Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 9

Ka Daraja Kyautar Rai

Ka Daraja Kyautar Rai

“Ta gare shi ne muke rayuwa, muke motsi, muka kuma kasance.”​—A. M. 17:28.

WAƘA TA 141 Rai, Kyauta Ce Daga Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Yaya Jehobah yake ɗaukan ranmu?

 A CE wani abokinka ya ba ka gida amma fentin gidan ya riga ya soma gogewa kuma akwai wuraren da ke yoyo. Duk da haka, kuɗin gidan zai kai miliyoyin naira idan aka sayar da shi. Babu shakka, za ka daraja gidan nan kuma ka kula da shi. Hakazalika, Jehobah ya ba mu wata kyauta mai daraja, wato rai. Jehobah ya nuna yana daraja ranmu ta wajen ba da Ɗansa don ya mutu a madadinmu.​—Yoh. 3:16.

2. Bisa ga 2 Korintiyawa 7:​1, mene ne Jehobah yake bukata daga gare mu?

2 Jehobah ne Tushen rai. (Zab. 36:9) Manzo Bulus ya amince da hakan saꞌad da ya ce: “Ta gare shi ne muke rayuwa, muke motsi, muka kuma kasance.” (A. M. 17:​25, 28) Don haka, za mu iya cewa ranmu kyauta ce daga wurin Allah. Allah yana tanada mana dukan abubuwan da muke bukata don mu rayu. (A. M. 14:​15-17) Amma ba ya yin muꞌujiza yanzu don kawai yana so mu rayu. A maimakon haka, yana so mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kula da lafiyar jikinmu kuma mu ci gaba da bauta masa. (Karanta 2 Korintiyawa 7:1.) Me ya sa ya kamata mu kāre ranmu da lafiyarmu, kuma ta yaya za mu iya yin hakan?

KA DARAJA KYAUTAR RAI

3. Wane dalili ne ya sa muke iya ƙoƙarinmu don mu kāre lafiyarmu?

3 Wani dalilin da ya sa muke bukatar mu kāre lafiyarmu shi ne, don mu bauta wa Jehobah da iya ƙarfinmu. (Mar. 12:30) Muna so mu ‘miƙa kanmu hadaya wadda take mai rai, mai tsarki, da kuma abin karɓa ga Allah,’ shi ya sa muke iya ƙoƙarinmu mu guji abin da zai sa mu rashin lafiya. (Rom. 12:1) Ko da yake muna yin ƙoƙari don mu kāre lafiyar jikinmu, mukan yi rashin lafiya. Amma muna yin iya ƙoƙarinmu don mu nuna wa Ubanmu na sama cewa muna daraja ran da ya ba mu.

4. Mene ne Sarki Dauda ya ƙudura cewa zai yi?

4 Sarki Dauda ya faɗi dalilin da ya sa yake daraja ran da Jehobah ya ba shi. Ya ce: “Wace riba ce mutuwata za ta kawo? Wace riba ce gangarawata kabari? Ƙurata za ta iya yabonka? Za ta iya yin shelar amincinka ne?” (Zab. 30:9) Mai yiwuwa saꞌad da Dauda ya kusan mutuwa ne ya rubuta kalaman nan. Amma ya ƙudura cewa zai yi duk abin da zai iya yi don ya kasance da rai da kuma ƙoshin lafiya domin ya ci gaba da bauta wa Jehobah. Babu shakka, mu ma abin da muke so mu yi ke nan.

5. Mene ne za mu iya yi ko da mun tsufa ko muna rashin lafiya?

5 Rashin lafiya da kuma tsufa za su iya hana mu yin abubuwan da muka saba yi a dā. Hakan zai iya sa mu baƙin ciki sosai. Duk da haka, zai dace mu yi iyakacin ƙoƙarinmu don mu ci gaba da kula da lafiyar jikinmu. Me ya sa? Domin kome tsufanmu ko rashin lafiyar da muke yi, za mu iya bauta wa Jehobah kamar yadda Sarki Dauda ya yi. Abin ban ƙarfafa ne sanin cewa Jehobah yana daraja mu ko da muna rashin lafiya ko mun tsufa. (Mat. 10:​29-31) Ko da ma mun mutu, Jehobah zai yi marmarin tā da mu. (Ayu. 14:​14, 15, Mai Makamantu Ayoyi) Don haka, yanzu da muke raye, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu mu kāre lafiyarmu da ranmu.

KA GUJI ABIN DA ZAI SA RANKA CIKIN HAƊARI

6. Mene ne Jehobah yake so mu yi idan ya zo ga batun ci da sha?

6 Littafi Mai Tsarki ba littafin da aka rubuta don a koya mana yadda za mu kula da lafiyar jikinmu ko abincin da za mu riƙa ci ba ne, amma yana gaya mana raꞌayin Jehobah game da abubuwan nan. Ya gargaɗe mu mu guji duk abin da zai iya jawo mana cuta. (M. Wa. 11:​10, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Yawan cin abinci da buguwa da giya suna da haɗari sosai kuma Littafi Mai Tsarki ya haramta hakan. (K. Mag. 23:20) Jehobah yana so mu riƙa kame kanmu saꞌad da muke yanke shawara game da abin da za mu ci da kuma abin da za mu sha.​—1 Kor. 6:12; 9:25.

7. Ta yaya gargaɗin da ke Karin Magana 2:11 yake taimaka mana mu yanke shawarwari game da lafiyar jikinmu?

7 Za mu iya nuna cewa muna daraja kyautar rai da Allah ya ba mu idan muna mai da hankali sosai saꞌad da muke yanke shawarwari. (Zab. 119:​99, 100; karanta Karin Magana 2:11.) Alal misali, za mu mai da hankali sosai yayin da muke zaɓan abubuwan da za mu ci. Idan akwai wani abincin da muke so sosai amma yana sa mu rashin lafiya, zai dace mu guji wannan abincin. Ƙari ga haka, za mu nuna cewa muna da hikima idan muna samun isasshen barci, da motsa jiki a kai a kai, da yin abubuwan da za su kāre lafiyarmu da kuma tsabtace gidanmu.

KA GUJI HATSARI

8. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da raꞌayin Jehobah a kan kāre lafiyarmu?

8 A cikin Dokar da Jehobah ya ba wa Israꞌilawa, an ambata abubuwan da za su taimaka musu su guji hatsari mai tsanani a gida ko a wurin aiki. (Fit. 21:​28, 29; M. Sha. 22:8) Ko da mutum ya kashe wani ba da gangan ba, zai fuskanci hukunci mai tsanani. (M. Sha. 19:​4, 5) Dokar ta ce a hukunta wanda ya ji wa ɗan da ba a haifa ba rauni ko da ba da gangan ba ne. (Fit. 21:​22, 23) Littafi Mai Tsarki ya nuna mana dalla-dalla cewa Jehobah yana so mu yi iya ƙoƙarinmu mu guji yin hatsari.

A irin waɗannan yanayoyin, ta yaya za mu nuna cewa muna daraja rai? (Ka duba sakin layi na 9)

9. Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu kāre kanmu daga yin hatsari? (Ka kuma duba hoton.)

9 Za mu nuna cewa muna daraja ran da Allah ya ba mu ta wajen yin iya ƙoƙarinmu mu kāre lafiyar jikinmu a gida da kuma wurin aiki. Alal misali, idan muna so mu yar da abubuwa masu tsini kamar allurai ko abubuwa masu guba ko kuma magani, za mu yi hakan yadda ba zai yi ma wasu lahani ba. Ƙari ga haka, ba za mu ajiye abubuwan nan inda yara ƙanana za su gani ba. Idan muka kunna wuta ko muna dafa ruwan zafi ko muna amfani da kayayyakin aiki, ba zai dace mu tafi mu bar abubuwan nan haka kawai ba. Ba zai dace mu yi tuki idan muna shan maganin da ke juya mana ido ba, ko idan rashin isasshen barci da kuma giya za su hana mu yin tuki da kyau. Ƙari ga haka, ba za mu bar waya ta raba hankalinmu saꞌad da muke tuki ba.

IDAN BALAꞌI YA AUKU

10. Mene ne za mu iya yi kafin balaꞌi ya auku da kuma saꞌad da yake aukuwa?

10 A wasu lokuta ba za mu iya hana abubuwa masu muni faruwa ba kamar su balaꞌi, annoba da yaƙe-yaƙe. Amma idan irin abubuwan nan suka faru, za mu iya kāre lafiyarmu kuma mu tsira ta wajen bin umurnin da hukumomin gwamnati suka ba mu. Alal misali, idan suka ce mu bar wurin ko kuma sun ba mu wasu dokoki. (Rom. 13:​1, 5-7) Muna iya shirya kanmu don balaꞌoꞌin da za su faru. Don haka, zai dace mu bi umurnin da shugabanni za su ba mu da za su taimaka mana mu kasance a shirye. Alal misali, za mu iya ajiye ruwa da abincin da ba zai lalace ba da kuma wasu kayan jinyar gaggawa da za su taimaka mana idan balaꞌi ya auku.

11. Mene ne ya kamata mu yi idan akwai wata cuta da take yaɗuwa a inda muke?

11 Mene ne za mu iya yi idan akwai cutar da take yaɗuwa a inda muke? Mu bi dokokin da shugabanni suka ba mu kamar na wanke hannuwa da ba da tazara da saka takunkumin fuska da kuma killace kanmu. Idan muka yi dukan abubuwan nan, za mu nuna cewa muna daraja kyautar rai da Allah ya ba mu.

12. Ta yaya ƙaꞌidar da ke Karin Magana 14:15 za ta taimaka mana mu riƙa zaɓan labaran da muke ji saꞌad da balaꞌi ya auku?

12 Idan wani balaꞌi ya auku, abokanmu da maƙwabtanmu da kafofin yaɗa labarai za su iya yaɗa labaran da ba gaskiya ba. Maimakon mu gaskata “kome” da muka ji, zai dace mu saurari bayanai na ƙwarai daga gwamnatoci da kuma likitoci. (Karanta Karin Magana 14:15.) Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu da ꞌyanꞌuwa a ofisoshin reshenmu suna yin iya ƙoƙarinsu don su sami bayanai na ƙwarai kafin su ba mu umurni game da halartan taro da yin waꞌazi. (Ibran. 13:17) Idan muka bi waɗannan umurnan, za mu kāre lafiyarmu da na wasu. Ƙari ga haka, zai sa mutane a yankinmu su kasance da raꞌayi mai kyau game da Shaidun Jehobah.​—1 Bit. 2:12.

KA ƘI AMINCEWA DA JINI

13. Idan ya zo ga batun jini, ta yaya muke nuna cewa muna daraja kyautar rai da Allah ya ba mu?

13 An san cewa Shaidun Jehobah suna daraja jini. Muna bin dokar Jehobah game da jini ta wajen ƙin amincewa da ƙarin jini ko da muna rashin lafiya mai tsanani. (A. M. 15:​28, 29) Amma hakan ba ya nufin cewa muna so mu mutu. A maimakon haka, muna daraja ran da Jehobah ya ba mu ne. Muna neman taimako daga wurin ƙwararrun likitoci da za su yarda su yi mana jinya ba tare da ƙarin jini ba.

14. Mene ne za mu iya yi don mu kāre kanmu daga yin jinya ta gaggawa?

14 Idan muka bi dukan shawarwarin da aka ambata a talifin nan, mai yiwuwa hakan zai sa ba za mu bukaci yin tiyata ko mu soma rashin lafiya mai tsanani ba. Idan muna da ƙoshin lafiya, hakan zai taimaka mana mu warke da sauri bayan an yi mana tiyata. Za mu iya kāre kanmu daga yin tiyata na gaggawa ta wajen cire abubuwa masu haɗari a gidanmu da wurin aiki da kuma yin biyayya ga dokokin hanya.

Da yake muna daraja rai, muna cika takardar ba da izini ga wakilin kiwon lafiya kuma muna ɗaukan ta a kowane lokaci (Ka duba sakin layi na 15) d

15. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa kasancewa da takardar ba da izini ga wakilin kiwon lafiya a kowane lokaci? (Ka kuma duba hoton.) (b) Kamar yadda muka gani a bidiyon, ta yaya za mu yanke shawarwari masu kyau game da jini?

15 Da yake muna daraja kyautar rai, muna cika takardar ba da izini ga wakilin kiwon lafiya kuma muna kasancewa tare da takardar a kowane lokaci. b Ta wannan takardar, muna ambata raꞌayinmu game da ƙarin jini da kuma wasu hanyoyin jinya. Shin taka takardar da ka cika ta kwana-kwanan nan ne? In kana bukatar ka cika wani ko ka canja wanda kake da shi a dā, ka yi hakan ba tare da ɓata lokaci ba. Yin hakan zai taimaka mana mu sami jinyar da muke bukata da sauri maimakon mu ɓata lokaci muna tattauna batun da likitoci. Ƙari ga haka, zai taimaka wa masu kiwon lafiya don kada su yi mana jinya ko su ba mu maganin da zai yi mana lahani. c

16. Mene ne za mu yi idan ba mu san yadda za mu cika takardar ba da izini ga wakilin kiwon lafiya ba?

16 Ko da mu matasa ne ko muna da ƙoshin lafiya, dukanmu za mu iya yin hatsari ko mu yi rashin lafiya. (M. Wa. 9:11) Don haka, zai dace mu cika takardar ba da izini ga wakilin kiwon lafiya. Idan ba ka san yadda za ka cika takardar ba, ka gaya wa dattawanku don su taimaka maka. Suna yin iya ƙoƙarinsu su san yadda za a cika takardar nan amma ba su ne za su yanke maka shawara ba. Kai ne za ka yi hakan da kanka. (Gal. 6:​4, 5) Amma za su iya taimaka maka ka san jinyar da kake so kuma ka rubuta hakan a takardar.

KA KASANCE DA SANIN YAKAMATA

17. Ta yaya za mu nuna cewa muna da sanin yakamata idan ya zo ga batun jinya?

17 Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ne suke taimaka mana mu san shawarwarin da za mu yanke game da lafiyarmu da kuma jinyar da muke so. (A. M. 24:16; 1 Tim. 3:​9, MMA) Amma idan muna yanke shawarwari game da jinya kuma muna tattauna game da hakan da wasu, zai dace mu bi ƙaꞌidar da ke Filibiyawa 4:5 da ta ce: “Ku nuna sanin yakamata a kowane lokaci.” (New World Translation) Idan muna da sanin yakamata, ba za mu riƙa yawan damuwa game da lafiyar jikinmu ba. Ko kuma mu yi ƙoƙarin tilasta wa mutane su kasance da irin raꞌayinmu game da jinya. Muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu da kuma daraja su ko da sun yanke shawarar da ta yi dabam da tamu.​—Rom. 14:​10-12.

18. Ta yaya za mu nuna godiyarmu don kyautar rai da Allah ya ba mu?

18 Idan muna kāre lafiyarmu kuma muna yin iya ƙoƙarinmu don mu bauta wa Jehobah, hakan zai nuna cewa muna godiya ga Jehobah wanda yake ba da rai. (R. Yar. 4:11) A yanzu, ba za mu iya guje wa rashin lafiya da kuma balaꞌoꞌi ba. Amma ba irin wannan rayuwar ce Mahaliccinmu yake so mu yi tun asali ba. Nan ba daɗewa ba, zai ba mu rai na har abada kuma ba za mu yi baƙin ciki ko mu mutu ba. (R. Yar. 21:4) Kafin lokacin, muna farin ciki cewa muna da rai da kuma damar bauta wa Jehobah, Ubanmu na sama mai ƙauna!

WAƘA TA 140 Za Mu Yi Rayuwa Har Abada!

a Wannan talifin zai taimaka mana mu daraja kyautar rai da Allah ya ba mu. Za mu ga hanyoyin da za mu iya kāre lafiyarmu da kuma ranmu saꞌad da balaꞌi ya auku, da kuma yadda za mu guji shiga hatsari. Za mu kuma tattauna abin da ya kamata mu yi don mu shirya kanmu idan muka bukaci jinya ta gaggawa.

b Ana kuma kiran takardar nan katin DPA.

d BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗanꞌuwa matashi yana cika takardar ba da izini ga wakilin kiwon lafiya kuma ya tabbata cewa ya ɗauki takardar yayin da yake fita.