Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

3 | Taimako Daga Mutane da Aka Ambata a Littafi Mai Tsarki

3 | Taimako Daga Mutane da Aka Ambata a Littafi Mai Tsarki

LITTAFI MAI TSARKI YA AMBATA . . . Maza da mata masu aminci da suka yi fama da matsaloli “kamar mu.”​—YAKUB 5:17.

Abin da Hakan Yake Nufi

A cikin Littafi Mai Tsarki akwai labaran maza da mata da suka yi fama da baƙin ciki iri-iri. Saꞌad da muka karanta labaransu, za mu ga ɗaya daga cikinsu da ya yi fama da irin yanayin da muke ciki.

Yadda Yin Hakan Zai Taimaka

Dukanmu muna bukatar mu san cewa mutane sun fahimci yadda muke ji. Hakan ya fi muhimmanci ma idan muna fama da matsalar ƙwaƙwalwa. Idan muka karanta labaran mutane a Littafi Mai Tsarki, za mu koya cewa su ma sun yi fama da irin yanayin da muke ciki. Hakan zai sa mu gane cewa su ma sun yi fama kamar mu kuma sun sami taimako saꞌad da suke fama da tsananin damuwa da yanayi mai wuya.

  • Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da furuci da waɗanda suke cikin yanayi mai wuya suka faɗa. Ka taɓa yin tunanin cewa, ‘Kai! Wannan yanayin ya ishe ni’? Musa da Iliya da Dauda sun yi hakan.​—Littafin Ƙidaya 11:14; 1 Sarakuna 19:4; Zabura 55:4.

  • Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da wata mata mai suna Hannatu da ke cike da “ɓacin zuciya” domin ta kasa haihuwa kuma kishiyarta ta yi ta wulaƙanta.​—1 Sama’ila 1:​6, 10.

  • Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da wani mutum mai suna Ayuba da ya fuskanci irin yanayin da muke ciki. Ko da yake shi mai bangaskiya ne sosai ya yi fama da tsananin baƙin ciki, har ma ya ce: “Ina ƙyamar raina, na gaji da rayuwa.”​—Ayuba 7:16.

Idan muka koya yadda suka jimre da yanayinsu, mu ma za mu iya samun ƙarfin jimrewa da matsalolinmu.