Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Allah Ya Yi Alkawarin Ba Wa Mutane Cikakkiyar Lafiyar Kwakwalwa

Allah Ya Yi Alkawarin Ba Wa Mutane Cikakkiyar Lafiyar Kwakwalwa

A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya ba da shawarwarin da za su taimaka wa mutane da suke fama da matsalar ƙwaƙwalwa.

Ban da haka ma, ya yi alkawari cewa zai kawar da dukan abubuwan da suke jawo matsalar ƙwaƙwalwa har abada.

A lokacin da Allah zai cika wannan alkawarin, ba za a sake tunawa da abubuwan dā ba, kamar su baƙin ciki da matsalar ƙwaƙwalwa da kuma abubuwan da suka faru da mu a dā ba, “tunaninsu ma ba zai zo wa mutane ba.”​—Ishaya 65:17.

Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimaka maka ka koya lokacin da Allah zai cika wannan alkawarin da kuma yadda zai yi hakan.