Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 18

Yadda Za Mu Iya Kafa da Kuma Cim ma Makasudai a Hidimarmu

Yadda Za Mu Iya Kafa da Kuma Cim ma Makasudai a Hidimarmu

“Ka aikata waɗannan abubuwan cikin aikinka, ka miƙa kanka gaba ɗaya gare su, domin kowa ya ga ci gabanka.”​—1 TIM. 4:15.

WAƘA TA 84 Yin Hidima a Inda Akwai Bukata

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Waɗanne irin maƙasudai ne za mu iya kafawa a hidimarmu?

 MU KIRISTOCI na gaskiya muna ƙaunar Jehobah sosai. Muna so mu bauta masa da iya ƙarfinmu. Amma don mu iya yin hakan, muna bukatar mu kafa maƙasudai, kamar yadda za mu kasance da halaye masu kyau, da koyan yin wasu abubuwa da kuma neman hanyoyin da za mu taimaka ma wasu.

2. Me ya sa ya dace mu kafa maƙasudai kuma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu cim ma su?

2 Me ya sa ya dace mu kyautata yadda muke bauta ma Jehobah? Babban dalilin shi ne don muna so mu faranta masa rai. Jehobah yana farin ciki a duk lokacin da ya ga cewa muna amfani da baiwarmu don mu bauta masa da dukan zuciyarmu. Wani dalilin kuma shi ne, don mu daɗa iya taimaka ma ’yan’uwanmu maza da mata. (1 Tas. 4:​9, 10) Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah, dukanmu muna bukatar mu daɗa kyautata yadda muke bauta masa. Bari mu ga yadda za mu yi hakan.

3. Bisa ga 1 Timoti 4:​12-16, me manzo Bulus ya ƙarfafa Timoti ya yi?

3 Ko da yake Timoti matashi ne a lokacin da manzo Bulus ya rubuta masa wasiƙa, Timoti ya jima da zama dattijo. Duk da haka, Bulus ya ƙarfafa shi ya ci gaba da kyautata yadda yake bauta wa Jehobah. (Karanta 1 Timoti 4:​12-16.) Idan ka yi tunani a kan shawarar Bulus, za ka lura cewa yana so Timoti ya inganta hidimarsa a hanyoyi biyu. Na ɗaya, ta wajen kasancewa da halaye masu kyau kamar ƙauna, bangaskiya, da kuma tsabta a ɗabi’arsa. Na biyu, ta kyautata yadda yake karatu ga jama’a da yadda yake ba da gargaɗi da kuma yadda yake koyarwa. Za mu tattauna misalin Timoti don mu ga yadda kafa maƙasudai da suka dace zai taimaka mana mu ci gaba da inganta yadda muke bauta wa Jehobah. Za mu kuma ga hanyoyi da za mu iya daɗa ƙwazo a hidimarmu.

KA KASANCE DA HALAYE MASU KYAU

4. Bisa ga Filibiyawa 2:​19-22, me ya sa Jehobah ya yi amfani da Timoti sosai?

4 Me ya sa Jehobah ya yi amfani da Timoti sosai? Ya yi hakan ne domin halayen Timoti masu kyau. (Karanta Filibiyawa 2:​19-22.) Abin da Bulus ya faɗa game da Timoti ya nuna mana cewa shi mai sauƙin kai ne, mai aminci ne, mai ƙwazo ne kuma za a iya yarda da shi. Yana nuna ma ’yan’uwa ƙauna kuma yana kula da su. Hakan ya sa Bulus ya ƙaunaci Timoti kuma bai yi shakkar ba shi ayyuka masu wuya ba. (1 Kor. 4:17) Haka ma idan mun kasance da irin halayen da Jehobah yake so, zai ƙaunace mu kuma za mu taimaka ma ’yan’uwanmu a ikilisiya.​—Zab. 25:9; 138:6.

Ka zaɓi hali ɗaya da kake so ka daɗa kasancewa da shi (Ka duba sakin layi na 5-6)

5. (a) Ta yaya za ka san halin da ya kamata ka kyautata yadda kake nunawa? (b) Kamar yadda muka gani a hoton, ta yaya ’yar’uwar take ƙoƙarin cim ma maƙasudinta na nuna wa mutane tausayi?

5 Ka zaɓi takamaiman maƙasudi. Ka yi addu’a kuma ka tambayi kanka, wanne ne cikin halayenka yake bukatar gyara? Ka zaɓi ɗaya da za ka kyautata yadda kake nunawa. Alal misali, za ka iya zaɓan ka koyi yadda za ka riƙa nuna tausayi ko yadda za ka kasance da marmarin taimaka ma ’yan’uwa. Za ka kuma iya koyan yadda za ka yi zaman lafiya da mutane da gafarta wa mutane. Wani abu da zai iya taimaka maka shi ne, ka tambayi abokinka ya gaya maka inda kake bukatar ka kyautata halinka.​—K. Mag. 27:6.

6. Ta yaya za ka iya cim ma maƙasudinka na kasancewa da wani hali mai kyau?

6 Ka yi iya ƙoƙarinka don ka cim ma maƙasudinka. Ta yaya za ka iya yin hakan? Hanya ɗaya ita ce yin nazarin halin da kake so ka kyautata yadda kake nuna shi. A ce kana so ka daɗa zama mai gafartawa. Za ka iya yin hakan ta wajen yin nazari da kuma bimbini a kan mutane a Littafi Mai Tsarki da suka gafarta ma wasu da waɗanda ba su yi hakan ba. Ka yi la’akari da misalin Yesu. Ya gafarta wa mutane da dukan zuciyarsa. (Luk. 7:​47, 48) Maimakon ya mai da hankali ga kurakuransu, ya mai da hankali ga abin da za su iya yi. Amma Farisawa a zamanin Yesu sukan “rena . . . mutane.” (Luk. 18:9) Bayan ka yi tunani a kan misalan nan, ka tambayi kanka: ‘Yaya nake ɗaukan mutane? Waɗanne halayensu ne nake mai da hankali a kai?’ Idan yana yi maka wuya ka gafarta ma wani, ka yi ƙoƙari ka rubuta halaye masu kyau na mutumin. Sai ka tambayi kanka, ‘Yaya Yesu yake ɗaukan wannan mutumin? Shin zai gafarta masa?’ Idan mun yi hakan, za mu canja yadda muke ɗaukan mutane. Da farko, ba zai yi mana sauƙi mu gafarta ma wanda ya yi mana laifi ba. Amma idan mun ci gaba da koyan yadda za mu gafarta wa mutane, a kwana a tashi, zai yi mana sauƙi mu yi hakan.

KA KOYI YADDA ZA KA YI WASU ABUBUWA

Ka ba da kanka ka koya yadda za ka kula da Majami’ar Mulki (Ka duba sakin layi na 7) *

7. Bisa ga Karin Magana 22:​29, a wace hanya ce Jehobah yake amfani da ƙwararrun masu aikin hannu?

7 Wani maƙasudi kuma da za ka iya kafawa shi ne yadda za ka koyi yin wasu abubuwa. Ka yi tunanin yawan ma’aikata da ake bukata don a gina ofisoshinmu, da Majami’un Manyan Taro da Majami’un Mulki. Yawancin ma’aikatan sun koyi aikin daga ’yan’uwa maza da mata da suka ƙware a yin aikin. Kamar yadda muka gani a hoton, ’yan’uwa maza da mata suna koyan aikin hannu da zai taimake su su iya kula da Majami’un Mulki da Majami’un Manyan Taro. Ta wannan hanyar da kuma wasu hanyoyi, Jehobah wanda shi ne “Sarkin zamanai,” da kuma Yesu Kristi wanda shi ne “Sarkin Sarakuna,” suna cim ma abubuwa masu muhimmanci ta wurin waɗannan ƙwararrun ma’aikata. (1 Tim. 1:17; 6:15; karanta Karin Magana 22:29.) Muna so mu yi aiki da ƙwazo kuma mu yi amfani da ƙwarewarmu mu ɗaukaka Jehobah, ba kanmu ba.​—Yoh. 8:54.

8. Ta yaya za ka iya sanin abin da ya kamata ka ƙware a yin sa?

8 Ka zaɓi takamaiman maƙasudi. Wane abu ne ya kamata ka mai da hankali a kai? Ka tambayi dattawan ikilisiyarku ko mai kula da da’ira abin da kake bukata ka ƙware a yin sa. Alal misali, idan sun ce kana bukatar ka ƙware a yadda kake jawabi da kuma koyarwa, ka tambaye su takamaiman abin da kake bukatar ka yi don ka ƙware. Sai ka yi iya ƙoƙarinka don ka ƙware a yin sa. Me zai taimake ka?

9. Me za ka iya yi don ka cim ma maƙasudinka?

9 Ka yi iya ƙoƙarinka don ka cim ma maƙasudinka. A ce kana so ka ƙware a yadda kake koyarwa. Za ka iya yin nazarin ƙasidar nan Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa. Idan aka ba ka jawabi a taron tsakiyar mako, za ka iya tambayar ɗan’uwan da ya ƙware ya saurari yadda za ka gudanar da jawabin kuma ya ba ka shawara. Ka shirya jawabin da aka ba ka tun da wuri don mutane su ga ƙoƙarin da kake yi kuma su san cewa za a iya dogara da kai.​—K. Mag. 21:5; 2 Kor. 8:22.

10. Ka ba da misalin yadda za mu iya koyan wani abu da kyau.

10 Me za ka iya yi idan maƙasudinka shi ne ka ƙware a yin abin da yake yi maka wuya? Kada ka karaya. Wani ɗan’uwa mai suna Garry bai iya karatu sosai ba. Ya tuna yadda ya sha kunya sosai a lokacin da ya yi ƙoƙari ya yi karatu a ikilisiya. Amma ya ci gaba da koya. Ya ce saboda horarwar da ya samu, yanzu yana iya ba da jawabi a ikilisiya da manyan taro!

11. Kamar Timoti, me zai taimaka mana mu sami ƙarin ayyuka a ƙungiyar Jehobah?

11 Shin daga baya Timoti ya ƙware a yin jawabi ko koyarwa ne? Littafi Mai Tsarki bai faɗi kome a kan batun nan ba. Amma babu shakka, shawarar da Bulus ya ba ma Timoti ya taimaka masa ya ci gaba da kyautata yadda yake yin hidimarsa. (2 Tim. 3:10) Haka ma, idan mun ƙware a abubuwan da muke yi, za mu iya yin ayyuka da yawa a ƙungiyar Jehobah.

KA NEMI HANYOYIN TAIMAKA MA WASU

12. Ta yaya ka amfana daga ayyukan da wasu suke yi?

12 Akwai abubuwan da wasu suke yi don su taimaka mana. Alal misali, idan muna asibiti, mukan yi farin ciki sa’ad da dattawa da ke Kwamitin Hulɗa da Asibitoci ko Rukunin Ziyartar Majiyyata suka ziyarce mu. Sa’ad da muke fama da matsaloli, mukan yi farin ciki idan wani dattijo ya saurare mu da kyau kuma ya ƙarfafa mu. A lokacin da muke bukatar taimako a yadda za mu gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki, mukan yi farin ciki idan wani majagaba da ya ƙware ya bi mu wurin ɗalibinmu kuma ya ba mu shawarwari. Duka ’yan’uwa maza da matan nan suna farin cikin taimaka mana. Mu ma za mu yi farin ciki idan muka nemi hanyoyin taimaka ma ’yan’uwanmu. Yesu ya ce: “Ya fi albarka a bayar da a karɓa.” (A. M. 20:35) Idan kana so ka ƙara ƙwazo a waɗannan hanyoyin, ko a wasu hanyoyi dabam, me zai taimake ka ka cim ma maƙasudinka?

13. Yayin da muke kafa maƙasudi, me ya kamata mu tuna?

13 Ka kafa takamaiman maƙasudi. Alal misali, idan ka ce ‘Ina so in daɗa ƙwazo a ikilisiya,’ hakan zai iya yi maka wuya idan ba ka kafa takamaiman maƙasudi ba. Zai ma iya yi maka wuya ka san lokacin da ka cim ma maƙasudin. Don haka, ka zaɓi takamaiman maƙasudi. Za ka iya rubuta maƙasudin da kuma yadda kake so ka cim ma shi.

14. Me ya sa ya kamata mu kasance a shirye mu canja maƙasudinmu?

14 Mu kasance a shirye mu canja maƙasudanmu idan da bukata. Me ya sa? Domin ba mu san yadda yanayinmu zai kasance ba. Ga misalin da ya nuna hakan: Manzo Bulus ya taimaka wajen kafa sabon ikilisiya a birnin Tasalonika. Kuma babu shakka ya so ya zauna a wurin don ya taimaka ma sabbin Kiristoci da ke wurin. Amma ’yan hamayya sun sa Bulus ya gudu ya bar birnin. (A. M. 17:​1-5, 10) Da a ce Bulus ya ci gaba da zama a birnin, da ya sa ’yan’uwansa a cikin haɗari. Amma Bulus bai karaya ba. A maimakon haka, ya canja abin da ya yi niyyar yi saboda yanayin da ya sami kansa a ciki. Daga baya, ya aiki Timoti ya je ya ƙarfafa sabbin Kiristoci da ke Tasalonika. (1 Tas. 3:​1-3) Babu shakka, ’yan’uwan da ke Tasalonika sun yi farin ciki sosai don yadda Timoti ya yarda ya yi musu hidima!

15. Ta yaya yanayin da ba mu yi tsammaninsa ba zai iya shafan maƙasudin da muka kafa? Ka ba da misali.

15 Za mu iya koyan darasi daga abin da ya faru da Bulus a Tasalonika. Mai yiwuwa mun kafa wani maƙasudi amma yanayinmu ya hana mu cim ma maƙasudin. (M. Wa. 9:11) Idan haka yanayinka yake, ka kasance a shirye ka zaɓi wani maƙasudi dabam da za ka iya cim ma. Abin da wasu ma’aurata masu suna Ted da Hiedi suka yi ke nan. Sun bar Bethel saboda ɗayansu yana rashin lafiya. Amma da yake suna ƙaunar Jehobah, sai suka nemi wasu hanyoyi da za su ƙara ƙwazo a hidimarsu. Da farko, sun soma yin hidimar majagaba. Daga baya, an naɗa su a matsayin majagaba na musamman kuma an horar da Ted a matsayin mataimakin mai kula da da’ira. Bayan haka, sai aka saka shekarar da idan mutum ya kai ba zai iya ci gaba da hidimar mai kula da da’ira ba. Sai Ted da Hiedi suka gane cewa ba za su iya ci gaba da wannan hidimar ba. Ko da yake hakan ya sa su baƙin ciki, sun gaya wa kansu cewa za su iya bauta wa Jehobah a wasu hanyoyi. Ted ya ce: “Mun koyi cewa za mu iya bauta wa Jehobah a hanyoyi dabam-dabam.”

16. Wane darasi ne za mu iya koya daga Galatiyawa 6:4?

16 Wasu abubuwa za su iya faruwa a rayuwarmu da ba za mu iya hana su faruwa ba. Don haka, bai kamata mu yi tunani cewa irin hidimar da muke yi ne zai sa mu kasance da daraja a gaban Jehobah ba kuma bai kamata mu gwada hidimarmu da na wasu ba. Hiedi ta bayyana cewa: “Idan kana gwada kanka da wasu, za ka daina yin farin ciki.” (Karanta Galatiyawa 6:4.) Yana da muhimmanci mu nemi hanyoyi da za mu iya taimakawa a ƙungiyar Jehobah. *

17. Ta yaya za ka iya cim ma maƙasudinka na samun ƙarin aiki a ƙungiyar Jehobah?

17 Za ka iya samun ƙarin ayyuka a ƙungiyar Jehobah idan kana yin rayuwa mai sauƙi kuma ka guji cin bashi. Ka kafa maƙasudan da za ka iya cim ma a cikin ƙanƙanin lokaci da za su taimaka maka ka iya kafa wanda za ka iya cim ma na dogon lokaci. Alal misali, idan kana so ka zama majagaba na kullum, za ka iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a kai a kai. Idan maƙasudinka shi ne ka zama bawa mai hidima, za ka iya ƙara ƙwazo a yin wa’azi kuma ka riƙa ziyartar ’yan’uwan da ke rashin lafiya da waɗanda suka tsufa a ikilisiyarku. Darussan da ka koya a yanzu, za su taimaka maka ka iya samun ƙarin ayyuka a nan gaba. Ka ƙudiri niyyar yin iya ƙoƙarinka a duk wani aiki da aka ba ka.​—Rom. 12:11.

Ka zaɓi takamaiman maƙasudin da za ka iya cim ma (Ka duba sakin layi na 18) *

18. Mene ne muka koya daga misalin Beverley? (Ka kuma duba hoton)

18 Kome tsufanmu, za mu iya kafa maƙasudai kuma mu cim ma su. Ka yi la’akari da misalin wata ’yar’uwa mai shekara 75 wadda sunanta Beverley. Tana fama da rashin lafiya da ke sa yin tafiya ya yi mata wuya. Amma ta so ta ƙara ƙwazo a wa’azi na musamman da aka yi a lokacin Tunawa da Mutuwar Yesu. Sai ta kafa takamammun maƙasudai. Da Beverley ta iya cim ma maƙasudanta, ta yi farin ciki sosai. Ƙoƙarin da ta yi ya ƙarfafa wasu ma su daɗa ƙwazo a yin wa’azi. Jehobah yana farin ciki domin aikin da ’yan’uwanmu tsofaffi suke yi, ko da ba sa iya yi da yawa don yanayinsu.​—Zab. 71:​17, 18.

19. Waɗanne irin maƙasudai ne za mu iya kafa a hidimarmu?

19 Ka kafa maƙasudai da za ka iya cim ma su. Ka koyi halaye da za su sa Jehobah ya ƙaunace ka sosai. Ka koyi yin wasu abubuwa da za su sa Jehobah ya yi amfani da kai kuma ka iya taimaka wa ƙungiyarsa. Ka nemi hanyoyi da za ka iya daɗa taimaka ma ’yan’uwanka. * Kamar yadda Jehobah ya taimaka ma Timoti, haka ma zai taimaka maka “domin kowa ya ga ci gabanka.”​—1 Tim. 4:15.

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

^ Timoti ya ƙware sosai a yin wa’azin Mulkin Allah. Duk da haka, manzo Bulus ya ƙarfafa shi ya ci gaba da kyautata yadda yake bauta wa Jehobah. Da yake Timoti ya bi shawarar Bulus, Jehobah ya daɗa amfani da shi kuma Timoti ya iya taimaka ma ’yan’uwansa Kiristoci sosai. Shin kai ma kana so ka bauta ma Jehobah da kyau kuma ka taimaka ma ’yan’uwanka kamar Timoti? Babu shakka, kana so ka yi hakan. Waɗanne maƙasudai ne za su iya taimaka maka ka yi hakan? Kuma me kake bukatar ka yi don ka iya kafa da kuma cim ma maƙasudan?

^ Ka duba jigon nan “Serving Where the Need Is Greater” a littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, babi na 10, sakin layi na 6-9 a Turanci.

^ Ka duba darasi na 60 mai jigo “Ka Ci Gaba da Ƙarfafa Dangantakarka da Jehobah” a littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!

^ BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa yana koya wa ’yan’uwa mata guda biyu yadda za su iya kula da Majami’ar Mulki kuma sun soma amfani da abin da suka koya.

^ BAYANI A KAN HOTO: Wata ’yar’uwa da ba ta iya barin gida saboda rashin lafiya tana yin nasara a yin wa’azi ta waya kuma tana gayyatar mutane zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu.