Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shawara A Kan Dandalinmu

Shawara A Kan Dandalinmu

Yadda Za Ka Nemi Talifofin da Ake Nunawa a Shafin Farko na Dandalinmu

ꞌYanꞌuwa da yawa suna amfani da talifofin da ake nunawa a shafin farko na dandalin jw.org a waꞌazi. Yana da sauƙi a tura ma wani talifofin nan ta waya kuma sukan bayyana yadda abubuwan da suke faruwa yanzu suke cika annabcin Littafi Mai Tsarki. Wani ɗanꞌuwa ya rubuta cewa, talifofin da suke fitowa a shafin farko na dandalinmu “su ne ainihin abubuwan da nake bukata a waꞌazi yanzu.”

Amma akan canja waɗannan talifofin a kai a kai. Ta yaya za ku nemi talifin da an riga an cire daga shafin farko na dandalin?

  • A shafin farko na dandalin jw.org, ka danna inda aka rubuta “Ƙarin Batutuwa” wanda ke saman shafin. A wurin, za ka ga batutuwa dabam-dabam da kuma talifofin da aka saka a shafin farko a jw.org.

  • A dandalin jw.org, ka shiga “Laburare,” sai ka shiga “Talifofi,” kuma ka shiga “Ƙarin Batutuwa.” Wannan sashen yana ɗauke da talifofi da yawa da aka saka a shafin farko na dandalinmu. Za ka iya samun waɗannan talifofin a manhajar JW Library®.