Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wajibi Ne Ka Zabi Irin Shawarwarin da Za Ka Yanke

Wajibi Ne Ka Zabi Irin Shawarwarin da Za Ka Yanke

Jehobah ya san cewa zaɓin da muka yi game da ƙaꞌidodin da za mu bi, zai iya sa mu yi farin ciki ko baƙin ciki. Shi ya sa yake so mu bi ƙaꞌidodinsa.

Jehobah yana so mu yi farin ciki kuma mu sami kwanciyar hankali.

“Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya koya muku domin amfanin kanku, wanda ya nuna muku hanyar da za ku bi. Ayya! Da a ce kun yi biyayya da umarnaina, da salamarku za ta kasance kamar ruwan rafi, nasarar adalcinku kuma za ta yi ta ɓullowa kamar raƙuman ruwan teku.”—Ishaya 48:​17, 18.

A matsayinsa na Mahaliccinmu, Allah ya san irin rayuwar da za mu yi da zai amfane mu. Yana so mu bi ƙaꞌidodinsa don mu yi rayuwa mai inganci. Idan muka bi umurnin Allah, ba za mu yi shakka cewa zaɓin da muka yi mai kyau ne ba. Ƙari ga haka, za mu riƙa yanke shawarwari masu kyau da za su sa mu yi farin ciki kuma mu sami kwanciyar hankali.

Jehobah ba zai ce mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ba.

“Wannan umarnin da nake umarce ku yau, bai fi ƙarfinku ba, ko ya gagare ku aikatawa ba.”—Maimaitawar Shari’a 30:11.

Bin ƙaꞌidodin Allah zai bukaci mu canja tunaninmu da yadda muke yin abubuwa. Amma Jehobah ba zai ce mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ba. Balle ma, a matsayinsa na Mahaliccinmu ya san abin da za mu iya yi. Idan muka ci gaba da koya game da Jehobah, za mu ga cewa “umarnansa ba su da nauyi.”—1 Yohanna 5:3.

Jehobah ya yi alkawari zai taimaka ma waɗanda suka bi ƙaꞌidodinsa.

“Ni Yahweh Allahnka ne, ina riƙe da hannun damanka. Ni ne kuma nake ce maka, ‘Kada ka ji tsoro, ni ne mai taimakonka.’”—Ishaya 41:13.

Za mu iya yin irin rayuwar da Allah yake so domin zai taimaka mana. Ta wurin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana, kuma hakan zai ƙarfafa mu, kuma ya sa mu kasance da bege.

Miliyoyin mutane a duniya sun ga cewa bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ya inganta rayuwarsu. Ka yi ƙoƙari ka san shawarwari masu kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Za ka iya soma yin hakan ta wurin nazarin ƙasidar nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! kyauta da ke dandalin jw.org/ha. Yana ɗauke da batutuwan nan:

  • Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Inganta Rayuwarka?

  • Littafi Mai Tsarki Ya Ce Za Mu Ji Daɗin Rayuwa

  • Za Ka Iya Amincewa da Littafi Mai Tsarki?

Yayin da kake karanta Kalmar Allah, za ka ga cewa ba tsohon yayi ba ne, amma za mu iya bin abin da ke ciki “har abada abadin.” (Zabura 111:8) Bin shawarwarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne hanya mafi kyau na yin rayuwa. Amma Allah ba zai tilasta mana mu yi hakan ba. (Maimaitawar Shari’a 30:​19, 20; Yoshuwa 24:15) Zaɓi ne da kowannnemu ya kamata ya yi.