Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 1

Ka Kasance da Tabbaci Cewa Maganar Allah ‘Gaskiya Ce’

Ka Kasance da Tabbaci Cewa Maganar Allah ‘Gaskiya Ce’

JIGON SHEKARARMU NA 2023: “Tushen maganarka gaskiya ne.”​—ZAB. 119:​160, New World Translation.

WAƘA TA 96 Kalmar Allah Tana da Daraja

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Me ya sa mutane da yawa a yau ba su gaskata da Littafi Mai Tsarki ba?

 YANA yi wa mutane da yawa wuya su gaskata da abubuwa a yau. Ba su san ko wane ne za su yarda da shi ba. Ba su san ko mutanen da suke girmamawa kamar ’yan siyasa da masana kimiyya da kuma ’yan kasuwa suna so su taimaka musu da gaske ba. Ƙari ga haka, ba sa daraja malaman addinai da suke da’awa cewa su Kiristoci ne. Don haka, ba za mu yi mamaki cewa ba sa yarda da Littafi Mai Tsarki ba, wato littafin da malaman addinan nan suke da’awa cewa suke bi.

2. Kamar yadda Zabura 119:160 ta faɗa, wane abu ne ya kamata mu gaskata da shi?

2 A matsayinmu na bayin Jehobah, muna da tabbaci cewa Jehobah Allah na gaskiya ne kuma yana son abin da zai amfane mu ne. (Zab. 31:5; Isha. 48:17) Mun san cewa za mu iya gaskata da abin da ke Littafi Mai Tsarki, domin “tushen maganar Allah gaskiya ne.” (Karanta Zabura 119:160. b) Mun yarda da abin da wani masanin Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa: “Babu abin da Allah ya faɗa da ba gaskiya ba ne, kuma dukansu za su faru. Bayin Allah za su iya gaskata da abin da ke ciki domin sun amince da Allah wanda ya faɗe shi.”

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Ta yaya za mu iya taimaka ma wasu su iya gaskata da Kalmar Allah kamar yadda muke yi? Bari mu yi tunani a kan dalilai guda uku da suka sa ya kamata mu gaskata da Littafi Mai Tsarki. Za mu ga cewa ba a canja abubuwan da aka rubuta a Littafi Mai Tsarki ba, cewa annabce-annabcen da ke ciki sun cika kuma yana da iko ya canja rayuwar mutane.

BA WANDA YA IYA CANJA SAƘON LITTAFI MAI TSARKI

4. Me ya sa wasu mutane suke ganin kamar an canja abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki?

4 Jehobah ya yi amfani da mutane 40 masu aminci don su rubuta Littafi Mai Tsarki. Amma a yanzu, ba mu da asalin rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā. Waɗanda muke da su su ne waɗanda aka kwafa. Hakan ya sa mutane suna tunani ko abin da muke karanta a Littafi Mai Tsarki a yau ya yi daidai da wanda waɗannan mutane suka rubuta. Ka taɓa tunanin yadda za mu gaskata cewa ya yi daidai da rubutu na farko?

Mutanen da aka koyar da su don su kwafa Nassosin Ibrananci sun yi hakan da kyau don su tabbatar cewa Kalmar Allah da suka kwafa daidai ne (Ka duba sakin layi na 5)

5. Ta yaya aka kwafa Nassosin Ibrananci? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

5 Don a kāre saƙon da ke Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya gaya wa mutanensa su kwafa abubuwan da ke ciki. Ya gaya wa kowane sarkin Isra’ila ya kwafa wa kansa Dokar da ya ba su, kuma ya naɗa Lawiyawa su koya wa mutane Dokar. (M. Sha. 17:18; 31:​24-26; Neh. 8:7) Bayan da Yahudawa suka komo daga bauta a Babila, ƙwararrun marubuta sun soma kwafan Nassosin Ibrananci da yawa. (Ezra 7:6) Marubutan sun mai da hankali yayin da suke yin aikin. Daga baya, marubutan suka fara ƙirga dukan kalmomin har da harufan don su tabbata cewa ba su yi kuskure ba. Amma domin su ajizai ne, an sami kurakurai kaɗan a cikin Littafi Mai Tsarkin da suka kwafa. Tun da yake mutane dabam-dabam ne suka kwafa rubuce-rubucen, daga baya an gano kurakuran. Ta yaya?

6. Ta yaya aka gano kurakurai a rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki da aka kwafa?

6 Masanan zamani suna da wata hanya mai kyau na gano kurakurai na waɗanda suka kwafa rubutun Littafi Mai Tsarki. Alal misali, a ce an gaya wa mutane 100 su kwafa wani rubutu da hannu. Idan wani a cikinsu ya yi kuskure, hanya ɗaya da za a iya gane kuskuren ita ce ta wajen gwada wanda ya kwafa da na sauran. Haka ma, ta wajen gwada rubuce-rubucen Littafin Mai Tsarki na dā da yawa, masanan sun iya sun gano kurakurai ko kuma wani abin da wataƙila wani ya cire.

7. Ta yaya marubuta da yawa suka mai da hankali yayin da suke kwafan rubutun Littafi Mai Tsarki?

7 Waɗanda suka kwafa rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā sun yi iya ƙoƙarinsu don su yi hakan daidai. Ga misalin da ya nuna cewa hakan gaskiya ne. A shekara ta 1008 ko 1009 bayan haihuwar Yesu ne aka gama kwafan nassosin Ibrananci da ya fi daɗewa. Ana kiran sa Leningrad Codex. Amma a kwanan nan, an samo rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā da yawa da aka rubuta su shekaru 1000 kafin Leningrad Codex. Amma wasu suna iya tunani cewa da yake an yi fiye da shekaru 1000 ana ta kwafan abin da ke cikin rubuce-rubucen nan, abin da ke cikin Leningrad Codex zai yi dabam sosai da abin da ke cikin rubuce-rubcen Littafi Mai Tsarki da aka rubuta kafin shi. Amma hakan bai faru ba. Sa’ad da masana suka gwada rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā da na yanzu, sun gano ɗan bambanci kaɗan, amma ma’anar ba ta canaja ba.

8. Mene ne bambancin rubuce-rubucen Nassosin Helenanci na dā da wasu rubuce-rubuce na dā?

8 Kiristocin ƙarni na farko ma sun kwafa Nassosi. Sun mai da hankali sosai sa’ad da suke kwafan littattafai 27 na Nassosin Helenanci. Sun yi amfani da littattafan a taronsu da kuma sa’ad da suke wa’azi. Wani masani da ya gwada rubuce-rubucen Nassosin Helenanci da littattafai da aka rubuta a lokaci ɗaya, ya ce: “A yau, muna da rubuce-rubucen Nassosin Helenanci na dā fiye da sauran littattafai da aka rubuta a lokacin, kuma a cike suke fiye da sauran littattafai.” Littafin nan Anatomy of the New Testament ya ce: “A yau muna da tabbaci cewa abin da muke karanta a Nassosin Helenanci daidai ne da abin da mawallafa na dā suka rubuta.”

9. Kamar yadda aka nuna a Ishaya 40:​8, wane tabbaci ne muke da shi game da Littafi Mai Tsarki?

9 Marubutan Littafi Mai Tsarki na dā sun mai da hankali sosai don su kwafa Littafi Mai Tsarki da kyau, shi ya sa muke karanta da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki da babu kuskure a yau. c Babu shakka, mun san cewa Jehobah ne ya tabbatar cewa ba a canja saƙon da ke cikin Kalmarsa da muke da shi a yau ba. (Karanta Ishaya 40:8.) Hakika, wasu suna iya cewa don ba a canja saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba, ba ya nufin cewa Allah ne ya sa aka rubuta shi. Saboda haka, bari mu tattauna wasu abubuwa da suka nuna cewa Allah ne ya sa aka rubuta shi.

ZA MU IYA GASKATA DA ANNABCE- ANNABCEN LITTAFI MAI TSARKI

Left: C. Sappa/​DeAgostini/​Getty Images; right: Image © Homo Cosmicos/​Shutterstock

Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki sun cika a dā kuma suna cika a yanzu (Ka duba sakin layi na 10-11) e

10. Ka ba da misalin annabcin da ya cika da ya nuna cewa abin da ke 2 Bitrus 1:21 gaskiya ne. (Ka duba hoton.)

10 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da annabce-annabce da yawa da sun riga sun cika, wasun su sun cika shekaru da yawa bayan an rubuta su. Abubuwan da suka faru sun nuna cewa waɗannan annabce-annabcen sun cika. Wannan ba abin mamaki ba ne domin mun san cewa Jehobah ne mawallafin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki. (Karanta 2 Bitrus 1:21.) Ka yi laꞌakari da annabcin da aka yi game da yadda za a hallaka Babila ta dā. A tsakanin shekara ta 778 da 732 kafin haihuwar Yesu, annabi Ishaya ya annabta cewa za a ci Babila da yaƙi. Ya faɗa cewa Sayirus ne zai ci birnin da yaƙi kuma ya faɗi yadda zai yi hakan. (Isha. 44:27–45:2) Ƙari ga haka, Ishaya ya annabta cewa daga baya za a halaka Babila gabaki ɗaya kuma babu wanda zai zauna a cikinta. (Isha. 13:​19, 20) Kuma hakan ya faru daidai yadda ya faɗa. Midiyawa da Fasiyawa sun ci Babila da yaƙi a shekara ta 539 kafin haihuwar Yesu, kuma yanzu babu wanda yake zama a wurin. Ka kalli bidiyon nan Littafi Mai Tsarki Ya Annabta Cewa Za A Hallaka Babila da ke littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, darasi na 3 batu na 5 a na’urarka.

11. Ka kwatanta yadda Daniyel 2:​41-43 suke cika a yau.

11 Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki ba su cika a dā kawai ba, a yau ma muna ganin cikarsu. Alal misali, ka yi tunanin yadda annabcin littafin Daniyel ya cika game da Gwamnatin Haɗin Gwiwa ta Birtaniya da Amirka. (Karanta Daniyel 2:​41-43.) Annabcin ya faɗa cewa gwamnatin za ta kasance da “ƙarfi” kamar ƙarfe da kuma “rashin ƙarfi” kamar laka. Kuma a yanzu mun ga cewa hakan gaskiya ne. Birtaniya da Amirka sun nuna suna da ƙarfi kamar ƙarfe a lokacin da suka ci Yaƙin Duniya na ɗaya da na biyu, kuma sun ci gaba da nuna iko sosai. Amma mazaunansu sun sa ikonsu ya ragu don suna amfani da ƙungiyoyin fararen hula da ƙungiyoyin kwadago da zanga-zanga don su hana wannan gwamnati yin wasu abubuwa da take so ta yi. Wani ƙwararen ɗan siyasa ya ce: “Ba ƙasar da ta kai Amirka rashin haɗin kai a batun siyasa.” Kuma Birtaniya ma tana fama da rashin haɗin kai domin mutanenta ba su yarda da irin tarayyar da za su riƙa yi da ƙasashen da ke Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Turai ba. Wannan rashin haɗin kai, ya sa gwamnatin Haɗin Gwiwa ta Birtaniya da Amirka ba ta ɗaukan mataki nan da nan yadda take so ta yi.

12. Wane tabbaci ne muke da shi game da annabcin Littafi Mai Tsarki?

12 Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da yawa da sun cika sun sa mun kasance da tabbaci cewa alkawuran da Allah ya yi game da nan gaba za su cika. Muna ji kamar wani marubucin zabura da ya yi addu’a ga Jehobah cewa: “Raina yana mutuwar neman cetonka, na sa zuciyata ga maganarka.” (Zab. 119:81) A Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya ba mu “sa zuciya da rayuwa ta nan gaba.” (Irm. 29:11) Za mu ji daɗin rayuwa a nan gaba don Jehobah ne ya yi mana alkawuran ba ɗan Adam ba. Idan muna nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki sosai, hakan zai sa mu amince da Kalmar Allah.

SHAWARWARIN LITTAFI MAI TSARKI SUNA TAIMAKA WA MILIYOYIN MUTANE

13. Kamar yadda yake a Zabura 119:​66, 138, wane dalili ne kuma zai sa mu amince da Littafi Mai Tsarki?

13 Wani dalili kuma da zai sa mu amince da Littafi Mai Tsarki shi ne domin yana taimaka wa mutanen da suka bi shawararsa. (Karanta Zabura 119:​66, 138.) Alal misali, ma’aurata da a dā sun so su kashe aurensu suna farin ciki yanzu domin sun bi shawarar Littafi Mai Tsarki. Yaransu suna farin ciki domin suna cikin iyalin da ke bauta wa Jehobah kuma suna kula da su da kuma nuna musu ƙauna.​—Afis. 5:​22-29.

14. Ka ba da misalin da ya nuna cewa bin shawarar Littafi Mai Tsarki yana taimaka wa mutane su canja rayuwarsu.

14 Ta wurin bin shawarar da ke Littafi Mai Tsarki, mugaye sun yi canje-canje a rayuwarsu kuma sun zama mutanen kirki. Ka yi la’akari da yadda shawarar Littafi Mai Tsarki ta taimaka ma wani fursuna mai suna Jack. d A dā shi mugu ne sosai kuma yana cikin waɗanda aka yi musu hukuncin ƙisa. Amma wata rana da ake nazari da wasu, yana nan yana saurarawa. Halin kirki da ’yan’uwa da ke gudanar da nazarin suka nuna ya ratsa zuciyar Jack, sai shi ma ya soma nazari. Da ya soma bin shawarar Littafi Mai Tsarki a rayuwarsa, sai ya canja halinsa kuma ya zama mutumin kirki. Da shigewar lokaci, Jack ya zama mai shela da bai yi baftisma ba kuma daga baya ya yi baftisma. Ya yi wa sauran fursunonin wa’azi game da Mulkin Allah kuma ya taimaka wa mutane huɗu a cikinsu su soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Jack ya riga ya zama mutumin kirki kafin ranar da za a kashe shi. Ɗaya daga cikin lawyoyin Jack ta ce: “Jack ba kamar mutumin da na sani shekaru 20 da suka shige ba. Koyarwar Shaidun Jehobah ya canja rayuwarsa.” Ko da yake an kashe Jack, misalinsa ya nuna cewa za mu iya amincewa da Kalmar Allah, kuma Kalmar tana da ikon canja rayuwar mutane.​—Isha. 11:​6-9.

Shawarar Littafi Mai Tsarki ta taimaka wa mutane da yawa daga wurare dabam-dabam su canja rayuwarsu (Ka duba sakin layi na 15) f

15. Ta yaya bin shawarar Littafi Mai Tsarki yake bambanta Shaidun Jehobah da wasu mutane a yau? (Ka duba hoton.)

15 Mutanen Jehobah suna da haɗin kai domin suna bin shawarar Littafi Mai Tsarki. (Yoh. 13:35; 1 Kor. 1:10) Siyasa da kabilanci da matsayin mutane suna jawo rashin haɗin kai a yau. Saboda haka, mutane da yawa sun lura cewa muna zaman lafiya da haɗin kai. Wani matashi mai suna Jean ya yi mamaki sosai sa’ad da ya ga haɗin kai da ke tsakanin Shaidun Jehobah. Ya yi girma a wata ƙasa a Afrika. Ya shiga soja sa’ad da aka soma yaƙi a ƙasarsu, amma daga baya ya koma wata ƙasa kusa da nasu. Ya haɗu da Shaidun Jehobah a ƙasar. Jean ya ce: “Na koyi cewa mabiyan addinin gaskiya ba sa saka hannu a siyasa. Maimakon haka, suna da haɗin kai kuma suna ƙaunar juna.” Ya ci gaba da cewa: “Na sadaukar da rayuwata don in kāre ƙasata. Amma sa’ad da na koyi gaskiya, na tsai da shawarar yin amfani da rayuwata don in bauta wa Jehobah.” Jean ya canja gabaki ɗaya. Maimakon yin faɗa da mutanen da suka fito daga wata al’umma, yanzu yana yi wa kowa wa’azin salama. Yadda Littafi Mai Tsarki yake taimaka wa mutane da suka fito daga wurare dabam-dabam ya nuna cewa za mu iya amince da Kalmar Allah.

KA CI GABA DA AMINCE DA KALMAR ALLAH

16. Me ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da amincewa da Kalmar Allah?

16 Yayin da yanayin duniya yake ci gaba da taɓarɓarewa, zai yi mana wuya mu amince da Kalmar Allah. Mutane za su yi ƙoƙari su sa mu soma shakkar koyarwar Littafi Mai Tsarki, ko Jehobah ne ya naɗa bawan nan mai aminci mai hikima ya yi mana ja-goranci a yau. Amma idan muna da tabbaci cewa Kalmar Allah gaskiya ce, za mu yi iya ƙoƙarinmu don kada mu bar su su raunana bangaskiyarmu. Za mu ƙudiri niyyar bin ƙa’idodin Jehobah har abada. (Zab. 119:112) Ba za mu ji kunyar yi musu wa’azi da ƙarfafa su su yi rayuwar da ta jitu da koyarwar da ke Kalmar Allah ba. (Zab. 119:46) Kuma za mu yi ‘haƙuri da farin ciki’ sa’ad da muke jimre wa mawuyacin yanayi har da tsanantawa.​—Kol. 1:11; Zab. 119:​143, 157.

17. Mene ne jigon shekararmu zai tuna mana?

17 Muna godiya sosai ga Jehobah don yadda ya sa muka koyi gaskiya! Gaskiyar tana taimaka mana mu kasance da kwanciyar hankali da kuma tabbaci. Ƙari ga haka, ta koya mana yadda za mu yi rayuwa a wannan duniyar da take daɗa taɓarɓarewa. Tana sa mu kasance da bege cewa a nan gaba za mu more rayuwa a Mulkin Allah. Bari jigon shekararmu na 2023 ya taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da tabbaci cewa Kalmar Allah gaskiya ce!​—Zab. 119:160.

WAƘA TA 94 Muna Godiya Jehobah Don Kalmarka

a Jigon da aka zaɓa na shekara ta 2023 zai ƙarfafa bangaskiyarmu. Jigon shi ne: “Tushen maganarka gaskiya ne.” (Zab. 119:​160, New World Translation) Babu shakka ka gaskata da maganar nan. Amma mutane da yawa ba su gaskata da Littafi Mai Tsarki ba, kuma ba su yarda cewa zai iya ba mu shawarwari masu kyau ba. A wannan talifin, za mu bincika dalilai uku da za mu iya amfani da su don mu tabbatar wa masu zuciyar kirki cewa za su iya gaskata da Littafi Mai Tsarki da shawarar da ke cikinsa.

b Zabura 119:160 (NW ): “Tushen maganarka gaskiya ne, kuma dukan shari’unka na adalci za su kasance har abada.”

c Don ƙarin bayani game da yadda aka kāre Littafi Mai Tsarki, ka shiga dandalin jw.org kuma ka rubuta “Tarihi da Littafi Mai Tsarki” a sashen bincike.

d An canja wasu sunayen.

e BAYANI A KAN HOTUNA: Allah ya annabta cewa za a hallaka birnin Babila na dā.

f BAYANI A KAN HOTUNA: Wani matashi ya koya daga Littafi Mai Tsarki yadda zai riƙa zaman lafiya da mutane kuma ya taimaka musu maimakon ya riƙa faɗa da su.