Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 12

Ka Dada Koya Game da Jehobah Ta Abubuwan da Ya Halitta

Ka Dada Koya Game da Jehobah Ta Abubuwan da Ya Halitta

“Halin Allahntaka na Allah da kuma ikonsa . . . ba abubuwan da aka iya gani da ido ba ne. Amma tun halittar duniya an bayyana waɗannan abubuwan a fili, ana kuma iya gane su bisa ga abubuwan da aka halitta.”​ROM. 1:20.

WAƘA TA 6 Sammai Suna Nuna Ɗaukakar Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Wace hanya ɗaya ce Ayuba ya yi amfani da ita don ya daɗa sanin Jehobah da kyau?

 AYUBA ya tattauna da mutane da yawa a rayuwarsa, tattaunawarsa da Jehobah ce ta fi muhimmanci. A tattaunawarsu, Jehobah ya gaya wa Ayuba ya kalli wasu abubuwa masu ban mamaki da ya halitta. Hakan zai taimaka ma Ayuba ya san yadda Jehobah yake da hikima, kuma zai ƙarfafa Ayuba ya daɗa gaskata cewa Jehobah zai tanada wa bayinsa dukan abubuwan da suke bukata. Alal misali, Allah ya tuna wa Ayuba cewa shi ne yake tanada wa dabbobi, don haka zai iya kula da Ayuba. (Ayu. 38:​39-41; 39:​1, 5, 13-16) Yayin da Ayuba yake lura da halittun Jehobah, ya koyi abubuwa game da halayen Jehobah.

2. Me ya sa zai iya mana wuya mu lura da halittun Jehobah?

2 Mu ma za mu iya daɗa koyan abubuwa da yawa game da Allahnmu idan muka lura da halittunsa. Amma a wasu lokuta, yakan yi mana wuya mu yi hakan. Idan a birni muke, mai yiwuwa ba za mu riƙa ganin halittun Jehobah a kullum ba. Ko da a ƙauye muke ma, za mu iya ji kamar ba mu da isashen lokacin da za mu lura da halittun Jehobah. Don haka, bari mu tattauna dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu ɗau lokaci don mu lura da halittu. Za mu tattauna yadda Jehobah da Yesu suka yi amfani da halittu don su yi koyarwa, da kuma abin da ya kamata mu yi don mu daɗa koya game da halittu.

ME YA SA YA KAMATA MU LURA DA HALITTU?

Jehobah ya so Adamu ya ji daɗin halittunsa kuma ya ba wa dabbobin suna (Ka duba sakin layi na 3)

3. Mene ne ya nuna cewa Jehobah ya so Adamu ya ji daɗin halittu?

3 Jehobah ya so Adamu da Hauwaꞌu su ji daɗin halittunsa. A lokacin da Allah ya halicci Adamu, ya sa shi a cikin aljanna mai kyau sosai kuma ya ba shi aikin kula da aljannar. (Far. 2:​8, 9, 15) Ka yi tunanin irin farin cikin da Adamu ya yi da ya ga hatsi suna tsira kuma furanni suna yaɗuwa. Babban gata ne aka ba wa Adamu ya kula da lambun Adnin! Jehobah ya kuma umurci Adamu ya ba wa dabbobin sunaye. (Far. 2:​19, 20) Jehobah zai iya ba wa dabbobin sunaye da kansa. Amma ya ba wa Adamu aikin. Babu shakka, kafin Adamu ya zaɓi sunan da zai ba su, yakan lura da kamanin dabbobin da kyau da kuma yadda suke yin abubuwa. Adamu ya ji daɗin yin aikin nan. Hakan ya taimaka masa ya gane yadda Jehobah yake da hikima, da kuma yadda abubuwan da ya halitta suke da kyau da ban shaꞌawa.

4. (a) Wane dalili ɗaya ne ya sa ya kamata mu lura da halittu? (b) A cikin dukan halittu, wanne ne ka fi so?

4 Dalili na farko da ya sa ya kamata mu lura da halittu shi ne, Jehobah yana so mu yi hakan. Jehobah ya ce: “Ku tā da idanunku sama ku duba.” Sai ya yi tambayar nan cewa: “Wane ne ya halicci waɗannan abubuwa?” Amsar a bayyane take. (Isha. 40:26) Jehobah ya halicci dukan abubuwan da ke sama da duniya da teku, kuma dukansu suna koya mana game da shi. (Zab. 104:​24, 25) Ƙari ga haka, ka yi tunanin yadda Jehobah ya halicce mu. Ya halicce mu ne yadda za mu iya jin daɗin kallon abubuwa masu kyau da ya halitta. Ya halicce mu yadda za mu iya gani, mu ji, mu taɓa, mu ɗanɗana, mu kuma shinshina. Hakan yana sa mu ji daɗin dukan abubuwan da Jehobah ya halitta.

5. Kamar yadda Romawa 1:20 ta faɗa, ta yaya za mu amfana idan muna lura da halittun Jehobah?

5 Littafi Mai Tsarki ya sake gaya mana wani dalili mai muhimmanci da ya sa ya kamata mu lura da halittu. Halittu na koya mana game da halayen Jehobah. (Karanta Romawa 1:20.) Alal misali, idan ka kalli abubuwan da Jehobah ya halitta, za ka ga cewa ya tsara su da kyau sosai. Hakan ya koya mana cewa Allah yana da hikima sosai. Kuma ka yi tunani a kan abinci iri-iri da za mu iya jin daɗinsu. Hakan na nuna yadda yake ƙaunar ꞌyan Adam. Idan muka gano halayen Jehobah daga abubuwan da ya halitta, hakan na sa mu daɗa saninsa da kyau kuma mu kusace shi. A yanzu, bari mu ga wasu hanyoyin da Jehobah ya yi amfani da su don ya koya wa ꞌyan Adam darussa masu muhimmanci.

ALLAH YA YI AMFANI DA HALITTU DON YA KOYA MANA GAME DA KANSA

6. Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda tsuntsaye suke ƙaura?

6 Jehobah ya tsara lokacin da abubuwa za su faru. Kowace shekara, tsakanin ƙarshen watan Fabrairu zuwa tsakiyar Mayu, Israꞌilawa sukan ga su shamuwa a sararin samaniya suna ƙaura zuwa ta arewa. Allah ya gaya wa Israꞌilawa cewa: “Shamuwa ta sararin sama ma, ta san ƙaꞌidar lokacin ƙaurarta.” (Irm. 8:7) Kamar yadda Jehobah ya tsara lokacin da tsuntsayen nan za su ƙaura, haka ma ya tsara lokacin da zai hukunta wannan muguwar duniyar. Yayin da muke lura da tsuntsayen da suke ƙaura a yau, hakan na tuna mana cewa za mu iya gaskata cewa Jehobah ya shirya lokacin da zai kawo ƙarshen wannan muguwar duniyar.​—Hab. 2:3.

7. Mene ne za mu iya koya daga yadda wata tsuntsuwa take firiya? (Ishaya 40:31)

7 Jehobah yana ƙarfafa bayinsa. Ta baƙin Ishaya, Jehobah ya yi alkawari cewa zai ƙarfafa mutanensa kuma “za su tashi sama kamar fikafikan gaggafa” a lokacin da suke sanyin gwiwa. (Karanta Ishaya 40:31.) Isra’ilawa sukan ga yadda gaggafa take firiya a sama da taimakon iska ba tare da motsa fikafikanta sosai ba. Hakan na tuna mana cewa, kamar yadda Jehobah yake ba wa tsuntsayen nan ƙarfi, zai iya ƙarfafa bayinsa! Idan ka ga babban tsuntsu yana firiya a sama ba tare da motsa fikafikansa sosai ba, ka tuna cewa Jehobah zai iya ƙarfafa ka don ka iya jimre matsalolinka.

8. Mene ne Ayuba ya koya yayin da ya lura da halittun Allah, kuma me hakan ya koya mana?

8 Jehobah ya cancanci mu gaskata da shi. Jehobah ya taimaka wa Ayuba ya daɗa gaskatawa da shi. (Ayu. 32:2; 40:​6-8) Da yake tattaunawa da Ayuba, Jehobah ya ambaci abubuwa da yawa da ya halitta, kamar taurari da gajimare da kuma walƙiya. Jehobah ya kuma yi magana a kan dabbobi kamar ɓauna da doki. (Ayu. 38:​32-35; 39:​9, 19, 20) Waɗannan abubuwan sun nuna ikon Jehobah. Ƙari ga haka, sun nuna cewa shi mai ƙauna ne da kuma hikima. Tattaunawar nan ta sa Ayuba ya gaskata da Jehobah fiye da dā. (Ayu. 42:​1-6) Hakazalika, idan muka lura da halittu, za su tuna mana cewa Jehobah yana da iko da kuma hikima sosai fiye da mu. Ƙari ga haka, yana da niyya da kuma ikon kawar da wahalolinmu. Wannan tabbacin zai iya taimaka mana mu daɗa gaskata da shi.

YESU YA YI AMFANI DA HALITTU DON YA KOYA WA MUTANE GAME DA UBANSA

9-10. Mene ne rana da ruwan sama suke koya mana game da Jehobah?

9 Yesu ya san halittu sosai. A matsayin “gwanin aiki,” ya yi aiki da Ubansa saꞌad da ya halicci sama da ƙasa. (K. Mag. 8:30) Daga baya, saꞌad da Yesu yake duniya, ya yi amfani da halittu don ya koya wa almajiransa game da Ubansa. Ka yi laꞌakari da wasu daga cikin darussan da ya koyar.

10 Jehobah yana ƙaunar kowa da kowa. A Huɗubarsa a kan Dutse, Yesu ya gaya wa almajiransa game da rana da ruwan sama, kuma abubuwa ne da mutane da yawa ba sa tunani a kai. Su biyun abubuwa ne masu muhimmanci da muke bukata don mu rayu. Jehobah zai iya hana mutanen da ba sa bauta masa abubuwan nan. Amma maimakon haka, ya tanadar wa kowa da kowa rana da kuma ruwan sama. (Mat. 5:​43-45) Yesu ya yi amfani da darasin nan don ya koya wa almajiransa cewa Jehobah yana so mu nuna wa kowa da kowa ƙauna. A duk lokacin da muka ga hasken rana ko kuma ana ruwan sama, za mu iya yin tunani a kan ƙaunar Jehobah ga dukan mutane. Misalinsa zai iya motsa mu mu nuna irin ƙaunar nan ta wajen yi wa kowa waꞌazi.

11. Ta yaya kallon tsuntsaye zai iya ƙarfafa mu?

11 Jehobah yana tanada mana abubuwan da muke bukata don mu rayu. A huɗubarsa a kan dutse, Yesu ya ƙara cewa: “Ku dubi tsuntsaye mana, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa tara a rumbuna. Duk da haka Ubanku na sama ne yake ciyar da su.” Mai yiwuwa waɗanda suke sauraran Yesu sun ga tsuntsaye suna firiya a lokacin da Yesu ya tambaye su cewa: “Ba ku fi su daraja ba?” (Mat. 6:26) Wannan hanya ce mai kyau da Yesu ya taimaka mana mu ga cewa Jehobah zai kula da mu! (Mat. 6:​31, 32) Wannan darasin daga halittu ya ci gaba da ƙarfafa bayin Jehobah masu aminci. Wata matashiya a Sifen wadda majagaba ce ta yi sanyin gwiwa don ba ta sami gida mai kyau da za ta zauna ba. Amma da ta ga tsuntsaye suna cin hatsi, hakan ya ƙarfafa ta. Ta ce: “Tsuntsayen nan sun tuna min cewa Jehobah ne yake kula da su kuma zai kula da ni.” Ba da daɗewa ba bayan hakan, ꞌyarꞌuwar ta sami gidan da za ta zauna.

12. Kamar yadda yake a Matiyu 10:​29-31, mene ne tsuntsayen da ake kira gwara suka koya mana game da Jehobah?

12 Jehobah yana daraja kowannenmu. Kafin Yesu ya aiki almajiransa su yi waꞌazi, ya taimaka masu kada su ji tsoron mutanen da za su ƙi su. (Karanta Matiyu 10:​29-31.) Ya yi hakan ta wajen gaya musu game da wani ɗan tsuntsu a Isra’ila da ake kira gwara. Wannan tsuntsun bai da daraja sosai a zamanin Yesu. Amma ya gaya wa almajiransa cewa: ‘Ba ɗayansu wanda zai fāɗi a ƙasa ba tare da sanin Ubanku ba.’ Sai ya ƙara da cewa: “Ai, kun fi ɗan tsuntsu daraja sau barkatai.” Ta hakan, Yesu ya tabbatar wa almajiransa cewa Jehobah yana daraja kowannensu, don haka ba su da dalilin da zai sa su ji tsoron tsanantawa. Babu shakka, mabiyan Yesu sun tuna da kalmomin Yesu a duk lokacin da suka ga tsuntsayen nan yayin da suke waꞌazi a garurruka da ƙauyuka. A duk lokacin da ka ga ƙaramin tsuntsu, ka tuna cewa Jehobah yana daraja ka domin kai ma ka “fi ɗan tsuntsu daraja sau barkatai.” Da taimakon Jehobah, bai kamata ka ji tsoron mutanen da suke ƙin ka ba.​—Zab. 118:6.

TA YAYA ZA MU DAƊA KOYA GAME DA ALLAH TA WAJEN HALITTU?

13. Mene ne zai taimaka mana mu koyi darussa daga halittu?

13 Za mu iya koyan ƙarin darussa game da Jehobah ta wajen halittu. Ta yaya? Da farko, muna bukatar mu ɗau lokaci don mu lura da wata halitta. Saꞌan nan mu yi tunani a kan abin da ta koya mana game da Jehobah. A wasu lokuta, yin hakan ba zai yi mana sauƙi ba. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Géraldine daga Kamaru ta ce: “A birni ne na yi girma, don haka na gano cewa in bukatar in sa ƙwazo sosai don in lura da halittu.” Wani dattijo mai suna Alfonso ya ce, “Na koyi cewa ina bukatar in nemi lokacin da zan riƙa kasancewa ni kaɗai don in lura da halittu, in kuma yi bimbini a kan abin da hakan zai koya min game da Jehobah.”

Da Dauda ya lura da halittun da ke kewaye da shi, hakan ya sa ya yi bimbini a kan abin da suka koya masa game da Jehobah (Ka duba sakin layi na 14)

14. Mene ne Dauda ya koya saꞌad da ya yi bimbini a kan halittun Allah?

14 Dauda ya yi tunani mai zurfi a kan halittun Allah. Ya gaya wa Jehobah cewa: “Sa’ad da na duba sararin sama, aikin yatsunka, da wata da taurarin da ka kafa a wurarensu, sai na ce, ‘Mene ne mutum da ka damu da shi?’ ” (Zab. 8:​3, 4) Babu shakka Dauda ya ji daɗin kallon taurari, amma ba shi ke nan ba. Ya yi tunani a kan abubuwan da taurarin suka koya masa game da Allah. Ya koyi yadda Jehobah yake da iko da hikima sosai. A wasu lokuta kuma, Dauda ya yi tunani a kan yadda jikinsa ya yi girma a cikin mahaifiyarsa. Da ya yi tunani a kan yadda aka tsara sassan jikinsa, ya daɗa gode wa Jehobah domin yawan hikimarsa.​—Zab. 139:​14-17.

15. Ka ba da misalin wasu halittun da ka taɓa gani da abin da suka koya maka game da Jehobah. (Zabura 148:​7-10)

15 Kamar Dauda, mai yiwuwa zai yi mana sauƙi mu nemi wani abu game da halittu da za mu yi tunani mai zurfi a kai. Akwai abubuwa da yawa game da halittu da za su iya taimaka mana mu daɗa sanin Jehobah da kyau. Alal misali, idan ka ji zafin rana, ka tuna cewa Jehobah yana da iko sosai. (Irm. 31:35) Ka yi tunani a kan hikimar Allah idan ka ga tsuntsu yana gina gida. Idan ka ga kare yana wasa da wutsiyarsa, ka tuna cewa Jehobah Allah ne mai farin ciki kuma yana so mu yi farin ciki. Kuma idan ka ga mahaifiya tana wasa da jaririnta, ka gode wa Jehobah don ƙaunarsa. Muna da hanyoyi da yawa da za mu koya game da Jehobah, domin dukan halittunsa, manya da ƙanana, waɗanda ke nesa da kusa suna yabon sa.​—Karanta Zabura 148:​7-10.

16. Mene ne ya kamata mu ƙudiri niyyar yi?

16 Allahnmu yana da hikima sosai, yana da ƙauna da iko kuma dukan abubuwan da ya yi suna da kyau. Idan muka lura da halittun da ke kewaye da mu da kyau, za mu iya koya game da halayen nan, da ma wasu da yawa. Bari mu ɗau lokaci a-kai-a-kai don mu ji daɗin lura da halittu, kuma mu yi tunani a kan abin da suke koya mana game da Jehobah. Idan muka yi hakan, za mu daɗa kusantar Mahaliccinmu. (Yak. 4:8) A talifi na gaba, za mu ga yadda iyaye za su iya amfani da halittu don su taimaka wa yaransu su kusaci Jehobah.

WAƘA TA 5 Ayyukan Allah Suna da Ban Al’ajabi

a Halittun Jehobah suna da ban mamaki sosai. Manyan halittunsa kamar rana, da ƙananan halittunsa kamar furanni suna ba mu mamaki. Abubuwan da Jehobah ya halitta za su iya koya mana wasu daga cikin halayen Jehobah. A wannan talifin, za mu tattauna dalilin da ya sa ya kamata mu mai da hankali ga halittun Jehobah da yadda hakan zai taimaka mana mu kusaci Allah.