Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 13

Yin Ibada ta Gaskiya Za Ta Sa Ka Daɗa Yin Farin Ciki

Yin Ibada ta Gaskiya Za Ta Sa Ka Daɗa Yin Farin Ciki

“Ya Ubangiji Allahnmu, ka cancanci ka karɓi ɗaukaka, da girma, da iko.”—R. YAR. 4:11.

WAƘA TA 31 Ka Bi Allah!

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Mene ne za mu yi don Jehobah ya amince da bautarmu?

 ME YAKE zuwa zuciyarka a duk lokacin da ka ji kalmar nan “ibada”? Mai yiwuwa za ka yi tunanin wani ɗan’uwa da ya tsuguna yana yin addu’a ga Jehobah kafin ya yi barci. Ko kuma ka yi tunanin iyalin da suke jin daɗin yin nazarin Littafi Mai Tsarki.

2 A duka yanayoyin nan, masu shelar suna yin ibada ne ga Jehobah. Shin Jehobah zai karɓi bautarsu? Ƙwarai kuwa, idan suna ƙoƙari su yi nufinsa kuma suna ƙaunarsa da kuma daraja shi yayin da suke yin hakan. Muna ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu. Mun san cewa ya cancanci mu bauta masa kuma yana so mu bauta masa da iya ƙarfinmu.

3. Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 A wannan talifin, za mu tattauna irin bautar da Jehobah ya amince da ita a zamanin dā, kuma za mu tattauna hanyoyi takwas da Jehobah yake so mu bauta masa. Yayin da muke hakan, zai dace mu yi tunanin yadda za mu inganta yadda muke ibada. Sa’an nan za mu tattauna dalilan da suke sa yin ibada ta gaskiya yake sa mu farin ciki.

BAUTAR DA JEHOBAH YA AMINCE DA ITA A ZAMANIN DĀ

4. Ta yaya mutanen da suka bauta wa Jehobah kafin Yesu ya zo duniya suka nuna cewa suna ƙaunarsa kuma suna daraja shi?

4 Kafin Yesu ya zo duniya, mutane masu aminci kamar Habila da Nuhu da Ibrahim da Ayuba sun nuna cewa suna ƙaunar Jehobah kuma suna daraja shi sosai. Ta yaya suka yi hakan? Ta wajen yi masa biyayya da nuna bangaskiya da kuma yi masa hadayu. Littafi Mai Tsarki bai gaya mana kome da kome da ya kamata su yi yayin da suke bauta masa ba. Amma sun yi iya ƙoƙarinsu su ɗaukaka Jehobah kuma ya amince da bautarsu. Daga baya, Jehobah ya ba Isra’ilawa dokarsa ta hannun Musa. Dokokin sun nuna yadda Jehobah yake so su bauta masa.

5. Wane canji ne Jehobah ya yi game da yadda mabiyan Yesu za su bauta masa?

5 Tun bayan mutuwar Yesu da tashinsa, Jehobah ba ya bukatar mutane su bauta masa bisa ga dokar da ya ba wa Isra’ilawa. (Rom. 10:4) An bukaci Kiristoci su bi sabuwar doka, wato “koyarwar Almasihu.” (Gal. 6:2) Ba ta wajen haddace dokar ko bin jerin abubuwa da ya kamata su yi da waɗanda bai kamata su yi ba ne za su bi koyarwar Almasihu, amma ta wurin bin misalin Yesu da kuma koyarwarsa ne. A yau ma, Kiristoci suna iya ƙoƙarinsu su bi misalin Kristi don su faranta wa Jehobah rai kuma su “sami kwanciyar rai.”—Mat. 11:29, Mai Makamantu Ayoyi.

6. Ta yaya wannan talifin zai amfane mu?

6 Yayin da muke tattauna kowanne cikin fannonin ibadarmu, ka tambayi kanka, ‘Shin na sami ci gaba a wannan fannin? Akwai abin da zan iya yi don in inganta yadda nake ibada?’ Ya kamata ka yi farin ciki da ci gaban da ka samu yanzu, amma ya kamata ka roƙi Jehobah ya taimake ka ka ga inda kake bukatar gyara.

A WAƊANNE HANYOYI NE ZA MU IYA BAUTA WA JEHOBAH?

7. Yaya Jehobah yake ɗaukan addu’o’in da muke masa daga zuciyarmu?

7 Yin addu’a ibada ce ga Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta addu’o’inmu da turaren da ake ƙonewa a mazauni kuma daga baya a haikali. (Zab. 141:2) Turaren yakan fitar da ƙanshin da yake faranta wa Allah rai. Hakazalika, Jehobah yana “jin daɗin” addu’armu ko da ba mu yi amfani da manyan kalmomi ba. (K. Mag. 15:8; M. Sha. 33:10) Muna da dalilai masu kyau da suke sa mu gaskata cewa Jehobah yana farin ciki yayin da muke gaya masa yadda muke ƙaunarsa da yadda muke gode masa. Yana so mu riƙa gaya masa abin da ke damunmu, abin da muke sa ran samuwa da abin da muke sha’awarsa. Kafin ka soma addu’a, zai dace ka yi tunanin abubuwa da kake so ka gaya wa Jehobah. Ta yin haka, za ka ba da “turare” mafi kyau ga Ubanka na sama.

8. A waɗanne lokuta ne za mu iya yabon Allah?

8 Muna bauta wa Jehobah ta wajen yabonsa. (Zab. 34:1) Za mu iya yabon Jehobah ta wajen gaya wa mutane yadda muke ƙaunar Jehobah da kuma yadda muke son halayensa da ayyukansa. Za mu ga dalilai da yawa na yabon Jehobah idan muna yin godiya don abubuwan da yake yi mana. Ba za mu rasa dalilan yabon Jehobah ba idan muna tunanin abubuwan da yake yi mana. Yin wa’azi yana ba mu damar ‘miƙa hadayar yabo ga Allah, wato, yabon shaidar darajar sunansa.’ (Ibran. 13:15) Kamar yadda ya dace mu riƙa tunanin abubuwa da za mu gaya wa Jehobah tun kafin mu fara addu’a, haka ma yana da kyau mu yi tunani sosai a kan abin da za mu faɗa ga waɗanda muke musu wa’azi. Muna so “hadayar yabo” da muke bayarwa ta fito daga zuciyarmu. Shi ya sa muke yin wa’azi da himma sosai.

9. Ta yaya halartan taro yanzu yake amfanar mu kamar yadda ya amfani Isra’ilawa? Ka ba da misalin yadda ka amfana daga halartan taro.

9 Halartan taro hanya ce ta yin ibada. Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa a zamanin dā cewa: “Sau uku a cikin shekara, dukan ’ya’yanku maza za su zo gaban Yahweh Allahnku a wurin da ya zaɓa.” (M. Sha. 16:16) Za su bukaci su bar gonakinsu da gidajensu ba tare da mai lura da su ba. Amma Jehobah ya yi musu alkawari cewa idan sun ‘haura domin su bayyana kansu a gaban Yahweh Allahnsu, ba wanda zai yi kwaɗayin ƙwace ƙasarsu.’ (Fit. 34:24) Yadda Isra’ilawan suka dogara ga Jehobah ya sa sun halarci waɗannan bukukuwa na shekara-shekara kuma sun amfana a hanyoyi da yawa. Alal misali, sun daɗa koya game da Dokar da Jehobah Ya Bayar ta Hannun Musa, sun yi tunanin irin alherin da Allah yake yi musu kuma sun ji daɗin yin tarayya da sauran ’yan’uwansu da suke ƙaunar Jehobah. (M. Sha. 16:15) Mu ma za mu amfana sosai idan muka yi iya ƙoƙarinmu mu halarci taro tare da ’yan’uwanmu a kullum. Kuma ka yi tunanin irin farin cikin da Jehobah yake yi yayin da muka shirya gajerun kalamai masu kyau da za mu yi.

10. Me ya sa rera waƙa yake da muhimmanci a ibadarmu ga Jehobah?

10 Rera waƙa tare da ’yan’uwanmu hanya ce ta bauta wa Jehobah. (Zab. 28:7) Isra’ilawa sun ɗauki rera waƙa da muhimmanci sosai a ibadarsu. Sarki Dauda ya zaɓi Lawiyawa 288 su riƙa yin waƙa a haikali. (1 Tar. 25:1, 6-8) A yau ma za mu iya nuna wa Allah cewa muna ƙaunarsa ta wajen rera waƙoƙin yabo. Ba sai mun iya waƙa sosai kafin mu rera waƙa ba. Ka yi la’akari da wannan misalin: Yayin da muke magana, muna iya yin kurakure da yawa. Amma hakan ba ya hana mu yin magana sa’ad da muke ikilisiya ko muke wa’azi. (Yak. 3:2) Haka ma, bai kamata mu ƙi rera waƙoƙin yabo ga Jehobah ba, ko da muna ganin muryarmu ba ta da daɗi.

11. Kamar yadda Zabura 48:13 ta nuna, me ya sa ya kamata mu keɓe lokacin nazari a matsayin iyali?

11 Yayin da muke nazarin Kalmar Allah da kuma koya wa yaranmu game da Jehobah, muna bauta masa ne. A ranar Assabaci, Isra’ilawa ba sa aiki kuma suna amfani da ranar wajen ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. (Fit. 31:16, 17) Isra’ilawa masu aminci sukan koya wa yaransu game da Jehobah da kuma alherinsa. A yau ma, muna bukatar mu keɓe lokacin karanta da kuma yin nazarin Kalmar Allah. Hakan sashe ne na ibadarmu ga Jehobah kuma yana taimaka mana mu daɗa kusantarsa. (Zab. 73:28) Kuma idan muka yi nazari tare a matsayin iyali, za mu taimaka wa yaranmu su kasance da dangantaka mai kyau da Ubanmu na sama mai ƙauna.—Karanta Zabura 48:13.

12. Me za mu koya daga yadda Jehobah ya ɗauki aikin waɗanda suka yi mazauni da kuma adonsa?

12 Gina wuraren ibada da kuma kula da su wata hanya ce da muke bauta wa Jehobah. Jehobah ya ɗauki aikin yin mazauni da kuma adon da ke jikinsa a matsayin ibada. (Fit. 36:1, 4) A yau ma, Jehobah yana ɗaukan aikin gina Majami’un Mulki da wasu wuraren ibada a matsayin ibadarmu a gare shi. Wasu ’yan’uwa suna ba da lokacinsu sosai wajen yin ayyukan nan. Hakika muna godiya sosai don waɗannan ayyukan da suke yi don tallafa wa hidimarmu. Ban da haka, suna yin wa’azi. Wasu a cikinsu ma za su so su zama majagaba. Dattawa za su nuna cewa suna goyon bayan waɗannan ’yan’uwan ta wajen naɗa su su zama majagaba ba tare da ɓata lokaci ba, idan suka cancanci hakan. Ko da mun iya aikin gine-gine ko ba mu iya ba, dukanmu za mu iya taimaka wajen tsabtace waɗannan wuraren ibada da kuma kula da su.

13. Yaya ya kamata mu ɗauki gudummawa da muke yi don tallafa wa ayyukan da ƙungiyar Jehobah take yi?

13 Ba da gudummawa don tallafa wa hidimar Mulkin Allah wata hanya ce ta bauta wa Jehobah. Jehobah ya ce kada Isra’ilawa su zo gabansa hannu wofi. (M. Sha. 16:16) Ya kamata su kai gudummawa bisa ga ƙarfinsu. Ta haka, za su nuna cewa suna godiya ga Jehobah don kome da ya yi musu. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah kuma muna godiya don dukan abubuwan da ya yi mana? Hanya ɗaya da za mu iya yin hakan ita ce ta wurin ba da gudummawa gwargwadon ƙarfinmu don aikin wa’azi da ake yi a faɗin duniya da kuma ikilisiyoyinmu. Ga abin da manzo Bulus ya faɗa game da batun: “Idan kuna da zuciyar bayarwa, Allah zai ji daɗin bayarwar, wato idan kun bayar gwargwadon ƙarfinku. Allah ba ya so ku yi abin da ƙarfinku bai kai ba.” (2 Kor. 8:4, 12) Jehobah yana farin ciki da duk abin da muka ba shi kome ƙanƙancin sa.—Mar. 12:42-44; 2 Kor. 9:7.

14. Bisa ga Karin Magana 19:17, yaya Jehobah yake ɗaukan taimakon da muke ba ’yan’uwanmu da suke da bukata?

14 Taimaka ma ’yan’uwanmu Kiristoci sa’ad da suke da bukata hanya ce kuma ta bauta wa Jehobah. Jehobah ya yi alkawari cewa zai albarkaci Isra’ilawa da suka taimaka wa matalauta. (M. Sha. 15:7, 10) Hakika a duk lokacin da muka taimaka ma wata ’yar’uwa ko ɗan’uwa, Jehobah yana ɗaukan hakan a matsayin kyauta da muka ba shi. (Karanta Karin Magana 19:17.) Alal misali, a lokacin da Kiristoci a Filibi suka tura wa Bulus kyauta a lokacin da yake kurkuku, Bulus ya kira kyautar hadaya da “Allah zai karɓa ya kuma ji daɗinsa.” (Filib. 4:18) Ka yi tunanin ’yan’uwa a ikilisiya kuma ka yi tambaya, ‘Shin akwai wanda yake bukatar taimakona?’ Jehobah yana farin ciki sa’ad da ya ga muna amfani da ƙarfinmu da ƙwarewarmu da dukiyarmu da kuma lokacinmu don taimaka ma ’yan’uwa da suke da bukata. Yana ɗaukan hakan a matsayin ibada.—Yak. 1:27.

BAUTA WA JEHOBAH YANA SA MU FARIN CIKI

15. Bauta wa Jehobah yana bukatar lokacinmu da kuma ƙarfinmu, amma me ya sa hakan bai fi ƙarfinmu ba?

15 Muna bukatar mu yi amfani da lokacinmu da kuma ƙarfinmu kafin mu iya bauta wa Jehobah da kyau. Amma hakan bai fi ƙarfinmu ba. (1 Yoh. 5:3) Me ya sa? Domin ƙauna ce take sa mu bauta wa Jehobah. Ka yi tunanin wani ƙaramin yaro da yake so ya ba babansa kyauta. Yaron zai iya ɗaukan awoyi da yawa yana zana masa hoto. Wannan yaron ba zai yi da-na-sani don lokacin da ya yi amfani da shi wajen yin zanen ba domin yana ƙaunar babansa kuma yana farin cikin ba shi kyautar. Hakazalika, muna farin cikin yin amfani da ƙarfinmu da kuma lokacinmu wajen bauta wa Jehobah domin muna ƙaunarsa sosai.

16. Bisa ga Ibraniyawa 6:10, yaya Jehobah yake ɗaukan ƙoƙarin da muke yi mu faranta masa rai?

16 Iyaye da suke ƙaunar yaransu ba za su sa rai cewa duka yaran za su ba su kyaututtuka iri ɗaya ba. Sun san yaran sun bambanta kuma dukansu ba za su iya yin abu iri ɗaya ba. Haka ma Ubanmu na sama ya san abin da kowannenmu zai iya yi. Mai yiwuwa za ka iya yin abubuwa fiye da wasu da ka sani kuma kake ƙaunar su. Ko kuma ba ka iya yin abubuwa kamar yadda wasu suke yi saboda tsufa, rashin lafiya ko hakkin kula da iyalinka. Kada ka yi sanyin gwiwa. (Gal. 6:4) Jehobah ba zai manta da aikin da kake yi ba. Muddin kana yin iya ƙoƙarinka kuma kana yin hakan da manufa mai kyau, zai yi farin ciki da kai. (Karanta Ibraniyawa 6:10.) Jehobah ya ma san abin da za ka so ka yi masa. Yana so ka yi farin ciki kuma ka gamsu da abin da za ka iya yi a bautarsa.

17. (a) Idan yana mana wuya mu yi wasu ayyukan ibada, me za mu iya yi? (b) Ta yaya yin ɗaya daga cikin abubuwa da aka nuna a cikin akwatin nan, “ Abin da Zai Sa Ka Daɗa Farin Ciki” ya taimaka maka?

17 Idan yana mana wuya mu yi ɗaya daga cikin abubuwan nan fa, kamar yin nazarin Littafi Mai Tsarki ko wa’azi? Mai yiwuwa idan muka yi abubuwan nan a kai a kai, za mu ga cewa za mu ji daɗin yin su kuma za mu amfana sosai. Za mu iya kwatanta ibadarmu da abubuwa kamar motsa jiki ko kuma koyan wani kayan kiɗa. Idan muna yin hakan jifa-jifa, zai iya yi mana wuya mu koyi yin su da kyau. Amma idan muka fara yin su a kullum, za mu iya yin su da kyau. Da farko za mu iya yin su na ’yan mintoci kawai, amma a hankali a hankali za mu iya ƙara yawan lokacin da muke ɗaukawa mu yi su. Idan mun ga sakamako mai kyau da muke samu, za mu iya jin daɗin yin abin sosai. Haka ma yake da bautarmu ga Jehobah.

18. Mene ne abu mafi muhimmanci da za mu iya yi, kuma me zai faru idan muka yi hakan?

18 Yin iya ƙoƙarinmu mu bauta wa Jehobah shi ne abu mafi muhimmanci da za mu iya yi. Yin hakan yana sa mu yi farin ciki, mu sami gamsuwa a rayuwa, kuma mu kasance da begen bauta wa Jehobah har abada. (K. Mag. 10:22) Muna samun kwanciyar hankali don mun san cewa Jehobah yana taimaka wa masu bauta masa a duk lokacin da suke cikin matsala. (Isha. 41:9, 10) Hakika, muna da dalilai masu yawa na yin farin ciki yayin da muke bauta wa Ubanmu mai ƙauna, wanda ya ‘cancanci ya karɓi ɗaukaka, da girma’ daga dukan halittunsa.—R. Yar. 4:11.

WAƘA TA 24 Ku Zo Tudun Jehobah

^ sakin layi na 5 A matsayin Mahaliccin kome da kome, Jehobah ya cancanci mu bauta masa. Zai amince da abubuwa da muke yi yayin da muke bauta masa idan muna bin umurninsa kuma muna yin rayuwar da ta jitu da ƙa’idodinsa. A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa takwas da muke yi yayin da muke bauta wa Jehobah. Za mu koyi yadda za mu inganta hanyoyin da muke yin abubuwan nan da yadda za su sa mu farin ciki.