Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 6

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Koya Mana Game da Mawallafinsa

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Koya Mana Game da Mawallafinsa

“Ka rubuta dukan maganar da na faɗa maka a cikin littafi.”​—IRM. 30:2.

WAƘA TA 96 Kalmar Allah Tana da Daraja

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Mene ne ya sa kake godiya domin Littafi Mai Tsarki?

 MUNA godiya sosai ga Jehobah don Littafi Mai Tsarki! A cikin Littafi Mai Tsarki, ya yi mana tanadin shawarwari da za su iya taimaka mana don mu jimre matsalolin da za mu fuskanta a yau. Ya kuma ba mu bege game da nan gaba. Mafi muhimmanci ma, Jehobah ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ya bayyana mana halayensa dabam-dabam. Yayin da muka yi tunani a kan halayensa masu kyau, hakan na ratsa zuciyarmu, yana sa mu kusace Jehobah kuma mu zama abokansa.​—Zab. 25:14.

2. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya bayyana kansa ga ꞌyan Adam?

2 Jehobah yana son mutane su san shi. A zamanin dā, ya bayyana kansa ta wajen mafarkai, da wahayoyi, har da malaꞌiku ma. (L. Ƙid. 12:6; A. M. 10:​3, 4) Ba za mu iya sanin mafarkan da wahayoyin da kuma saƙonnin da malaꞌiku suka bayar idan ba a rubuta su ba. Shi ya sa Jehobah ya sa mutane su rubuta “a cikin littafi” abin da yake so mu sani. (Irm. 30:2) Da yake “Allah, hanyarsa cikakkiya ce ƙwarai,” za mu iya tabbata cewa wannan hanyar da yake amfani ya yi magana da mu za ta amfane mu.​—Zab. 18:30.

3. Mene ne Jehobah ya yi don ya tabbata cewa muna da Littafi Mai Tsarki a yau? (Ishaya 40:8)

3 Karanta Ishaya 40:8. Kalmar Allah ta yi tanadin shawarwari masu kyau ga amintattun maza da mata na ɗarurruwan shekaru yanzu. Ta yaya hakan ya yiwu? Wannan tambaya ce mai muhimmanci domin an rubuta Littafi Mai Tsarki da daɗewa a kan naɗaɗɗun littattafan da suka lalace da shigewar lokaci. Don haka, ba mu da asalin Littafi Mai Tsarki da aka rubuta a kan naɗaɗɗun littattafan yanzu. Amma Jehobah ya tabbatar cewa an iya an kwafa daga ainihin naɗaɗɗun littattafan. Ko da yake waɗanda suka kwafi littattafan nan ajizai ne, sun ƙware a aikin sosai. Game da Nassosin Ibrananci, wani masani ya rubuta cewa: “Muna da tabbaci cewa babu wani littafin da aka kwafa a dā kamar Littafi Mai Tsarki a Ibrananci.” Ko da yake an rubuta Littafi Mai Tsarki da daɗewa a kan abubuwan da za su iya lalacewa, kuma waɗanda suka kwafi Littafi Mai Tsarki ajizai ne, za mu iya tabbata cewa kalmomin da muke karantawa a cikin Littafi Mai Tsarki a yau suna ɗauke da raꞌayin Mawallafin, wato Jehobah.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Jehobah ne yake ba da “kowace baiwa mai kyau, da kowace cikakkiyar kyauta.” (Yak. 1:17) Littafi Mai Tsarki ɗaya ne daga cikin kyaututtuka masu kyau da Jehobah ya ba mu. Idan wani ya ba mu kyauta, kyautar tana nuna mana yadda ya san mu da kuma bukatunmu. Haka ma yake da wanda ya ba mu kyautar Littafi Mai Tsarki. Idan muka bincika wannan kyautar, za mu koyi abubuwa da yawa game da Jehobah. Za mu ga cewa ya san mu kuma ya san abubuwan da muke bukata sosai. A wannan talifin, za mu tattauna abubuwan da za mu iya koya a cikin Littafi Mai Tsarki game da halayen Jehobah guda uku: wato hikima da adalci da kuma ƙauna. Bari mu fara da tattauna yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah yana da hikima sosai.

LITTAFI MAI TSARKI YANA NUNA HIKIMAR ALLAH

5. A wace hanya ɗaya ce Littafi Mai Tsarki take nuna hikimar Allah?

5 Jehobah ya san cewa muna bukatar ja-gorancinsa. Kuma kyautar da ya ba mu, wato Littafi Mai Tsarki yana cike da hikimarsa. Shawarar Littafi Mai Tsarki tana taimaka wa mutane. Littafi Mai Tsarki yana canja rayuka. A lokacin da Musa ya rubuta littattafai na farko na Littafi Mai Tsarki, ya gaya wa Israꞌilawa cewa: “Wannan ba magana ba ce kawai, amma ranku ne.” (M. Sha. 32:47) Waɗanda suke bin shawarar Littafi Mai Tsarki za su iya yin nasara kuma su ji daɗin rayuwa. (Zab. 1:​2, 3) Ko da yake an rubuta Littafi Mai Tsarki tun da daɗewa, har yanzu yana gyara rayukan mutane. Alal misali, a dandalin jw.org, a ƙarƙashin “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane,” an nuna misalan mutane fiye da 30 waɗanda koyarwar Littafi Mai Tsarki ta yi ‘aiki a zuciyarsu’ domin sun “ba da gaskiya.”​—1 Tas. 2:13.

6. Me ya sa za mu iya ce babu littafin da ya kai Littafi Mai Tsarki?

6 Babu wani littafi da ke kama da Kalmar Allah. Domin Mawallafin Littafi Mai Tsarki, wato Jehobah, shi ne mafi iko a dukan duniya, shi madawwami ne kuma ya fi kowa hikima. Mutane sukan ci gaba da karanta wasu littattafai duk da cewa mawallafansu sun mutu, amma da shigewar lokaci, shawarwarinsu za su zama tsohon yayi. Akasin haka, shawarwarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su amfane mu har abada, kuma sun yi shekaru da yawa suna taimaka wa mutane. Saꞌad da muke karanta Littafi Mai Tsarki kuma muna tunani a kan abubuwan da muke koya, Mawallafin yakan yi amfani da ruhu mai tsarki ya taimaka mana mu ga yadda za mu yi amfani da shawarwarinsa a rayuwarmu. (Zab. 119:27; Mal. 3:16; Ibran. 4:12) Babu shakka, wannan Mawallafin Littafi Mai Tsarki yana marmarin ya taimaka maka. Hakan ya kamata ya sa mu so karanta Littafi Mai Tsarki kowane lokaci!

Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya sa mutanen Allah su kasance da haɗin kai a zamanin dā da kuma a zamaninmu? (Ka duba sakin layi na 7-8)

7. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya sa mutanen Allah a dā suka kasance da haɗin kai?

7 Wani dalili kuma da ya sa Littafi Mai Tsarki yake ɗauke da hikimar Allah shi ne, yana taimaka wa mutanen Allah su kasance da haɗin kai. A lokacin da Isra’ilawa suka shiga Ƙasar Alkawari, sun zauna a wurare dabam-dabam. Wasu sun zama masu kama kifi, wasu masu kiwon dabbobi, wasu kuma manoma. Israꞌilawan da suke zama a wani ɓangaren ƙasar za su iya daina damuwa game da sauran Israꞌilawa da suke wani ɓangare dabam. Jehobah ya shirya lokutan da Israꞌilawan za su haɗu tare don a karanta da kuma bayyana musu Kalmarsa. (M. Sha. 31:​10-13; Neh. 8:​2, 8, 18) Ka yi tunanin yadda wani Ba-israꞌile mai aminci zai ji idan ya iso Urushalima kuma ya ga miliyoyin Israꞌilawa daga wurare dabam-dabam! Ta wannan hanyar, Jehobah ya taimaka wa mutanensa su kasance da haɗin kai. Daga baya, da aka kafa ikilisiyar Kirista, ikilisiyar ta ƙunshi mutanen da suke yaruka dabam-dabam kuma suka fito daga ƙasashe dabam-dabam. Wasun su suna da arziki, wasu kuma talakawa ne. Amma domin dukansu suna ƙaunar Littafi Mai Tsarki, sun bauta wa Allah da haɗin kai. Waɗanda ba su jima da zama Kiristoci ba za su iya fahimtar Kalmar Allah ta taimakon ꞌyanꞌuwa masu bi da kuma ta zuwa taro.​—A. M. 2:42; 8:​30, 31.

8. Ta yaya ne Littafi Mai Tsarki yake sa mutanen Allah a yau su kasance da haɗin kai?

8 Allahnmu mai hikima ya ci gaba da yin amfani da Littafi Mai Tsarki don ya koyar da mutanensa, kuma ya sa su kasance da haɗin kai. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da gaskiya game da Jehobah da ya kamata mu sani. A kowane lokaci muna halartan taron mako, da manyan taro, da kuma taron yanki inda ake karanta da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki abu ne mai muhimmanci da Jehobah yake amfani da shi don ya taimaka wa mutanensa su “bauta masa da zuciya ɗaya.”​—Zaf. 3:9.

9. Wane hali ne muke bukata don mu fahimci saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki? (Luka 10:21)

9 Ka yi tunanin wata hanya kuma da Jehobah yake nuna hikima. Ya sa an rubuta sashen Littafi Mai Tsarki da yawa yadda mutane masu sauƙin kai ne kawai za su iya karanta kuma su fahimce ta. (Karanta Luka 10:21.) Mutane a koꞌina suna karanta Littafi Mai Tsarki. Wani masani ya faɗi cewa, “mutane da yawa suna karanta Littafi Mai Tsarki fiye da kowane littafi, kuma suna yin hakan a hankali.” Amma masu sauƙin kai ne kawai suke gane abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma su aikata shi.​—2 Kor. 3:​15, 16.

10. A wace hanya ce kuma Littafi Mai Tsarki yake nuna hikimar Jehobah?

10 Akwai wata hanya kuma da muka sake koya game da hikimar Jehobah a cikin Littafi Mai Tsarki. Jehobah yana amfani da Littafi Mai Tsarki ba don ya koyar da mutanensa gabaki ɗaya kawai ba ne, amma don ya koyar da kuma ƙarfafa kowannenmu ne. Idan muka karanta Kalmar Jehobah, za mu ga cewa Jehobah ya damu da kowannenmu. (Isha. 30:21) Idan kana fuskantar wata matsala, sau nawa ne kake karanta wata aya a cikin Littafi Mai Tsarki kuma ka ji kamar domin kai ne aka rubuta ayar? Duk da haka, an rubuta Littafi Mai Tsarki domin miliyoyin mutane su iya fahimta. Me ya sa Littafi Mai Tsarki yake ɗauke da bayanan da kake bukata? Hakan ya yiwu ne domin Mawallafin Littafi Mai Tsarki mai hikima ne sosai.​—2 Tim. 3:​16, 17.

LITTAFI MAI TSARKI YANA NUNA ADALCIN ALLAH

11. Saꞌad da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, ta yaya ne Allah ya nuna adalci?

11 Adalci wani hali ne na Jehobah. (M. Sha. 32:4) Duk wanda yake yin adalci ba ya nuna bambanci, kuma haka Jehobah yake. (A. M. 10:​34, 35; Rom. 2:11) Za mu iya tabbata cewa Jehobah ba ya nuna bambanci domin ya sa an rubuta Littafi Mai Tsarki a yarukan da mutane da yawa suke amfani da shi a lokacin. An rubuta littattafai 39 na farko a cikin Littafi Mai Tsarki da harshen Ibrananci, kuma yaren da mutanen Allah suka fi ganewa ke nan a lokacin. Amma a ƙarni na farko, da harshen Hellenanci ne aka rubuta sauran littattafai 27 na Littafi Mai Tsarki domin yaren da mutane suka fi amfani da shi ke nan a lokacin. Jehobah bai sa a rubuta Kalmarsa a yare guda ɗaya kawai ba. A yau, mutane kusan biliyan takwas a duniya suna yaruka da yawa. Ta yaya ne mutane da yawa za su iya koya game da Jehobah?

12. A wace hanya ɗaya ce Daniyel 12:4 ta cika a wannan kwanakin ƙarshe?

12 Ta wurin annabi Daniyel, Jehobah ya yi alkawari cewa a kwanakin ƙarshe, “ilimi” da ake samuwa daga cikin Littafi Mai Tsarki “zai ƙaru.” Mutane da yawa za su fahimta. ‘(Karanta Daniyel 12:4. b)’ Abin da ya taimaka wa mutane da yawa su fahimci Littafi Mai Tsarki shi ne, an fassara Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki. An wallafa su kuma an rarraba wa mutane da yawa. Littafi Mai Tsarki ne littafin da aka fi fassarawa da kuma rarrabawa a duk faɗin duniya. Kamfanonin da suke fassara Littafi Mai Tsarki sukan sayar da su da tsada sosai. Amma Shaidun Jehobah sun fassara Littafi Mai Tsarki gaba ɗayansa ko kuma rabinsa a yaruka fiye da 240, kuma kowa zai iya samun sa kyauta. Ta haka, mutane a faɗin duniya suna koya game da “labari mai daɗi na mulkin sama” kafin ƙarshen ya zo. (Mat. 24:14) Allahnmu mai adalci yana so ya ba wa mutane da yawa damar sanin sa ta wajen karanta Kalmarsa. Yana yin hakan ne domin yana ƙaunar dukanmu sosai.

LITTAFI MAI TSARKI YANA NUNA ƘAUNAR ALLAH

13. Me ya sa za mu iya ce Littafi Mai Tsarki yana nuna ƙaunar Jehobah? (Yohanna 21:25)

13 Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu san cewa halin Allah mafi girma shi ne ƙauna. (1 Yoh. 4:8) Ka yi laꞌakari da abin da Jehobah ya sa aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki da abin da bai yarda a rubuta ba. Ya tanadar mana daidai abin da muke bukata don mu kasance da dangantaka mai kyau da shi, mu ji daɗin rayuwa yanzu kuma mu sami rai na har abada. Amma da yake Jehobah yana ƙaunar mu, bai ba mu bayanai da yawa da ba ma bukata ba.​—Karanta Yohanna 21:25.

14. A wace hanya ce kuma Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa Allah yana ƙaunarmu?

14 Jehobah yana kuma nuna mana ƙauna ta yadda yake yin magana da mu a hanyar da ke girmama mu. A cikin Littafi Mai Tsarki, bai ba mu dokoki marasa iyaka ba, ko kuma ya gaya mana ainihin abin da za mu yi a kowane fannin rayuwarmu ba. A maimakon haka, yana amfani da labaran mutane, da annabce-annabce da kuma shawarwarin da za su taimaka mana mu yi zaɓi mai kyau. Ta hakan, Kalmar Allah tana sa mu ƙaunaci Allah kuma mu yi masa biyayya daga zuciyarmu.

Me ya sa ya kamata mu yi tunani a kan yadda Jehobah ya bi da mabiyansa a dā? (Ka duba sakin layi na 15)

15. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ya damu da mu? (b) A hoton nan, waye yarinyar nan da ɗanꞌuwan nan da kuma ꞌyarꞌuwar nan suke bimbini a kai? (Far. 39:​1, 10-12; 2 Sar. 5:​1-3; Luk. 2:​25-38)

15 Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa Jehobah ya damu da mu sosai. Ta yaya? Kalmarsa tana cike da labaran mutane. Za mu iya fahimtar yadda mutanen nan suka ji domin su mutane ne “kamar mu.” (Yak. 5:17) Idan muka lura da yadda ya yi shaꞌani da mutane kamar mu, hakan zai sa mu fahimci cewa Jehobah “mai jinƙai ne, mai yawan tausayi kuma.”​—Yak. 5:11.

16. Idan muka karanta game da mutanen da suka yi kuskure, me hakan yake koya mana game da Jehobah? (Ishaya 55:7)

16 Littafi Mai Tsarki ya nuna mana wata hanya da Jehobah yake ƙaunarmu. Ya tabbatar mana cewa Allahnmu ba zai yashe mu ba idan muka yi kuskure. Israꞌilawa sun yi ta yi wa Jehobah zunubi a kai a kai. Duk da haka, Jehobah ya gafarta musu idan suka tuba da gaske. (Karanta Ishaya 55:7.) Kiristoci a ƙarni na farko ma sun san cewa Allah yana ƙaunarsu sosai. Ruhu mai tsarki ya ja-goranci Manzo Bulus ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa masu bi su “yafe” ma wani mutum da ya tuba daga zunubi mai tsanani da yake yi, kuma su yi masa “ta’aziyya.” (2 Kor. 2:​6, 7; 1 Kor. 5:​1-5) Abin ban shaꞌawa ne cewa Jehobah ba ya ƙin bayinsa domin sun yi kuskure! A maimakon haka, yana taimaka musu cikin ƙauna, ya yi musu gyara kuma ya sake sa su zama abokansa. Ya yi alkawari cewa zai yi hakan wa duk waɗanda suka yi zunubi kuma suka tuba da gaske.​—Yak. 4:​8-10.

KA DARAJA KYAUTA MAI KYAU, WATO LITTAFI MAI TSARKI

17. Me ya sa babu wani littafi kamar Littafi Mai Tsarki?

17 Jehobah ya ba mu kyauta mai kyau. Me ya sa babu littafi kamar Littafi Mai Tsarki? Kamar yadda muka koya, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah yana da hikima, shi mai adalci ne kuma yana ƙaunar mu sosai. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana so mu san shi. Kuma yana so mu zama abokansa.

18. Ta yaya za mu nuna cewa muna godiya don kyauta mai kyau da Jehobah ya ba mu, wato Littafi Mai Tsarki?

18 Ba ma so mu yi wasa da wannan kyauta mai kyau da Allah ya ba mu, wato Kalmarsa. (Yak. 1:17) Don haka, bari mu ci gaba da gode masa don wannan kyautar. Za mu iya yin hakan ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kansa. Idan muka yi hakan, mu kasance da tabbacin cewa Mawallafin Littafi Mai Tsarki zai albarkaci ƙoƙarin da muke yi kuma za mu “sami sanin Allah.”​—K. Mag. 2:5.

WAƘA TA 98 Nassosi Hurarre Ne Daga Allah

a Littafi Mai Tsarki yana taimaka mana mu kusaci Jehobah. Mene ne Littafi Mai Tsarki zai iya koya mana game da hikimar Allah, adalcinsa da kuma ƙaunarsa? Abin da za mu koya zai iya taimaka mana mu daɗa daraja Kalmar Allah, kuma mu riƙa ɗaukan Littafi Mai Tsarki a matsayin kyauta daga Ubanmu na sama.

b Daniyel 12:4 (Mai Makamantu Ayoyi): “Amma kai, Daniyel, sai ka rufe maganar, ka kuma kulle littafin, har zuwa ƙarshen lokaci. Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru.”