Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

1923​—⁠Shekaru Dari da Suka Shige

1923​—⁠Shekaru Dari da Suka Shige

HASUMIYAR TSARO ta 1 ga Janairu, 1923 ta ce: “Da alama cewa abubuwa masu kyau za su faru a shekara ta 1923. Babban gata ne a gare mu mu gaya wa . . . mutanen da suke shan wahala cewa abubuwa za su yi kyau a nan gaba.” A 1923, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun canja yadda suke taronsu da kuma waꞌazi. Hakan ya sa sun ƙara zama da haɗin kai.

YIN TARO YA ƘARA MUSU DANƘON ZUMUNCI

Wata Kalanda dauke da nassosi da kuma lambobin waka

A wannan shekarar, ƙungiyar Jehobah ta yi wasu canje-canje da suka taimaka wa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki su kasance da haɗin kai. An soma wallafa littattafai da ke bayyana nassosin da ake tattaunawa a kowane taron mako, da ake kira Taron Adduꞌoꞌi da Yabo ga Jehobah. Ƙari ga haka, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun wallafa kalanda, kuma a ciki akwai nassosin da za a yi nazarin su kowane mako, da kuma waƙoƙin da mutum zai yi amfani da su saꞌad da yake yin nazari da kansa ko tare da iyalinsa.

A taron, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sukan faɗi abubuwan da suka faru da su saꞌad da suke waꞌazi, da wani abu da ya sa suke gode wa Jehobah. Ƙari ga haka, sukan rera waƙa, ko ma su yi adduꞌa. Wata mai suna Eva Barney da ta yi baftisma a 1923 saꞌad da take shekara 15, ta ce: “Wasu sukan tashi tsaye kuma su ce, ‘Ina so in gode wa Ubangiji don alherinsa a gare ni.’” Wasu ꞌyanꞌuwa suna yawan son faɗin abin da ya faru da su. ꞌYarꞌuwa Barney ta ci-gaba da cewa: “Wani ɗanꞌuwa da ya tsufa mai suna Godwin, yakan so ya yi godiya don abubuwa da yawa. Amma idan matarsa ta ga cewa fuskar mai gudanar da nazarin ta soma canjawa don maganarsa ta yi yawa, sai ta ɗan ja rigarsa. In ya ji haka, sai ya yi shiru kuma ya zauna.”

Sau ɗaya a kowane wata, kowace ikilisiya takan yi Taron Adduꞌoꞌi da Yabo na musamman. Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 1923, ta bayyana yadda taron nan zai kasance. Ta ce: “A yi amfani da rabin lokacin a ba wa ꞌyanꞌuwa dama su faɗi abin da ya faru da su a waꞌazi, kuma a ƙarfafa su. . . . Muna kyautata zaton cewa wannan taron zai ƙara sa ꞌyanꞌuwa su kasance da haɗin kai.”

Wani Ɗanꞌuwa mai shekara 19 mai suna Charles Martin, daga Vancouver a Kanada, ya amfana sosai daga wannan taron. Daga baya ya ce: “A wannan taron ne na fara koyan abin da zan faɗa in muna waꞌazi gida-gida. A ko da yaushe, wani zai ba da labarin abin da ya faru da shi saꞌad da yake waꞌazi. Hakan ya taimaka min in san abin da zan faɗa a waꞌazi, kuma idan mutane suka ba da hujja don ba sa so su ji waꞌazin, in san amsar da zan ba su.”

YIN WAꞌAZI YA ƘARA HAƊA KANSU

Littafin Taro na 1 ga Mayu, 1923

Wani abin da ya ƙara sa ꞌyanꞌuwan su kasance da haɗin kai shi ne, yadda aka sa ranar da kowa zai fita waꞌazi. Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 1923 ta sanar da cewa: “An zaɓi Talata 1 ga Mayu, 1923, ta zama ranar da kowa zai fita waꞌazi . . . , don dukanmu mu yi aikin nan da haɗin kai. Kuma daga wannan ranar, kowace ranar Talata na farko a kowane wata, dukanmu za mu fita waꞌazi. . . . Kowane mai shela a kowace ikilisiya, ya yi ƙoƙari ya yi waꞌazi a wannan ranar.”

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki matasa ma sun yi wannan aikin. Wata mai suna Hazel Burford, mai shekara 16 ta ce: “A littafin taro a lokacin, akan faɗi yadda za mu yi waꞌazi, don kowa ya haddace abin da zai faɗa. Nakan bi kakana mu yi waꞌazin nan da ƙwazo.” Amma ꞌYarꞌuwa Burford ta yi mamaki sosai don wani ɗanꞌuwa bai so ta riƙa zuwa waꞌazi ba. Ta ce: “Wani ɗanꞌuwa tsoho ya ƙi ƙememe cewa bai kamata in yi wa mutane waꞌazi ba. A lokacin, wasu ba su fahimci cewa ya kamata dukan ɗalibai, har da ‘samari da ꞌyan mata,’ su yabi Mahaliccinmu ba. (Zab. 148:​12, 13) Duk da haka, ꞌYarꞌuwa Burford ba ta daina ba. Daga baya, ta je Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead kuma ta zama mai waꞌazi a ƙasar waje, a ƙasar Panama. Kuma ꞌyanꞌuwan nan sun soma amincewa da waꞌazin da matasa suke yi.

MANYAN TARONMU SUN ƘARA HAƊA KAN ꞌYANꞌUWA

Manyan taronmu ma sun taimaka ma ꞌyanꞌuwa su kasance da haɗin kai. A yawancin tarukan nan, akan zaɓi ranar da za a fita yin waꞌazi. Misali, a taron da aka yi a birnin Winnipeg, a Kanada, an ƙarfafa dukan ꞌyanꞌuwa su fita waꞌazi a ranar 31 ga Maris. Irin waꞌazin nan yana sa a yi wa mutane da yawa waꞌazi, kuma an sami sakamako mai kyau. A ranar 5 ga Agusta, mutane wajen 7,000 sun halarci wani babban taro a Winnipeg. Kafin wannan lokacin, ba a taɓa yin taron da aka tara jamaꞌa sosai haka a Kanada ba.

Wani taro mai muhimmanci da Shaidun Jehobah suka yi a 1923, shi ne wanda aka yi a Los Angeles da ke Kalifoniya a ranar 18-26 ga Agusta. ꞌYan makonni kafin wannan taron, an yi tallar taron a jaridu, kuma Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun rarraba takardar gayyata fiye da 500,000. An manne fosta a motocin kasuwa da motocin mutane don a gayyaci jamaꞌa.

Babban taro da Daliban Littafi Mai Tsarki suka yi a Los Angeles a 1923

A ranar Asabar, 25 ga Agusta, Ɗanꞌuwa Rutherford ya yi wani jawabi mai jigo, “Tumaki da Awaki.” Ya bayyana cewa “tumakin” su ne waɗanda suke da zuciyar kirki, wato, waɗanda za su yi rayuwa a aljanna. Ƙari ga haka, ya yi wani jawabi kuma ya karanta wani gargaɗi. A gargaɗin, ya bayyana cewa coci-cocin Kiristendam ba su da gaskiya, kuma ya ƙarfafa masu zuciyar kirki su fita daga “Babila Babba.” (R. Yar. 18:​2, 4) Daga baya, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki masu ƙwazo a duk faɗin duniya, sun rarraba miliyoyin takardu da ke ɗauke da wannan gargaɗin.

“Wannan taron zai ƙara sa ꞌyanꞌuwa su kasance da haɗin kai”

A rana ta ƙarshe na babban taron, mutane fiye da 30,000 sun saurari jawabi ga jamaꞌa da Ɗanꞌuwa Rutherford ya bayar. Jigon jawabin shi ne, “All Nations Marching to Armageddon, but Millions Now Living Will Never Die” (Yaƙin Armageddon Zai Shafi Dukan Ƙasashe, Amma Miliyoyin Mutane da Suke Raye a Yau Ba Za Su Taɓa Mutuwa Ba). Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun san cewa mutane da yawa za su halarci taron, don haka, sun yi hayar wani sabon wurin wasa a Los Angeles. Don kowa ya ji abin da ake faɗa, ꞌyanꞌuwan sun yi amfani da kayan sauti na wurin wasan, wanda sabon yayi ne a lokacin. Ƙari ga haka, mutane da yawa sun saurara ta rediyo.

AN ƘARA YIN WAꞌAZI A ƘASASHE DA YAWA

A 1923, an sami ƙaruwa sosai a fannin waꞌazi a ƙasar Afirka, da Turai, da Indiya, da Amirka ta Kudu. A Indiya, wani Ɗanꞌuwa mai suna A. J. Joseph ya taimaka wajen wallafa littattafai a yaren Hindi da Tamil da Telugu da Urdu. Ya yi hakan duk da cewa yana kula da matarsa da yara shida.

Danꞌuwa William R. Brown da iyalinsa

A ƙasar Saliyo, wasu Ɗaliban Littafi Mai Tsarki masu suna Alfred Joseph da Leonard Blackman, sun rubuta wa hedkwata a Brooklyn, da ke New York cewa suna bukatar taimako. An amsa saƙonsu a ranar 14 ga Afrilu, 1923. Alfred ya ce: “A ranar Asabar da dare, an kira ni a waya.” Da ya amsa, sai ya ji wani mutum mai babbar murya ya ce, “Kai ne ka tura saƙo cewa kuna bukatar masu waꞌazi?” Sai Alfred ya ce, “E”. Sai mutumin ya ce, “Ni ne aka aiko.” Ashe Ɗanꞌuwa William R. Brown ne. A ranar ce suka iso daga Karibiya, da shi da matarsa mai suna Antonia, da yaransu mata biyu masu suna Louise da Lucy. Ba da jimawa ba, Ɗanꞌuwa Brown da iyalinsa za su kai inda ꞌyanꞌuwan suke.

Alfred ya ci-gaba da cewa: “Washegari ni da Leonard muna tattauna Littafi Mai Tsarki kamar yadda muke yi kowane mako, sai kwatsam, wani dogon mutum ya bayyana a bakin ƙofa. Ɗanꞌuwa Brown ne. Saboda ƙwazonsa, ya so ya yi jawabi washegari.” Kafin ya kai wata ɗaya, Ɗanꞌuwa Brown ya rarraba dukan littattafan da ya zo da su. Ba da daɗewa ba, an kawo masa ƙarin littattafai guda 5,000 kuma duk ya gamar da su, har yana ma bukatar ƙarin littattafai. Amma ba a ce da shi mai sayar da littattafai ba, a maimako an dinga kiran sa Bible Brown. Domin a dukan shekarun da ya yi yana hidima, yana yawan ambata Nassosi a cikin jawabansa.

Ofishinmu da ke Magdeburg wajen shekara ta 1923

A ƙasar Jamus, ꞌyanꞌuwa sun yanke shawara cewa za su ƙaura da ofishinmu da ke Barmen, domin ofishin ya yi ƙarami sosai. Ban da haka, sun ji cewa sojojin Faransa za su kai wa birnin hari. ꞌYanꞌuwan sun samo wani babban gini a birnin Magdeburg, kuma ya dace da wurin buga littattafai. A ranar 19 ga Yuni, ꞌyanꞌuwan sun gama kwashe injunan buga littattafai da sauran kayan da suke bukata kuma sun ƙaura zuwa sabon ofishin da ke Magdeburg. Da aka sanar wa hedkwata cewa ꞌyanꞌuwa sun gama ƙaura zuwa sabon ofishinmu, sai washegari jaridu suka ba da rahoto cewa sojojin Faransa sun kwace birnin Barmen. ꞌYanꞌuwan sun gode wa Jehobah don yadda ya taimaka musu kuma ya kāre su.

Danꞌuwa George Young tare da Sarah Ferguson (a hannun dama) da ꞌyarꞌuwarta

A ƙasar Barazil kuma, wani ɗanꞌuwa mai suna George Young ya buɗe sabon ofishinmu kuma ya soma wallafa Hasumiyar Tsaro a yaren Portuguese. Ɗanꞌuwan nan ya yi tafiye-tafiye sosai don ya yi waꞌazi. A cikin ꞌyan watanni, ya rarraba littattafai fiye da 7,000. Da ya zo Barazil, ꞌYarꞌuwa Sarah Ferguson ta yi farin ciki saꞌad da ya ziyarci iyalinsu. Tun daga 1899 ne take karanta Hasumiyar Tsaro, amma ba ta taɓa samun damar yin baftisma ba. Bayan ꞌyan watanni ꞌYarꞌuwa Ferguson da yaranta guda biyu sun samu sun yi baftisma.

“MU CI-GABA DA YIN HIDIMA DA FARIN CIKI”

A ƙarshen shekarar, Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Disamba, 1923, ta bayyana yadda canji da aka yi a yadda suke yin taro da waꞌazi ya shafi Ɗaliban. Hasumiyar Tsaron ta ce: “Ba shakka, mun ga yadda ꞌyanꞌuwa a ikilisiyoyi . . . suke nuna bangaskiya sosai . . . Don haka, mu kasance a shirye don ƙarin ayyuka da za su zo a shekara mai zuwa, kuma mu ci-gaba da yin hidima da farin ciki a shekara ta 1924.”

Shekara ta 1924 shekara ce da ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka cim ma abubuwa da dama. ꞌYanꞌuwan da suke ofishinmu sun yi watanni suna aiki a wani fili da ke Saten Island, wanda bai da nisa daga hedkwatarmu a Brooklyn. A farko-farkon 1924 ne aka kammala ginin da ake yi a wurin, kuma ayyukan da aka yi a wannan ginin sun ƙara sa ꞌyanꞌuwa su kasance da haɗin kai kuma su yi waꞌazi sosai fiye da yadda suka yi a dā.

Masu gini a filin da ke Staten Island