Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Na Sami Abin da Ya Fi Aikin Likita Daraja

Na Sami Abin da Ya Fi Aikin Likita Daraja

“ABIN da kuke gaya mini shi ne abin da na yi ta sa rai a kai tun ina ƙarami.” Da farin ciki, na furta waɗannan kalmomin ga wasu ma’aurata da suka zo yin jinya a asibitina a 1971. A lokacin, ban daɗe da buɗe asibitina ba jim kaɗan bayan na zama ƙwararren likita. Su wane ne ma’auratan kuma mene ne na yi ta marmarin sa tun ina ƙarami? Bari in gaya muku yadda wannan tattaunawar ta canja yadda nake tunani, da kuma dalilin da ya sa na tabbata cewa abin da na sa rai a kai tun ina ƙarami ya kusan faruwa.

An haife ni a 1941 a birnin Paris a ƙasar Faransa, kuma iyalinmu ba su da kuɗi sosai. Ni mai son koyan abubuwa ne sosai, amma sa’ad da na kai shekara 10, na kamu da tarin fuka kuma hakan ya sa na daina zuwa makaranta. Likitoci sun shawarce ni in zauna a gida don kar in gajiyar da huhuna. Don haka, na yi watanni ina karanta kamus a gida da kuma saurarar shirin da Jami’ar Paris take yi a gidan rediyon Sorbonne. Na yi farin ciki sosai sa’ad da likitocina suka ce na warke kuma zan iya zuwa makaranta. Na gaya wa kaina cewa aikin da likitoci suke yi yana da muhimmanci sosai! Tun daga lokacin, na soma marmarin warkar da mutane. A duk lokacin da babana ya tambaye ni abin da nake so in yi a rayuwata, amsa ɗaya nake ba shi cewa, “Ina so in zama likita.” Yadda zama likita ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwata ke nan.

KIMIYYA TA SA NA KUSACI ALLAH

Iyalinmu ’yan Katolika ne amma ban san Allah sosai ba kuma akwai tambayoyi da yawa da na so in sami amsoshinsu. Sai da na soma nazarin kiwon lafiya a makarantar jami’a ne na tabbata cewa akwai mahalicci.

Na tuna lokaci na farko da na yi amfani da madubin ƙara girma na kalli ƙwayoyin halittun shuke-shuke. Na yi mamaki sosai da na ga yadda ƙwayoyin suke kāre kansu daga zafi da kuma sanyi. Na kuma lura da wani abu da ke cikin ƙwayoyin da ake kira cytoplasm kuma na ga yadda suke shanyewa idan aka sa musu gishiri, sa’an nan su ƙara girma idan aka sa musu ruwa. Hakan ne yake sa ƙananan halittu su iya sabawa da yanayoyi dabam-dabam. Da na yi la’akari da yadda ƙwayoyin halittu suke da ban mamaki, sai na gaskata cewa akwai mahalicci.

A shekara ta biyu da nake nazarin kiwon lafiya, na ga ƙarin hujjojin da suka nuna mini cewa akwai Allah. Da muke koya game da jikin ɗan Adam, mun koyi yadda kashin hannunmu yake taimaka mana mu iya lanƙwasa da kuma miƙe yatsunmu. Yadda tsokar jikinmu ta manne wa ƙashi kuma suke aiki tare da juna yana da ban mamaki sosai. Alal misali, mun koyi cewa akwai wata jijiya da ta haɗa ɗaya daga cikin tsokar hannunmu da ƙasusuwa biyu na yatsunmu. Wannan jijiyar takan rabu gida biyu. Yayin da ta kai gaɓar farko na yatsar, ɗaya za ta tsaya a kan gaɓar, ɗayan jijiyar kuma za ta wuce zuwa ƙarshen yatsar. Tsokar tana sa jijiyoyin su zauna kusa da ƙasusuwan yatsunmu. Da ba haka aka yi yatsunmu ba, da jijiyoyin yatsunmu ba za su iya lanƙwashewa ba. Hakan ya nuna min cewa Wanda ya tsara jikin ’yan Adam yana da hikima sosai.

Ƙari ga haka, da na soma nazarin yadda jariri yake numfashi bayan an haife shi, sai na ƙara ganin hikimar Wanda ya tsara jikin ’yan Adam. Na koyi cewa sa’ad da jariri yake ciki, ba ya bukatar ya yi numfashi domin yana samun iska daga wurin mamarsa. Shi ya sa babu iska a cikin jakar iska da ke huhunsa. Amma makonni kaɗan kafin a haife jaririn, kitse zai taru a cikin jakar iskar da ke cikin huhunsa. Sa’an nan bayan an haife jaririn kuma ya shaƙi numfashinsa na farko, wani abin mamaki yakan faru. Wani rami a zuciyar jaririn zai rufu, kuma hakan zai sa jini ya soma zuwa huhunsa. Saboda kitsen da ke cikin jakar iskar, iska za ta iya shiga huhun. Nan take, sai jaririn ya soma numfashi da kansa.

Na so in san Wanda ya halicci abubuwan nan. Don haka, sai na soma nazarin Littafi Mai Tsarki sosai. Na yi mamakin dokokin da Jehobah ya ba Isra’ilawa game da tsabta da kuma kiwon lafiya fiye da shekaru 3,000 da suka wuce. Allah ya umurce Isra’ilawa cewa idan za su yi bayan gida, su tona rami kuma su rufe shi bayan sun gama, su riƙa yin wanka kullum kuma su wāre duk wani mai cuta da yake yaɗuwa. (L. Fir. 13:50; 15:11; M. Sha. 23:13) Littafi Mai Tsarki ya bayyana waɗannan abubuwan, amma shekaru 150 da suka wuce ne kawai ’yan kimiyya suka gano yadda cututtuka suke yaɗuwa. Ƙari ga haka, dokokin da Jehobah ya ba Isra’ilawa game da jima’i da ke cikin Littafin Firistoci sun taimaka wajen kāre lafiyar al’ummar. (L. Fir. 12:1-6; 15:16-24) A ƙarshe na gano cewa Mahalicci ya ba Isra’ilawa dokokin nan domin amfanin su ne, kuma ya albarkace waɗanda suka yi biyayya ga dokokin. Hakan ya tabbatar mini cewa Allah ne mawallafin Littafi Mai Tsarki ko da yake ban san sunansa a lokacin ba.

YADDA NA HAƊU DA WADDA NA AURA KUMA NA SAN JEHOBAH

Ni da Lydie a ranar aurenmu, 3 ga Afrilu, 1965

Sa’ad da nake karatu in zama likita, na haɗu da wata budurwa mai suna Lydie kuma muka soma soyayya. Mun yi aure a 1965. A lokacin, na riga na yi rabin shekarun da ya kamata in yi a makaranta. Kafin 1971, mun riga mun haifi yara uku daga cikin yara shida da muke da su. Lydie ta goya mini baya sosai a aikina da kuma a iyalinmu.

Na yi shekaru uku ina aiki a asibitin gwamnati kafin in buɗe nawa asibitin. Ba da daɗewa ba bayan hakan, sai ma’auratan da na ambata ɗazu suka zo jinya a asibitina. Da nake so in rubuta musu magungunan da za su saya, sai matar ta ce mini: “Likita, don Allah kada ka rubuta maganin da aka yi da jini.” Na yi mamaki kuma na ce mata: “Me ya sa?” Sai ta ce: “Mu Shaidun Jehobah ne.” A lokacin, ban taɓa ji game da Shaidun Jehobah ba, ko abin da suke koyarwa game da jini. Matar ta fitar da Littafi Mai Tsarki kuma ta nuna mini dalilin da ya sa ba sa karɓan jini. (A. M. 15:28, 29) Bayan haka, sai ita da maigidanta suka nuna mini abubuwan da Mulkin Allah zai yi. Zai kawo ƙarshen wahala, ciwo da kuma mutuwa. (R. Yar. 21:3, 4) Sai na ce musu: “Abin da kuke gaya mini shi ne abin da na yi ta sa rai a kai tun ina ƙarami. Dalilin da ya sa na zama likita shi ne in kawo wa mutane sauƙi.” Na ji daɗin tattaunawar har muka yi awa ɗaya da rabi muna yin hakan. Bayan da ma’auratan suka tafi, sai na so in fita sha’anin ɗarikar Katolika nan da nan. Na kuma koya cewa sunan Mahalicci da nake ƙauna sosai shi ne Jehobah!

Na haɗu da ma’auratan sau uku a asibitina kuma sau ukun, mun tattauna har na fiye da awa ɗaya. Na gayyace su zuwa gidana don mu iya tattauna Littafi Mai Tsarki da kyau. Ko da yake Lydie ta yarda a yi nazari da ita, a lokacin ba ta yarda cewa wasu koyarwar Katolika ba daidai ba ne. Don haka, na gayyace wani fāda zuwa gidanmu. Mun yi muhawwara sosai a kan koyarwar coci, har cikin dare kuma mun yi amfani da Littafi Mai Tsarki kaɗai. Muhawwarar ce ta tabbatar wa Lydie cewa abubuwan da Shaidun Jehobah suke koyarwa gaskiya ne. Bayan haka, mun ci gaba da kusantar Jehobah har muka yi baftisma a 1974.

NA SA YIN NUFIN JEHOBAH FARKO A RAYUWATA

Da na koyi abin da Allah yake so ya yi wa ’yan Adam, sai na canja abin da ya fi muhimmanci a rayuwata. Bauta wa Jehobah ta zama abin da ya fi muhimmanci a rayuwata da Lydie. Mun ƙudura cewa za mu rene yaranmu bisa ga ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Mun koya wa yaranmu su ƙaunaci Jehobah da kuma mutane, kuma hakan ya sa iyalinmu ta kasance da haɗin kai.​—Mat. 22:37-39.

Ni da Lydie mukan yi farin ciki a duk lokacin da muka tuna yadda haɗin kanmu ya shafi yaranmu. Sun san cewa muna bin umurnin da Yesu ya bayar cewa: “Bari zancenku ya zama, I, i; da A’a, a’a.” (Mat. 5:37, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Alal misali, akwai ranar da Lydie ta ƙi ta bar wata ’yarmu ta fita yawo da wasu matasa tsararta sa’ad da take shekara 17. Sai ɗaya daga cikin matasan ta ce mata: “Idan mamarki ba ta yarda ba, ki gaya wa babanki!” Amma sai ’yarmu ta ce: “Shi ma ba zai yarda ba domin bakinsu ɗaya ne.” Yaranmu sun ga cewa muna haɗa kai wajen bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Muna farin ciki sosai domin a yau, membobin iyalinmu da yawa suna bauta wa Jehobah.

Ko da yake na canja abin da ya fi muhimmanci a rayuwata saboda abin da na koya, na so in yi amfani da ƙwarewa da nake da shi wajen taimaka wa bayin Jehobah. Don haka, na ba da kaina in yi aiki a matsayin likita a Bethel da ke birnin Paris. Daga baya kuma na yi aiki a matsayin likita a sabuwar Bethel da aka gina a garin Louviers. Yanzu, na yi kusan shekaru 50 ina zuwa aiki a Bethel. A cikin waɗannan shekarun, na sami abokan kirki da yawa, wasunsu ma sun fi shekaru 90 yanzu. Na yi farin ciki da na haɗu da wani ɗan’uwa da bai jima da zuwa Bethel ba. Na gano cewa ni ne likitan da ya taimaka wa mamarsa ta haife shi shekaru 20 da suka wuce.

NA GA YADDA JEHOBAH YAKE KULA DA MUTANENSA SOSAI

Yadda nake ƙaunar Jehobah ya daɗa ƙaruwa yayin da nake lura da yadda Jehobah yake yi wa mutanensa ja-goranci da kuma kāre su ta wajen ƙungiyarsa. A wajen 1980, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta soma wani shiri a Amirka don taimaka wa likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya su fahimci dalilin da ya sa Shaidun Jehobah ba sa karɓan ƙarin jini.

A 1988, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta kafa Sashen Ba da Bayani Game da Asibitoci. Da farko, wannan sashen ya ja-goranci Kwamitin Hulɗa da Asibitoci da aka kafa a Amirka kaɗai don a taimaka ma ’yan’uwanmu su iya samun likitocin da za su yi musu jinya ba tare da jini ba. Da aka soma yin wannan shirin a dukan duniya, sai aka kafa Kwamitin Hulɗa da Asibitoci a ƙasar Faransa. Ganin yadda ƙungiyar Jehobah take kula da ’yan’uwanmu maza da mata a lokacin da suke rashin lafiya ya burge ni sosai.

NA SAMI ABIN DA NA SA RAI A KAI

Har yanzu, muna jin daɗin yin wa’azin Mulkin Allah

Da ma aikin likita ne na sa farko a rayuwata. Amma da na yi tunani a kan abin da ya fi muhimmanci a rayuwata, sai na gano cewa ya fi muhimmanci in taimaka wa mutane su san Wanda ya halicci rai, wato Jehobah, kuma su bauta masa. Kuma yin hakan ya fi aikin likita da nake yi. Bayan na yi ritaya, ni da matata mukan yi awoyi da dama muna wa’azi kowane wata a matsayin majagaba. Har yanzu muna iya ƙoƙarinmu a yin wa’azin Mulkin Allah.

Ni da Lydie a 2021

Ina kan yin iya ƙoƙarina don in taimaka wa marasa lafiya, amma na san cewa kome ƙwarewar likita, ba zai iya warkar da dukan cututtuka ba, ko ma ya hana mutuwa. Don haka, ina marmarin lokacin da wahala da rashin lafiya da kuma mutuwa za su shuɗe. A Mulkin Allah, zan sami damar koya game da halittun Allah har abada, haɗe da yadda ya tsara jikin ’yan Adam. Hakika, dukan abubuwan da na sa rai a kai sun kusan faruwa. Na san cewa za mu ji daɗin rayuwa sosai a nan gaba!