Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Idan Kirista ya kashe aurensa ba bisa ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ba kuma ya sake yin aure, yaya ya kamata ikilisiya ta ɗauki aurensa na dā da kuma sabon aurensa?

A irin wannan yanayin, sa’ad da mutumin ya sake yin aure, a idon ikilisiya tsohon auren ya riga ya mutu, sabon auren kuma ya kafu. Don mu fahimci dalilin da ya sa muka faɗi hakan, bari mu tattauna abin da Yesu ya faɗa game da kashe aure da kuma sake yin aure.

A Matiyu 19:​9, Yesu ya faɗi dalili ɗaya da zai sa a iya kashe aure. Ya ce: “Duk wanda ya saki matarsa, idan dai ba saboda an same ta da yin zina ba, ya kuma aure wata, ya yi zina.” Abin da Yesu ya faɗa ya koya mana cewa (1) zina ne kawai zai iya sa ma’aurata su kashe aurensu, kuma (2) idan mutum ya saki matarsa ba tare da wannan dalilin ba kuma ya sake auran wata, ya yi zina. *

Shin abin da Yesu ya faɗa yana nufin mutumin da ya yi zina kuma ya saki matarsa zai iya yin aure bisa ga ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki? Ya dangana ne ga matakin da matar ta ɗauka. Idan maigida ya yi zina, matar da ya ci amanarta za ta yanke shawarar ko za ta gafarta masa ko a’a. Idan ta ƙi gafarta masa kuma ta kashe aurensu, kowannensu zai iya sake yin aure bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.

A wani ɓangaren kuma, matan za ta iya so ta ci gaba da zama da maigidanta kuma ta ce za ta gafarta masa. Amma me zai faru idan maigidan ya ƙi amincewa da gafarar matarsa, kuma ya je ya kashe auren da kansa? Da yake tana so ta gafarta masa kuma su ci gaba da zaman aurensu, ba zai iya sake yin aure bisa ga ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. Idan maigidan ya je ya sake yin aure ba bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba, ya sake yin zina ke nan, kuma dattawa za su sake kafa masa kwamitin shari’a don zunubinsa.​—1 Kor. 5:​1, 2; 6:​9, 10.

Idan mutum ya sake yin aure ba bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba, yaya ikilisiya za ta ɗauki aurensa na dā da kuma sabon aurensa? Shin bisa ga ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki aurensa na dā bai mutu ba? Shin har ila matarsa ta dā za ta iya gafarta masa ko ta ƙi gafarta masa? Shin ikilisiya za ta riƙa ɗaukan sabon auren a matsayin zina kawai suke yi?

A dā ikilisiya tana ɗaukan sabon auren a matsayin zina kawai suke yi muddin matarsa ta dā tana da rai, ba ta sake yin aure ba, kuma ba ta yi zina ba. Amma sa’ad da Yesu yake tattauna batun kashe aure da sake yin aure, bai ambata wadda aka ci amanarta ba. Amma ya ambata cewa mutumin da ya saki matarsa ba tare da ta yi zina ba kuma ya sake yin aure, ya yi zina. A irin wannan yanayin, mutumin ya yi zina sa’ad da ya saki matarsa kuma ya sake yin aure, don haka, aurensa na dā ya mutu.

“Duk wanda ya saki matarsa, idan dai ba saboda an same ta da yin zina ba, ya kuma aure wata, ya yi zina.”​—Mat. 19:9.

Idan mutum ya kashe aurensa kuma ya sake yin aure, matarsa ta dā, wadda ya ci amanarta, ba za ta iya ce za ta gafarta masa ko ta ƙi gafarta masa ba. Don haka, matar ba za ta ɓata lokaci tana tunanin ko za ta gafarta masa ko ba za ta gafarta masa ba. Ban da haka, ko da matarsa ta dā ta mutu, ta sake yin aure, ko ta yi zina, hakan ba zai shafi yadda ikilisiya take ɗaukan sabon auren ba. *

A misalin da muka ambata, maigidan ya yi zina, kuma hakan ya sa suka kashe aurensu. To me zai faru idan maigidan bai yi zina ba, amma ya kashe aurensu kuma ya sake yin aure? Ko kuma idan maigidan bai yi zina ba kafin ya kashe auren, amma ya yi hakan bayan ya kashe auren kuma ya sake yin aure duk da cewa matarsa ta dā ta so ta gafarta masa? A yanayoyi biyun nan, sa’ad da maigidan ya kashe aurensa kuma ya sake yin aure, ya yi zina ne. Don haka, aurensa na dā ya mutu. Sabon auren ya jitu da dokar ƙasa. Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 1979, shafi na 32 ya ce, “yanzu maigidan ya yi sabon aure. Don haka, ba zai iya komawa ga matarsa ta dā ba domin auren ya riga ya mutu saboda kashe auren da zina da sake aure da ya yi.”

Wannan canjin da muka yi, ba ya nufin cewa Kiristoci sun daina ɗaukan aure da tsarki, ko kuma cewa zina ba zunubi mai tsanani ba ne. Idan mutum ya kashe aurensa ba bisa ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ba kuma ya sake yin aure, za a kafa masa kwamitin shari’a domin ya yi zina. (Idan matar da ya aura Kirista ce, ita ma za a kafa mata kwamitin shari’a domin ta yi zina.) Ko da yake ba za a riƙa ɗaukan sabon auren a matsayin zina ba, maigidan ba zai cancanci yin ayyuka a ikilisiya ba har tsawon shekaru da yawa, ko har sai mutane sun daina fushi don abin da ya yi. Kafin a amince ya yi wasu ayyuka a ikilisiya, dattawa za su yi la’akari da yanayin matarsa da ya ci amanarta, ko kuma yara da mai yiwuwa maigidan ya yi banza da su.​—Mal. 2:​14-16.

Saboda mummunan sakamakon kashe aure, da sake yin aure ba bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba, zai dace Kiristoci su yi koyi da Jehobah kuma su ɗauki aure a matsayin abu mai tsarki sosai.​—M. Wa. 5:​4, 5; Ibran. 13:4.

^ Don bayanin ya yi mana sauƙi, za mu yi amfani da namiji a matsayin wanda ya yi zina, mace kuma a matsayin wadda aka ci amanarta. Amma kamar yadda yake a Markus 10:​11, 12, Yesu ya nuna cewa wannan gargaɗin ya shafi maza da mata.

^ Wannan bayanin ya canja yadda muka fahimci batun nan a dā, cewa ikilisiya za ta ɗauki sabon auren a matsayin zina kawai suke yi, har sai matarsa ta dā ta mutu, ta sake yin aure, ko ta yi zina.