Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 45

Kar Ka Yi Wasa da Gatan Bauta wa Jehobah a Haikalinsa na Alama

Kar Ka Yi Wasa da Gatan Bauta wa Jehobah a Haikalinsa na Alama

“Ku yi masa sujada, shi wanda ya yi sama, da duniya.”—R. YAR. 14:7.

WAƘA TA 93 Ka Albarkaci Taronmu

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Mene ne wani malaꞌika yake cewa, kuma ya hakan ya kamata ya sa mu ji?

 IDAN malaꞌika ya zo wurinka yana maka magana, za ka saurare shi kuwa? A yau, akwai wani malaꞌika da yake magana “ga kowace alꞌumma, da zuriya, da yare, da kabila.” Mene ne yake gaya musu? Yana cewa: “Ku ji tsoron Allah, . . . Ku yi masa sujada, shi wanda ya yi sama, da duniya.” (R. Yar. 14:​6, 7) Jehobah ne kaɗai Allah na gaskiya da ya cancanci kowa ya bauta masa. Muna godiya sosai da Jehobah ya ba mu damar bauta masa a haikalinsa na alama.

2. Mene ne haikalin Jehobah na alama? (Ka kuma duba akwatin nan “ Abin da Ba Ya Nufi.”)

2 Amma mene ne ainihi ake nufi da haikali na alama kuma a ina ne za mu samo bayanai game da shi? Wannan haikalin ba gini ne da mutane suka gina ba. Yana nufin shirye-shiryen da Jehobah ya yi don mu bauta masa yadda ya dace ta wurin hadayar Yesu Kristi. Manzo Bulus ya bayyana waɗannan shiryen-shiryen a wasiƙar da ya rubuta wa Kiristoci a ƙarni na farko da ke zama a Yahudiya. b

3-4. Me ya sa Bulus ya damu da Kiristoci Ibraniyawa, kuma ta yaya ya taimaka musu?

3 Me ya sa Bulus ya rubuta wa Kiristocin da ke zama a Yahudiya wannan wasiƙar? Ga dalilai biyu da mai yiwuwa suka sa ya yi hakan. Na ɗaya, yana so ya ƙarfafa su. Yawancinsu kafin su zama Kiristoci, suna bin alꞌadun Yahudawa. Yanzu da suka zama Kiristoci, mai yiwuwa shugabannin addininsu a dā suna musu baꞌa. Me ya sa? Domin Kiristoci ba su da wani haikalin da za su je su yi ibada, babu bagaden da za su miƙa hadaya ga Jehobah, kuma ba su da firist da zai yi musu hidima. Wannan zai iya sa mabiyan Kiristi su karaya kuma bangaskiyarsu ta yi sanyi. (Ibran. 2:1; 3:​12, 14) Ƙila wasunsu ma sun yi tunanin koma bin addinin Yahudawa.

4 Na biyu, Bulus ya gaya wa Kiristocin cewa ba sa yin iya ƙoƙarinsu don su fahimci sabbin koyarwa ko koyarwa masu wuyar fahimta, wato “abinci mai ƙauri” da ke Kalmar Allah. (Ibran. 5:​11-14) Wataƙila wasu daga cikinsu suna kan bin Dokar Musa. Amma Bulus ya bayyana musu cewa hadayun da Dokar ta ce su riƙa yi ba za su iya wanke zunubansu gabaki ɗaya ba. Saboda haka, an ajiye wannan Dokar a “gefe.” Sai Bulus ya soma koya musu wasu abubuwa masu wuyar fahimta. Ya tuna wa ꞌyanꞌuwan wata mafita mafi kyau da Allah ya shirya ta wurin hadayar Yesu Kristi, kuma wannan shi ne zai taimaka musu su yi “kusa da Allah.”—Ibran. 7:​18, 19.

5. Me muke bukatar mu fahimta daga littafin Ibraniyawa kuma me ya sa?

5 Bulus ya bayyana musu yadda ibadar da suke yi yanzu ya fi ibadar da suke yi a dā. Ayyukan ibada da Yahudawa suke yi bisa ga Dokar Musu ‘kamar hoto ne kawai na abin da zai zo, amma Almasihu shi ne ainihin abin.’ (Kol. 2:17) Hoton abu ba shi ne ainihin abin ba. Haka ma ayyukan ibada da Yahudawa suke yi yana wakiltar abubuwan da za su faru a nan gaba ne. Muna bukatar mu fahimci shirye-shiryen da Jehobah ya yi mana don a gafarta mana zunubanmu. Hakan zai sa mu iya bauta masa yadda yake so. Yanzu bari mu gwada ‘hoton,’ wato ayyukan ibada da Yahudawa suke yi, da “ainihin abin,” wato yadda Kiristoci suke ibada, kamar yadda aka bayyana a littafin Ibraniyawa. Ta haka, za mu fahimci abin da haikali na alama yake nufi kuma mu ga yadda ya shafe mu.

MAZAUNIN

6. Wane amfani ne mazaunin yake wa Yahudawa?

6 Yadda Yahudawa suke ibada a dā. Saꞌad da Bulus yake tattaunawar nan, ya yi magana ne game da mazaunin da Musa ya yi a shekara ta 1512 kafin haihuwar Yesu. (Ka duba hoton nan “Yadda Yahudawa Suke Ibada a Dā da Yadda Kiristoci Suke Ibada.”) Mazaunin tenti ne da Israꞌilawa suke ɗaukawa yayin da suke ƙaura. Sun yi kusan shekaru 500 suna amfani da shi har sai lokacin da aka gama gina haikali a Urushalima. (Fit. 25:​8, 9; L. Ƙid. 9:22) Mazaunin ko kuma “Tentin Saduwa,” shi ne wurin da Israꞌilawa suke zuwa don su bauta wa Jehobah kuma su miƙa hadayunsu. (Fit. 29:​43-46) Amma wannan mazaunin yana wakiltar wani abu mai muhimmanci da Kiristoci za su samu a nan gaba.

7. Yaushe ne Jehobah ya shirya wa Kiristoci wannan haikali na alama?

7 Yadda Kiristoci suke ibada. Mazaunin da Yahudawa suke amfani da shi “kwatanci” ne na “abubuwan da suke a sama,” kuma yana wakiltar haikalin Jehobah na alama. Bulus ya ce wannan mazaunin “kwatanci ne ga wannan zamani.” (Ibran. 8:5; 9:9) Don haka, saꞌad da Bulus ya rubuta wasiƙar nan ga Ibraniyawa, Jehobah ya riga ya shirya wannan haikali na alama. Ya yi hakan ne a shekara ta 29 bayan haihuwar Yesu. A shekarar ce Yesu ya yi baftisma, aka naɗa shi da ruhu mai tsarki kuma ya soma yi wa Jehobah hidima a matsayin “Babban Firist mai girma” a cikin wannan haikali na alama. cIbran. 4:14; A. M. 10:​37, 38.

BABBAN FIRIST

8-9. Kamar yadda yake a Ibraniyawa 7:​23-27, me ya bambanta babban firist na Israꞌilawa da Yesu Kristi Babban Firist mai girma?

8 Yadda Yahudawa suke ibada a dā. Babban firist ne yake tsayawa a gaban Allah a madadin mutanen. Haruna ne ya zama babba firist na farko a Israꞌila kuma Jehobah ya naɗa shi ne saꞌad da aka gama ƙera mazaunin. Amma kamar yadda Bulus ya bayyana, mutane da yawa sun zama firistoci domin “mutuwa takan hana su ci gaba da aikinsu.” d (Karanta Ibraniyawa 7:​23-27.) Kuma da yake firistocin nan ajizai ne, su ma suna bukatar su miƙa hadaya don nasu zunuban. Hakan ya nuna bambancin da ke tsakanin babban firist na Israꞌila da Babban Firist mai girma, wato Yesu Kristi.

9 Yadda Kiristoci suke ibada. Yesu Kristi, Babban Firist ɗinmu mai girma “yana hidimarsa . . . a ainihin tentin kasancewar Allah wanda Ubangiji da kansa ne ya kafa, ba mutum ba.” (Ibran. 8:​1, 2) Manzo Bulus ya bayyana cewa “Yesu yana riƙe da matsayin firist na har abada, domin shi da kansa yana nan har abada.” Bulus ya ƙara da cewa Yesu “marar tabo” ne, “an ware shi daga masu zunubi.” Kuma shi ba kamar babban firist na Israꞌilawa ba ne, domin “ba ya bukata ya dinga miƙa hadaya kullum” don zunubansa. Yanzu bari mu ga bambancin da ke tsakanin bagade da hadayun da Yahudawa suke yi da kuma ayyukan ibada da Kiristoci suke yi.

BAGADE DA HADAYUN DA AKE YI

10. Hadayun da ake yi a kan bagaden, alamun mene ne?

10 Yadda Yahudawa suke ibada a dā. Kafin a shiga mazaunin, akwai wani bagade da aka yi da tagulla kuma a wurin ake miƙa hadayu ga Jehobah. (Fit. 27:​1, 2; 40:29) Amma waɗannan hadayun ba za su iya cire zunuban mutanen gabaki ɗaya ba. (Ibran. 10:​1-4) Hadayun da ake bayarwa a mazaunin suna wakiltar hadayar Yesu, wadda ita kaɗai ce za ta cire zunuban ꞌyan Adam gabaki ɗaya.

11. A wane bagade ne Yesu ya miƙa kansa a matsayin hadaya? (Ibraniyawa 10:​5-7, 10)

11 Yadda Kiristoci suke ibada. Yesu ya san cewa Jehobah ya aiko shi duniya ne don ya ba da ransa a matsayin fansa ga ꞌyan Adam. (Mat. 20:28) Don haka, saꞌad da Yesu ya yi baftisma, ya miƙa kansa ga Jehobah don ya yi nufinsa. (Yoh. 6:38; Gal. 1:4) Bagaden da Yesu ya yi hadaya a kai ba bagaden da mutane suka gina ba ne. “Nufin” Allah ne bagaden, kuma nufin Allah shi ne Yesu ya ba da ransa a madadin ꞌyan Adam. Yesu ya ba da ransa “sau ɗaya tak” don ya cire zunuban duk wanda ya ba da gaskiya gare shi. (Karanta Ibraniyawa 10:​5-7, 10.) Yanzu bari mu ga maꞌanar abubuwan da ke cikin mazaunin.

WURI MAI TSARKI DA MAFI TSARKI

12. Wane ne zai iya shiga wuri Mai Tsarki da wuri Mafi Tsarki?

12 Yadda Yahudawa suke yin ibada a dā. Yadda aka gina mazauni da haikali da aka gina daga baya kusan irin ɗaya ne. Dukansu suna da ɗakuna biyu, wato “Wuri Mai Tsarki” da “Wuri Mafi Tsarki,” kuma akwai labulen da ya raba tsakaninsu. (Ibran. 9:​2-5; Fit. 26:​31-33) A cikin wuri Mai Tsarki, akwai fitila, da bagaden ƙona turare, da teburi don ajiye gurasa. Firistoci “waɗanda aka keɓe” ne kawai suke da izinin shiga wuri Mai Tsarki don su yi hidima. (L. Ƙid. 3:​3, 7, 10) A cikin wuri Mafi Tsarki kuma, akwai akwatin yarjejeniya (sanduƙin alkawari) wanda yake nuna cewa Jehobah yana wurin. (Fit. 25:​21, 22) Babban firist ne kaɗai zai iya shiga wuri Mafi Tsarki a ranar Dauƙar Alhakin Zunubi. (L. Fir. 16:​2, 17) Kowace shekara yana shiga wurin da jinin dabbobi don ya roƙi gafarar zunubansa da na mutanen. Daga baya, Jehobah ya yi amfani da ruhunsa don ya bayyana maꞌanar abubuwan da ke cikin mazaunin.—Ibran. 9:​6-8. e

13. A ibadar da Kiristoci suke yi, mene ne wuri Mai Tsarki da Mafi Tsarki suke wakilta?

13 Yadda Kiristoci suke ibada. An shafe wasu mabiyan Yesu Kristi da ruhu mai tsarki, kuma suna da dangantaka ta musamman da Jehobah. Waɗannan shafaffu guda 144,000 za su yi hidima a matsayin firistoci tare da Yesu a sama. (R. Yar. 1:6; 14:1) Wuri Mai Tsarki da ke cikin mazaunin yana wakiltar matsayinsu na ꞌyaꞌyan Allah ko da yake suna duniya. (Rom. 8:​15-17) Wuri Mafi Tsarki kuma yana wakiltar sama inda Jehobah yake. “Labulen” da ya raba tsakanin wuri Mai Tsarki da Mafi Tsarki yana wakiltar jikin Yesu. Saꞌad da yake duniya, da yake yana da jiki irin na ꞌyan Adam, ba zai iya zuwa sama don ya yi hidima a matsayin Babban Firist a haikalin Jehobah ba. Da ya mutu, ya ba da jikinsa a matsayin hadaya, kuma hakan ya buɗe wa shafaffu hanyar zuwa sama. Amma kafin su iya zuwa sama, wajibi ne su ma su rabu da jikinsu na ꞌyan Adam. (Ibran. 10:​19, 20; 1 Kor. 15:50) Bayan an ta da Yesu daga mutuwa, ya shiga wuri Mafi Tsarki na haikali na alama, kuma daga baya dukan shafaffu za su kasance tare da shi a wurin.

14. Bisa ga Ibraniyawa 9:​12, 24-26, me ya sa shirye-shiryen da Jehobah ya yi don a bauta masa suka fi yadda Yahudawa suke yin ibada a dā?

14 A nan, mun ga cewa shirye-shiryen da Jehobah ya yi don a bauta masa ta wurin fansar Yesu da hidimar firist da Yesu yake yi sun fi ibada da Yahudawa suke yi a dā. Babban firist a Israꞌila yakan shiga wuri Mafi Tsarki da mutane suka gina, kuma yana shiga ne da jinin dabbobi. Amma Yesu, “sama ne da kansa ya shiga” don ya zo gaban Jehobah, kuma babu inda ya kai sama tsarki. A sama, ya miƙa wa Jehobah darajar kamiltaccen ransa da ya bayar a madadinmu don ya “kawar da zunubai.” (Karanta Ibraniyawa 9:​12, 24-26.) Hadayar Yesu ce kawai za ta iya wanke zunuban ꞌyan Adam har abada. Yanzu za mu koyi yadda za mu bauta wa Jehobah a haikalinsa na alama ko da muna begen zuwa sama ko rayuwa a aljanna a duniya.

FILIN HAIKALIN

15. Su wane ne suke hidima a filin da ke mazaunin?

15 Yadda Yahudawa suke ibada a dā. Mazaunin yana da fili ko kuma farfajiya guda ɗaya. Filin babba ne kewaye da katanga, kuma a wurin ne firistoci suke hidimarsu. A wurin ne aka ajiye bagaden ƙona hadaya tare da daron jan ƙarfe wanda firistocin suke amfani da shi don su tsabtace kansu kafin su soma hidima. (Fitowa 30:​17-20; 40:​6-8) Amma haikalin da aka gina daga baya yana da fili a waje inda waɗanda ba firistoci ba za su iya tsayawa don su bauta wa Jehobah.

16. Su wane ne suke hidima a fili na ciki da fili na waje a haikalin?

16 Yadda Kiristoci suke ibada. Kafin shafaffu su je sama don su yi hidimar firist tare da Yesu, suna yin hidimarsu da dukan zuciya a nan duniya, wato a farfajiya ko fili na ciki a haikalin. Daron jan ƙarfe da ke cikin mazaunin da na cikin haikalin da aka gina daga baya yana tuna wa shafaffu da dukan Kiristoci cewa yana da muhimmanci su kasance da tsabta a kowane fannin rayuwarsu. To a ina ne taro mai girma ko babban taro, wato waɗanda suke goyon bayan shafaffu suke yin tasu hidimar? Manzo Yohanna ya gan su “suna tsaye a gaban kujerar mulkin . . . suna yi [ma Allah] hidima dare da rana a cikin haikalinsa.” Taro mai girman suna yin hidima a nan duniya, wato fili na waje na haikali na alama. (R. Yar. 7:​9, 13-15) Muna godiya sosai don damar da Jehobah ya ba mu mu bauta masa a haikalinsa.

GATAN DA MUKE DA SHI NA YI WA JEHOBAH HIDIMA

17. Waɗanne irin hadayu ne muke da gatan miƙa wa Jehobah?

17 A yau dukan Kiristoci suna da gatan miƙa wa Jehobah hadaya. Suna yin hakan ne ta wajen yin amfani da lokacinsu da ƙarfinsu da kuma abubuwan da suke da su don su bauta masa. Kamar yadda Bulus ya gaya wa Ibraniyawa, zai yiwu mu “dinga miƙa hadayar yabo ga Allah ta wurin Yesu, wato yabon shaidar darajar Sunansa ke nan.” (Ibran. 13:15) Za mu nuna cewa muna daraja damar da ya ba mu na bauta masa idan muna iya ƙoƙarinmu a hidimarmu.

18. Bisa ga Ibraniyawa 10:​22-25, waɗanne abubuwa ne bai kamata mu yi wasa da su ba, kuma mene ne ya kamata mu ci-gaba da tunawa?

18 Karanta Ibraniyawa 10:​22-25. Da ya kusan kammala wasiƙar da yake rubuta wa Ibraniyawa, Bulus ya ambata wasu ayyukan ibada da bai kamata mu yi wasa da su ba. Waɗannan ayyukan sun haɗa da yin adduꞌa da yin waꞌazi da halartar taro da kuma ƙarfafa junanmu ‘yayin da muke ganin cewa Ranar [Jehobah] tana matsowa kusa.’ A ta ƙarshe-ƙarshen littafin Ruꞌuyar da aka yi wa Yohanna, wani malaꞌika ya maimaita furucin nan: “Yi wa Allah sujada,” don ya nuna muhimmancinsa. (R. Yar. 19:10; 22:9) Bari mu ci gaba da tuna waɗannan koyarwa masu muhimmanci game da haikalin Jehobah na alama, da kuma gatan da muke da shi na bauta wa Allahnmu mai girma!

WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka

a Ɗaya daga cikin koyarwar Littafi Mai Tsarki mai wuyar fahimta shi ne game da haikalin Jehobah na alama. Mene ne wannan haikalin? Wannan talifin ya tattauna abin da littafin Ibraniyawa ya faɗa game da haikalin nan. Bari wannan nazarin ya sa ka ƙara daraja gatan da kake da shi na bauta wa Jehobah.

b Don ka ga abin da ke cikin littafin Ibraniyawa, ka kalli bidiyon nan Gabatarwar Littafin Ibraniyawa a jw.org/ha.

c A cikin Nassosin Helenanci na Kirista, littafin Ibraniyawa ne kaɗai ya ce da Yesu Babban Firist.

d Wani bincike ya nuna cewa a lokacin da aka halaka haikalin da ke Urushalima a shekara ta 70 bayan haihuwar Yesu, mai yiwuwa akwai manyan firistoci da suka kai 84.

g Ka duba akwatin nan “Yadda Ruhun Ya Bayyana Maꞌanar Haikali na Ruhaniya” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2010, shafi na 22.