Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 11

Ku Ci-gaba da Saka ‘Sabon Hali’ Bayan Kun Yi Baftisma

Ku Ci-gaba da Saka ‘Sabon Hali’ Bayan Kun Yi Baftisma

Ku “ɗauki sabon halin nan.”—KOL. 3:10.

WAƘA TA 49 Mu Riƙa Faranta Ran Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane abu ne ya fi shafan halinmu?

 KO DA mun jima da yin baftisma ko a’a, dukanmu muna so mu kasance da irin halin da Jehobah yake so. Shi ya sa dole ne mu kiyaye tunaninmu. Me ya sa? Domin tunaninmu ne yake shafan halinmu. Idan muna yawan tunani a kan sha’awoyin jikinmu, za mu riƙa faɗin ko yin abubuwan da ba su dace ba. (Afis. 4:17-19) Amma idan muna tunani a kan abubuwa masu kyau, za mu iya faranta ran Jehobah ta furucinmu da ayyukanmu.—Gal. 5:16.

2. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a talifin nan?

2 Kamar yadda muka koya a talifi na baya, ba za mu iya guje wa tunani marar kyau gaba ɗaya ba, amma za mu iya ƙin aikata su. Kafin mu yi baftisma, muna bukatar mu guji faɗa ko yin abin da Jehobah ba ya so. Wannan shi ne abu na farko kuma mafi muhimmanci da muke bukatar mu yi don mu kawar da halinmu na dā. Amma don mu faranta wa Jehobah rai, dole ne mu bi wannan umurni cewa: ‘Ku ɗauki sabon hali.’ (Kol. 3:10) A wannan talifin, za mu amsa tambayoyin nan: Me ake nufi da ‘sabon hali’? Ta yaya za mu ɗauki ko saka sabon hali kuma mu ci gaba da kasancewa da shi?

ME AKE NUFI DA ‘SABON HALI’?

3. Bisa ga Galatiyawa 5:22, 23, me ake nufi da ‘sabon hali,’ kuma ta yaya mutum zai saka shi?

3 ‘Sabon hali’ yana nufin mu yi tunani da kuma ayyuka kamar Jehobah. Mutum zai iya saka ‘sabon hali’ ta wajen kasancewa da halayen da ruhu mai tsarki yake haifarwa kuma ya bar ruhun ya shafi tunaninsa da yadda yake ji da kuma ayyukansa. (Karanta Galatiyawa 5:22, 23.) Alal misali, zai ƙaunaci Jehobah da kuma bayinsa. (Mat. 22:36-39) Zai yi farin ciki ko a lokacin da yake fuskantar matsaloli. (Yak. 1:2-4) Shi mai son zaman lafiya ne. (Mat. 5:9) Yana da haƙuri da kuma kirki. (Kol. 3:13) Yana son abu mai kyau kuma yana yin su. (Luk. 6:35) Ayyukansa suna nuna cewa shi mai bangaskiya ne sosai. (Yak. 2:18) Yana kame kansa sa’ad da aka ɓata masa rai kuma yana shawo kan jarrabobi da yake fuskanta.—1 Kor. 9:25, 27; Tit. 3:2.

4. Idan muna so mu saka ‘sabon hali’ za mu iya nuna halayen da ke Galatiyawa 5:22, 23 ɗaya bayan ɗaya? Ka bayyana.

4 Kafin mu saka sabon hali, muna bukatar mu kasance da dukan halayen da aka ambata a Galatiyawa 5:22, 23 da kuma wasu nassosi. * Halaye da aka ambata a nassosin ba sa kamar kaya dabam-dabam da muke saka su ɗaya bayan ɗaya. Gaskiyar ita ce, suna da alaƙa da juna. Alal misali, idan kana ƙaunar maƙwabcinka, za ka yi haƙuri da shi kuma ka yi masa nagarta. Kuma kafin ka yi wa maƙwabcinka nagarta, dole ne ka zama mai tawali’u da kamun kai.

TA YAYA ZA MU SAKA ‘SABON HALI’?

Yayin da muke daɗa yin tunani kamar Yesu, za mu daɗa yin koyi da halayensa (Ka duba sakin layi na 5, 8, 10, 12, 14)

5. Me ake nufi da mu kasance da ‘tunanin Almasihu’ kuma me ya sa ya dace mu yi nazarin rayuwar Yesu? (1 Korintiyawa 2:16)

5 Karanta 1 Korintiyawa 2:16. Muna bukatar mu kasance da ‘tunanin Almasihu’ idan muna so mu saka sabon hali, wato mu san yadda Yesu yake yin tunani kuma mu yi koyi da shi. Yesu ya nuna dukan halayen da ruhu mai tsarki yake haifarwa. Ya nuna halayen Jehobah daidai ba tare da kuskure ba. (Ibran. 1:3) Yayin da tunaninmu yake daɗa jituwa da na Yesu, za mu daɗa yin koyi da halayensa kuma hakan zai iya taimaka mana mu saka sabon hali.—Filib. 2:5.

6. Me ya kamata mu tuna yayin da muke ƙoƙarin saka sabon hali?

6 Shin zai yiwu mu iya yin koyi da misalin Yesu? Za mu iya cewa, ‘Ai Yesu kamili ne. Ba zan iya zama kamar shi ba!’ Idan haka kake ji, ka tuna da wannan: Da farko, an halicce ka a kamannin Jehobah da Yesu ne. Don haka, idan ka so, za ka iya yin koyi da su kuma za ka iya yin hakan iya gwargwadon ƙarfinka. (Far. 1:26) Na biyu, ruhu mai tsarki ne ruhun da ya fi iko a sama da duniya. Da taimakon ruhu mai tsarki, za ka iya cim ma abubuwan da ba za ka iya yi da naka ƙarfi ba. Na uku, a yanzu, Jehobah bai ce mana mu nuna halaye da ruhu mai tsarki yake haifarwa daidai ba tare da kuskure ba. Gaskiyar ma ita ce, Ubanmu mai ƙauna zai ba waɗanda za su yi rayuwa a duniya shekaru 1,000 don su zama kamilai. (R. Yar. 20:1-3) Abin da Jehobah yake bukatar mu yi a yanzu shi ne mu yi iya ƙoƙarinmu kuma mu nemi taimakonsa.

7. Mene ne za mu tattauna yanzu?

7 Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu? Za mu tattauna halaye huɗu da ruhu mai tsarki yake sa mu kasance da su. Za mu ga darussa da za mu iya koya daga yadda Yesu ya nuna kowanne cikin halayen. Yayin da muke yin hakan, za mu tattauna wasu tambayoyi da za su taimaka mana mu ga yadda za mu daɗa nuna halayen nan.

8. Ta yaya Yesu ya nuna ƙauna?

8 Yesu yana ƙaunar Jehobah sosai shi ya sa ya yi sadaukarwa domin mu da kuma Ubansa. (Yoh. 14:31; 15:13) Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar ’yan Adam sosai ta yadda ya yi rayuwarsa a duniya. A kullum, ya nuna wa mutane ƙauna kuma ya tausaya musu har a lokacin da wasu suka yi hamayya da shi. Hanya mai muhimmanci da ya nuna wa mutane ƙauna ita ce ta wajen koya musu game da Mulkin Allah. (Luk. 4:43, 44) Yesu ya kuma nuna yadda yake ƙaunar Jehobah da ’yan Adam ta wajen yarda ya sha wahala har ya mutu a hannun masu zunubi. Ta haka, ya buɗe mana hanyar samun rai na har abada.

9. Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu a yadda muke nuna ƙauna?

9 Mun yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma mun yi baftisma domin muna ƙaunar Ubanmu na sama. Don haka, kamar Yesu, zai dace mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah ta yadda muke bi da mutane. Manzo Yohanna ya rubuta cewa: “Duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa wanda yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda bai taɓa gani ba.” (1 Yoh. 4:20) Za mu iya tambayar kanmu: ‘Shin ina ƙaunar mutane sosai? Ina nuna wa mutane tausayi sa’ad da nake sha’ani da su ko da sun nuna mini rashin hankali? Ƙauna tana sa in yi amfani da lokacina da kuma kuɗina in taimaki mutane su koya game da Jehobah? Shin zan ci gaba da yin hakan ko da yawancin mutane ba sa nuna godiya don abin da nake yi ko wasu suna hamayya da ni? Zan iya yin ƙoƙari don in ƙara lokacin da nake amfani da shi a wa’azi?’—Afis. 5:15, 16.

10. Ta yaya Yesu ya nuna cewa shi mai son zaman lafiya ne?

10 Yesu mutum ne mai son zaman lafiya. Sa’ad da mutane suka yi masa mugunta, bai rama ba. Amma ya yi wani abu fiye da haka. Idan tashin hankali yana so ya ɓarke a tsakanin mutane, yakan yi ƙoƙari ya kwantar da hankalinsu kuma ya ƙarfafa mutane su riƙa sasanta da juna. Alal misali, ya gaya musu cewa idan suna so Jehobah ya amince da bautarsu, dole ne su sasanta da ’yan’uwansu. (Mat. 5:9, 23, 24) Kuma sau da yawa, ya taimaka wa manzanninsa su sasanta da juna sa’ad da suke gardama a kan ko wane ne ya fi girma.—Luk. 9:46-48; 22:24-27.

11. Ta yaya za mu zama masu son zaman lafiya?

11 Son zaman lafiya ya wuce guje ma yin abin da zai jawo rigima kawai. Muna bukatar mu ɗauki matakin sasantawa da mutane kuma mu ƙarfafa ’yan’uwanmu su ma su sasanta da ’yan’uwansu. (Filib. 4:2, 3; Yak. 3:17, 18) Za mu iya tambayar kanmu: ‘Wace sadaukarwa ce zan iya yi don in zauna lafiya da mutane? Ina riƙe mutane a zuciya sa’ad da suka ɓata mini rai? Ina jira sai mutumin ya ɗauki mataki kafin mu sasanta ko ina ɗau mataki da kaina ko da mutumin ne ke da laifi? Idan zai yiwu, ina ƙarfafa waɗanda suke da matsala su sasanta?’

12. Ta yaya Yesu ya yi wa mutane kirki?

12 Yesu mutumin kirki ne. (Mat. 11:28-30) Ya yi wa mutane kirki ta wajen bi da su a hankali kuma bai nace a kan ra’ayinsa ba. Alal misali, sa’ad da wata matar Kan’ana ta roƙe shi ya warkar da ’yarta, da farko ya ƙi, amma da ta nuna bangaskiya sosai, sai ya nuna mata alheri kuma ya warkar da ’yarta. (Mat. 15:22-28) Ko da yake Yesu mai kirki ne, bai ƙi ba da gargaɗi ba. A wasu lokuta, yakan yi hakan ta wajen yi wa mutane gyara. Alal misali, sa’ad da Bitrus ya so ya hana shi yin nufin Jehobah, Yesu ya tsawata masa a gaban sauran almajiransa. (Mar. 8:32, 33) Bai yi hakan don ya ƙasƙantar da Bitrus ba, amma ya yi hakan ne don ya gargaɗe shi kuma ya koya wa sauran almajiran cewa suna bukatar su riƙa ƙarfafa shi ya yi nufin Allah, ba wai su sa shi sanyin gwiwa ba. Ba shakka Bitrus ya ji kunya amma ya koyi darasi daga gargaɗin da Yesu ya yi masa.

13. Ta yaya za mu yi wa mutane kirki?

13 Don ka nuna ma waɗanda kake ƙauna kirki, a wasu lokuta za ka bukaci ka yi musu gargaɗi. Yayin da kake yin hakan, ka yi koyi da Yesu ta wajen tabbata cewa gargaɗi da kake ba su ya jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ka bi da su a hankali. Ka gaskata cewa suna son su yi abin da ya dace. Kuma ka gaya wa kanka cewa waɗanda suke ƙaunar ka da Jehobah, za su amince da gargaɗin da ka ba su. Ka tambayi kanka: ‘Idan na ga wani yana yin abu marar kyau, ina yi masa gargaɗi? Idan ya dace in ba da gargaɗi, ina yin hakan cikin hankali ne ko da fushi? Mene ne ainihin dalilin da ya sa nake so in ba da gargaɗin? Shin ina so in ba da gargaɗin don abin da ya yi ya ɓata min rai ne ko don ina so in taimaka masa ne?’

14. Ta yaya Yesu yake yin nagarta?

14 Yesu ya san nagarta kuma yana aikata su. Yesu yana ƙaunar Ubansa, don haka, duk wani abin kirki da yake yi, yana yi ne da dalili mai kyau. Mutum mai nagarta yakan nemi hanyoyin da zai taimaka wa mutane a kullum kuma yana yi musu alheri. Ba sanin abu mai kyau ne kawai ake bukata a gare mu ba. Amma muna bukatar mu aikata abu mai kyau da dalili mai kyau. Wani zai iya tambaya, ‘Shin zai yiwu mutum ya yi abu mai kyau da mummunar nufi?’ E, zai yiwu. Alal misali, Yesu ya yi magana game da waɗanda suke ba da kyauta ga talakawa amma suna yin hakan yadda mutane za su gan su kuma su yaba musu. Ko da yake ba da kyauta yana da kyau, Jehobah bai yi farin ciki da su ba.—Mat. 6:1-4.

15. Ta yaya za mu zama masu yin nagarta?

15 Idan muna yin abin da ya dace da manufa mai kyau, hakan zai nuna cewa mu masu nagarta ne da gaskiya. Za ka iya yi wa kanka tambayoyin nan: ‘Shin na san abu mai kyau kuma ina yin sa? Wane dalili nake da shi na yin abu mai kyau?’

TA YAYA ZA MU KĀRE SABON HALINMU?

16. Mene ne ya kamata mu yi a kowace rana kuma me ya sa?

16 Kada mu ɗauka cewa bayan mun yi baftisma, mun riga mu gama saka sabon halin kuma ba ma bukatar mu yi wani abu kuma. Sabon halinmu yana kama da “sabon riga” kuma muna bukatar mu ci gaba da kāre shi. Hanya ɗaya da za mu iya yin hakan ita ce ta wajen yin abubuwan da za su nuna cewa muna da halayen da ruhu mai tsarki yake haifarwa a kullum. Me ya sa? Domin Jehobah Allah ne da ke nuna halayensa ta ayyuka kuma ruhunsa yana aiki sosai. (Far. 1:2) Don haka, idan muna da kowane ɗaya daga cikin halayen da ruhu mai tsarki ke haifarwa, dole ne mu yi abubuwa da za su nuna hakan. Alal misali, almajirin Yesu mai suna Yakub ya rubuta cewa: ‘Bangaskiya marar ayyuka daidai take da gawa.’ (Yak. 2:26) Haka ma yake da sauran halayen da ruhu mai tsarki yake haifarwa. A duk lokacin da muka nuna ɗaya daga cikin halayen, muna nuna cewa ruhu mai tsarki yana taimaka mana.

17. Me ya kamata mu yi idan mun kasa nuna halaye da ruhu mai tsarki yake haifarwa?

17 Ko Kiristoci da suka jima da yin baftisma ma, a wasu lokuta sukan kasa nuna halayen da ruhu mai tsarki yake haifarwa. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne mu ci gaba da ƙoƙari. Ka yi la’akari da misalin nan. A ce sabuwar rigarka ta yage, za ka yar da rigar nan take ne? A’a. Idan zai yiwu, za ka ɗinka rigar. Kuma bayan haka, za ka yi hankali don kar ta sake yagewa. Haka ma, idan a wasu lokuta ba ka iya nuna ƙauna da haƙuri da kuma kirki ga wani ba, kada ka yi sanyin gwiwa. Za ka iya ba mutumin haƙuri daga zuciyarka don ku sasanta kuma ku kyautata dangantakarku da juna. Ka ƙudura cewa za ka yi iya ƙoƙarinka don ka nuna halayen a gaba.

18. Wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi?

18 Muna farin ciki sosai don misali mai kyau da Yesu ya kafa mana. Yayin da muke daɗa koyi da halayensa da tunaninsa, zai daɗa mana sauƙi mu zama kamar sa. Yayin da muke daɗa zama kamar sa, zai daɗa mana sauƙi mu saka sabon halin. A talifin nan, mun tattauna halaye guda huɗu ne kawai da ruhu mai tsarki yake haifarwa. Zai dace ka nemi lokaci ka yi nazarin sauran halayen da ruhu mai tsarki yake haifarwa, kuma ka yi tunani ko kana nuna halayen da kyau. Za ka sami talifofi da yawa da suka tattauna wannan batun a Littafin Bincike don Shaidun Jehobah ƙarƙashin jigon nan “Rayuwar Kirista,” sai ka duba ƙarƙashin “ ’Yar Ruhu.” Ka tabbata cewa idan ka yi iya ƙoƙarinka, Jehobah zai taimaka maka ka saka sabon halin kamar riga kuma ka ci gaba da kasancewa da shi.

WAƘA TA 127 Irin Mutumin da Ya Kamata In Zama

^ sakin layi na 5 Ko da daga ina muka fito, za mu iya ci gaba da saka “sabon hali.” Kafin mu iya yin hakan, dole ne mu ci gaba da kyautata tunaninmu kuma mu yi koyi da Yesu. A wannan talifin, za mu bincika tunanin Yesu da ayyukansa. Za mu kuma koyi yadda za mu ci gaba da yin koyi da Yesu bayan mun yi baftisma.

^ sakin layi na 4 Galatiyawa 5:22, 23 ba su ambata duka halayen da ruhu mai tsarki yake haifarwa ba. Don ƙarin bayani, ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro ta Yuni, 2020.