Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 37

Za Ku Iya Yarda da ’Yan’uwanku

Za Ku Iya Yarda da ’Yan’uwanku

“Ƙauna tana . . . gaskata abu duka, tana kafa bege ga abu duka.”​—1 KOR. 13:​4, 7, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Me ya sa ba ma mamakin ganin yadda mutane ba sa yarda da juna a duniya?

 MUTANE a wannan muguwar duniya ba su san wa za su yarda da shi ba. Saboda rashin gaskiya na ’yan kasuwa da ’yan siyasa da malaman addinai, mutane ba sa yarda da juna. Wasu ba sa yarda da abokansu da maƙwabtansu har ma da iyalansu. Bai kamata hakan ya ba mu mamaki ba. Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa: “A kwanakin ƙarshe . . . , mutane za su zama . . . marasa aminci, . . . masu ɓata sunayen waɗansu, . . . masu cin amana.” Hakan yana nufin cewa mutane za su zama kamar Shaiɗan, wanda shi ne allahn wannan zamanin da ba za a iya yarda da shi ba.​—2 Tim. 3:​1-4; 2 Kor. 4:4.

2. (a) Su waye ne za mu iya yarda da su da dukan zuciyarmu? (b) Mene ne wasu za su iya yin tunani a kai?

2 Amma a matsayinmu na Kiristoci, mun san cewa za mu iya yarda da Jehobah da dukan zuciyarmu. (Irm. 17:​7, 8) Mun tabbata cewa yana ƙaunar mu, kuma ba zai “ƙyale” abokansa ba. (Zab. 9:10) Mun kuma yarda da Yesu Kristi domin ya ba da ransa a madadinmu. (1 Bit. 3:18) Kuma mun shaida yadda shawarwarin Littafi Mai Tsarki suke taimaka mana a rayuwa. (2 Tim. 3:​16, 17) Mun tabbata cewa za mu iya yarda da Jehobah da Yesu da kuma Littafi Mai Tsarki. Amma wasu suna tunanin ko za su iya yarda da ’yan’uwansu a ikilisiya. Idan haka ne, me ya sa ya dace mu yarda da su?

MUNA BUKATAR TAIMAKON ’YAN’UWANMU

A duk faɗin duniya, muna da ’yan’uwa da za mu iya yarda da su domin suna ƙaunar Jehobah kamar yadda muke yi (Ka duba sakin layi na 3)

3. Wane babban gata ne muke da shi? (Markus 10:​29, 30)

3 Jehobah ne ya jawo mu cikin iyalin da ke bauta masa a dukan duniya. Wannan gata ne babba kuma muna amfana daga hakan! (Karanta Markus 10:​29, 30.) A dukan duniya muna da ’yan’uwa maza da mata da su ma suke ƙaunar Jehobah, kuma suna yin iya ƙoƙarinsu su bi ƙa’idodinsa. Yarenmu da al’adarmu da ma tufafinmu za su iya bambanta da nasu, amma muna ƙaunar su sosai, ko da ba mu taɓa ganin su ba. Muna farin cikin kasancewa tare da su musamman a lokacin da muke yabo da kuma bauta ma Ubanmu na sama.​—Zab. 133:1.

4. Me ya sa muke bukatar ’yan’uwanmu Kiristoci?

4 Yanzu ne lokacin da ya fi dacewa mu yi kusa da ’yan’uwanmu. A wasu lokuta suna taimaka mana mu iya jimre matsalolinmu. (Rom. 15:1; Gal. 6:2) Ƙari ga haka, suna taimaka mana mu ci gaba da yin ayyukan ibada kuma mu ci gaba da zama abokan Jehobah. (1 Tas. 5:11; Ibran. 10:​23-25) Ka yi tunanin abin da zai faru da a ce ’yan’uwanmu Kiristoci ba sa taimaka mana mu iya yin tsayayya da abokan gābanmu, wato Shaiɗan da kuma wannan muguwar duniya. Nan ba da daɗewa ba, Shaiɗan da kuma mutanen da suke ƙarƙashin ikonsa za su kai wa bayin Allah hari. Amma a lokacin, za mu yi farin ciki domin goyon baya da ’yan’uwanmu za su ba mu!

5. Me ya sa zai iya yi ma wasu wuya su yarda da ’yan’uwansu Kiristoci?

5 Amma yana yi ma wasu wuya su yarda da ’yan’uwansu Kiristoci, mai yiwuwa sun taɓa gaya ma wani sirrinsu, sai ya gaya ma wasu, ko ya kasa cika alkawarin da ya yi musu. Ko kuma wani ɗan’uwa ya faɗi ko ya yi abin da ya ɓata musu rai sosai. Idan hakan ya faru, zai iya yi musu wuya su yarda da wasu. To mene ne zai taimaka mana mu iya yarda da ’yan’uwanmu Kiristoci?

ƘAUNA ZA TA SA MU YARDA DA ’YAN’UWANMU

6. Ta yaya ƙauna za ta taimaka mana mu yarda da ’yan’uwanmu? (1 Korintiyawa 13:​4-8)

6 Ƙauna ce take sa mu yarda da mutane. Korintiyawa na ɗaya sura 13 ta bayyana wasu halaye da ƙauna take sa mu kasance da su. Halayen za su taimaka mana mu yarda da ’yan’uwanmu ko kuma mu sake yarda da su idan sun taɓa ɓata mana rai. (Karanta 1 Korintiyawa 13:​4-8.) Alal misali, aya 4 ta ce “ƙauna tana da haƙuri da kirki.” Jehobah yana haƙuri da mu har a lokacin da muka yi masa zunubi. Don haka, mu ma zai dace mu yi haƙuri da ’yan’uwanmu idan suka yi ko faɗi abin da zai ɓata mana rai. Aya 5 ta ƙara da cewa: “[Ƙauna] ba ta jin tsokana, ba ta riƙe laifi a zuciya.” Ba zai dace mu “riƙe laifi a zuciya” ba, wato mu riƙa tuna da laifuffuka da ’yan’uwanmu suka yi mana don mu tunasar da su a nan gaba. Littafin Mai-Wa’azi 7:9 ta ce bai dace mu zama masu “saurin fushi” ba. Don haka, zai dace mu bi shawarar da ke Afisawa 4:​26, da ta ce: “Kada ma fushinku ya daɗe ya kai har rana ta fāɗi”!

7. Ta yaya ƙa’idodin da ke Matiyu 7:​1-5 za su iya taimaka mana mu yarda da ’yan’uwanmu?

7 Wani abu kuma da zai taimaka mana mu yarda da ’yan’uwanmu shi ne in muna ɗaukan su yadda Jehobah yake ɗaukan su. Allah yana ƙaunar su kuma ba ya tuna da laifuffuka da suka yi. Mu ma ya kamata mu yi hakan. (Zab. 130:3) Zai fi dacewa mu mai da hankali ga halayensu masu kyau, kuma mu yi tunanin abubuwa masu kyau da za su iya yi. (Karanta Matiyu 7:​1-5.) Ƙari ga haka, da yake ƙauna “tana gaskata abu duka,” ya kamata mu riƙa ɗauka cewa suna so su yi abin da ya dace kuma ba niyyarsu ba ne su ɓata mana rai. (1 Kor. 13:7) Nassin ba ya nufin cewa Jehobah yana so mu yarda da kowa haka kawai ba, amma mu yarda da su domin sun nuna cewa sun cancanci hakan. b

8. Mene ne zai taimaka maka ka soma yarda da ’yan’uwanka?

8 Mutum yana bukatar ya nuna cewa ya cancanci mu yarda da shi kafin mu yi hakan, kuma hakan zai iya ɗaukan lokaci. Me zai taimaka maka ka soma yarda da ’yan’uwanka? Ka yi ƙoƙari ka san su da kyau. Ka tattauna da su a taro. Ka kuma yi wa’azi tare da su. Ka riƙa haƙuri da su, kuma ka ba su lokaci don su nuna maka cewa sun cancanci ka yarda da su. Mai yiwuwa ba kome game da sha’aninka ne za ka so ka gaya musu da farko ba, amma yayin da kake daɗa sanin su, za ka iya daɗa yarda da su. (Luk. 16:10) Amma me za ka yi idan wani ɗan’uwa ya ci amanarka? Kada ka yi saurin daina abokantaka da shi, amma ka ɗan ba shi lokaci. Kuma kada ka bar halaye marasa kyau na ’yan’uwa kalila su sa ka daina yarda da ’yan’uwanka. Game da wannan batun, za mu tattauna misalan wasu bayin Allah masu aminci da suka ci gaba da yarda da wasu duk da cewa wasu sun ci amanarsu.

KA ƊAU DARASI DAGA WAƊANDA SUKA CI GABA DA YARDA DA WASU

Duk da abin da Eli ya gaya wa Hannatu, Hannatu ta ci gaba da bin tsarin Jehobah (Ka duba sakin layi na 9)

9. (a) Ta yaya Hannatu ta ci gaba da bin tsarin Jehobah, duk da cewa wasu da suke ja-goranci sun yi kuskure sosai? (b) Mene ne labarin Hannatu ya koya maka game da amincewa da tsarin Jehobah? (Ka duba hoton.)

9 Shin wani ɗan’uwa da ke ja-goranci ya taɓa faɗa ko ya yi abin da ya ɓata maka rai? Za ka iya amfana daga misalin Hannatu. A lokacin, Babban Firist mai suna Eli ne yake ja-goranci a bautar Jehobah a Isra’ila. Amma membobin iyalinsa ba sa yin abin da ya dace. Yaransa waɗanda su ma firistoci ne sukan yi abubuwa marasa kyau har da lalata. Amma babansu bai tsauta musu yadda ya kamata ba. Jehobah bai saukar da Eli daga matsayinsa nan take ba. Amma Hannatu ba ta daina zuwa yin ibada a mazauni a lokacin da Eli yake hidima a matsayin babban firist ba. Sa’ad da Eli ya ga Hannatu tana addu’a da baƙin ciki, sai ya ɗauka cewa ta bugu da giya. Ba tare da bincika gaskiyar batun ba, sai ya yi wa matar nan da ke baƙin ciki baƙar magana. (1 Sam. 1:​12-16) Duk da haka, Hannatu ta yi alkawari cewa idan ta haifi ɗa za ta kai shi mazauni don ya yi hidima a ƙarƙashin ja-gorancin Eli. (1 Sam. 1:11) Shin ya kamata a yi wa ’ya’yan Eli gyara ne? Ƙwarai kuwa, kuma Jehobah ya yi hakan a lokacin da ya dace. (1 Sam. 4:17) Kafin lokacin, Jehobah ya yi wa Hannatu albarka ta wajen ba ta ɗa mai suna Sama’ila.​—1 Sam. 1:​17-20.

10. A wace hanya ce Sarki Dauda ya ci gaba da yarda da wasu duk da cewa an ci amanarsa?

10 Wani babban abokinka ya taɓa cin amanarka? Idan haka ne, ka yi tunani a kan labarin Sarki Dauda. Ɗaya daga cikin abokansa shi ne wani mutum mai suna Ahitofel. Amma a lokacin da Absalom ɗan Dauda ya yi ƙoƙarin yi wa babansa juyin mulki, Ahitofel ya haɗa kai da Absalom. Babu shakka Dauda ya yi baƙin ciki sosai da yake ya ga abokinsa da ɗansa sun juya masa baya! Amma Dauda bai bar wannan aukuwar ya sa shi ya daina yarda da wasu ba. Ya ci gaba da yarda da wani abokinsa mai aminci mai suna Hushai wanda ya ƙi ya yi masa tawaye. Hakan ya taimaka wa Dauda sosai. Hushai ya nuna masa cewa shi abokin kirki ne, har ya ɗau hatsari domin Dauda.​—2 Sam. 17:​1-16.

11. A wace hanya ce ɗaya daga cikin masu yi wa Nabal hidima ya nuna cewa ya yarda da Abigiyel?

11 Ka kuma yi la’akari da misalin ɗaya daga cikin bayin Nabal. Dauda da mutanensa sun yi wa bayin wani Ba’isra’ile mai suna Nabal alheri kuma sun kāre su. Nabal mai arziki ne sosai, kuma akwai lokacin da Dauda ya roƙe shi ya ba su abinci, wato duk abin da Nabal zai iya bayarwa. Da Nabal ya ƙi ya ba su abinci, Dauda ya yi fushi har ya yanke shawarar kashe dukan mazan gidan Nabal. Ɗaya daga cikin bayin Nabal ya gaya wa matar Nabal wato Abigiyel abin da ke faruwa. Da yake shi ma yana cikin iyalin Nabal, ya san cewa Abigiyel za ta iya cece shi. Maimakon ya gudu ya bar gidan, ya ba da gaskiya cewa Abigiyel za ta iya daidaita batun. Ya ɗauki wannan matakin ne domin kowa ya san cewa Abigiyel mace ce mai hikima kuma bai yi kuskure ba. Abigiyel ta nuna hikima da kuma ƙarfin hali yayin da ta roƙi Dauda ya canja ra’ayinsa. (1 Sam. 25:​2-35) Ta ba da gaskiya cewa Dauda zai yi abin da ya kamata.

12. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya yarda da almajiransa duk da cewa su ajizai ne?

12 Yesu ya yarda da almajiransa duk da kurakuransu. (Yoh. 15:​15, 16) A lokacin da Yakub da kuma Yohanna suka roƙi Yesu ya ba su matsayi na musamman a cikin Mulkinsa, Yesu bai ɗauka cewa suna bauta ma Jehobah da mummunan nufi ne ba, kuma bai dakatar da su daga zama manzanninsa ba. (Mar. 10:​35-40) Daga baya dukan almajiran Yesu sun gudu sun bar shi a daren da aka kama shi. (Mat. 26:56) Duk da hakan, Yesu bai daina yarda da su ba. Ya san ajizancinsu sosai, amma ya “nuna musu ƙaunarsa har zuwa ƙarshe.” (Yoh. 13:1) Bayan da Yesu ya tashi daga mutuwa, ya ba wa manzanninsa masu aminci guda 11 babban aiki, wato ja-goranci a wa’azi da kuma kula da tumakinsa. (Mat. 28:​19, 20; Yoh. 21:​15-17) Bai yi kuskure da ya yi hakan ba. Dukansu sun riƙe amincinsu har sun mutu. Hakika, Hannatu da Dauda da bawan Nabal da Abigiyel da Yesu, duk sun nuna mana misali mai kyau na yarda da ’yan Adam ajizai.

YADDA ZA MU SAKE YARDA DA ’YAN’UWANMU DA SUKA CI AMANARMU

13. Wane abu ne zai iya hana mu yarda da ’yan’uwanmu?

13 Ka taɓa gaya ma wani ɗan’uwa abu cikin sirri, amma daga baya sai ka ji cewa ya gaya ma wani? Hakan yana da ban haushi sosai. Akwai wata ’yar’uwa da ta gaya ma wani dattijo sirrinta. Washegari, matar dattijon ta kira ’yar’uwar don ta ƙarfafa ta bisa ga abin da maigidanta ya gaya mata. Babu shakka, ya yi wa ’yar’uwar wuya ta sake yarda da dattijon. Amma ’yar’uwar ta yi abin da ya dace, kuma ta yi magana da wani dattijo da ya taimaka mata ta sake yarda da dattawa.

14. Me ya taimaka ma wani ɗan’uwa ya sake yarda da wasu dattawa?

14 Wani ɗan’uwa ya daɗe yana fushi da wasu dattawa biyu da yana gani ba zai iya yarda da su ba. Amma ya soma tunani a kan abin da wani ɗan’uwa da yake daraja sosai ya faɗa. Abin da ɗan’uwan ya ce shi ne: “Shaiɗan ne maƙiyinmu ba ’yan’uwanmu ba.” Ɗan’uwan ya yi tunani sosai a kan maganar da kuma abin da ya kamata ya yi. Bayan ya yi addu’a Jehobah ya taimaka masa, sai ya je ya yi sulhu da dattawan.

15. Me ya sa zai iya ɗaukan lokaci kafin mu sake yarda da ’yan’uwanmu da suka taɓa ɓata mana rai? Ka ba da misali.

15 Idan an taɓa hana ka yin wani aikin da kake yi a cikin ikilisiya, hakan zai iya sa ka baƙin ciki sosai. Grete da mahaifiyarta sun bauta wa Jehobah da aminci a lokacin da aka hana aikinmu a ƙarƙashin gwamnatin Nazi na Jamus kafin Yaƙin Duniya na Biyu. Da farko, an ba wa Grete aikin rubuta Hasumiyar Tsaro da tafireta ma ’yan’uwa. Amma da ’yan’uwan sun ji cewa mahaifinta yana hamayya da Shaidun Jehobah, sai suka daina ba ta aikin domin suna tsoro cewa mahaifinta zai kai ƙarar ikilisiyar ga hukumomi. Bai ƙare a hakan ba. Daga lokacin da aka soma Yaƙin Duniya na Biyu har zuwa ƙarshensa, ’yan’uwan sun daina ba wa Grete da mahaifiyarta Hasumiyar Tsaro, kuma ko da sun haɗu da su a hanya, ba sa yi musu magana. Hakan ya sa ta baƙin ciki sosai! Kuma ya ɗau lokaci sosai kafin ta iya gafarta wa ’yan’uwan kuma ta sake yarda da su. Daga baya ta gaya wa kanta cewa Jehobah ya riga ya gafarta musu kuma ya dace ita ma ta yi hakan. c

“Shaiɗan ne maƙiyinmu ba ’yan’uwanmu ba”

16. Me ya sa zai dace mu yi iya ƙoƙarinmu don mu riƙa yarda da ’yan’uwanmu?

16 Idan irin wannan abin ya taɓa faruwa da kai, ka yi ƙoƙari don ka sake yarda da ’yan’uwanka. Hakan zai iya ɗaukan lokaci, amma yin hakan zai kawo sakamako mai kyau. Ka yi la’akari da wannan misalin, idan ka taɓa cin guba, za ka soma yin hankali da abincin da kake ci. Amma domin ka ci guba sau ɗaya, hakan ba zai sa ka daina cin abinci gabaki ɗaya ba. Haka ma, ba zai dace mu bar abin da wani ya yi mana a dā ya sa mu daina yarda da ’yan’uwanmu ba, da yake mun san cewa su ajizai ne. Idan mun sake soma yarda da ’yan’uwanmu, hakan zai sa mu daɗa yin farin ciki, kuma hakan zai taimaka mana mu san abin da za mu iya yi don mu sa ’yan’uwa a ikilisiya su ci gaba da yarda da juna.

17. Me ya sa yake da muhimmanci mu yarda da juna, kuma mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Yawancin mutane a wannan muguwar duniya ba sa yarda da juna. Amma za mu iya yarda da ’yan’uwanmu Kiristoci domin muna ƙaunar su kuma su ma suna ƙaunar mu. Hakan yana sa mu yi farin ciki, kuma yana daɗa sa mu kasance da haɗin kai. Ƙari ga haka, zai kāre mu a lokuta masu wuya a nan gaba. Amma me za ka yi idan wani ya taɓa ɓata maka rai kuma hakan ya sa ka daina yarda da shi? Ka ɗauki yanayin yadda Jehobah yake ɗaukansa, ka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, ka ƙaunaci ’yan’uwanka sosai, kuma ka yi koyi da misalai masu kyau da ke Littafi Mai Tsarki. Za mu iya daina fushi kuma mu sake yarda da ’yan’uwanmu Kiristoci. Idan mun yi hakan, za mu amfana sosai daga abokai da yawa da suka “fi ɗan’uwa aminci.” (K. Mag. 18:24) Amma bai kamata mu yarda da ’yan’uwanmu kawai ba. Mu ma muna bukatar mu sa su yarda da mu. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda za mu sa ’yan’uwanmu su yarda da mu.

WAƘA TA 99 Miliyoyin ’Yan’uwa

a Muna bukatar mu yarda da ’yan’uwanmu. Yin hakan bai da sauƙi, domin a wasu lokuta sukan ɓata mana rai. A wannan talifin, za mu ga yadda ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma yin tunani a kan misalan wasu bayin Allah a dā za su iya taimaka mana mu yarda da ’yan’uwanmu, ko kuma mu sake yarda da su idan sun taɓa ɓata mana rai.

b Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu cewa wasu a cikin ikilisiya ba za su cancanci mu yarda da su ba. (Yahu. 4) A wasu lokuta, ’yan’uwan ƙarya za su so su yaudare mu da “maganganun ƙarya.” (A. M. 20:30) Zai dace kada mu yarda da su ko mu saurare su.

c Don ƙarin bayani game da labarin Grete, ka duba littafin nan 1974 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafi na 129-131.