Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 16

Bauta wa Jehobah da Iya Karfinka Zai Sa Ka Farin Ciki

Bauta wa Jehobah da Iya Karfinka Zai Sa Ka Farin Ciki

“Bari kowa ya gwada aikinsa ya gani.”​—GAL. 6:4.

WAƘA TA 37 Mu Riƙa Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciya

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne yake sa mu farin ciki sosai?

 JEHOBAH yana so mu yi farin ciki. Mun san hakan domin farin ciki yana ɗaya daga cikin halayen da ruhu mai tsarki yake haifarwa. (Gal. 5:22) Da yake bayarwa tana sa farin ciki fiye da karɓa, za mu yi farin ciki idan muna yin ayyukan ibada ko kuma muna taimaka ma ’yan’uwanmu a hanyoyi dabam-dabam.​—A. M. 20:35.

2-3. (a) Waɗanne abubuwa biyu ne a Galatiyawa 6:4 za su taimaka mana mu ci gaba da yin farin ciki? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 A Galatiyawa 6:​4, manzo Bulus ya ambata abubuwa biyu da za su taimaka mana mu ci gaba da yin farin ciki. (Karanta.) Na farko, zai dace mu kafa maƙasudin bauta ma Jehobah da dukan zuciyarmu. Idan muna bauta masa da dukan zuciyarmu, ya kamata mu yi farin ciki. (Mat. 22:​36-38) Na biyu, zai dace mu guji gwada kanmu da wasu. Ko da mene ne muke iya yi saboda lafiyar jiki da muke da shi, da koyarwa da muka samu da kuma baiwa da muke da ita, ya kamata mu gode wa Jehobah domin shi ne ya ba mu kome da kome. A wani ɓangaren kuma, idan wasu sun fi mu iya wa’azi a wani fanni, zai dace mu yi farin ciki domin suna yin amfani da baiwarsu su bauta ma Jehobah, ba don su ɗaukaka kansu ba. Don haka, a maimakon mu gwada kanmu da su, zai dace mu yi koyi da su.

3 A wannan talifin, za mu ga abin da zai taimaka mana idan muna damuwa domin ba ma iya bauta ma Jehobah yadda muke so. Za mu kuma tattauna yadda za mu iya amfani da duk wata baiwa da muke da ita da kyau da kuma abin da za mu iya koya daga misalin wasu.

IDAN MUNA GANIN KAMAR ƘARFINMU YA KASA

Idan muna yin iya ƙoƙarinmu a duk rayuwarmu, Jehobah zai farin ciki (Ka duba sakin layi na 4-6) *

4. Wane abu ne zai iya sa mu sanyin gwiwa? Ka ba da misali.

4 Wasu bayin Jehobah ba za su iya yin wasu abubuwan da suke so su yi a ibadarsu ba saboda tsufa ko rashin lafiya, kuma hakan yakan sa su sanyin gwiwa. Abin da ya faru da Carol ke nan. Ta taɓa yin hidima a inda ake bukatar masu shela. A lokacin, ta yi nazari da mutane 35 kuma ta taimaka wa mutane da yawa su yi baftisma. Carol ta cim ma abubuwa da yawa a hidimarta! Amma sai ta soma rashin lafiya, kuma hakan ya sa ba ta yawan fita daga gida! Ta ce: “Na san rashin lafiyana ne yake hana ni yin abubuwan da wasu suke yi. Duk da haka, nakan ji kamar ban kai su aminci ba. Da yake ba na iya yin abubuwan da nake so in yi, nakan yi sanyin gwiwa.” Carol tana so ta yi iya ƙoƙarinta a bauta ma Jehobah. Hakan yana da kyau! Mun tabbata cewa Ubanmu mai tausayi yana farin ciki don abin da take yi.

5. (a) Me ya kamata mu tuna idan muna sanyin gwiwa domin kasawarmu? (b) Kamar yadda muka gani a hotunan, ta yaya ɗan’uwan ya ci gaba da bauta ma Jehobah da duka ƙarfinsa?

5 Idan a wasu lokuta kakan yi baƙin ciki domin kasawarka, ka tambayi kanka, ‘Mene ne Jehobah yake bukata daga gare ni?’ Yana so ka yi iya ƙoƙarinka ne. Ka yi la’akari da wannan misalin: A ce wata ’yar’uwa mai shekara 80 tana sanyin gwiwa domin ba ta iya yin abubuwan da take yi sa’ad da take shekara 40. Ko da yake tana yin iya ƙoƙarinta, a ganinta hakan ba ya faranta wa Jehobah rai. Amma hakan gaskiya ne? Ka yi la’akari da wannan. Idan ’yar’uwar ta yi iya ƙoƙarinta a bauta ma Jehobah sa’ad da take shekara 40, kuma tana yin iya ƙoƙarinta yanzu da take shekara 80, hakan yana nufin cewa ba ta daina yin iya ƙoƙarinta a bautar Jehobah ba. Idan mun soma ji kamar ibadarmu ba ta faranta ma Jehobah rai, zai dace mu tuna wa kanmu cewa Jehobah ne zai zaɓi abin da zai faranta masa rai, ba mu ba. Idan mun yi iya ƙoƙarinmu, Jehobah zai yi farin ciki.​—Ka duba misalin da ke Matiyu 25:​20-23.

6. Me za mu iya koya daga misalin Maria?

6 Za mu iya ci gaba da farin ciki idan mun mai da hankali a kan abubuwan da za mu iya yi, maimakon abubuwan da ba za mu iya yi ba. Ka yi la’akari da wata ’yar’uwa mai suna Maria, wadda ba ta iya yin wa’azi sosai saboda rashin lafiya. Da farko, hakan ya sa ta baƙin ciki kuma ta ji kamar ba ta da amfani. Amma sai ta yi la’akari da wata ’yar’uwa a ikilisiyarsu da ba ta iya tashiwa a kan gado saboda rashin lafiya kuma ta ɗau matakin taimaka mata. Maria ta ce: “Na shirya yadda za mu riƙa yin wa’azi da ita ta waya da kuma ta wasiƙa. A duk ran da muka yi wa’azi tare, nakan yi farin ciki idan na koma gida domin na taimaka wa ’yar’uwata.” Mu ma za mu iya daɗa farin ciki idan mun mai da hankali a kan abin da za mu iya yi maimakon wanda ba za mu iya yi ba. Amma idan za mu iya yin abubuwa fiye da wasu a ibadarmu ko kuma mun ƙware sosai a wasu fannoni na ibadarmu fa?

KA YI AMFANI DA BAIWARKA!

7. Wace shawara mai kyau ce manzo Bitrus ya ba Kiristoci?

7 A wasiƙarsa ta farko, manzo Bitrus ya gaya wa ’yan’uwansa su yi amfani da baiwar da suke da ita don su ƙarfafa ’yan’uwansu. Ya rubuta cewa: ‘Allah ya ba kowa baiwar yin wani abu. Domin haka, sai ku yi amfani da baiwarku ga yin hidima ga ’yan’uwanku, a matsayinku na masu riƙon amanar alherin Allah iri iri.’ (1 Bit. 4:10) Ba zai dace mu ƙi amfani da baiwarmu domin muna tsoron sa wasu kishi ko sanyin gwiwa ba. Idan mun yi hakan, ba za mu iya bauta ma Jehobah da iya ƙarfinmu ba.

8. Bisa ga 1 Korintiyawa 4:​6, 7, me ya sa ya dace mu guji yin taƙama da baiwarmu?

8 Muna bukatar mu yi amfani da baiwarmu, amma dole ne mu yi hankali don kada mu yi taƙama da ita. (Karanta 1 Korintiyawa 4:​6, 7.) Alal misali, a ce ka ƙware a samun mutane da za ka yi nazari da su. Kada ka daina yin amfani da baiwar! Amma zai dace kada mu yi taƙama da baiwarmu. A ce bai jima da ka soma nazari da wani ba, kuma kana marmarin gaya ma ’yan’uwa da ke rukunin wa’azinku. Amma sa’ad da ka haɗu da su, ka tarar da wata ’yar’uwa tana ba da labarin yadda ta ba da mujalla. Mujalla ta bayar, kai kuma ka soma nazari da wani. Me ya kamata ka yi? Ka san cewa labarinka zai ƙarfafa ’yan’uwa da ke rukunin, amma za ka iya bari sai wani lokaci dabam kafin ka ba da labarin domin kada ka sa ’yar’uwar da ta ba da mujallar ta ji wani iri. Yin hakan zai dace, amma kada ka daina yin amfani da wannan baiwar da kake da ita!

9. Yaya ya kamata mu yi amfani da baiwarmu?

9 Ya kamata mu tuna cewa Jehobah ne ya ba mu duk wata baiwa da muke da ita. Mu yi amfani da baiwar don mu ƙarfafa ’yan’uwanmu, ba don mu ɗaukaka kanmu ba. (Filib. 2:3) Idan mun yi amfani da baiwarmu da kuma ƙarfinmu don yin nufin Jehobah, za mu yi farin ciki domin muna amfani da baiwarmu don mu ɗaukaka sunan Jehobah, ba domin mun fi wasu ko kuma muna nuna iyawarmu ba.

10. Me ya sa bai dace mu gwada kanmu da wasu ba?

10 Idan ba mu yi hankali ba, za mu iya gwada iyawarmu da kasawar wasu. Alal misali, wani ɗan’uwa zai iya ƙware a ba da jawabi. Iyawarsa ke nan. Amma zai iya soma tunani kamar ya fi wani ɗan’uwa da bai ƙware a ba da jawabi ba. Amma mai yiwuwa ɗan’uwan mai bayarwa ne sosai ya iya koyar da yaransa kuma yana wa’azi da ƙwazo. Muna farin ciki sosai domin muna da ’yan’uwa da yawa da suke amfani da baiwarsu don su bauta ma Jehobah kuma su taimaka ma ’yan’uwansu!

KA KOYI DARASI DAGA MISALIN WASU

11. Me ya sa ya kamata mu ƙoƙarta mu bi misalin Yesu?

11 Ko da yake bai dace mu riƙa gwada kanmu da wasu ba, za mu iya amfana daga bin misalin wasu. Ka yi la’akari da misalin Yesu. Ko da yake shi kamili ne, za mu iya amfana daga halayensa masu kyau. (1 Bit. 2:21) Idan mun yi iya ƙoƙarinmu don mu bi misalinsa, za mu kyautata yadda muke bauta ma Jehobah da kuma yin wa’azi.

12-13. Me za mu iya koya daga Sarki Dauda?

12 A Kalmar Allah, akwai misalin maza da mata masu aminci da za mu iya yin koyi da su ko da yake su ajizai ne. (Ibran. 6:12) Ka yi la’akari da Dauda, wanda Jehobah ya ce da shi “mutum ne da nake ƙauna ƙwarai,” ko kuma kamar yadda wani juyin Littafi Mai Tsarki ya faɗa, “irin mutum da ya fi faranta mini rai.” (A. M. 13:22) Amma Dauda ba kamili ba ne, ya yi zunubai masu tsanani. Duk da haka, za mu iya bin misalinsa. Me ya sa? Domin a lokutan da aka gaya masa zunubansa, bai ba da hujjoji don ya kuɓutar da kansa ba. Amma ya amince da horo da aka yi masa, kuma ya yi nadama don abin da ya yi. Hakan ya sa Jehobah ya gafarta masa.​—Zab. 51:​3, 4, 10-12.

13 Za mu iya yin koyi da Dauda ta wajen tambayar kanmu: ‘Me nake yi idan aka yi min gargaɗi? Ina yarda cewa na yi kuskure ko kuma ina ba da hujjoji? Ina saurin ɗora ma wasu laifi? Ina yin iya ƙoƙarina don kada in maimaita kuskuren?’ Za ka iya yi wa kanka irin tambayoyin nan yayin da kake karanta game da bayin Allah a Littafi Mai Tsarki. Shin su ma sun yi fama da matsalolin da kake fama da su? Waɗanne halaye masu kyau ne suka nuna? A kowane labari, ka tambayi kanka: ‘Ta yaya zan iya yin koyi da wannan bawan Allahn?’

14. Ta yaya za mu amfana idan muka lura da misalin ’yan’uwanmu?

14 Za mu kuma amfana ta wajen lura da ’yan’uwa manya da ƙanana. Alal misali, akwai wani a ikilisiyarku da ke jimre matsaloli? Mai yiwuwa tsararsa ne ke matsa masa ko kuma yana fama da rashin lafiya? Shin ɗan’uwan yana nuna halaye masu kyau da za ka so ka yi koyi da su? Ta wajen lura da misali mai kyau da yake kafawa, kai ma za ka iya koyan yadda za ka jimre naka matsaloli. Muna farin ciki cewa akwai ’yan’uwa da suke kafa mana misali mai kyau da za mu iya bi!​—Ibran. 13:7; Yak. 1:​2, 3.

KA YI FARIN CIKI YAYIN DA KAKE BAUTA MA JEHOBAH

15. Wace shawara ce manzo Bulus ya bayar, da za ta iya taimaka mana mu ci gaba da yin farin ciki yayin da muke bauta ma Jehobah?

15 Idan muna so a sami zaman lafiya da haɗin kai a ikilisiya, kowannenmu yana bukatar ya yi iya ƙoƙarinsa a bauta ma Jehobah. Ka yi la’akari da Kiristoci a ƙarni na farko. Jehobah ya ba su baiwa da ayyuka dabam-dabam. (1 Kor. 12:​4, 7-11) Hakan bai raba kansu ko ya sa su yi gasa da juna ba. A maimakon haka, Bulus ya gaya musu cewa su yi abin da ake bukata domin “a gina jikin Almasihu.” Bulus ya rubuta wa Afisawa cewa: “Ta wurin aikin kowace gaɓa daidai jikin yake ƙara girma, yana ginuwa da halin ƙauna.” (Afis. 4:​1-3, 11, 12, 16) Da ’yan’uwa a ikilisiya suka yi abin da Bulus ya faɗa, sun sa salama da haɗin kai su kasance a ikilisiyar, kuma abin da muke gani a ikilisiyoyinmu a yau ke nan.

16. Me ya kamata mu ƙuduri niyyar yi? (Ibraniyawa 6:10)

16 Ka yi iya ƙoƙarinka don ka guji gwada kanka da wasu. Ka yi koyi da halaye masu kyau na Yesu. Ka koya daga misalin bayin Allah masu aminci a dā da yanzu. Yayin da kake ci gaba da yin iya ƙoƙarinka, ka tuna da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, cewa Jehobah “ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanku da kuka yi ba.” (Karanta Ibraniyawa 6:10.) Ka ci gaba da yin farin ciki yayin da kake bauta ma Jehobah, kuma ka tuna cewa yana farin ciki yayin da yake ganin kana iya ƙoƙarinka don ka bauta masa.

WAƘA TA 65 Mu Riƙa Samun Ci Gaba!

^ Dukanmu za mu iya amfana idan muna lura da misali mai kyau na wasu. Amma dole ne mu guji gwada kanmu da wasu. Wannan talifin zai taimaka mana mu ci gaba da farin ciki kuma mu guji girman kai ko sanyin gwiwa yayin da muka ga abubuwan da wasu suka yi.

^ BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa ya yi hidima a Bethel sa’ad da yake matashi. Da ya yi aure, ya bar Bethel kuma ya soma hidimar majagaba da matarsa. Bayan ya haifi ’ya’ya, sai ya koya musu yadda za su yi wa’azi. Yanzu da ya tsufa, yana ci gaba da yin iya ƙoƙarinsa ta wajen yin wa’azi ta wasiƙa.