu, ya ce, ‘Ubangiji, ka cece ni!’ ” Yesu ya miƙa hannunsa kuma ya ceto shi. Yana da muhimmanci mu tuna cewa Bitrus ya yi tafiya a kan ruwa sa’ad da ya mai da hankali a kan Yesu. Amma da ya kalli iskar, sai ya soma tsoro da shakka kuma ya soma nutsewa.​—Mat. 14:​24-31.

7. Me za mu iya koya daga abin da ya faru da Bitrus?

7 Za mu iya koyan darasi daga misalin Bitrus. Sa’ad da Bitrus ya sauka daga jirgin, bai yi tsammanin cewa zai ji tsoron iskar kuma ya soma nutsewa ba. Ya so ya ci gaba da tafiya a kan ruwan har sai ya kai wurin da Ubangijinsa yake. Amma maimakon ya mai da hankali a kan Yesu, sai ya soma mai da hankali a kan iskar. A yau, ba za mu iya yin tafiya a kan ruwa ba, amma muna fuskantar abubuwa da ke jarraba bangaskiyarmu. Idan muka daina mai da hankali ga Jehobah da kuma alkawuran da ya yi mana, hakan zai raunana bangaskiyarmu, kuma zai zama kamar muna nutsewa cikin damuwa ne. Don haka, ko da wace irin matsala ce muke fuskanta, mu riƙa tuna cewa Jehobah yana da ikon taimaka mana. Ta yaya za mu yi hakan?

8. Me zai taimaka mana kada mu mai da hankali sosai ga abubuwan da muke bukata?

8 Za mu amfana idan muka dogara ga Jehobah maimakon mu riƙa damuwa. Ka tuna cewa Ubanmu na sama ya tabbatar mana cewa zai tanadar mana da abubuwan da muke bukata idan muka saka Mulkinsa farko a rayuwarmu. (Mat. 6:​32, 33) Jehobah ba ya fasa cika wannan alkawarin. (M. Sha. 8:​4, 15, 16; Zab. 37:25) Tun da Jehobah yana yin tanadi ma tsuntsaye da kuma furanni, hakika ba ma bukatar mu damu game da abin da za mu ci da kuma abin da za mu saka! (Mat. 6:​26-30; Filib. 4:​6, 7) Kamar yadda ƙauna take sa iyaye su yi wa yaransu tanadin abinci da kuma kayan sakawa, haka ma Jehobah yana yi mana tanadi domin yana ƙaunar mu. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai kula da mu!

9. Me za ka iya koya daga abin da ya faru da wasu ma’aurata?

9 Ka yi la’akari da wani labari da ya nuna cewa Jehobah zai iya biyan bukatunmu. Wasu ma’aurata majagaba sun yi tafiya na fiye da awa ɗaya zuwa wani sansanin ’yan gudun hijira, domin su ɗauki wasu ’yan’uwa mata zuwa taro. Ɗan’uwan ya ce: “Bayan taro mun ce musu su zo gidanmu don mu ci abinci tare, amma sai muka tuna cewa ba mu da abinci a gida.” Mene ne waɗannan ma’auratan za su yi? Ɗan’uwan ya ci gaba da cewa: “Da muka isa gida, sai muka ga jakunkuna guda biyu cike da abinci a ƙofar gidanmu. Ba mu san wane ne ya ajiye mana abincin ba. Jehobah ya ba mu abin da muke bukata.” Bayan wani lokaci, motarsu ta lalace. Da motar suke wa’azi, kuma ba su da kuɗin gyara motar. Sun kai motar wurin mai gyara don su san ko nawa za su kashe a gyara motar. Sai wani mutum ya shigo kuma ya yi tambaya ya ce: “Motar wane ne wannan?” Ɗan’uwan ya ce motar tasa ce kuma tana bukatar gyara. Mutumin ya ce: “Ba damuwa. Matata tana son irin wannan motar, kuma irin kalar nan take so. Nawa za ka sayar mini da motar?” Sai mutumin ya sayi motar, kuma ya ba shi isasshen kuɗin da zai iya saya musu wata mota. Ɗan’uwan ya kammala da cewa: “Mun yi farin ciki sosai. Mun san cewa Jehobah ne ya sa hakan ya faru.”

10. Ta yaya Zabura 37:5 ta ƙarfafa mu kada mu riƙa damuwa a kan abubuwan da muke bukata?

10 Idan muka saurari makiyayinmu kuma muka daina damuwa a kan abubuwan biyan bukata, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai yi mana tanadi. (Karanta Zabura 37:5; 1 Bit. 5:7) Ka yi la’akari da yanayoyin da aka ambata a  sakin layi na 5. A ce wani a iyalinmu ne yake kula da mu, ko kuma da albashinmu ne muke kula da kanmu. Sai daga baya, wanda yake kula da mu ya kasa yin hakan, ko muka rasa aikinmu. Jehobah zai iya kula da mu ta wata hanya dabam. Za mu iya tabbata da hakan. A yanzu, bari mu tattauna wani abu da makiyayinmu ya ce mu daina yi.

“KADA KU YANKE WA KOWA HUKUNCI”

Za mu iya daina shari’anta mutane idan muna tunanin halayensu masu kyau (Ka duba sakin layi na 11, 14-16) *

11. Mene ne Yesu ya ce mu daina yi a Matiyu 7:​1, 2, kuma me ya sa hakan zai yi mana wuya a wasu lokuta?

11 Karanta Matiyu 7:​1, 2. Yesu ya san cewa ’yan Adam ajizai ne. Don haka, za su iya mai da hankali ga kurakuran juna. Shi ya sa ya ce: ‘Kada ku yanke wa kowa hukunci.’ Kome ƙoƙarin da muke yi don kada mu shari’anta ’yan’uwanmu, a wasu lokuta hakan yana yi mana wuya. Idan mun lura cewa mun soma mai da hankali a kan kurakuran wasu, me ya kamata mu yi? Mu saurari Yesu kuma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu daina shari’anta mutane.

12-13. Ta yaya yin tunani a kan yadda Jehobah ya ɗauki Dauda zai taimaka mana mu daina shari’anta mutane?

12 Yin tunani a kan yadda Allah yake mai da hankali a kan halaye masu kyau na mutane, zai taimaka mana sosai. Mun ga tabbacin hakan a abin da ya yi sa’ad da Dauda ya yi kuskure. Alal misali, Dauda ya yi zina da Batsheba, kuma ya sa aka kashe mijinta. (2 Sam. 11:​2-4, 14, 15, 24) Abin da Dauda ya yi ya jawo baƙin ciki ma shi da iyalinsa gabaki ɗaya. (2 Sam. 12:​10, 11) Akwai wani lokaci kuma da Dauda ya nuna cewa bai dogara ga Jehobah ba. Ya yi hakan ta wajen sa a ƙirga yawan sojojin Isra’ila. Abin da Jehobah bai umurce shi ya yi ba. Mai yiwuwa girman kai ne ya sa Dauda ya yi hakan, kuma ya dogara ga yawan sojojin da yake da su. Mene ne hakan ya jawo? Hakan ya sa Isra’ilawa 70,000 suka mutu daga cuta!​—2 Sam. 24:​2-4, 10-15.

13 A ce kana Isra’ila a lokacin, yaya za ka ɗauki Dauda? Da za ka ce bai kamata Jehobah ya yi masa jinƙai ba? Amma Jehobah ya yi masa jinƙai domin ya mai da hankali ga ayyuka masu kyau da Dauda ya yi, da kuma yadda Dauda ya tuba da gaske. Don haka, Jehobah ya gafarci Dauda duk da cewa Dauda ya yi zunubi mai tsanani. Jehobah ya san cewa Dauda yana ƙaunar sa sosai kuma yana so ya yi abin da yake da kyau a gabansa. Muna farin ciki cewa Jehobah ya fi mai da hankali ga halayenmu da kuma ayyukanmu masu kyau.​—1 Sar. 9:4; 1 Tar. 29:​10, 17.

14. Mene ne zai taimaka ma Kiristoci su daina shari’anta mutane?

14 Jehobah ba ya ɗaukan mu a matsayin kamiltattu, kuma bai kamata mu ɗauki ’yan’uwanmu a matsayin kamiltattu ba. Ya kamata mu san cewa za su iya yin kuskure. Yana da sauƙi mu mai da hankali a kan kurakuran wasu kuma mu soma sūkar su. Amma idan muna da dangantaka mai kyau da Jehobah, za mu ci gaba da ƙaunar ’yan’uwanmu ko da mun san kurakuransu. Lu’u lu’un da ba a sarrafa ba bai da kyaun gani, amma mutum mai hikima ya san cewa idan an sarrafa shi zai yi kyau sosai. Kamar yadda Jehobah da Yesu suke yi, ya dace mu mai da hankali ga halaye masu kyau na mutane, ba ga kasawarsu ba.

15. Ta yaya mai da hankali ga yanayin mutane zai taimaka mana kada mu shari’anta su?

15 Ban da mai da hankali ga halaye masu kyau na ’yan’uwanmu, me zai taimaka mana kada mu mai da hankali ga kurakuransu? Ka yi ƙoƙari ka sa kanka a yanayinsu. Ka yi la’akari da wannan misalin. Wata rana a cikin haikali, Yesu ya ga wata gwauruwa tana saka anini biyu a cikin akwatin gudummawa. Bai ce: “Me ya sa ba ta saka fiye da hakan ba?” A maimakon ya mai da hankali ga yawan kuɗin da ta saka, Yesu ya mai da hankali ga dalilin da ya sa ta yi hakan. Ya sa kansa a cikin yanayinta, kuma ya yaba mata domin ta ba da iya gwargwadon ƙarfinta.​—Luk. 21:​1-4.

16. Me za ka iya koya daga labarin Veronica?

16 Labarin Veronica ya koya mana cewa yana da muhimmanci mu riƙa saka kanmu a yanayin wasu. A ikilisiyar da ta taɓa yin hidima, akwai wata mahaifiya da ɗanta. Veronica ta ce: “A ganina ba sa zuwa taro da kuma wa’azi yadda ya kamata. Hakan ya sa na soma kallon su wani iri. Amma da na je wa’azi tare da ’yar’uwar, ta bayyana mini matsalolin da take fuskanta domin ɗanta yana fama da wani irin rashin lafiya. Tana yin iya ƙoƙarinta ta taimaka wa kanta da kuma ɗanta don su kusaci Jehobah kuma su sami abin biyan bukata. A wasu lokuta, rashin lafiyar ɗanta yana sa ta halarci taro a wata ikilisiya dabam.” Veronica ta kammala da cewa: “Ban taɓa sanin cewa tana fama da matsaloli kamar haka ba. A yanzu, ina ƙaunar ’yar’uwar da kuma daraja ta domin yadda take yin iya ƙoƙarinta a bautar Jehobah.”

17. Mene ne Yakub 2:8 ta umurce mu mu yi, kuma ta yaya za mu iya yin hakan?

17 Me za mu yi idan muka lura cewa mun shari’anta wani ɗan’uwanmu? Zai dace mu tuna cewa hakkinmu ne mu ƙaunaci ’yan’uwanmu. (Karanta Yakub 2:8.) Ƙari ga haka, zai dace mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu daina shari’anta mutane. Za mu iya yin abubuwan da suka jitu da addu’o’inmu ta wajen yin cuɗanya da mutumin da muka shari’anta. Hakan zai taimaka mana mu fahimci yanayinsa da kyau. Za mu iya gaya masa ya bi mu zuwa wa’azi, ko kuma ya zo gidanmu don mu ci abinci tare. Yayin da muke ƙara fahimtar yanayin ɗan’uwanmu da kyau, za mu iya yin koyi da Jehobah da Yesu ta wajen mai da hankali ga halaye masu kyau na ɗan’uwanmu. Ta yin hakan, za mu nuna cewa muna bin umurnin da makiyayinmu ya ba mu cewa mu daina shari’anta mutane.

18. Ta yaya za mu nuna cewa muna saurarar muryar makiyayinmu?

18 Kamar yadda tumaki suke jin muryar makiyayinsu, haka ma mabiyan Yesu suna jin muryarsa. Idan mun yi iya ƙoƙarinmu don mu daina yawan damuwa a kan abubuwan da muke bukata, kuma muka daina shari’anta mutane, Jehobah da Yesu za su albarkace mu don ƙoƙarinmu. Ko da muna cikin ‘ƙaramin garke’ ko kuma “waɗansu tumaki,” bari dukanmu mu ci gaba da saurarar muryar makiyayinmu kuma mu yi abin da ya faɗa. (Luk. 12:32; Yoh. 10:​11, 14, 16) A talifi na gaba, za mu tattauna abubuwa biyu da Yesu ya gaya wa almajiransa su yi.

WAƘA TA 101 Mu Riƙa Hidima da Haɗin Kai

^ sakin layi na 5 Sa’ad da Yesu ya ce tumakinsa za su ji muryarsa, yana nufin cewa almajiransa za su ji koyarwarsa kuma su aikata abin da suka ji. A wannan talifin, za mu tattauna koyarwar Yesu guda biyu masu muhimmanci. Wato mu daina damuwa game da abubuwan biyan bukata, kuma mu daina shari’anta mutane. Za mu tattauna yadda za mu bi waɗannan gargaɗin.

^ sakin layi na 51 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa ya rasa aikinsa, ba shi da isasshen kuɗin da zai kula da iyalinsa kuma suna bukatar wurin kwana. Idan bai yi hattara ba, zai iya damuwa ainun kuma hakan zai shafi bautarsa ga Jehobah.

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa ya zo taro a makare. Amma yana nuna halaye masu kyau ta wajen yin wa’azi sa’ad da yake yin ayyukansa na yau da kullum, da taimaka ma wata tsohuwa, da kuma tsabtace Majami’ar Mulki.