Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 25

Jehobah Yana Yi ma Waɗanda Suke Gafarta wa Mutane Albarka

Jehobah Yana Yi ma Waɗanda Suke Gafarta wa Mutane Albarka

“Yadda Ubangiji ya gafarta muku zunubanku, haka ma ku ma ku gafarta wa juna.”—KOL. 3:13.

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane tabbaci ne Jehobah ya ba masu zunubi da suka tuba?

 KO DA yake Jehobah shi ne Mahaliccinmu, da Mai Ba Mu Doka, da kuma Mai Shari’a, shi Ubanmu ne mai ƙauna. (Zab. 100:3; Isha. 33:22) Idan muka yi zunubi kuma muka tuba da gaske, zai iya gafarta mana, kuma yana marmarin yin hakan. (Zab. 86:5) Ta baƙin annabi Ishaya, Jehobah ya tabbatar mana cewa: “Ko da kun yi ja wur da zunubi, za ku yi fari fat kamar auduga.”—Isha. 1:18.

2. Idan muna so mu yi zaman lafiya da mutane, me muke bukatar mu yi?

2 Da yake mu ajizai ne, mukan yi ma wasu laifi. (Yak. 3:2) Amma hakan ba ya nufin cewa ba za mu iya yin abokantaka da su ba. Za mu yi hakan idan muna gafartawa. (K. Mag. 17:9; 19:11; Mat. 18:21, 22) Idan wani ya yi abin da ya ɗan ɓata mana rai, Jehobah yana so mu gafarta wa mutumin. (Kol. 3:13) Zai dace mu yi hakan domin Jehobah “a shirye yake ya gafarce” mu.—Isha. 55:7.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 A wannan talifin, za mu tattauna yadda ʼyan Adam ajizai za su iya yin koyi da yadda Jehobah yake gafartawa. Waɗanne zunubai ne muke bukatar mu gaya wa dattawa? Me ya sa Jehobah ya ƙarfafa mu mu riƙa gafarta wa mutane? Kuma mene ne za mu iya koya daga ʼyan’uwanmu da suka sha wahala domin laifin wasu?

IDAN KIRISTA YA YI ZUNUBI MAI TSANANI

4. (a) Idan bawan Jehobah ya yi zunubi mai tsanani, me yake bukata ya yi? (b) Mene ne dattawa suke ƙoƙari su sani sa’ad da suke tattaunawa da mai zunubi?

4 Muna bukatar mu gaya wa dattawa idan wani ya yi zunubi mai tsanani. Littafin 1 Korintiyawa 6:9, 10 sun ambata wasu cikin waɗannan zunuban. Idan wani ya yi zunubi mai tsanani ya taka dokar Allah ke nan. Idan Kirista ya yi irin wannan zunubin, yana bukatar ya yi addu’a ga Jehobah, kuma ya gaya wa dattawa. (Zab. 32:5; Yak. 5:14) Wane hakki ne dattawa suke da shi? Jehobah ne kaɗai yake da hakkin gafarta zunubi gabaki ɗaya, kuma yana gafarta mana zunubanmu domin hadayar Yesu. * Amma Jehobah ya ba wa dattawa hakkin yin amfani da Littafi Mai Tsarki don su san ko ya dace a yi wa mai zunubi yankan zumunci. (1 Kor. 5:12) Ɗaya daga cikin abubuwan da zai taimaka musu shi ne yin ƙoƙari su san amsoshin tambayoyin nan: Mutumin ya yi zunubin da gangan ne? Ya yi ƙoƙari ya ɓoye zunubin ne? Ya daɗe yana yin zunubin ne? Mafi muhimmanci ma shi ne, ya nuna cewa ya tuba da gaske? Akwai abubuwan da suka nuna cewa Jehobah ya gafarta masa?—A. M. 3:19.

5. Wane sakamako ne ake samu sanadiyyar aikin da dattawa suke yi?

5 Yayin da dattawa suke tattaunawa da mutumin da ya yi zunubi, niyyarsu ita ce su yanke shawarar da ta yi daidai da wanda Jehobah ya riga ya yanke a sama. (Mat. 18:18) Ta yaya wannan shirin yake taimaka wa ʼyan’uwa a ikilisiya? Yana kāre ʼyan’uwa a ikilisiya ta wajen tabbata cewa an fitar da mai zunubin da ya ƙi tuba daga cikin ikilisiya, domin kada ya ɓata sauran ʼyan’uwa. (1 Kor. 5:6, 7, 11-13; Tit. 3:10, 11) Ƙari ga hakan, tsarin zai iya taimaka wa mai zunubi ya tuba kuma Jehobah ya gafarta masa. (Luk. 5:32) Dattawa za su yi addu’a a madadin wanda ya tuba, kuma su roƙi Jehobah ya taimaka masa domin ya gyara dangantakarsa da Jehobah.—Yak. 5:15.

6. Idan aka yi wa mutum yankan zumunci, Jehobah zai iya gafarta masa? Ka bayyana.

6 A ce mutumin da dattawa suka tuntuɓa ya ƙi tuba fa? Idan haka ne, za a yi masa yankan zumunci. Idan ya taka dokar ƙasa, dattawa ba za su kāre shi daga hukuma ba. Jehobah ya ƙyale hukumomi su yi shari’a kuma su hukunta duk wanda ya taka dokar ƙasa, ko da ya tuba ko bai tuba ba. (Rom. 13:4) Amma idan mutumin ya gane cewa abin da ya yi laifi ne, kuma ya tuba ya daina zunubin da yake yi, Jehobah yana a shirye ya gafarta masa. (Luk. 15:17-24) Jehobah zai yi hakan ko da mutumin ya yi zunubi mai tsanani sosai.—2 Tar. 33:9, 12, 13; 1 Tim. 1:15.

7. Mene ne gafarta wa mutum yake nufi?

7 Muna farin ciki cewa ba mu ne muke da hakkin tsai da shawara wa Jehobah ko zai gafarta wa mai zunubi ko ba zai gafarta masa ba! Duk da haka, akwai matakin da muke bukatar mu ɗauka. Wane mataki ke nan? A wasu lokuta, wani zai iya yi mana babban laifi kuma ya roƙe mu mu gafarta masa. Amma zai iya yiwuwa bai nemi gafarar mu ba. Duk da haka, za mu iya ɗaukan matakin gafarta wa mutumin, ta wajen daina yin fushi da shi. Gaskiyar ita ce, sai mun sa aniya kafin mu iya yafewa kuma hakan zai iya ɗaukan lokaci, musamman ma idan laifin da mutumin ya yi mana ya ɓata mana rai sosai. Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 1994, ta ce: “Idan ka gafarta wa mai zunubi, hakan ba ya nufin cewa ka amince da abin da ya yi. Kirista da ya gafarta ma wani da ya yi masa laifi, yana nuna cewa ya bar kome a hannun Jehobah. Jehobah ne mai shari’a a sama da ƙasa, kuma zai yi shari’ar adalci a lokacin da ya dace.” Me ya sa Jehobah yake ƙarfafa mu mu gafarta ma waɗanda suka yi mana zunubi, kuma mu bar kome a hannunsa?

ABIN DA YA SA JEHOBAH YAKE ƘARFAFA MU MU GAFARTA

8. Ta yaya yadda muke gafartawa yake nuna cewa muna godiya don yadda Jehobah yake nuna mana jinƙai?

8 Gafartawa tana nuna cewa muna godiya don yadda Jehobah yake nuna mana jinƙai. Akwai lokacin da Yesu ya kwatanta Jehobah da wani sarki da ya yafe wa bawansa bashi mai yawa. Amma bawan ya ƙi gafarta ma wani bawa da ya karɓi ɗan bashi daga wurinsa. (Mat. 18:23-35) Wane darasi ne Yesu yake koyarwa? Idan muna godiya don yadda Jehobah yake nuna mana jinƙai, hakan zai sa mu riƙa gafarta ma waɗanda suka yi mana laifi. (Zab. 103:9) Shekaru da yawa da suka shige, wata Hasumiyar Tsaro ta ce: “Ko da sau nawa ne muka gafarta wa mutane, ba zai kai yadda Allah yake nuna mana jinƙai da kuma gafarta mana saboda hadayar Yesu ba.”

9. Ga su waye ne Jehobah yake nuna jinƙai? (Matiyu 6:14, 15)

9 Idan muka gafarta wa mutane, Jehobah ma zai gafarta mana. Jehobah yana nuna jinƙai ga waɗanda suke nuna wa ʼyan’uwansu jinƙai. (Mat. 5:7; Yak. 2:13) Yesu ya bayyana hakan sarai a lokacin da ya koya wa mabiyansa yadda za su yi addu’a. (Karanta Matiyu 6:14, 15.) Mun koyi darasi makamancin wannan daga abin da Jehobah ya gaya wa bawansa Ayuba. Wannan mutum mai aminci ya yi baƙin ciki sosai saboda abin da Elifaz da Bildad da kuma Zofar suka gaya masa. Jehobah ya gaya wa Ayuba ya yi addu’a a madadinsu. Bayan hakan, sai Jehobah ya yi masa albarka.—Ayu. 42:8-10.

10. Me zai faru da mu idan muka riƙe mutane a zuciya? (Afisawa 4:31, 32)

10 Muna yi wa kanmu lahani idan muka riƙe mutane a zuciya. Riƙe mutum a zuciya yana kama da ɗaukan kaya mai nauyi. Jehobah yana so mu sauke kayan don mu sami kwanciyar hankali. (Karanta Afisawa 4:31, 32.) Jehobah ya ƙarfafa mu cewa mu “daina yin fushi kuma mu rabu da hasala.” (Zab. 37:8, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Bin wannan shawarar zai taimaka mana. Riƙe mutumin da ya yi mana laifi a zuciya yana iya yi mana lahani sosai. (K. Mag. 14:30) Riƙe wanda ya yi mana laifi a zuciya ba zai yi wa mai laifin kome ba, kamar yadda idan muka sha guba, mu ne za ta yi wa lahani. Saboda haka, idan muka gafarta wa mutanen da suka yi mana laifi, muna yi wa kanmu alheri ne. (K. Mag. 11:17) Yin hakan zai sa mu kasance da kwanciyar hankali kuma mu ci gaba da bauta wa Jehobah.

11. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da ramako? (Romawa 12:19-21)

11 Jehobah ne zai rama mana. Jehobah bai umurce mu mu rama laifin da wani ya yi mana ba. (Karanta Romawa 12:19-21.) Da yake mu ajizai ne kuma ba kome ne za mu iya sani ba, ba za mu iya yin shari’a kamar yadda Jehobah yake yi ba. (Ibran. 4:13) Kuma a wasu lokuta, yadda muke ji yana iya hana mu yin abin da ya dace. Jehobah ya sa Yakub ya rubuta cewa: “Fushin mutum ba ya kai shi ga aikata adalcin Allah.” (Yak. 1:20) Saboda haka, zai dace mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi abin da ya dace kuma a ƙarshe zai yi mana adalci.

Ka guji yin fushi da riƙe mutane a zuciya. Ka bar kome a hannun Jehobah. Zai kawar da dukan wahalolin da zunubi ya jawo (Ka duba sakin layi na 12)

12. Ta yaya za mu nuna cewa mun amince da yadda Jehobah yake yin shari’a?

12 Gafarta wa mutane yana nuna cewa mun amince da yadda Jehobah yake shari’a. Idan muka bar kome a hannun Jehobah, muna nuna cewa mun gaskata Jehobah zai kawar da wahalolin da zunubi ya janyo. A sabuwar duniya da ya yi alkawarinta, “ba za a sāke tunawa da abubuwan” da suka sa mu baƙin ciki ba, “tunaninsu ma ba zai zo” zuciyarmu ba. (Isha. 65:17) Amma idan wani ya yi mana laifin da ya ɓata mana rai sosai, za mu iya gafarta masa da gaske kuma mu guji riƙe shi a zuciya? Ka ga yadda wasu suka yi hakan.

ZA MU AMFANA IDAN MUNA GAFARTA WA MUTANE

13-14. Mene ne ka koya game da gafartawa daga labarin Tony da José?

13 ʼYan’uwanmu Kiristoci sun ɗau matakin gafarta ma waɗanda suka yi musu laifi duk da cewa laifin ya ci musu rai sosai. Ta yaya suka amfana daga yin hakan?

14 Shekaru da yawa kafin wani mai suna Tony * da yake zama a ƙasar Filifins ya zama Mashaidin Jehobah, ya gano cewa wani mai suna José ne ya kashe yayansa. A lokacin, Tony yana son faɗa sosai kuma ya so ya rama abin da aka yi wa yayansa. An kama José kuma aka saka shi a kurkuku domin abin da ya yi. Bayan an saki José daga kurkuku, Tony ya rantse cewa zai nemi José kuma ya kashe shi. Ya sayi bindiga domin ya yin hakan. Amma sai Tony ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Ya ce: “Yayin da nake nazari, sai na koyi cewa ina bukatar in canja salon rayuwata kuma hakan yana nufin in daina yawan fushi.” Da shigewar lokaci, Tony ya yi baftisma kuma aka naɗa shi dattijo a ikilisiya. Ya yi mamaki sosai da ya ji cewa José ma ya zama Mashaidin Jehobah! A lokacin da su biyun suka haɗu, sai suka rungumi juna, kuma Tony ya gaya wa José cewa ya gafarta masa. Tony ya ce wannan matakin da ya ɗauka ya sa shi farin ciki sosai har ba zai iya bayyana yadda yake ji ba. Jehobah ya yi wa Tony albarka sosai domin ya gafarta wa José.

Labarin Peter da Sue ya nuna mana cewa za mu iya daina yin fushi da kuma riƙe mutane a zuciya (Ka duba sakin layi na 15-16)

15-16. Me ka koya game da gafartawa daga labarin Peter da Sue?

15 A shekara ta 1985, wasu ma’aurata masu suna Peter da Sue sun halarci taro a Majami’ar Mulki, sai farat ɗaya bam ya tashi. Wani mutum ne ya saka bam a Majami’ar Mulkin! Sue ta ji rauni sosai. * Peter da Sue sukan tambayi kansu, ‘Wane irin mutum ne ya yi wannan mugun abu?’ Shekaru da yawa bayan hakan, an kama mutumin, kuma aka yi masa ɗaurin rai da rai a kurkuku. Mutumin ba Mashaidin Jehobah ba ne. Da aka tambayi Peter da Sue ko sun gafarta ma wannan mutumin sun ce: “Jehobah ya koya mana cewa idan muka riƙe mutum a zuciya, hakan zai yi mana lahani sosai. Don haka, tun da farko mun roƙi Jehobah ya taimaka mana mu guji riƙe mutumin a zuciya.”

16 Gafarta wa mutumin ya yi musu sauƙi ne? Bai yi musu sauƙi ba. Sun ce: “A duk lokacin da jikin Sue ya tashi, hakan yana sa mu fushi sosai. Amma ba ma ci gaba da tunanin abin da ya faru, don haka, muna saurin hucewa. Gaskiyar ita ce, idan wata rana mutumin da ya saka bam ɗin ya zama Mashaidin Jehobah, za mu marabce shi. Abin da ya faru ya koya mana cewa idan muka bi ƙa’idodin Jehobah, za mu sami kwanciyar hankali fiye da yadda muke tsammani! Sanin cewa nan ba da daɗewa ba Jehobah zai kawar da dukan lahanin da muke da shi yana taimaka mana.”

17. Mene ne ka koya game da gafartawa daga labarin Myra?

17 Wata ’yar’uwa mai suna Myra tana da aure da kuma yara biyu a lokacin da ta soma bauta wa Jehobah. Mijinta ya ƙi bauta wa Jehobah. Da shigewar lokaci, ya yi zina kuma ya bar iyalinsa. Myra ta ce: “Da mijina ya bar ni da yaranmu biyu, na yi baƙin ciki sosai, na yi da-na-sani, na ɗora wa kaina laifi kuma na yi fushi sosai kamar yadda mutane da yawa sukan yi idan aka ci amanarsu.” Ko da yake sun kashe auren, Myra ta ci gaba da baƙin ciki domin yadda mijinta ya ci amanarta. Ta ƙara cewa: “Na yi watanni ina damuwa da kuma fushi, amma sai na lura cewa hakan yana shafan dangantakata da Jehobah da kuma sauran mutane.” Myra ta ce yanzu ba ta baƙin ciki kuma ta daina riƙe mijinta na dā a zuciya, tana fatan cewa wata rana zai soma bauta wa Jehobah. Myra tana mai da hankali ga abin da zai faru a nan gaba kuma ta taimaka wa yaranta biyu su soma bauta wa Jehobah. A yau, Myra da yaranta da iyalan yaranta suna bauta wa Jehobah da farin ciki.

JEHOBAH SHI NE MAI SHARI’AR ADALCI

18. Mene ne za mu iya tabbata cewa Jehobah wanda shi ne Mai Shari’a Mafi Girma zai yi?

18 Sanin cewa ba mu ne da hakkin zaɓan yadda za a hukunta mutane ba yana ba mu kwanciyar hankali! Jehobah Mai Shari’a mafi girma ne zai ɗau wannan matakin. (Rom. 14:10-12) Muna da tabbaci cewa zai yanke hukunci daidai bisa ga ƙa’idodinsa. (Far. 18:25; 1 Sar. 8:32) Ba zai taɓa yin rashin adalci ba!

19. Mene ne Jehobah zai yi saboda adalcinsa?

19 Muna ɗokin ganin lokacin da Jehobah zai kawar da ajizanci da kuma zunubi. A lokacin, za mu warke daga kowane lahani da muke da ita. (Zab. 72:12-14; R. Yar. 21:3, 4) Ba za mu ma sake tunaninsu ba. Yayin da muke jiran wannan lokacin ya zo, muna godiya ga Jehobah domin ya ba mu baiwar yin koyi da yadda yake gafartawa.

WAƘA TA 18 Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

^ Jehobah yana so ya gafarta wa masu zunubi da suka tuba. A matsayin Kiristoci, muna so mu yi koyi da misalinsa idan wani ya yi mana laifi. A wannan talifin, za mu tattauna zunuban da za mu iya gafarta wa ʼyan’uwanmu, da kuma waɗanda muke bukatar mu gaya wa dattawa. Ban da haka, za mu tattauna dalilan da suka sa Jehobah yake so mu riƙa gafarta wa juna da kuma albarkun da za mu samu idan muka yi hakan.

^ Ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 1996.

^ An canja wasu sunayen.