Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shawara a Kan Yin Nazari

Shawara a Kan Yin Nazari

Yadda Za Ka San Ƙarin Haske da Aka Yi a Kan Koyarwarmu

Muna rayuwa ne a lokaci mai ban shaꞌawa, lokacin da Jehobah yake ƙara bayyana mana abubuwa da yawa da suke Kalmarsa. (Dan. 12:4) Amma wani lokaci, sanin dukan ƙarin hasken da muke samu zai iya zama mana da wuya. A ina ne za mu samu bayanai a kan ƙarin hasken da ake yi?

• Littafin nan Watch Tower Publications Index, yana da jigon nan, Beliefs Clarified.” A wurin, za a iya samun ƙarin hasken da aka yi wa koyarwarmu bisa ga shekarar da aka yi hakan. Idan kana so ka ga batutuwan da aka yi gyara a kai, ka rubuta “understanding clarified” (da alamar nan “ ”) a inda aka ce “Bincika,” a Watchtower Library ko Watchtower ONLINE LIBRARY, sai ka bincika.

Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah na Turanci shi ma yana ɗauke da wasu ƙarin hasken, kuma an jera su ne bisa ga batun da aka tattauna. Ka nemi jigon nan Jehovah’s Witnesses,” a ƙarƙashinsa, ka duba “Views and Beliefs,” sai ka duba “Clarification of Our Beliefs.”

Yayin da kake nazari, ka gwada zaɓan ɗaya daga cikin ƙarin hasken da aka yi wa koyarwarmu na kwana-kwanan nan, ka bincika gyara da aka yi da kuma dalilin da ya sa aka yi gyaran bisa ga Littafi Mai Tsarki.