Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 10

Za Ku Iya “Kawar da Halinku na Dā”

Za Ku Iya “Kawar da Halinku na Dā”

“Ku kawar da halinku na dā da ayyukansa.” —KOL. 3:9, New World Translation.

WAƘA TA 29 Muna Ɗaukaka Sunanka

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Yaya rayuwarka take kafin ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki?

 YAYA rayuwarka take kafin Shaidun Jehobah su soma nazari da kai? Yawancinmu ba ma ma son mu yi tunanin yadda rayuwarmu take a dā. Mai yiwuwa a lokacin mun yi rayuwa bisa ga ra’ayin mutanen duniya. Idan haka ne, a lokacin ba mu da bege, kuma ba mu san Allah ba. (Afis. 2:12) Amma nazarin Littafi Mai Tsarki ya canja yadda muke rayuwa!

2. Me ka gano da ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki?

2 Bayan da ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki, sai ka gano cewa kana da Uba a sama da ke ƙaunar ka sosai. Ka kuma gano cewa idan kana so ka faranta ran Jehobah ko ka zama ɗaya daga cikin bayinsa, dole ne ka yi canje-canje a tunaninka da kuma salon rayuwarka. Ƙari ga haka, ka koyi yadda za ka yi abubuwan da Jehobah yake so, kuma ka guji waɗanda ba ya so.—Afis. 5:3-5.

3. Bisa ga Kolosiyawa 3:9, 10, me Jehobah yake so mu yi, kuma me za mu tattauna a talifin nan?

3 Jehobah Mahaliccinmu da kuma Ubanmu na sama yana da ikon gaya mana yadda za mu yi rayuwa, kuma yana so mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ‘kawar da halinmu na dā da ayyukansa’ kafin mu cancanci yin baftisma. * (Karanta Kolosiyawa 3:9, 10, NWT.) Talifin nan zai taimaka ma waɗanda suke so su yi baftisma su sami amsoshin tambayoyi ukun nan: (1) Mene ne “halinku na dā” yake nufi? (2) Me ya sa Jehobah ya ce mu kawar da shi? (3) Ta yaya za mu iya yin hakan? Mu kuma da muka yi baftisma, talifin zai taimaka mana mu guji irin tunani da kuma halayen da muke da su a dā.

ME AKE NUFI DA “HALINKU NA DĀ”?

4. Waɗanne abubuwa ne mutum zai iya yi idan yana ‘da hali na dā’?

4 Mutumin da ke da ‘hali na dā,’ yana yin rayuwa bisa ga sha’awar jiki ne. Zai iya kasance mai son kai, mai saurin fushi da marar godiya da kuma mai ɗagun kai. Ƙari ga haka, zai iya zama wanda yake jin daɗin kallon batsa da fina-finan da ake nuna lalata ko kuma faɗa. Ba shakka yana da wasu halaye masu kyau kuma zai iya yin baƙin ciki don abubuwan da yake faɗa ko kuma yi. Amma bai da niyyar canja halayensa da kuma tunaninsa.—Gal. 5:19-21; 2 Tim. 3:2-5.

Bayan mun kawar da ‘halinmu na dā,’ sha’awoyin jiki da halaye marasa kyau ba za su shawo kanmu ba (Ka duba sakin layi na 5) *

5. Za mu iya kawar da halinmu na dā gabaki ɗaya? Ka bayyana. (Ayyukan Manzanni 3:19)

5 Da yake mu ajizai ne, ba za mu iya kawar da dukan tunanin banza da sha’awoyi marasa kyau daga zukatanmu ba. A wasu lokuta, mukan faɗa ko yi wasu abubuwa kuma daga baya mu yi da-na-sani. (Irm. 17:9; Yak. 3:2) Amma bayan mun kawar da halinmu na dā, sha’awoyin jiki da halaye marasa kyau ba za su shawo kanmu ba. Salon rayuwarmu za ta canja gabaki ɗaya.—Isha. 55:7; karanta Ayyukan Manzanni 3:19.

6. Me ya sa Jehobah ya ce mu kawar da tunani da kuma halaye marasa kyau?

6 Jehobah yana ƙaunar mu sosai kuma yana so mu ji daɗin rayuwa, shi ya sa ya ce mu daina yin tunani da ayyuka marasa kyau. (Isha. 48:17, 18) Ya san cewa waɗanda ba su kawar da sha’awoyi marasa kyau ba sukan jawo wa kansu da ma wasu baƙin ciki. Ba ya jin daɗi sa’ad da muka jawo wa kanmu da ma wasu baƙin ciki.

7. Bisa ga Romawa 12:1, 2, wane zaɓi ne kowannenmu yake bukatar ya yi?

7 Wasu ’yan’uwanmu da abokanmu za su iya yi mana dariya domin muna ƙoƙarin kawar da halinmu na dā. (1 Bit. 4:3, 4) Za su iya ce muna da ’yancin yin abin da muka ga dama kuma bai kamata mu bar wasu su gaya mana abin da za mu yi ba. Waɗanda suka ƙi bin ƙa’idodin Jehobah za su iya gani kamar suna da ’yanci, amma hakan ba gaskiya ba ne. Gaskiyar ita ce, suna barin duniyar Shaiɗan ta yi musu ja-goranci. (Karanta Romawa 12:1, 2.) Dukanmu muna da zaɓin da ya kamata mu yi: Ko mu ƙi kawar da halinmu na dā, wanda ya ƙunshi halayen mutanen duniya da kuma yin zunubi, ko kuma mu bar Jehobah ya canja mu mu zama masu halin kirki.—Isha. 64:8.

TA YAYA ZA MU ‘KAWAR DA HALINMU NA DĀ?’

8. Waɗanne abubuwa ne za su iya taimaka mana mu daina tunani da kuma halaye marasa kyau?

8 Jehobah ya san cewa kawar da halinmu na dā ba zai kasance mana da sauƙi ba kuma yin hakan zai iya ɗau lokaci. (Zab. 103:13, 14) Amma ta wurin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki, da ruhunsa da kuma ƙungiyarsa, Jehobah yana ba mu hikima da ƙarfi da kuma taimakon da muke bukata don mu iya kawar da halinmu na dā. Babu shakka, ya riga ya taimake ka. Yanzu, bari mu tattauna wasu abubuwa da za ka iya yi da za su taimake ka ka kawar da halinka na dā, kuma ka cancanci yin baftisma.

9. Mene ne Kalmar Allah za ta taimake ka ka yi?

9 Ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ka bincika kanka da kyau. Kalmar Allah tana kamar madubi; za ta iya taimaka maka ka bincika yadda kake tunani da yadda kake magana da kuma ayyukanka. (Yak. 1:22-25) Wanda yake nazari da kai ko wasu Kiristoci da suka manyanta za su iya ba ka shawara game da yadda za ka iya yin hakan. Alal misali, za su iya amfani da Littafi Mai Tsarki su taimaka maka ka san kasawarka da iyawarka. Za su kuma koya maka yadda za ka iya bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimake ka ka daina halaye marasa kyau. Ƙari ga haka, Jehobah yana a shirye ya taimake ka a kullum. Shi ya fi sanin yadda zai taimake ka domin ya san abin da ke zuciyarka. (K. Mag. 14:10; 15:11, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Don haka, ka riƙa yin addu’a da kuma nazarin Kalmarsa a kullum.

10. Mene ne ka koya daga labarin Elie?

10 Ka tabbatar wa kanka cewa ƙa’idodin Jehobah ne suka fi dacewa. Za mu amfana idan muka yi dukan abubuwan da Jehobah ya ce mu yi. Waɗanda suke bin ƙa’idodinsa suna daraja kansu, rayuwarsu tana kasancewa da ma’ana kuma suna farin ciki na ƙwarai. (Zab. 19:7-11) Amma waɗanda ba sa bin ƙa’idodin Jehobah suna fama da munanan sakamako da ayyukan jiki suke kawowa. Ka yi la’akari da abin da wani mutum mai suna Elie ya faɗa game da ƙin bin ƙa’idodin Jehobah. Iyayensa Shaidun Jehobah ne kuma sun rene shi bisa ga ƙa’idodin Jehobah. Amma sa’ad da Elie yake matashi, ya soma bin abokan banza. Ya soma shan ƙwayoyi da yin lalata da kuma sata. Elie ya ce ya zama mai saurin fushi da kuma yawan faɗa. Ya ce: “A taƙaice, na yi dukan abubuwan da bai kamata Kirista ya yi ba.” Amma Elie bai manta da abin da ya koya sa’ad da yake yaro ba. A hankali, ya sake soma nazarin Littafi Mai Tsarki, ya yi iya ƙoƙarinsa ya daina halayensa marasa kyau kuma ya yi baftisma a 2000. Ta yaya ya amfana daga bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki? Elie ya ce: “Yanzu ina da zuciya mai tsabta da kuma kwanciyar hankali.” * Kamar yadda misalin nan ya nuna, waɗanda suka ƙi bin ƙa’idodin Jehobah suna jawo wa kansu baƙin ciki. Duk da haka, Jehobah yana shirye ya taimake su su canja halinsu.

11. Waɗanne abubuwa ne Jehobah ya tsana?

11 Ka tsani abubuwan da Jehobah ya tsana. (Zab. 97:10) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ya tsani ɗagun kai “da harshe mai faɗin ƙarya, da hannuwa masu zub da jinin marasa laifi.” (K. Mag. 6:16, 17) Yana kuma “ƙyamar masu zub da jini da masu ruɗi.” (Zab. 5:6) Jehobah ya tsani halayen nan sosai shi ya sa ya hallaka mugayen mutane a zamanin Nuhu domin sun cika duniya da mugunta. (Far. 6:13) Ga wani misali kuma: Ta wurin annabinsa Malakai Jehobah ya ce ya tsani mutanen da suke ƙulla makirci don su kashe aurensu. Allah ya ƙi amincewa da bautarsu kuma zai hukunta su domin mugayen ayyukansu.—Mal. 2:13-16; Ibran. 13:4.

Ya kamata mu yi ƙyamar yin abin da Jehobah ba ya so kamar yadda muke ƙyamar ruɓaɓɓen abinci (Ka duba sakin layi na 11-12)

12. Me ake nufi da yin ƙyamar abin da ke mugu?

12 Jehobah yana so mu yi “ƙyamar abin da ke mugu.” (Rom. 12:9, Mai Makamantu Ayoyi) Kalmar nan ‘ƙyama’ tana nufin mu tsani abu da dukan ranmu. Yaya za ka ji idan aka ce ka ci abinci da ya ruɓe? Za ka yi ƙyamar hakan ba kaɗan ba. Haka ma, ko tunanin yin abin da Jehobah ya haramta kawai ma ya kamata ya sa mu ƙyama.

13. Me ya sa dole ne mu kiyaye tunaninmu?

13 Ka kiyaye tunaninka. Mukan yi abubuwan da muke tunaninsu ne. Shi ya sa Yesu ya gaya mana cewa mu guji irin tunanin da zai sa mu yin zunubi mai tsanani. (Mat. 5:21, 22, 28, 29) Muna so mu faranta wa Ubanmu na sama rai, ko ba haka ba? Shi ya sa yake da muhimmanci mu yi saurin kawar da duk wani tunani marar kyau da ya shiga zuciyarmu!

14. Mene ne furucinmu yake nunawa, kuma waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?

14 Ka mai da hankali ga abubuwan da kake faɗa. Yesu ya ce: “Abin da yake fitowa daga baki, daga zuciya yake fitowa.” (Mat. 15:18) A gaskiya, abin da muke faɗa yana nuna abin da yake zuciyarmu. Don haka, ka yi wa kanka tambayoyin nan: ‘Ina faɗin gaskiya ko da hakan zai jefa ni cikin matsala? Idan ina da aure, shin ina guje wa yin abubuwan da za su nuna kamar ina son wadda ba matata ba? Shin ina guje wa maganganun iskanci da dukan zuciyata? Idan wani ya ɓata min rai, ina yin magana a cikin hankali?’ Yin tunani a kan tambayoyin nan zai taimake ka sosai. Furucinmu kamar botin da ke jikin riga yake. Idan muka cire botin ɗin, zai mana sauƙi mu cire rigar daga jikinmu. Haka ma, idan muna so mu kawar da halinmu na dā, dole ne mu daina zage-zage da ƙarya da kuma maganganun iskanci.

15. Me ake nufi da mu rataye halinmu na dā “a kan gungume”?

15 Ka kasance a shirye ka yi abin da ya dace. Manzo Bulus ya yi amfani da wani kwatanci mai kyau don ya nuna mana cewa yana da muhimmanci mu canja salon rayuwarmu. Ya rubuta cewa dole ne mu rataye halinmu na dā “a kan gungume.” (Rom. 6:6, New World Translation) Yesu ya yarda a rataye shi a kan gungume don ya faranta ran Jehobah. Haka ma, idan muna so mu faranta ma Jehobah rai, dole ne mu daina yin tunani da kuma abubuwa da Jehobah ba ya so. Sai mun yi hakan ne zuciyarmu za ta kasance da tsabta kuma za mu sami begen yin rayuwa har abada. (Yoh. 17:3; 1 Bit. 3:21) Ka tuna cewa Jehobah ba zai canja ƙa’idodinsa don ya faranta mana rai ba. A maimakon haka, mu ne muke bukatar mu canja salon rayuwarmu don ya jitu da ƙa’idodinsa.—Isha. 1:16-18; 55:9.

16. Me ya sa dole ne ka ci gaba da yin iya ƙoƙarinka don ka shawo kan sha’awoyin jiki?

16 Ka ci gaba da yin iya ƙoƙarinka don kada sha’awoyin jiki su shawo kanka. Bayan ka yi baftisma, za ka bukaci ka ci gaba da yin iya ƙoƙarinka don ka shawo kan sha’awoyin jiki. Ka yi la’akari da misalin wani mutum mai suna Maurício. Sa’ad da yake matashi, ya soma yin lalata da maza. Daga baya ya haɗu da Shaidun Jehobah kuma ya fara nazarin Littafi Mai Tsarki. Ya yi baftisma a 2002 bayan ya canja salon rayuwarsa. Ko da yake yanzu Maurício ya yi shekaru da yawa yana bauta wa Jehobah, ya ce: “A gaskiya, a wasu lokuta nakan yi fama da sha’awoyin jiki.” Amma bai bar hakan ya sa shi sanyin gwiwa ba. A maimakon haka, ya ce: “Sanin cewa Jehobah zai yi farin ciki idan ban bi sha’awoyin jikina ba, yana ƙarfafa ni.” *

17. Mene ne ya ƙarfafa ka a labarin Nabiha?

17 Ka roƙi Jehobah ya taimake ka kuma ka dogara ga ruhunsa mai tsarki, ba ga ƙarfinka ba. (Gal. 5:22; Filib. 4:6) Dole ne mu dage idan muna so mu kawar da halinmu na dā kuma kada mu koma ga yinsa. Ka yi la’akari da labarin wata mata mai suna Nabiha. Mahaifinta ya yashe ta sa’ad da take shekara shida kawai. Nabiha ta ce: “Hakan ya sa ni baƙin ciki sosai.” Da take girma, Nabiha ta zama mai saurin fushi da yawan faɗa. A hankali, ta soma sayar da ƙwayoyi. Sai aka kama ta kuma ta yi shekaru a kurkuku. Shaidun Jehobah da suke zuwa wa’azi a kurkuku sun soma nazari da ita. Nabiha ta soma canja salon rayuwarta. Ta ce: “Ya yi min sauƙi in daina wasu halayena marasa kyau. Amma bai yi min sauƙi in daina shan taba ba.” Nabiha ta yi fiye da shekara ɗaya tana fama kafin ta iya daina shan taba. Me ya taimaka mata ta iya yin hakan? Ta ce abin da ya fi taimaka mata shi ne yin addu’a babu fasawa. A yanzu takan ce: “Ina da tabbaci cewa da yake na iya canja salon rayuwata don in faranta wa Jehobah rai, kowa ma zai iya yin hakan!” *

ZA KA IYA CANCANCI YIN BAFTISMA

18. Bisa ga 1 Korintiyawa 6:9-11, mene ne bayin Allah da yawa sun iya yi?

18 A ƙarni na farko, wasu daga cikin maza da mata da Jehobah ya zaɓa su yi sarauta da Yesu sun yi abubuwa marasa kyau a dā. Alal misali, wasunsu a dā mazinata ne. Wasu kuma maza masu kwana da maza ne da kuma ɓarayi. Amma da taimakon ruhu mai tsarki, sun iya canja salon rayuwarsu. (Karanta 1 Korintiyawa 6:9-11.) Haka ma a yau, Littafi Mai Tsarki ya taimaka ma miliyoyin mutane su canja salon rayuwarsu. * Sun iya daina halaye masu wuyan bari. Don haka, kai ma za ka iya canja salon rayuwarka kuma ka daina halaye marasa kyau don ka cancanci yin baftisma.

19. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

19 Ban da kawar da halinsu na dā, waɗanda suke so su yi baftisma suna saka sabon hali. Talifi na gaba zai tattauna yadda za mu yi hakan, da kuma yadda wasu za su iya taimaka mana.

WAƘA TA 41 Allah Ka Ji Roƙona

^ sakin layi na 5 Muna bukatar mu canja halayenmu idan muna so mu cancanci yin baftisma. Talifin nan zai taimake mu mu san abin da ake nufi da halinmu na dā, da dalilin da ya sa muke bukatar mu kawar da shi, da yadda za mu iya yin hakan. A talifi na gaba kuma, za mu tattauna yadda za mu ci gaba da saka sabon hali har bayan mun yi baftisma.

^ sakin layi na 3 MA’ANAR WASU KALMOMI: “Kawar da halinku na dā” yana nufin mu guji halaye da sha’awoyin da Jehobah ba ya so. Ya kamata mu soma yin hakan tun kafin mu yi baftisma.—Afis. 4:22.

^ sakin layi na 10 Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan, Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane—‘Ina Bukatar Komawa ga Bauta wa Jehobah,’ ” wanda aka buga a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 2012.

^ sakin layi na 16 Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan “The Bible Changes Lives—‘They Were Very Kind to Me,’ ” wanda aka wallafa a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Mayu, 2012.

^ sakin layi na 17 Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan, “The Bible Changes Lives—‘I Became an Angry, Aggressive Young Woman,’ ” wanda aka wallafa a fitowar Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 2012.

^ sakin layi na 64 BAYANI A KAN HOTUNA: Kawar da halaye marasa kyau yana kama da tuɓe tsohon riga.