Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 35

Ka Ci Gaba da Zama Mai Hakuri

Ka Ci Gaba da Zama Mai Hakuri

“Ku ɗauki halin . . . haƙuri.”​—KOL. 3:​12, Maimakamantu[n] Ayoyi.

WAƘA TA 114 Ku Kasance Masu “Haƙuri”

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Me ya sa kake son mutane masu haƙuri?

 DUKANMU muna son mutanen da suke da haƙuri. Me ya sa? Domin muna daraja waɗanda suke iya jiran abu ba tare da yin fushi ba. Muna farin ciki idan mutane suna haƙuri da mu duk da kurakurenmu. Kuma muna farin ciki domin wanda ya yi nazari da mu ya bi da mu cikin haƙuri, yayin da muke koyan abubuwa a Littafi Mai Tsarki da amincewa da su da kuma aikata su. Mafi muhimmanci ma, muna godiya sosai domin yadda Jehobah yake haƙuri da mu!​—Rom. 2:4.

2. A wane yanayi ne zai iya yi mana wuya mu yi haƙuri?

2 Ko da yake muna son mutane masu haƙuri, zai iya yi mana wuya mu da kanmu mu zama masu haƙuri. Alal misali, a ce mun je mu sayi wani abu, sai muka sami mutane da yawa da suka riga mu. Zai yi mana wuya mu yi haƙuri, musamman ma in muna sauri za mu wani wuri. A irin yanayin nan, za mu iya yin fushi idan mutane suka ɓata mana rai. Ƙari ga haka, a wasu lokuta za mu iya gaji da jiran alkawarin sabuwar duniya da Allah ya yi mana. Za ka so ka ƙara zama mai haƙuri? A wannan talifin, za mu tattauna abin da ake nufi da zama mai haƙuri, da kuma dalilin da ya sa hakan yake da muhimmanci. Za mu kuma tattauna abin da zai taimaka mana mu ƙara zama masu haƙuri.

ME AKE NUFI DA ZAMA MAI HAƘURI?

3. Mene ne mai haƙuri yakan yi idan mutane suka ɓata masa rai?

3 Ga hanyoyi huɗu da za mu iya nuna cewa mu masu haƙuri ne. Na ɗaya, mai haƙuri ba ya saurin fushi. Idan mutane suka ɓata masa rai, yakan yi ƙoƙari ya kame kansa don kada ya rama abin da aka yi masa. Kuma ko da ya gaji sosai, ba ya yin abubuwan da za su ɓata wa mutane rai. Furucin nan “marar saurin fushi,” ya soma bayyana a Littafi Mai Tsarki ne saꞌad da aka ce Jehobah mai “jinƙai ne, mai alheri, marar saurin fushi, mai yawan ƙauna marar canjawa, cike da aminci kuma.”​—Fit. 34:6.

4. Mene ne mai haƙuri yakan yi idan yana jiran wani abu?

4 Na biyu, mai haƙuri ba ya yin fushi saꞌad da yake jiran wani abu. Mai haƙuri yakan kame kansa don kar hankalinsa ya tashi ko da abin da yake jira bai zo a lokacin da yake tsammani ba. (Mat. 18:​26, 27) Akwai yanayoyi da za su bukace mu mu jira da haƙuri. Alal misali, idan wani yana magana, zai dace mu saurare shi da haƙuri ba tare da katse maganarsa ba. (Ayu. 36:2) Muna bukatar haƙuri saꞌad da muke taimaka ma ɗalibinmu ya fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki, ko kuma ya daina wani hali da bai dace ba.

5. A wace hanya ce kuma za mu iya nuna haƙuri?

5 Na uku, mai haƙuri ba ya ɗaukan mataki cikin hanzari. Akwai wasu yanayoyi da za su bukace mu mu ɗauki mataki cikin hanzari. Amma idan mutum mai haƙuri yana da wani aiki mai muhimmanci da yake bukatar ya yi, ba ya soma aikin da garaje ko ya yi ta sauri-sauri don ya gama. A maimakon haka, yakan ɗau lokaci don ya shirya yadda zai yi aikin. Bayan haka, yakan ɗau lokaci don ya yi aikin da kyau.

6. Mene ne mai haƙuri zai yi idan yana fuskantar matsaloli ko kuma tsanantawa?

6 Na huɗu, mai haƙuri yakan jimre matsaloli ba tare da yin gunaguni ba. Ba laifi ba ne mu gaya wa abokinmu yadda muke ji game da wata matsala. Amma mai haƙuri ya fi tunani game da abubuwa masu kyau da suka faru da shi, kuma yakan yi iya ƙoƙarinsa don ya ci gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki. (Kol. 1:11) Mu Kiristoci, muna bukatar mu yi haƙuri a dukan yanayoyi da muka ambata. Me ya sa? Ga wasu dalilai.

DALILIN DA YA SA HAƘURI YAKE DA KYAU

Kamar yadda manomi yake yin haƙuri saꞌad da yake jira da tabbaci cewa zai girbi abin da ya shuka, mu ma muna bukatar mu yi haƙuri yayin da muke jira da tabbaci cewa Jehobah zai cika dukan alkawuran da ya yi a lokacin da ya dace (Ka duba sakin layi na 7)

7. Bisa ga littafin Yakub 5:​7, 8, me ya sa yin haƙuri yake da muhimmanci? (Ka kuma duba hoton.)

7 Muna bukatar mu zama masu haƙuri don mu sami ceto. Kamar yadda bayin Jehobah masu aminci suka yi a dā, mu ma muna bukatar mu yi haƙuri yayin da muke jiran Allah ya cika alkawuransa. (Ibran. 6:​11, 12) Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mu da manomi. (Karanta Yakub 5:​7, 8.) Manomi yakan yi aiki sosai don ya shuka iri kuma ya yi ban ruwa, amma bai san lokacin da irin zai yi girma ba. Don haka, manomin yakan yi haƙuri kuma ya jira da tabbaci cewa zai girbi abin da ya shuka. Haka ma, muna yin ayyukan ibada da ƙwazo duk da cewa ‘ba mu san ranar da Ubangijinmu zai dawo ba.’ (Mat. 24:42) Muna haƙuri kuma muna jira da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawuran da ya yi a lokacin da ya dace. Idan muka daina haƙuri za mu gaji da jira, kuma hakan zai sa mu daina bauta wa Jehobah a hankali a hankali. Ƙari ga haka, za mu iya soma neman abubuwa da muke ganin za su sa mu farin ciki yanzu. Amma idan muna da haƙuri, za mu iya jimre har zuwa ƙarshe kuma mu sami ceto.​—Mik. 7:7; Mat. 24:13.

8. Ta yaya haƙuri zai sa mu kasance da dangantaka mai kyau da mutane? (Kolosiyawa 3:​12, 13)

8 Haƙuri yana sa mu kasance da dangantaka mai kyau da mutane. Yana taimaka mana mu saurari mutane da kyau yayin da suke magana. (Yak. 1:19) Yana kuma sa mu zauna lafiya da mutane. Ko da mun gaji sosai, haƙuri zai taimaka mana kada mu mai da martani cikin hanzari ko mu yi wa ꞌyanꞌuwanmu baƙar magana. Ƙari ga haka, idan muna da haƙuri, ba za mu yi saurin fushi ba don wani ya yi mana baƙar magana. Maimakon mu rama abin da aka yi mana, mu ci gaba da yin haƙuri da juna da kuma gafarta wa juna da dukan zuciyarmu.​—Karanta Kolosiyawa 3:​12, 13.

9. Ta yaya haƙuri zai taimaka mana idan muna so mu yanke shawara? (Karin Magana 21:5)

9 Haƙuri zai iya taimaka mana mu yanke shawarar da ta dace. Maimakon mu yi saurin yanke shawara, haƙuri zai taimaka mana mu yi bincike don mu san ko wace shawara ce ta fi dacewa. (Karanta Karin Magana 21:5.) Alal misali, idan muna neman aiki, zai yi mana sauƙi mu karɓi aiki na farko da muka samu, ko da hakan zai hana mu bauta wa Jehobah da ƙwazo. Amma idan muna da haƙuri, za mu yi tunani a kan inda wurin aikin yake, da awoyi nawa za mu yi muna aikin. Ƙari ga haka, za mu yi tunani ko hakan zai sa mu yi nisa da iyalinmu ko kuma ya shafi dangantakarmu da Jehobah. Idan muna da haƙuri, za mu guji yanke shawarar da ba ta dace ba.

YADDA ZA MU ƘARA ZAMA MASU HAƘURI

10. Ta yaya Kirista zai iya zama mai haƙuri kuma ya ci gaba da kasancewa da halin?

10 Ka roƙi Allah ya sa ka ƙara zama mai haƙuri. Haƙuri yana ɗaya daga cikin halayen da ruhu mai tsarki yake ba mu. (Gal. 5:​22, 23) Don haka, za mu iya roƙan Allah ya ba mu ruhu mai tsarki, kuma ya sa mu kasance da halayen da ruhun yake haifarwa. Idan mun shiga yanayi da ke bukatar mu yi haƙuri, mu “yi ta roƙo” Allah ya ba mu ruhu mai tsarki don mu iya yin haƙuri. (Luk. 11:​9, 13) Za mu kuma iya roƙan Jehobah ya taimaka mana mu kasance da irin raꞌayinsa game da abubuwa. Bayan mun yi adduꞌa, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci gaba da yin haƙuri a kullum. Idan mun ci gaba da roƙan Jehobah ya sa mu ƙara zama masu haƙuri, kuma muka ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu nuna haƙuri, Jehobah zai taimaka mana mu kasance da halin nan ko da ba mu da shi a dā.

11-12. A wace hanya ce Jehobah yake yin haƙuri?

11 Ka yi tunani mai zurfi a kan labarai da ke Littafi Mai Tsarki. A Littafi Mai Tsarki, akwai labaran mutane da yawa da suka nuna haƙuri. Yin tunani a kan labaransu zai taimaka mana mu zama masu haƙuri. Kafin mu tattauna wasu daga cikin labaran nan, bari mu tattauna game da Jehobah wanda shi ne ya fi kowa haƙuri.

12 A gonar Adnin, Shaiɗan ya ɓata sunan Jehobah ta wajen sa Hauwaꞌu ta yi shakkar cewa Jehobah Sarki ne mai ƙauna da kuma adalci. Maimakon Jehobah ya halaka Shaiɗan nan da nan, ya kame kansa kuma ya yi haƙuri, domin ya san cewa zai ɗau lokaci kafin ya iya tabbatar ma kowa da kowa cewa Mulkinsa ne ya fi dacewa. Kuma yayin da yake jira, yana jimre abubuwan da mutane suke yi da ke ɓata sunansa. Ƙari ga haka, Jehobah ya ci gaba da yin haƙuri domin mutane da yawa su sami damar yin rayuwa har abada. (2 Bit. 3:​9, 15) Saboda haƙurinsa, miliyoyin mutane sun koya game da shi. Idan muka mai da hankali a kan sakamako mai kyau da haƙurin Jehobah yake kawowa, zai yi mana sauƙi mu jira lokacin da Jehobah zai kawo ƙarshen wannan duniyar.

Idan muna da haƙuri, ba za mu yi saurin fushi ba saꞌad da aka ɓata mana rai (Ka duba sakin layi na 13)

13. Ta yaya Yesu ya nuna haƙuri kamar Ubansa? (Ka kuma duba hoton.)

13 Yesu ma yana da haƙuri kamar Ubansa, kuma ya nuna wannan halin saꞌad da yake duniya. Akwai lokutan da bai yi masa sauƙi ya nuna haƙuri ba, musamman ga Farisiyawa da marubuta waɗanda munafukai ne. (Yoh. 8:​25-27) Amma kamar Ubansa, Yesu ma ba mai saurin fushi ba ne. Saꞌad da aka zage shi kuma an ɓata masa rai, bai rama ba. (1 Bit. 2:23) Yesu ya jimre matsaloli ba tare da yin gunaguni ba. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce mana “ku lura fa da wannan mutumin da ya yi haƙuri da irin ƙiyayyar da masu zunubi suka yi masa.” (Ibran. 12:​2, 3) Da taimakon Jehobah, mu ma za mu iya yin haƙuri kuma mu jimre kowace irin matsala.

Idan muka yi haƙuri kamar yadda Ibrahim ya yi, za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi mana albarka yanzu, kuma a sabuwar duniya, zai yi mana albarku fiye da hakan (Ka duba sakin layi na 14)

14. Me za mu iya koya daga yadda Ibrahim ya yi haƙuri? (Ibraniyawa 6:15) (Ka kuma duba hoton.)

14 Wasunmu sun sa rai cewa ƙarshen wannan duniyar za ta zo shekaru da yawa da suka wuce. Kuma a yanzu suna damuwa cewa wataƙila ba za su kasance da rai ba saꞌad da ƙarshen za ta zo. Me zai taimaka mana mu ci gaba da yin haƙuri yayin da muke jira? Ka yi laꞌakari da misalin Ibrahim. Saꞌad da Ibrahim ya kai shekara 75 kuma ba shi da ꞌyaꞌya a lokacin, Jehobah ya yi masa alkawari cewa: “Zan sa ka zama babbar alꞌumma.” (Far. 12:​1-4) Shin Ibrahim yana raye saꞌad da annabcin nan ya cika? E, amma ba dukansu ba. Bayan ya tsallake Kogin Yufiretis, kuma ya ƙara yin shekaru 25 yana jira, Ibrahim ya ga yadda aka haifi ɗansa na farko, wato Ishaku a hanya mai ban mamaki. Bayan shekaru 60 kuma, ya ga yadda aka haifi jikokinsa guda biyu wato Isuwa da Yakubu. (Karanta Ibraniyawa 6:15.) Amma Ibrahim bai ga yadda zuriyarsa ta zama babbar alꞌumma kuma ta gāji Ƙasar Alkawari ba. Duk da haka, ya kasance da dangantaka mai kyau da Mahaliccinsa. (Yak. 2:23) Kuma bayan an tashi Ibrahim daga matuwa, zai yi farin cikin sanin cewa bangaskiyarsa da kuma haƙurinsa sun sa mutane daga dukan alꞌummai su sami albarka! (Far. 22:18) Wane darasi ne muka koya? Mai yiwuwa ba za mu iya shaida yadda dukan alkawuran Jehobah za su cika ba. Amma idan muka yi haƙuri kamar Ibrahim, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai yi mana albarka a yanzu, kuma zai yi mana albarku fiye da hakan a sabuwar duniya.​—Mar. 10:​29, 30.

15. Wane abu ne kowannenmu zai iya yin nazari a kai?

15 Akwai labaran mutane da yawa da suka nuna haƙuri a cikin Littafi Mai Tsarki. (Yak. 5:10) Me zai hana ka ka yi nazari game da su? b Alal misali, an naɗa Dauda ya zama sarkin Israꞌila tun yana yaro, amma sai da ya jira har na shekaru da yawa kafin ya zama sarki. Simeyon da Hannatu sun bauta wa Jehobah da aminci yayin da suke jiran Almasihu da aka yi alkawarin sa. (Luk. 2:​25, 36-38) Yayin da kake yin nazari game da labaran nan, ka bincika amsoshin tambayoyin nan: ‘Mene ne ya taimaka ma wannan mutumin ya iya yin haƙuri? Ta yaya ya amfana don ya yi haƙuri? Ta yaya zan yi koyi da shi? Za ka kuma iya koyan darasi daga marasa haƙuri. (1 Sam. 13:​8-14) Za ka iya yin tambayar nan: ‘Mene ne ya sa suka ƙasa yin haƙuri? Wane sakamako ne hakan ya jawo musu?’

16. A waɗanne hanyoyi ne muke amfana don muna yin haƙuri?

16 Ka yi tunani a kan amfanin yin haƙuri. Idan muna da haƙuri, za mu zama masu farin ciki da kuma kamun kai. Don haka, haƙuri zai sa mu kasance da lafiyar jiki da kuma lafiyar ƙwaƙwalwa. Idan muna haƙuri da mutane, za mu kasance da dangantaka mai kyau da su. Ikilisiyarmu za ta kasance da haɗin kai. Idan ba ma saurin fushi, ko da wani ya ɓata mana rai, ba za mu yi abin da zai sa yanayin ya ƙara muni ba. (Zab. 37:8; K. Mag. 14:29) Abu mafi muhimmanci ma shi ne, idan mu masu haƙuri ne, muna yin koyi da Ubanmu na sama ke nan, kuma hakan zai sa mu ƙara yin kusa da shi.

17. Mene ne ya kamata mu ƙudiri niyyar yi?

17 Babu shakka, haƙuri hali ne mai kyau da ke amfanar mu! Duk da cewa yin haƙuri bai da sauƙi, da taimakon Jehobah, za mu iya ci gaba da zama masu haƙuri. Kuma yayin da muke haƙuri muna jiran sabuwar duniya, za mu iya kasance da tabbaci cewa ‘idanun Yahweh suna a kan masu tsoronsa, a kan masu sa zuciya ga ƙaunarsa marar canjawa.’ (Zab. 33:18) Bari dukanmu mu ƙudiri niyyar ci gaba da saka haƙuri kamar riga.

WAƘA TA 41 Allah Ka Ji Roƙona

a Yawancin mutane a yau ba su da haƙuri. Amma Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa mu ɗauki halin haƙuri. Wannan talifin zai nuna mana dalilin da ya sa haƙuri yake da muhimmanci da kuma yadda za mu ƙara kasancewa da halin.

b Don ka ga misalin mutanen da suka yi haƙuri a Littafi Mai Tsarki, ka bincika ƙarƙashin jigon nan “Yadda Kake Ji, Halaye, da Kuma Ɗabiꞌa,” saꞌan nan ka duba ƙarƙashin ƙaramin jigon nan “Haƙuri” a Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah.