Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Riƙa Tunani Kafin Ka Yanke Shawara

Ka Riƙa Tunani Kafin Ka Yanke Shawara

Mene ne za ka yi idan kana so ka yi tafiya zuwa wurin da ba ka taɓa zuwa ba?

  1. 1. Za ka bi hanyar da ka ga dama?

  2. 2. Za ka bi mutanen da kake ganin sun san hanyar?

  3. 3. Za ka nemi taimako ta wajen amfani da naꞌurar GPS ko taswira ko kuma za ka tambayi wani amininka da ya san hanyar?

Idan muka zaɓi na ɗaya ko na biyu za mu isa wani wuri, amma ba lalle ne ya zama wurin da muke so mu je ba. Idan muka zaɓi na ukun, za mu iya kasance da tabbaci cewa za mu isa wurin da za mu je.

Rayuwarmu tana kama da yin tafiya. Kuma muna sa rai cewa zai sa mu farin ciki a nan gaba. Irin wuraren da muke neman shawara za su iya sa mu yi farin ciki ko baƙin ciki a rayuwa.

Ko da yake yawancin shawarwarin da muke yankewa ba sa shafan rayuwarmu, amma wasu suna shafan rayuwarmu sosai don suna da muhimmanci. Waɗannan shawarwari masu muhimmanci ne za su nuna abin da muke gani ya dace da wanda bai dace ba. Shawarwarin nan za su iya sa mu da ꞌyanꞌuwa da abokanmu farin ciki ko baƙin ciki na dogon lokaci. Shawarwarin nan, sun ƙunshi shawarwari game da:

  • Jimaꞌi da aure

  • Faɗin gaskiya, aiki da kuma kuɗi

  • Yadda za a yi renon yara

  • Yadda za mu yi maꞌamala da mutane

Me zai taimaka maka ka kasance da tabbaci cewa zaɓin da ka yi a waɗannan wuraren zai sa kai da iyalinka farin ciki?

Abin da ya kamata mu tambayi kanmu shi ne: Mene ne zai taimaka min in yanke shawara game da abin da ya dace da wanda bai dace ba?

Mujallar nan za ta bayyana dalilin da ya sa za mu dogara ga abin da ke Littafi Mai Tsarki game da abin da ya dace da wanda bai dace ba, da kuma yadda zai taimaka maka.