Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI Na 5

‘Ƙaunar Almasihu Tana Bi da Mu’

‘Ƙaunar Almasihu Tana Bi da Mu’

“Saboda ƙaunar Almasihu da take bi da mu . . . waɗanda suke da rai, kada su yi zaman ganin dama.”​—2 KOR. 5:​14, 15.

WAƘA TA 13 Mu Riƙa Bin Misalin Yesu

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1-2. (a) Yaya za mu iya ji idan muka yi tunani a kan rayuwar Yesu da hidimar da ya yi? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

 IDAN wanda muke ƙauna ya mutu, mukan yi kewarsa sosai. Da farko za mu iya yin baƙin ciki sosai idan muka yi tunanin abin da ya faru ꞌyan kwanaki kafin ya mutu, musamman idan ya sha wahala sosai kafin ya mutu. Daga baya za mu iya yin farin ciki idan muka yi tunani a kan wani abin da ya koya mana ko wani abin da ya yi ko ya faɗa don ya ƙarfafa mu ko don ya sa mu yi murmushi.

2 Haka ma, mukan yi baƙin ciki sosai idan muka karanta game da yadda Yesu ya sha wahala kuma ya mutu. A lokacin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, mukan ɗauki lokaci sosai don mu yi tunani a kan muhimmancin hadayar da Yesu ya yi. (1 Kor. 11:​24, 25) Amma mukan yi farin ciki idan muka yi tunani a kan dukan abubuwan da Yesu ya faɗa da abubuwan da ya yi a lokacin da yake duniya. Muna samun ƙarfafa idan muka yi tunani a kan abin da yake yi yanzu da kuma abin da zai yi mana a nan gaba. Kamar yadda za mu gani a wannan talifin, yin bimbini a kan abubuwan nan da kuma ƙaunar da yake nuna mana zai sa mu yi abubuwan da za su nuna cewa muna godiya.

MUNA BIN YESU DON MU NUNA GODIYARMU

3. Waɗanne dalilai ne muke da su da suka sa ya kamata mu yi godiya sosai don fansar da Yesu ya yi?

3 Mukan yi godiya sosai idan muka yi tunani a kan rayuwar Yesu da kuma mutuwarsa. A lokacin da Yesu yake duniya, ya koya wa mutane abubuwa masu kyau da Mulkin Allah zai yi. Muna godiya sosai domin wannan gaskiyar a kan Mulkin Allah. Muna kuma godiya domin fansar da Yesu ya bayar domin hakan ya sa muna jin daɗin dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma Yesu. Duk waɗanda suka ba da gaskiya ga Yesu suna da begen yin rayuwa har abada kuma a nan gaba za su sake ganin ƙaunatattunsu da suka mutu. (Yoh. 5:​28, 29; Rom. 6:23) Ba mu yi kome da ya sa muka cancanci waɗannan albarkun ba, kuma ba za mu iya biyan Allah da Kristi don abin da suka yi mana ba. (Rom. 5:​8, 20, 21) Amma za mu iya nuna musu yadda muke godiya sosai. Ta yaya za mu iya yin hakan?

Ta yaya yin tunanin misalin Maryamu daga Magadala zai iya taimaka maka ka nuna godiya? (Ka duba sakin layi na 4-5)

4. Ta yaya ne Maryamu daga Magadala ta nuna godiya don abin da Yesu ya yi mata. (Ka duba hoton.)

4 Ka yi la’akari da misalin wata Bayahudiya mai suna Maryamu daga Magadala. Ta sha wahala sosai domin aljanu guda bakwai sun yi ta wahalar da ita. Ba mamaki ta yi tunani cewa babu wanda zai iya taimaka mata. Don haka, ka yi tunanin irin godiyar da ta yi sa’ad da Yesu ya ceto ta daga wahalar da take sha! Godiyar da ta nuna ya sa ta zama mabiyar Yesu kuma ya sa ta yi amfani da lokacinta da ƙarfinta da kuma abubuwan da take da su don ta tallafa wa Yesu sa’ad da yake duniya. (Luk. 8:​1-3) Ko da yake Maryamu ta nuna godiya sosai don abin da Yesu ya yi mata, mai yiwuwa ba ta san cewa Yesu zai yi mata abubuwa fiye da hakan a nan gaba ba. Mai yiwuwa ba ta san cewa zai ba da ransa a madadin ꞌyan Adam domin duk “wanda ya ba da gaskiya gare shi” ya sami rai na har abada ba. (Yoh. 3:16) Duk da haka, Maryamu ta nuna godiyarta ga Yesu Kristi ta wajen nuna masa ƙauna marar canjawa. A lokacin da Yesu yake shan wahala a kan gungume, Maryamu ta tsaya kusa da wurin domin ta damu da shi kuma ta so ta ƙarfafa waɗanda suke wurin. (Yoh. 19:25) Bayan da Yesu ya mutu, Maryamu da wasu mata biyu sun kai kayan ƙanshi don su shafa wa gawarsa. (Mar. 16:​1, 2) Jehobah ya albarkaci Maryamu sosai domin ƙauna marar canjawa da ta nuna wa Yesu. Bayan da aka tā da shi daga mutuwa, Yesu ya sami Maryamu kuma ya tattauna da ita. Wannan gata ne da almajiransa kaɗan ne kawai suka samu.​—Yoh. 20:​11-18.

5. Ta yaya ne za mu nuna godiyarmu don dukan abubuwan da Jehobah da Yesu suka yi mana?

5 Mu ma za mu iya nuna godiyarmu don abubuwan da Jehobah da Yesu suka yi mana ta wajen yin amfani da lokacinmu da ƙarfinmu ko kuɗinmu don mu bauta wa Jehobah. Alal misali, za mu iya ba da kanmu don mu taimaka wajen gina da kuma kula da wuraren ibada.

YADDA MUKE ƘAUNAR JEHOBAH DA YESU YANA SA MU ƘAUNACI MUTANE

6. Me ya sa za mu iya ce fansa kyauta ce ga kowannenmu?

6 Idan muka yi la’akari da yadda Jehobah da Yesu suke ƙaunar mu, hakan zai sa mu ma mu ƙaunace su. (1 Yoh. 4:​10, 19) Muna daɗa ƙaunarsu sa’ad da muka gano cewa Yesu ya mutu saboda kowannenmu ne. Manzo Bulus ya amince da hakan kuma ya nuna godiyarsa sa’ad da ya rubuta wa Kiristoci da ke Galatiyawa cewa: ‘Ɗan Allah . . . ya ƙaunace ni har ya ba da ransa domina.’ (Gal. 2:20) Jehobah zai iya jawo ka kusa da shi don ka zama abokinsa domin Yesu ya riga ya mutu saboda mu. (Yoh. 6:44) Sanin cewa Jehobah ya ga abu mai kyau a zuciyarka kuma ya ba da abu mafi tamani don ka zama abokinsa yana sa ka farin ciki, ko ba haka ba? Hakan ba ya sa ka daɗa ƙaunar Jehobah da kuma Yesu? Don haka za mu iya tambayar kanmu cewa: “Me ya kamata in yi don ƙaunar da suka nuna mini?”

Ya kamata yadda muke ƙaunar Allah da kuma Kristi ya sa mu mu yi wa’azi ga kowane irin mutane (Ka duba sakin layi na 7)

7. Kamar yadda yake a hoton, ta yaya dukanmu za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da kuma Yesu? (2 Korintiyawa 5:​14, 15; 6:​1, 2)

7 Yadda muke ƙaunar Jehobah da kuma Yesu yana sa mu nuna wa mutane ƙauna. (Karanta 2 Korintiyawa 5:​14, 15; 6:​1, 2.) Hanya ɗaya da za mu iya nuna cewa muna ƙaunar su ita ce ta wajen yin wa’azi da ƙwazo. Mukan yi wa kowa da muka haɗu da shi wa’azi. Ba ma ƙin yi wa mutane wa’azi saboda launin fatarsu ko ƙabilarsu. Muna yi wa kowa wa’azi ko da suna da kuɗi ko ba su da kuɗi, ko sun je makaranta ko ba su je makaranta ba. Idan muka yi wa kowa da muka haɗu da shi wa’azi, muna yin nufin Jehobah ke nan domin nufinsa ne “dukan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.”​—1 Tim. 2:4.

8. Ta yaya ne za mu nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna?

8 Ƙari ga haka, mukan nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da Kristi ta wajen nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna. (1 Yoh. 4:21) Mukan damu da su sosai kuma mu taimaka musu. Mukan ta’azantar da su idan suka rasa ƙaunatattunsu, mu ziyarce su idan suna rashin lafiya kuma mu yi iya ƙoƙarinmu mu ƙarfafa su a lokacin da suke sanyin gwiwa. (2 Kor. 1:​3-7; 1 Tas. 5:​11, 14) Mukan yi addu’a a madadin su domin mun san cewa “addu’ar mai adalci tana da ƙarfin aiki da iko sosai.”​—Yak. 5:16.

9. A wace hanya ce kuma za mu iya nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna?

9 Muna kuma nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna ta wajen yin iyakacin ƙoƙarinmu don mu yi zaman lafiya da su. Mukan yi iya ƙoƙarinmu don mu yi koyi da yadda Jehobah yake gafarta wa mutane. Da yake Jehobah ya yarda ya ba da Ɗansa ya mutu don zunubanmu, ya kamata mu kasance a shirye don mu gafarta wa ꞌyanꞌuwanmu idan suka yi mana laifi. Kada mu zama kamar mugun bawan da Yesu ya ambata a wani kwatanci. Duk da cewa maigidansa ya yafe masa bashi mai yawa da yake bin sa, wannan bawan ya ƙi ya gafarta wa abokin aikinsa ƙaramin bashi da yake bin sa. (Mat. 18:​23-35) Idan ka sami saɓani da wani a cikin ikilisiya, za ka iya ɗaukan mataki don ku sasanta kafin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu? (Mat. 5:​23, 24) Idan ka yi hakan, za ka nuna cewa kana ƙaunar Jehobah da kuma Yesu sosai.

10-11. A wace hanya ce dattawa za su iya nuna cewa suna ƙaunar Jehobah da kuma Yesu? (1 Bitrus 5:​1, 2)

10 A wace hanya ce dattawa za su iya nuna cewa suna ƙaunar Jehobah da Yesu? Wata hanya mai muhimmanci na yin hakan ita ce ta wajen kula da tumakin Yesu. (Karanta 1 Bitrus 5:​1, 2.) Yesu ya bayyana wa manzo Bitrus hakan dalla-dalla. Bayan da Bitrus ya yi musun sanin Yesu sau biyu, da alama ya yi marmarin ya nuna wa Yesu cewa yana ƙaunarsa. Bayan da aka tā da Yesu daga mutuwa, sai Yesu ya tambayi Bitrus ya ce: “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Mun tabbata cewa Bitrus ya yi iyakacin ƙoƙarinsa don ya nuna wa Ubangijinsa cewa yana ƙaunarsa. Yesu ya gaya wa Bitrus cewa: “Ka yi kiwon tumakina.” (Yoh. 21:​15-17) Kuma daga lokacin har ƙarshen rayuwarsa, Bitrus ya kula da tumakin Ubangiji don ya nuna cewa yana ƙaunar Yesu.

11 Dattawa, a cikin makonni kafin ranar Tunawa da Mutuwar Yesu da kuma bayan haka, ta yaya za ku nuna cewa abin da Yesu ya faɗa wa Bitrus yana da muhimmanci a gare ku? Za ku iya nuna yadda kuke ƙaunar Jehobah da kuma Yesu ta wajen kai ziyarar ƙarfafa ga ꞌyanꞌuwa a kai a kai da kuma yin iyakacin ƙoƙarinku ku taimaka ma waɗanda suka yi sanyin gwiwa don su komo ga Jehobah. (Ezek. 34:​11, 12) Za ku kuma iya ƙarfafa ɗaliban Littafi Mai Tsarki da wasu da suke son saƙonmu da suka halarci wannan taron. Ya kamata ku taimaka musu su ga cewa muna marabtarsu domin muna sa rai cewa su ma za su iya zama mabiyan Yesu.

MUNA DA ƘARFIN ZUCIYA DON MUNA ƘAUNAR KRISTI

12. Me ya sa yin tunanin abin da Yesu ya faɗa a dare na ƙarshe kafin a kashe shi zai sa mu kasance da ƙarfin zuciya? (Yohanna 16:​32, 33)

12 A dare na ƙarshe kafin a kashe Yesu, Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “A cikin duniyar nan kuna shan azaba, amma ku kasance da ƙarfin zuciya gama na yi nasara a kan duniya.” (Karanta Yohanna 16:​32, 33.) Me ya taimaka wa Yesu ya kasance da ƙarfin zuciya sa’ad da maƙiyansa suka yi masa barazana kuma ya riƙe amincinsa har mutuwa? Ya dogara ga Jehobah. Da yake Yesu ya san cewa mabiyansa za su fuskanci gwaji irin wanda ya fuskanta, Yesu ya roƙe Jehobah don ya kāre su. (Yoh. 17:11) Me ya sa hakan yana sa mu kasance da ƙarfin zuciya? Domin Jehobah ya fi maƙiyanmu iko. (1 Yoh. 4:4) Jehobah yana ganin kome. Saboda haka, muna da tabbaci cewa idan mun dogara ga Jehobah, za mu iya daina jin tsoro kuma mu nuna ƙarfin zuciya.

13. Ta yaya Yusufu mutumin Arimatiya ya nuna ƙarfin zuciya?

13 Ka yi la’akari da misalin Yusufu, mutumin Arimatiya. Shi mutum ne mai matsayi sosai tsakanin Yahudawa kuma yana cikin alƙalan Kotun Ƙoli na Yahudawa. Amma a lokacin da Yesu yake hidimarsa a duniya, Yusufu bai kasance da ƙarfin zuciya ba. Yohanna ya ce shi “almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin tsoron Yahudawa.” (Yoh. 19:38) Ko da yake Yusufu ya amince da saƙo game da Mulkin Allah, ya ƙi ya nuna wa mutane cewa ya ba da gaskiya ga Yesu. Babu shakka, ya ji tsoro cewa zai rasa matsayinsa a cikin al’ummar. Amma Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa bayan da Yesu ya mutu, Yusufu “ya yi ƙarfin hali ya tafi wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.” (Mar. 15:​42, 43) A wannan lokacin, Yusufu ya daina ɓoye cewa shi almajirin Yesu ne.

14. Me ya kamata ka yi idan kana jin tsoron mutane?

14 Ka taɓa jin tsoron mutane kamar yadda Yusufu ya yi? Shin a makarantarka ko a wurin aikinka, kakan ji kunyar gaya wa mutane cewa kai Mashaidin Jehobah ne? Shin kana jinkirin soma yin wa’azi ko yin baftisma don kana tsoron abin da mutane za su faɗa game da kai? Kada ka bar hakan ya hana ka yin abin da ka san ya dace. Ka yi addu’a ga Jehobah da dukan zuciyarka. Ka roƙe shi ya ba ka ƙarfin zuciya don ka yi nufinsa. Yayin da kake ganin yadda Jehobah yake amsa addu’o’inka, za ka daɗa ƙarfin zuciya.​—Isha. 41:​10, 13.

FARIN CIKI YANA TAIMAKA MANA MU BAUTA WA JEHOBAH BABU FASAWA

15. Bayan da Yesu ya bayyana ga almajiransa, mene ne farin cikin da suka yi ya taimaka musu su yi? (Luka 24:​52, 53)

15 Almajiran Yesu sun yi baƙin ciki sosai sa’ad da Yesu ya mutu. Ka yi tunanin abin da ya faru da su. Sun rasa abokinsu kuma sun ji kamar ba su da mafita. (Luk. 24:​17-21) Amma sa’ad da Yesu ya bayyana a gare su, ya ɗauki lokaci ya bayyana musu yadda rayuwarsa ta cika annabcin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ya ba su wani aiki mai muhimmanci su yi. (Luk. 24:​26, 27, 45-48) A lokacin da Yesu ya koma sama bayan kwanaki 40, almajiransa sun riga sun daina baƙin ciki kuma sun soma farin ciki. Sun yi farin ciki sosai don sun san cewa Yesu yana raye kuma zai taimaka musu su yi aiki mai muhimmanci da ya ba su su yi. Farin cikin da suka yi ya taimaka musu su yabi Jehobah babu fashi.​—Karanta Luka 24:​52, 53; A. M. 5:42.

16. A wace hanya ce za mu iya bin misalin almajiran Yesu?

16 A wace hanya ce za mu iya bin misalin almajiran Yesu? Za mu iya yin farin ciki yayin da muke bauta wa Jehobah a kowane lokaci a cikin shekara, ba sai lalle a lokacin Tunawa da Mutuwar Yesu ba. Hakan yana nufin cewa za mu sa Mulkin Allah farko a rayuwarmu. Alal misali, wasu sun shirya lokacinsu yadda za su iya yin wa’azi, su halarci taro kuma su yi ibada ta iyali a kai a kai. Wasu ma sun sadaukar da kayayyakin da mutane za su iya ganin kamar suna da muhimmanci sosai don su iya ƙara himma a ikilisiya ko kuma su ƙaura inda ake bukatar masu shela sosai. Ko da yake muna bukatar jimrewa yayin da muke ci gaba da bauta wa Jehobah, Jehobah ya yi alkawari cewa zai yi mana albarka sosai idan mun saka al’amuran Mulkinsa farko a rayuwa.​—K. Mag. 10:22; Mat. 6:​32, 33.

A lokacin Tunawa da Mutuwar Yesu, ka ɗauki lokaci ka yi bimbini a kan abin da Jehobah da kuma Yesu sun yi maka (Ka duba sakin layi na 17)

17. Me ka ƙudura cewa za ka yi a wannan lokacin Tunawa da Mutuwar Yesu? (Ka duba hoton.)

17 Muna ɗokin Tunawa da Mutuwar Yesu a ranar Talata, 4 ga Afrilu. Amma kada ka jira har sai lokacin ya isa kafin ka soma tunanin rayuwar Yesu da mutuwarsa da kuma yadda shi da Jehobah suka nuna mana ƙauna. Ka riƙa tunanin waɗannan abubuwan a kai a kai makonni kafin ranar Tunawa da Mutuwar Yesu da kuma bayan hakan. Alal misali, ka ɗauki lokaci ka karanta kuma ka yi bimbini a kan littafin nan Taimako Don Nazarin Kalmar Allah, a ƙarƙashin jigon nan, “Muhimman Aukuwa a Rayuwar Yesu a Duniya.” Yayin da kake hakan, ka mai da hankali ga ayoyin da za su taimaka maka ka daɗa nuna godiya, da ƙauna, kuma ka daɗa kasancewa da ƙarfin zuciya da farin ciki. Sai ka yi tunanin hanyoyin da za ka iya nuna godiya ga Jehobah da kuma Yesu. Ka tabbata cewa Yesu zai yi farin ciki yayin da kake iya ƙoƙarinka ka tuna da shi a wannan lokacin Tunawa da Mutuwar Yesu.​—R. Yar. 2:19.

WAƘA TA 17 “Na Yarda”

a A lokacin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, ana ƙarfafa mu mu yi tunani sosai a kan rayuwar Yesu da mutuwarsa da kuma irin ƙaunar da Uban da shi Yesu suka nuna mana. Yin hakan zai sa mu yi abin da zai nuna cewa muna godiya ga Jehobah da Yesu Kristi. A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi da za mu iya nuna godiyarmu don fansa da kuma yadda za mu nuna ƙauna ga Jehobah da kuma Yesu. Za mu kuma koyi yadda za mu nuna godiyarmu ga ꞌyanꞌuwa maza da mata da yadda za mu nuna ƙarfin zuciya da kuma yadda za mu yi farin ciki yayin da muke yin ayyukan ibada.