Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 30

Annabcin da Aka Yi Tun Dā da Ya Shafe Ka

Annabcin da Aka Yi Tun Dā da Ya Shafe Ka

“Kai da macen, zan sa ƙiyayya tsakaninku.”​—FAR. 3:15.

WAƘA TA 15 Mu Yabi Ɗan Allah!

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne Jehobah ya yi nan da nan bayan Adamu da Hauwa’u sun yi zunubi? (Farawa 3:15)

 JIM KAƊAN bayan Adamu da Hauwa’u sun yi zunubi, Jehobah ya sa jikokinsu sun kasance da bege ta wajen wani annabci mai ban ƙarfafa. Annabcin yana Farawa 3:15.​—Karanta.

2. Me ya sa wannan annabcin yake da muhimmanci?

2 Annabcin yana cikin littafi na farko a Littafi Mai Tsarki. Dukan littattafan da ke Littafi Mai Tsarki suna da alaƙa da wannan annabcin a wasu hanyoyi. Kamar yadda igiya take riƙe tsintsiya, haka ma annabcin da ke Farawa 3:​15, yake haɗa saƙon da ke Littafi Mai Tsarki su zama saƙo ɗaya, wato Allah zai aiko da mai ceto da zai halaka Shaiɗan da kuma dukan mabiyansa. * Hakan zai sa waɗanda suke ƙaunar Jehobah su ji daɗin rayuwa!

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 A wannan talifin, za mu amsa tambayoyin nan game da annabcin da ke Farawa 3:15: Su waye ne aka ambata a cikin annabcin? Yaya annabcin yake cika? Kuma ta yaya muke amfana daga hakan?

SU WAYE NE AKA AMBATA A CIKIN ANNABCIN?

4. Wane ne “macijin” kuma ta yaya muka sani?

4 Waɗanda aka ambata a Farawa 3:​14, 15 su ne “macijin,” da ‘zuriyar’ macijin, da wata “mace,” da kuma ‘zuriyar’ macen. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da kowannensu yake wakilta. * Bari mu soma da “macijin.” A zahiri, ba zai yiwu maciji ya fahimci abin da Jehobah ya faɗa a lambun Adnin ba. Don haka, wanda Jehobah yake yi wa magana, halitta ne mai hikima sosai. Waye ke nan? Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9 ta ba mu amsar. Ayar ta ce “macijin nan na tun dā” shi ne Shaiɗan. Amma su waye ne zuriyar macijin?

MACIJIN

Shaiɗan Iblis, wanda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9 ta kira shi “macijin nan na tun dā” (Ka duba sakin layi na 4)

5. Su waye ne zuriyar macijin?

5 A wasu lokuta, idan Littafi Mai Tsarki ya ambaci zuriya, yana nufin waɗanda suke yin koyi da wani sosai har ya zama kamar ubansu. Don haka, zuriyar macijin tana nufin halittun ruhu da kuma ’yan Adam da suke ƙin Jehobah kuma suna hamayya da mutanensa kamar yadda Shaiɗan yake yi. Hakan ya ƙunshi mala’iku da suka bar aikin da Allah ya ba su a sama suka zo duniya a zamanin Nuhu, da kuma mugayen mutanen da suke yin abubuwa kamar ubansu, wato Shaiɗan.​—Far. 6:​1, 2; Yoh. 8:44; 1 Yoh. 5:19; Yahu. 6.

ZURIYAR MACIJIN

Aljanu da kuma ’yan Adam da suka ƙi Jehobah da mutanensa (Ka duba sakin layi na 5)

6. Me ya sa ba Hauwa’u ba ce macen da aka ambata?

6 Yanzu, bari mu gane wanda “macen” take wakilta. Ba Hauwa’u ba ce. Me ya sa muka ce hakan? Ka yi la’akari da dalili ɗaya. Annabcin ya ce zuriyar macen zai “murƙushe” kan macijin. Kamar yadda muka gani, macijin yana wakiltar halittar ruhu, wato Shaiɗan. Don haka, babu ɗan Adam ajizi daga zuriyar Hauwa’u da zai iya murƙushe shi. To, ta yaya za a halaka Shaiɗan?

7. Kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​1, 2, 5, 10 suka nuna, wace ce macen da aka ambata a Farawa 3:15?

7 Littafi na ƙarshe a Littafi Mai Tsarki, ya gaya mana wace ce macen nan da aka ambata a Farawa 3:15. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​1, 2, 5, 10.) Wannan macen ba a duniya take ba domin wata na ƙafafunta, kuma tana sanye da rawani da ke ɗauke da taurari 12. Ta haifi irin ɗa da ba a saba gani ba, wato Mulkin Allah. Mulkin yana sama, don haka, macen ma za ta kasance a sama. Tana wakiltar sashen ƙungiyar Jehobah da ke sama wanda ya ƙunshi mala’iku.​—Gal. 4:26.

MACEN

Sashen ƙungiyar Jehobah da ke sama da ya ƙunshi mala’iku (Ka duba sakin layi na 7)

8. Wane ne sashe mafi muhimmanci na zuriyar macen, kuma yaushe ne ya zama hakan? (Farawa 22:​15-18)

8 Kalmar Allah ta taimaka mana mu fahimci ko wane ne sashe mafi muhimmanci na zuriyar macen. An annabta cewa zai fito ne daga zuriyar Ibrahim. (Karanta Farawa 22:​15-18.) Kamar yadda aka annabta, Yesu ya fito daga zuriyar Ibrahim ne. (Luk. 3:​23, 34) Amma zuriyar zai kasance da iko fiye da ɗan Adam domin zai murƙushe Shaiɗan kuma ya halaka shi gabaki ɗaya. Don haka, sa’ad da Yesu yake wajen shekara 30, an shafe shi da ruhu mai tsarki a matsayin Ɗan Allah makaɗaici. Bayan an shafe Yesu, ya zama sashe mafi muhimmanci na zuriyar macen. (Gal. 3:16) Bayan Yesu ya mutu kuma ya tashi daga matattu, Allah ya “girmama shi da ɗaukaka da daraja” kuma ya ba shi “dukan iko a sama da kuma nan duniya,” haɗe da ikon “rushe ayyukan Shaiɗan.”​—Ibran. 2:7; Mat. 28:18; 1 Yoh. 3:8.

ZURIYAR MACEN

Yesu Kristi da shafaffu 144,000 da za su yi sarauta da shi (Ka duba sakin layi na 8-9)

9-10. (a) Ban da Yesu, su waye ne kuma suke cikin zuriyar macen, kuma yaushe ne suka zama hakan? (b) Mene ne za mu tattauna yanzu?

9 Amma ban da Yesu, akwai wasu ma da suke cikin zuriyar macen. Manzo Bulus ya bayyana su sa’ad da ya gaya ma shafaffun Kiristoci Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba cewa: “In kuwa ku na Almasihu Yesu ne, kun zama zuriyar Ibrahim ke nan, kuma masu cin gādon nan bisa ga alkawarinsa.” (Gal. 3:​28, 29) Idan Jehobah ya shafe Kirista da ruhu mai tsarki, Kiristan zai zama ɗaya daga cikin zuriyar macen. Don haka, zuriyar macen ta ƙunshi Yesu Kristi da kuma shafaffu 144,000 da za su yi sarauta tare da shi. (R. Yar. 14:1) Dukansu suna yin koyi da Ubansu, Jehobah.

10 Yanzu da muka san waɗanda aka ambata a Farawa 3:​15, bari mu tattauna yadda Jehobah yake sa annabcin nan ya cika a hankali, da kuma yadda muke amfana daga hakan.

MENE NE JEHOBAH YA RIGA YA YI DON ANNABCIN YA CIKA?

11. Mene ne annabcin yake nufi sa’ad da ya ce za a sari ‘diddigen ƙafar’ zuriyar macen?

11 Annabcin da ke Farawa 3:​15, ya nuna cewa macijin zai “sari diddigen” ƙafar zuriyar macen. Annabcin nan ya cika sa’ad da Shaiɗan ya sa Yahudawa da kuma Romawa su kashe Ɗan Allah. (Luk. 23:​13, 20-24) Kamar yadda rauni a ƙafa zai iya hana mutum tafiya na ɗan lokaci, haka ma, mutuwar Yesu ta sa bai iya yin kome ba yayin da yake cikin kabari har tsawon kwana uku.​—Mat. 16:21.

12. Ta yaya za a murƙushe kan macijin, kuma yaushe ne za a yi hakan?

12 Annabcin da ke Farawa 3:15 ya nuna cewa Yesu ba zai ci gaba da kasancewa a cikin kabari ba. Me ya sa? Domin annabcin ya nuna cewa zuriyar zai murƙushe kan macijin. Hakan yana nufin cewa Yesu zai bukaci ya tashi daga mutuwa. Abin da ya faru ke nan! A rana ta uku bayan ya mutu, an tā da Yesu daga mutuwa, kuma an ba shi rai marar mutuwa a sama. Idan lokacin Jehobah ya yi, Yesu zai murƙushe Shaiɗan kuma ya halaka shi. (Ibran. 2:14) Waɗanda za su yi mulki tare da Yesu za su haɗa hannu su halaka dukan maƙiyan Allah, wato zuriyar macijin.​—R. Yar. 17:14; 20:​4, 10. *

TA YAYA MUKE AMFANA DAGA ANNABCIN NAN?

13. Ta yaya muke amfana daga yadda annabcin nan yake cika?

13 Idan kai bawan Allah ne, kana amfana daga cikar wannan annabcin. Yesu ya zo duniya a matsayin mutum. Ya bi halin Ubansa daidai. (Yoh. 14:9) Saboda haka, ta wajensa ne muka san Jehobah Allah kuma muka soma ƙaunar sa. Muna kuma amfana daga koyarwar Yesu da yadda yake yi wa ikilisiyar Kirista ja-goranci a yau. Ya koya mana yadda za mu yi rayuwa da zai sa Jehobah ya amince da mu. Kuma da yake an sari diddigen ƙafar Yesu ko kuma an kashe shi, dukanmu muna amfana. Ta yaya? Sa’ad da Yesu ya tashi daga mutuwa, Jehobah ya karɓi hadayar da ya yi, kuma hadayar ce take “tsabtace mu daga dukan zunubi.”​—1 Yoh. 1:7.

14. Ta yaya muka san cewa annabcin da Jehobah ya yi a lambun Adnin bai cika nan da nan ba? Ka bayyana.

14 Abin da Jehobah ya faɗa a lambun Adnin ya nuna cewa zai ɗauki lokaci sosai kafin annabcin nan ya cika gabaki ɗaya. Zai ɗauki lokaci kafin macen ta haifi zuriyar da aka yi annabcinta, kafin Shaiɗan ya tattara mabiyansa, kuma kafin ƙiyayya ta kasance tsakanin rukunonin nan biyu. Muna amfana daga wannan annabcin domin yana tuna mana cewa duniyar nan da take ƙarƙashin ikon Shaiɗan za ta tsane mu. Daga baya, Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi makamancin hakan. (Mar. 13:13; Yoh. 17:14) Babu shakka, muna ganin yadda wannan annabcin yake cika, musamman ma a cikin shekaru 100 da suka shige. Ta yaya?

15. Me ya sa duniyar Shaiɗan tana daɗa tsanar mu, amma me ya sa bai kamata mu ji tsoro ba?

15 Jim kaɗan bayan an naɗa Yesu a matsayin Sarki a 1914, an kori Shaiɗan daga sama zuwa duniya. A yanzu yana duniya kuma ba zai iya koma sama ba, yana jiran hukuncin da za a yi masa. (R. Yar. 12:​9, 12) Amma bai naɗe hannu kawai yana jira ba. Shaiɗan yana fushi sosai kuma yana kai wa bayin Allah hari. (R. Yar. 12:​13, 17) Shi ya sa duniyar Shaiɗan ta tsane mu fiye da dā. Amma ba ma bukatar mu ji tsoron Shaiɗan da mutanensa. Muna bukatar mu kasance da tabbaci kamar manzo Bulus wanda ya ce: “Idan Allah yana tare da mu, wa ya isa ya yi gāba da mu?” (Rom. 8:31) Za mu iya gaskata da Jehobah da dukan zuciyarmu domin kamar yadda muka gani, da yawa daga cikin sassan annabcin da aka yi a Farawa 3:15 sun riga sun cika.

16-18. Ta yaya Curtis da Ursula da kuma Jessica suka amfana daga fahimtar annabcin da ke Farawa 3:15?

16 Alkawarin da Jehobah ya yi a Farawa 3:15 zai iya taimaka mana mu iya jimre duk wani yanayi da muka sami kanmu a ciki. Wani ɗan’uwa da ke wa’azi a ƙasar waje da yake hidima a yankin Guam, mai suna Curtis, ya ce: “Akwai abubuwa da yawa da suka faru a rayuwata da suka sa ya yi mini wuya in kasance da aminci ga Jehobah. Amma yin bimbini a kan annabcin da ke Farawa 3:15 ya taimaka mini in ci gaba da dogara ga Jehobah.” Curtis yana marmarin lokacin da Jehobah zai kawo ƙarshen dukan matsalolin da muke fuskanta.

17 Wata ’yar’uwa mai suna Ursula da ke zama a yankin Bavaria, ta ce fahimtar annabcin da ke Farawa 3:15 ya taimaka mata ta gaskata cewa Jehobah ne ya hure Littafi Mai Tsarki. Ta ga yadda sauran annabce-annabce suke da alaƙa da wannan annabcin kuma hakan ya burge ta sosai. Ta kuma ce: “Na yi farin ciki sosai da na koyi cewa Jehobah ya ɗau mataki nan da nan domin ’yan Adam su kasance da bege.”

18 Wata ’yar’uwa mai suna Jessica daga Micronesia ta ce: “Ba zan taɓa mantawa da yadda na ji ba sa’ad da na gano cewa na sami gaskiya! Annabcin da ke Farawa 3:15 yana cika. Annabcin yana taimaka min in tuna cewa Jehobah bai yi mu mu sha wahala kamar yadda muke sha a yanzu ba. Annabcin ya kuma tabbatar min da cewa bauta ma Jehobah zai sa in yi rayuwa mafi inganci a yanzu, kuma in sami rai na har abada a nan gaba.”

19. Me ya sa muke da tabbaci cewa sashe na ƙarshe na annabcin zai cika?

19 Kamar yadda muka gani, annabcin da ke Farawa 3:15 yana cika. Mun gane waɗanda zuriyar macen da kuma zuriyar macijin suke wakilta. Yesu ya riga ya warke daga rauni da aka yi masa a diddigen ƙafarsa, kuma yanzu shi Sarki ne da ke da rai marar mutuwa. A yanzu, Jehobah ya kusan gama zaɓan waɗanda za su yi sarauta da Yesu a sama. Da yake sashen farko na annabcin ya riga ya cika, muna da tabbaci cewa sashe na ƙarshen ma zai cika, wato yadda za a murƙushe kan macijin. Bayin Allah za su yi farin ciki sosai sa’ad da aka halaka Shaiɗan! Kafin lokacin, kada mu yi sanyin gwiwa. Za mu iya dogara ga Allahnmu. Ta wurin zuriyar macen Allah zai kawo albarku masu yawa ga “dukan kabilun duniya.”​—Far. 22:18.

WAƘA TA 23 Jehobah Ya Soma Sarautarsa

^ Kafin mu iya fahimtar saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kyau, dole ne mu fahimci annabcin da ke Farawa 3:15. Tattauna wannan annabcin zai ƙarfafa bangaskiyarmu, kuma ya tabbatar mana da cewa Jehobah zai cika alkawuran da ya yi.

^ Ka duba sashe na 5 mai jigo, “Saƙon da Ke Cikin Littafi Mai Tsarki” a littafin nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah.

^ Ka duba akwatin nan “Waɗanda Aka Ambata a Farawa 3:​14, 15.”