Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 9

Ka Bi Misalin Yesu ta Wajen Taimaka wa Mutane

Ka Bi Misalin Yesu ta Wajen Taimaka wa Mutane

“Ya fi albarka a bayar da a karɓa.”​—A. M. 20:35.

WAƘA TA 17 “Na Yarda”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane hali mai kyau ne bayin Jehobah suke nunawa?

 TUN DA daɗewa kafin zamaninmu, Littafi Mai Tsarki ya yi annabci cewa “da yardar rai, mutanen [Allah] za su miƙa kansu” a hidimarsa, a ƙarƙashin ja-gorancin Ɗansa. (Zab. 110:3) Muna ganin cikar wannan annabcin a yau. A kowace shekara, bayin Jehobah suna amfani da miliyoyin awoyi wajen yin wa’azi. Ba a biyan su don wannan aikin kuma suna yin hakan da yardar ransu. Ƙari ga haka, suna taimaka wa ’yan’uwansu su daɗa kasancewa da bangaskiya, suna ba su abin da suke bukata kuma suna ƙarfafa su. Dattawa da bayi masu hidima suna amfani da lokacinsu wajen shirya jawabai a taro da kuma kai ziyarar ƙarfafawa ga ’yan’uwansu. Me yake sa su yin waɗannan abubuwan? Ƙauna ce. Suna ƙaunar Jehobah da kuma maƙwabtansu.​—Mat. 22:37-39.

2. Wane misali ne Yesu ya kafa mana kamar yadda aka faɗa a Romawa 15:1-3?

2 Yesu ya nuna cewa ya fi damuwa da mutane maimakon kansa. Muna yin iya ƙoƙarinmu mu bi misalin Yesu. (Karanta Romawa 15:1-3.) Yin hakan zai sa mu sami sakamako mai kyau. Yesu ya ce: “Ya fi albarka a bayar da a karɓa.”​—A. M. 20:35.

3. Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 A wannan talifin, za mu tattauna wasu abubuwan da Yesu ya yi don ya taimaka wa mutane kuma za mu ga yadda za mu iya bin misalinsa. Za mu kuma tattauna yadda za mu daɗa kasancewa da halin sadaukarwa.

KU BI MISALIN YESU

Duk da cewa Yesu ya gaji, mene ne ya yi sa’ad da jama’a suka zo wurinsa? (Ka duba sakin layi na 4)

4. Mene ne Yesu ya yi don ya nuna cewa ya fi damuwa da mutane maimakon kansa?

4 Yesu ya taimaka wa mutane har ma a lokacin da ya gaji. Ka yi tunanin abin da Yesu ya yi a lokacin da taron jama’a suka je suka same shi a kan tudu, mai yiwuwa kusa da Kafarnahum. Kafin su zo, Yesu ya yi ta addu’a duk daren. Amma da ya ga jama’ar, sai ya tausaya wa masu ciwo da kuma talakawa da ke tsakaninsu. Ba warkar da su kawai ya yi ba, amma ya ba da jawabi mafi ban ƙarfafa da ake kira Huɗubar Yesu a kan Dutse.​—Luk. 6:12-20.

A waɗanne hanyoyi ne za mu iya bin misalin Yesu na sadaukarwa? (Ka duba sakin layi na 5)

5. A wace hanya ce magidanta suke bin misalin Yesu na sadaukar da kai har a lokacin da suka gaji?

5 Yadda magidanta suke bin misalin Yesu. Ku yi la’akari da wannan yanayin: A ce da yamma, wani maigida ya dawo gida a gajiye. Mai yiwuwa saboda gajiyar, ya so ya fasa Ibada ta Iyali da yamman. Amma ya roƙi Jehobah ya ba shi ƙarfin gudanar da ibada ta iyalin tare da iyalinsa. Jehobah ya taimaka masa kuma magidancin ya yi nazari da iyalinsa kamar yadda ya saba yi kowane mako. Hakan ya koya wa yaran darasi mai muhimmanci cewa ayyukan ibada ne suka fi muhimmanci ga iyayensu.

6. Ka ba da misalin yadda Yesu ya sadaukar da lokacinsa don ya taimaka wa mutane.

6 Yesu ya saurari mutane har ma a lokacin da ya so ya kasance shi kaɗai. Yaya kuke ganin Yesu ya ji sa’ad da ya ji labari cewa an kashe abokinsa Yohanna Mai Baftisma? Babu shakka ya yi baƙin ciki sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da Yesu ya ji [mutuwar Yohanna], sai ya tashi ya shiga jirgin ruwa ya haye zuwa wani wuri inda ba kowa domin ya kasance shi kaɗai.” (Mat. 14:10-13) Mun fahimci dalilin da ya sa ya so ya kasance shi kaɗai. Yawancin mu mukan so mu yi makoki mu kaɗai. Amma ba a bar Yesu ya yi hakan ba. Tun ma kafin ya kai inda yake so ya je, taron jama’a sun riga sun isa wurin. Mene ne Yesu ya yi da ya gan su? Ya yi tunanin yanayin jama’ar kuma “ya . . . ji tausayinsu.” Yesu ya gane cewa suna bukatar taimako da kuma ƙarfafa daga wurin Allah, shi ya sa “ya fara koya musu abubuwa da yawa,” ba abubuwa kaɗan ba.​—Mar. 6:31-34; Luk. 9:10, 11.

7-8. Ka ba da misalin yadda dattawa masu ƙauna suke bin misalin Yesu a duk lokacin da akwai bukata.

7 Yadda dattawa masu ƙauna suke bin misalin Yesu. Muna godiya don yadda dattawa suke sadaukar da kansu don su taimaka mana. A yawancin lokuta, ba dukan ’yan’uwa a ikilisiya ba ne suke ganin ayyukan da dattawa suke yi. Alal misali, idan wani ɗan’uwa ya yi rashin lafiya, membobin Kwamitin Hulɗa da Asibitoci sukan je su taimaka masa nan da nan. A yawancin lokuta, da dare ne ake bukatar taimakonsu a cikin gaggawa! Duk da haka, saboda tausayi waɗannan dattawan tare da iyalansu suna sadaukarwa don su taimaka wa ’yan’uwansu da suke da bukata.

8 Dattawa ma suna ba da kai wajen gina Majami’un Mulki da wasu wuraren ibada har ma suna taimakawa da ba da agaji. Kuma suna amfani da lokaci da yawa wajen koyarwa da kuma ƙarfafa mu a ikilisiyoyi. Ya kamata mu yaba wa ’yan’uwan nan da iyalansu. Bari Jehobah ya yi musu albarka don sadaukarwa da suke yi! Amma zai dace dattawa su yi amfani da sanin yakamata. Kada su mai da hankali ga kula da ikilisiya har su rasa lokacin kula da iyalansu.

YADDA ZA KU IYA KOYAN HALIN SADAUKARWA

9. Bisa ga abin da ke Filibiyawa 2:4, 5, wane hali ne ya kamata dukan Kiristoci su kasance da shi?

9 Karanta Filibiyawa 2:4, 5. Ko da yake ba dukanmu ne dattawa ba, ya kamata dukan mu mu kasance da halin sadaukarwa kamar yadda Yesu ya yi. Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu “ya ɗauki matsayin bawa.” (Filib. 2:7) Ka yi tunanin abin da furucin yake nufi. Bawa mai kyau zai nemi hanyoyin faranta ran maigidansa. Da yake mu bayin Jehobah ne kuma muna yin hidima wa ’yan’uwanmu, babu shakka muna yin iya ƙoƙarinmu mu bar Jehobah da kuma ’yan’uwanmu su yi amfani da mu. Shawarwarin da ke gaba za su iya taimaka mana mu yi hakan.

10. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu?

10 Ka yi tunanin irin halin da kake da shi. Ka yi wa kanka tambayoyi kamar haka: ‘Ina a shirye don in yi amfani da lokacina da ƙarfina don in taimaka wa ’yan’uwana? Me zan yi idan aka ce in riƙa zuwa in ziyarce wani ɗan’uwan da ba ya iya barin gidansa, ko kuma in riƙa kai wata ’yar’uwa tsohuwa zuwa taro? Ina shirye in taimaka da share wurin da za a yi babban taro ko Majami’ar Mulki?’ A lokacin da muka yi alkawarin bauta wa Jehobah, mun ce za mu ba shi kome da muke da shi don mu yi masa hidima. Don haka, yana so mu yi amfani da ƙarfinmu da lokacinmu da kuma dukiyarmu wajen taimaka wa mutane. Kuma a duk lokacin da ya ga muna hakan, yana farin ciki sosai. Idan muka ga cewa muna bukatar mu yi gyara a halinmu, me za mu yi?

11. Ta yaya addu’a za ta taimaka mana mu kasance a shirye mu taimaka ma ’yan’uwanmu?

11 Ka yi addu’a ga Jehobah da dukan zuciyarka. Mai yiwuwa ka gane cewa kana bukatar ka daɗa kasancewa da halin sadaukarwa, amma ba ka jin yin hakan. Me za ka yi idan haka kake ji? Ka yi addu’a ga Jehobah da dukan zuciyarka. Ka gaya wa Jehobah gaskiyar yadda kake ji kuma ka roƙe shi ya taimaka maka ka kasance da niyya da kuma ƙarfin yin canje-canje.​—Filib. 2:13.

12. A wace hanya ce ’yan’uwa maza matasa za su iya taimakawa a ikilisiyarsu?

12 Idan kai matashi ne da ya yi baftisma, ka roƙe Jehobah ya taimaka maka ka kasance da niyyar taimaka wa ’yan’uwanka a ikilisiya. A wasu ƙasashe, dattawa sun fi bayi masu hidima yawa. Kuma yawancin bayi masu hidimar nan ba yara ba ne. Yayin da ƙungiyar Jehobah take daɗa girma, muna bukatar ƙarin dattawa da za su kula da ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Idan kana shirye ka taimaka wa ’yan’uwa a duk lokacin da akwai bukata, za ka yi farin ciki. Me ya sa? Domin za ka faranta ran Jehobah, ’yan’uwa za su ga cewa kana shirye ka taimaka musu kuma za ka kasance da kwanciyar hankali domin ka san cewa kana taimaka wa ’yan’uwa.

Kiristoci daga Yahudiya suna haye Kogin Urdun zuwa birnin Pella. Waɗanda suka riga suka isa wurin suna raba wa Kiristocin da suka zo daga baya abinci (Ka duba sakin layi na 13)

13-14. Me za mu iya yi don mu taimaka wa ’yan’uwanmu? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

13 Ku yi lura don ku san lokacin da wani yake da bukata. Manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci da suke zama a Yahudiya cewa: “Kada ku daina yin alheri da zumuntar tarayya ta abin da kuke da shi, gama irin waɗannan hadayu suke faranta wa Allah rai.” (Ibran. 13:16) Wannan shawara ce mai kyau domin ba da daɗewa ba bayan aka tura musu wannan wasiƙar, Kiristocin sun bukaci su bar gidajensu da kasuwancinsu da iyalansu da ba Kiristoci ba kuma “su gudu zuwa cikin duwatsu.” (Mat. 24:16) Babu shakka a lokacin ya kasance da muhimmanci su taimaka wa juna. A ce sun ƙi bin shawarar Bulus kafin lokacin guduwar nan, da zai yi musu wuya su lallaɓa da ’yan abubuwa da suka samu a sabon gidansu.

14 Ba a kowane lokaci ba ne ’yan’uwanmu za su gaya mana abin da suke bukata. Alal misali, matar wani ɗan’uwa za ta iya rasuwa ta bar shi. Idan hakan ya faru, ɗan’uwanmu zai bukaci a taimaka masa da dahuwa, ko wasu ayyukan gida ko a taimaka masa idan yana so ya je wani wuri. Mai yiwuwa ba zai gaya mana kome ba domin ba ya so ya taƙura mana. Amma zai yi farin ciki sosai idan muka taimaka masa tun kafin ya tambaye mu. Kada mu ɗauka cewa wani zai taimaka masa ko mu ga kamar ɗan’uwanmu zai gaya mana abin da yake bukata a duk lokacin da yake da bukata. Ka tambayi kanka, ‘Da a ce ni ne ke wannan yanayin, yaya zan so a taimaka mini?’

15. Me ya zama dole mu yi idan muna so mu taimaka wa mutane?

15 Ka sa ya yi wa mutane sauƙi su nemi taimako daga wurinka. Babu shakka akwai ’yan’uwa a ikilisiyarmu da suke a shirye su taimaka wa mutane a kowane lokaci. Ba sa sa mu ji kamar muna damun su. Mun san cewa suna shirye su taimaka mana a duk lokacin da muke da bukata kuma za mu so mu zama kamar su. Wani dattijo mai suna Alan da yake da shekaru 45 ya ce yana so ya zama irin mutumin da zai sa ya yi wa ’yan’uwa sauƙi su nemi taimakon sa. Ga abin da Alan ya faɗa game da misalin da Yesu ya kafa, ya ce: “Yesu mutum ne mai ayyuka da yawa. Duk da haka, yara da manya ba su yi shakkar zuwa wurinsa don neman taimako ba. Sun san cewa ya damu da su sosai. Ina so in bi misalin Yesu da dukan zuciyata don mutane su ɗauke ni a matsayin wanda ya damu da su, mai ƙauna da kuma mai saurin taimaka wa mutane.”

16. Ta yaya bin abin da ke Zabura 119:59, 60 zai taimaka mana mu bi misalin Yesu sau da ƙafa?

16 Kada mu yi sanyin gwiwa idan muka yi kuskure yayin da muke ƙoƙarin bin misalin Yesu. (Yak. 3:2) Ɗalibin da yake koyon yin zane ba zai iya yin zane daidai yadda malaminsa yake yi ba. Amma yayin da yake koya daga kurakurensa kuma yana ƙoƙarin bin malaminsa sau da ƙafa, zai ci gaba da samun ƙwarewa. Haka ma idan muna yin abin da muke koya daga nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma muna yin iya ƙoƙarinmu don mu gyara halinmu, za mu yi nasara wajen bin misalin da Yesu ya bar mana.​—Karanta Zabura 119:59, 60.

AMFANIN YIN SADAUKARWA

Idan dattawa suna bin misalin Yesu na sadaukarwa, za su kafa wa matasa misali mai kyau (Ka duba sakin layi na 17) *

17-18. Yayin da muke bin misalin Yesu na sadaukarwa, wane amfani ne za mu samu?

17 Idan muna taimaka wa mutane, mutane za su yi koyi da mu. Wani dattijo mai suna Tim ya ce: “An naɗa wasu ’yan’uwa matasa bayi masu hidima. Wani dalilin da ya sa aka naɗa su shi ne sun ga yadda ’yan’uwa suke taimaka ma wasu, kuma hakan ya sa su ma suka yi koyi da ’yan’uwan. Waɗannan ’yan’uwan suna taimaka wa dattawa da kuma ’yan’uwansu a cikin ikilisiya.”

18 Yawancin mutane a yau suna nuna halin son kai sosai. Amma ba haka yake da bayin Jehobah ba. Mun koyi yadda Yesu ya nuna halin sadaukarwa kuma mun ƙudura cewa za mu bi misalinsa. Hakika ba za mu iya bin misalin Yesu daidai ba tare da yin kuskure ba. Duk da haka, za mu iya bin misalinsa “sau da ƙafa.” (1 Bit. 2:21, New World Translation) Yayin da muke iya ƙoƙarinmu mu bi misalin Yesu, mu ma za mu yi farin ciki domin muna faranta wa Jehobah rai.

SONG 13 Christ, Our Model

^ sakin layi na 5 A kowane lokaci, Yesu yana damuwa da mutane. A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyin da za mu iya bin misalinsa. Ƙari ga haka, za mu koyi yadda za mu amfana daga bin misalinsa na sadaukarwa.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa matashi mai suna Dan, ya ga yadda dattawa biyu suka kawo wa babansa ziyara a asibiti. Ƙaunar da dattawan suka nuna wa baban Dan ya sa Dan ya nemi hanyoyin taimaka ma ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Wani ɗan’uwa matashi mai suna Ben kuma ya ga yadda Dan yake kula da ’yan’uwa a ikilisiya. Misalin Dan ya sa Ben ya soma taimakawa ta wajen yin shara a Majami’ar Mulki.