Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 38

Ka Nuna Cewa Kai Amintacce Ne

Ka Nuna Cewa Kai Amintacce Ne

“Amintaccen mutum yakan riƙe amanar asiri.”​—K. MAG. 11:13.

WAƘA TA 101 Mu Riƙa Hidima da Haɗin Kai

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Ta yaya za mu iya sanin amintaccen mutum?

 AMINTACCEN mutum yakan yi ƙoƙari ya cika alkawuransa kuma yakan faɗi gaskiya. (Zab. 15:4) Mutane sun san cewa za su iya yarda da shi. Yadda muke so ’yan’uwanmu su ɗauke mu ke nan. Me za mu iya yi don su yarda da mu?

2. Ta yaya za mu tabbatar wa mutane cewa mu amintattu ne?

2 Ba za mu iya tilasta wa mutane su yarda da mu ba. Dole ne mu tabbatar wa mutane cewa mu amintattu ne. Mutane sukan ce yarda yana kamar kuɗi. Da wuya ake samun sa, amma da sauƙi ake rasa shi. Babu shakka, Jehobah ya tabbatar mana cewa za mu iya yarda da shi. A kullum, za mu iya yarda da shi domin “dukan ayyukansa yana yin su da aminci.” (Zab. 33:4) Yana so mu yi koyi da shi. (Afis. 5:1) Bari mu tattauna misalan wasu bayin Jehobah da suka yi koyi da Ubansu na sama ta wajen nuna cewa su amintattu ne. Za mu kuma tattauna halaye guda biyar da za su taimaka mana mu zama amintattu.

KA KOYA DAGA MISALIN AMINTATTUN BAYIN JEHOBAH

3-4. Ta yaya annabi Daniyel ya nuna cewa shi amintacce ne, kuma mene ne hakan ya kamata ya sa mu yi?

3 Annabi Daniyel ya kafa mana misali mai kyau na yadda za mu zama amintattu. Ko da yake an kai shi bauta a Babila, ba da daɗewa ba, Daniyel ya tabbatar wa mutanen cewa za a iya yarda da shi. Mutane sun daɗa yarda da Daniyel sa’ad da Jehobah ya taimaka masa ya bayyana wa sarkin Babila, wato Nebuchadnezzar ma’anar mafarkinsa. Akwai lokacin da Daniyel ya gaya wa sarkin cewa Jehobah yana fushi da shi, kuma wannan ba saƙo ne da sarki zai so ya ji ba. Daniyel ya bukaci ƙarfin zuciya kafin ya iya idar da saƙon domin Sarki Nebuchadnezzar mai saurin fushi ne sosai. (Dan. 2:12; 4:​20-22, 25) Shekaru da yawa bayan hakan, Daniyel ya sake nuna cewa shi amintacce ne sa’ad da ya bayyana ma’anar wani rubutu da ya bayyana a bango a fadar sarkin Babila. (Dan. 5:​5, 25-29) Daga baya Sarki Darius da hakimansa sun lura cewa Daniyel yana da “ruhun ban mamaki.” Sun ce Daniyel “mutum ne mai aminci, wanda yake yin kome daidai, kuma babu inda za a same shi da kuskure.” (Dan. 6:​3, 4) Hakika, har ma sarakunan da ba sa bauta wa Allah, sun lura cewa wannan bawan Allah mutum ne da za a iya yarda da shi!

4 Yayin da muke yin tunani a kan misalin Daniyel, zai dace mu tambayi kanmu: ‘Yaya mutanen da ba Shaidun Jehobah ba suke gani na? Shin an san ni a matsayin wanda yake cika hakkinsa kuma za a iya yarda da shi?’ Me ya sa ya dace mu yi wa kanmu muhimman tambayoyin nan? Domin za mu sa a ɗaukaka Jehobah idan mu amintattu ne.

Nehemiya ya zaɓi mutanen da aka yarda da su don su yi ayyuka masu muhimmanci (Ka duba sakin layi na 5)

5. Me ya taimaka ma Hananiya ya zama amintacce?

5 A shekara ta 455 kafin haihuwar Yesu, bayan Gwamna Nehemiya ya sake gina katangar birnin Urushalima, ya naɗa amintattun mutane da za su riƙa kula da birnin. Ɗaya daga cikin mutane da Nehemiya ya zaɓa, shi ne Hananiya, wanda shi ne shugaban babban gidan da sojoji ke zama. Littafi Mai Tsarki ya ce “Hananiya ya fi yawancin mutane aminci da tsoron Allah.” (Neh. 7:2) Da yake Hananiya yana tsoron Allah kuma ba ya so ya yi abin da zai ɓata ma Jehobah rai, ya yi duk wani aiki da aka ba shi da dukan ƙarfinsa. Irin halayen nan za su taimaka mana mu zama amintattu a hidimarmu ga Allah.

6. Ta yaya Tikikus ya nuna cewa shi amintaccen aboki ne ga manzo Bulus?

6 Ka yi la’akari kuma da misalin Tikikus, wani ɗan’uwa da Bulus ya yarda da kuma dogara da shi. Bulus ya dogara da Tikikus kuma ya kira shi “mai hidima cikin aminci.” (Afis. 6:​21, 22) Bulus ya yarda da Tikikus, shi ya sa ya ce masa ya kai wasiƙunsa ga ’yan’uwa da ke Afisa da kuma Kolosi. Kuma ya ƙarfafa da ta’azantar da su. Tikikus ya tuna mana da ’yan’uwa masu aminci da suke kula da mu a ikilisiya.​—Kol. 4:​7-9.

7. Mene ne ka koya game da zama amintacce daga dattawa da kuma bayi masu hidima a ikilisiyarku?

7 A yau, muna farin ciki sosai domin dattawanmu da kuma bayi masu hidima amintattu ne. Kamar Daniyel da Hananiya da kuma Tikikus, ba sa wasa da aikinsu. Alal misali, a duk lokacin da muka halarci taron tsakiyar mako, mun san cewa an riga an zaɓi waɗanda za su gudanar da kowace sashe na taron. Dattawa suna farin ciki idan dukan waɗanda aka ba su aiki a taron sun yi shiri da kyau kuma sun gudanar da aikin da aka ba su. Alal misali, ba ma shakkar gayyatar ɗalibanmu zuwa taro domin mun tabbata cewa akwai wanda zai ba da jawabi. Kuma mun san cewa za mu sami littattafan da muke bukata don mu yi wa’azi. ’Yan’uwan nan suna kula da kuma tanadar mana da abubuwan da muke bukata a ikilisiya kuma mun gode wa Jehobah domin su! Ta waɗanne hanyoyi ne kuma za mu iya nuna cewa mu amintattu ne?

KA NUNA CEWA KAI MAI AMINCI NE TA WAJEN RIƘE AMANA

8. Me za mu yi don mu guji wuce gona da iri yayin da muke nuna damuwa game da ’yan’uwanmu? (Karin Magana 11:13)

8 Muna ƙaunar ’yan’uwanmu kuma muna so mu san yadda suke. Amma dole ne mu guji wuce gona da iri. Wasu Kiristoci a ƙarni na farko suna yin “gulma . . .  , suna shiga al’amuran waɗansu, wanda bai kamata ba.” (1 Tim. 5:13) Bai kamata mu zama kamar su ba. Amma a ce wani ya gaya mana wani bayani game da kansa kuma ya ce kada mu gaya ma wasu fa. Alal misali, idan wata ’yar’uwa ta gaya mana game da rashin lafiyar da take fama da shi ko kuma wani matsala dabam, zai dace mu guji gaya wa mutane. b (Karanta Karin Magana 11:13.) Yanzu bari mu tattauna wasu yanayoyi da zai dace mu riƙe amana.

9. Ta yaya membobin iyali za su nuna cewa su amintattu ne?

9 Ka sa membobin iyalinka su yarda da kai. Alal misali, wata ’yar’uwa Kirista za ta iya kasancewa da hali da ke da ban dariya. Shin zai dace maigidanta ya riƙa magana game da halin a waje kuma ya sa ta ji kunya? Ba zai dace ya yi hakan ba! Da yake yana ƙaunar matarsa, ba zai yi wani abin da zai ɓata mata rai ba. (Afis. 5:33) Matasa ma suna so a riƙa girmama su. Yana da muhimmanci iyaye su tuna da hakan. Ba zai dace iyaye su ƙasƙantar da yaransu ta wajen gaya wa mutane kurakuren yaransu ba. (Kol. 3:21) Yara ma suna bukatar su yi hankali don kada su gaya wa mutane wasu bayanai game da iyalinsu domin kada su kunyatar da membobin iyalinsu. (M. Sha. 5:16) Idan kowane mamban iyali ya yi iya ƙoƙarinsa don ya rufa wa iyalin asiri, membobin iyalin za su daɗa ƙaunar juna.

10. Mene ne abokai na ƙwarai suke yi wa juna? (Karin Magana 17:17)

10 Ka sa abokanka su yarda da kai. A wasu lokuta, za mu so mu gaya wa abokanmu abubuwan da ke zuciyarmu. Amma ba kowane lokaci ba ne hakan yake mana sauƙi. Don haka, za mu iya yin baƙin ciki sosai idan muka ji cewa abokinmu ya gaya ma wasu abin da muka gaya masa a asirce. Amma muna farin ciki sosai idan muna da abokin da ba ya gaya wa mutane abin da muka gaya masa a asirce! Irin mutumin nan aboki na ƙwarai ne.​—Karanta Karin Magana 17:17.

Dattawa ba sa gaya wa membobin iyalinsu abubuwan da aka gaya musu cikin sirri (Ka duba sakin layi na 11) c

11. (a) A wace hanya ce dattawa da matansu za su iya nuna cewa za a iya yarda da su? (b) Wane darasi ne za mu iya koya daga dattijon da ba ya gaya wa iyalinsa abin da suka tattauna a ikilisiya? (Ka duba hoton.)

11 Ka yi abin da zai sa ’yan’uwanka su yarda da kai a ikilisiya. Dattawan da ba sa faɗan abin da aka gaya musu a asirce suna “kamar mafaka daga iska.” (Isha. 32:2) Za mu iya gaya wa dattawa abubuwan da ke zuciyarmu don mun san cewa ba za su gaya wa mutane abubuwan da muka gaya musu a asirce ba. Ba zai dace mu matsa musu su gaya mana asirin ’yan’uwa ba. Ƙari ga haka, muna godiya ga matan dattawa da ba sa matsa wa mazajensu su gaya musu asirin wasu. Hakika, idan dattijo bai gaya wa matarsa asirin wasu ba, yana taimaka mata ne. Ga abin da matar wani dattijo ta faɗa: “Ina godiya don yadda maigidana ba ya gaya min abubuwa game da ’yan’uwan da suka kai musu ziyara ko waɗanda suke bukatar taimako daga dattawa, ba ya ma ambata sunayensu. Ina farin ciki cewa maigidana ba ya gaya min abubuwan nan don kar su dame ni. Don haka, ina iya saki jiki in tattauna da kowa a ikilisiya. Kuma na tabbata cewa idan na gaya wa maigidana asirina, ba zai je yana gaya ma wasu ba.” Hakika, ya kamata dukanmu mu zama mutanen da za a iya yarda da mu. Me zai taimaka mana mu cim ma hakan. Bari mu tattauna halaye biyar da za su taimake mu.

KA KOYI HALAYEN DA ZA SU SA A YARDA DA KAI

12. Me ya sa za mu iya cewa ƙauna ce hali mafi muhimmanci da za ta sa mutane su yarda da mu? Ka ba da misali.

12 Ƙauna ita ce babban abin da za ta iya sa a yarda da mu. Yesu ya ce dokoki guda biyu mafi muhimmanci su ne mu ƙaunaci Jehobah kuma mu ƙaunaci maƙwabtanmu. (Mat. 22:​37-39) Muna ƙaunar Jehobah shi ya sa muna iya ƙoƙarinmu mu zama masu aminci. Alal misali, muna ƙaunar ’yan’uwanmu shi ya sa ba ma gaya ma wasu abin da suka gaya mana cikin sirri. Ba zai dace mu faɗi wani abin da zai sa su sha kunya, ya cutar da su, kuma ya sa su baƙin ciki ba.​—Yoh. 15:12.

13. A wace hanya ce sauƙin kai zai taimaka mana mu zama masu aminci?

13 Sauƙin kai zai taimaka mana mu zama masu aminci. Kirista mai sauƙin kai ba zai yi ƙoƙarin burge wasu da cewa shi ne mutum na farko da ya kawo labari ba. (Filib. 2:3) Ba zai yi ƙoƙari ya sa wasu su ɗauka cewa ya san wasu abubuwa da bai kamata ya faɗa ba. Sauƙin kai zai taimaka mana mu guji gaya wa mutane ra’ayinmu game da batutuwan da Littafi Mai Tsarki ko kuma littattafanmu ba su faɗi kome a kai ba.

14. A wace hanya ce basira take taimaka mana mu kasance da aminci?

14 Basira za ta taimaka wa Kirista ya san “lokacin yin shiru, da lokacin yin magana.” (M. Wa. 3:7) A wasu al’adu, akan ce “gaba da na gabansa, yin shiru ya fi yin magana daraja.” Ma’ana, akwai lokutan da ya kamata mutum ya yi shiru maimakon ya yi magana. Shi ya sa Karin Magana 11:12 ta ce: “Mai fahimta yakan yi shiru.” Ka yi la’akari da wannan misalin. Akwai wani dattijo da ya ƙware sosai kuma sau da yawa akan ce ya taimaka da sasanta matsaloli a wasu ikilisiyoyi. Ga abin da wani ɗan’uwa ya faɗa game da dattijon, ya ce: “Ba ya faɗan asirin ’yan’uwa a ikilisiyoyin da yake ziyarta.” Hakan ya sa dattawa da suke hidima tare da shi a ikilisiyarsa suna daraja shi sosai. Sun san cewa ba zai gaya ma wasu sirrinsu ba.

15. Ka ba da misalin da ya nuna cewa in mu masu gaskiya ne, mutane za su yarda mu.

15 Zama mai gaskiya wani abu ne kuma da zai sa mutane su yarda da mu. Ana yarda da mai gaskiya domin an san cewa a kowane lokaci yana faɗin gaskiya. (Afis. 4:25; Ibran. 13:18) Alal misali, a ce kana so ka ƙware a yadda kake koyarwa, sai ka gaya ma wani ya saurari jawabinka don ya ba ka shawara a kan yadda za ka ƙware. Wa za ka yarda da shawararsa? Wanda yake gaya maka abin da kake so ka ji ne ko kuma wanda zai gaya maka gaskiya? Mun san zaɓin da za ka yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwamma tsautawa a sarari, Da ƙauna wadda ta ke a ɓoye. Raunuka daga hannun masoyi amintattu ne.” (K. Mag. 27:​5, 6, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Ko da yake ba zai yi sauƙi mu karɓi gyara daga wurin abokinmu ba, a ƙarshe gaskiyar da ya faɗa zai taimaka mana.

16. Ta yaya Karin Magana 10:19 ta nuna muhimmancin kamun kai?

16 Wajibi ne mu kame kanmu sosai idan muna so mutane su yarda da mu. Kamun kai zai taimaka mana mu yi shiru idan aka jarraba mu mu faɗi wani abu da aka gaya mana a asirce. (Karanta Karin Magana 10:19.) Zai iya yi mana wuya mu kame kanmu idan muna amfani da dandalin sada zumunta. Idan ba mu yi hankali ba, za mu gaya wa mutane da yawa sirrin da bai kamata mu faɗa ba. Kuma da zarar mun fallasa wani sirri, ba za mu iya hana mutane yin amfani da bayanan yadda suka ga dama ba, ko kuma mu hana matsaloli tasowa sakamakon hakan. Ƙari ga haka, kamun kai zai taimaka mana mu yi shuru a lokacin da ’yan hamayya suke so su ruɗe mu mu ba da bayanan da za su jefa ’yan’uwanmu a cikin haɗari. Hakan zai iya faruwa ne idan ’yan sanda a ƙasashen da aka hana aikinmu suna yi mana tambayoyi. Za mu iya bin ƙa’idar da ke Littafi Mai Tsarki cewa mu ‘kame bakinmu’ a wannan yanayin da ma wasu dabam. (Zab. 39:1) Ko da muna sha’ani da iyalinmu ne ko abokanmu ko ’yan’uwanmu a cikin ikilisiya, yana da muhimmanci mu yi abin da zai sa a yarda da mu. Kuma abin da zai taimaka mana mu yi hakan shi ne kamun kai.

17. Ta yaya za mu taimaka ma ’yan’uwa a ikilisiya su ci gaba da yarda da juna?

17 Muna farin ciki sosai domin yadda Jehobah ya kawo mu cikin ƙungiyarsa, inda muke ƙaunar juna kuma muke yarda da juna! Hakkinmu ne mu yi abin da zai sa ’yan’uwanmu su yarda da mu. Yayin da kowannenmu yake yin iya ƙoƙarinsa ya kasance da halaye masu kyau kamar ƙauna da sauƙin kai da basira da gaskiya da kuma kamun kai, za mu ci gaba da yarda da juna a cikin ikilisiya. Dole ne mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu domin mu tabbatar wa ’yan’uwanmu cewa za su iya yarda da mu. Bari dukanmu mu ci gaba da yin koyi da Jehobah, kuma mu nuna cewa mu amintattu ne.

WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah

a Idan muna so mutane su yarda da mu, dole ne mu tabbatar musu cewa za su iya yin hakan. A wannan talifin, za mu koyi dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu yarda da juna, da kuma irin halayen da za mu nuna da za su sa mutane su yarda da mu.

b Idan mun san cewa wani ɗan’uwa ya yi zunubi mai tsanani, zai dace mu gaya masa ya nemi taimakon dattawa. Idan bai yi hakan ba, mu gaya wa dattawa da kanmu domin amincinmu ga Jehobah da kuma ikilisiya.

c BAYANI A KAN HOTUNA: Wani dattijo da bai gaya wa iyalinsa batun da suka tattauna da wata ’yar’uwa sa’ad da suka kai mata ziyarar ƙarfafa ba.