Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 2

WAƘA TA 19 Jibin Maraice na Ubangiji

Ka Yi Shiri don Rana Mafi Muhimmanci a Shekara?

Ka Yi Shiri don Rana Mafi Muhimmanci a Shekara?

“Ku dinga yin haka don tunawa da ni.”LUK. 22:19

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da ya sa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu yake da muhimmanci sosai, da yadda za mu yi shiri don taron, da kuma yadda za mu taimaka wa mutane su ma su halara.

1. Me ya sa ranar Taron Tunawa da Mutuwar Yesu ce rana mafi muhimmanci a shekara? (Luka 22:​19, 20)

 A GUN bayin Jehobah, rana mafi muhimmanci a shekara ita ce ranar Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Kuma wannan taron ne kaɗai Yesu ya fito fili ya umurci mabiyansa su riƙa yi. (Karanta Luka 22:​19, 20.) Akwai abubuwa da yawa da suka sa muke marmarin wannan taron. Bari mu bincika wasu cikinsu.

2. Me ya sa kake marmarin zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

2 Taron Tunawa da Mutuwar Yesu yana taimaka mana mu yi tunani a kan muhimmancin fansar Yesu. Yana kuma tuna mana hanyoyin da za mu nuna godiyarmu don wannan fansar. (2 Kor. 5:​14, 15) Ban da haka ma, yana ba mu damar “ƙarfafa juna.” (Rom. 1:12) ꞌYanꞌuwa da yawa da suka daina zuwa taro, sukan zo wannan taro kowace shekara. Wasun su sukan komo ga Jehobah don yadda ꞌyanꞌuwa suka karɓe su hannu bi-biyu. Kuma mutane da yawa sukan soma nazarin Littafi Mai Tsarki domin abubuwan da suka gani da abubuwan da suka ji a taron sun burge su. Shi ya sa dukanmu muna son Taron Tunawa da Mutuwar Yesu sosai!

3. Ta yaya Taron Tunawa da Mutuwar Yesu yake haɗa kanmu da ꞌyanꞌuwanmu a duk faɗin duniya? (Ka kuma duba hoton.)

3 Ka kuma yi tunanin yadda Taron Tunawa da Mutuwar Yesu yake haɗa kanmu a duk faɗin duniya. A duk faɗin duniya, da zarar yammar nan ta yi, Shaidun Jehobah sukan soma yin wannan taron. Kuma dukanmu mukan ji jawabin da ke bayyana muhimmancin fansar Yesu. Mukan rera waƙoƙin yabo guda biyu. Akan zagaya da burodi da kuma ruwan inabi. Ban da haka, akan yi adduꞌa sau huɗu kuma dukanmu mu ce “amin.” Cikin saꞌoꞌi 24, dukan ikilisiyoyinmu a faɗin duniya sukan bi wannan tsarin. Ba ka ganin Jehobah da Yesu suna yin farin ciki sosai idan suka ga dukanmu mun taru haka muna yabon su?

Taron Tunawa da Mutuwar Yesu yana haɗa kanmu a duk faɗin duniya (Ka duba sakin layi na 3) f

4. Me za mu tattauna a wannan talifin?

4 A wannan talifin za mu amsa tambayoyin nan: Ta yaya za mu shirya zuciyarmu don Taron Tunawa da Mutuwar Yesu? Ta yaya za mu taimaka wa mutane su amfana daga taron? Kuma ta yaya za mu taimaka ma waɗanda suka daina zuwa taro? Samun amsoshin tambayoyin nan za su taimaka mana mu yi shiri don wannan taro mai muhimmanci sosai.

TA YAYA ZA MU SHIRYA ZUCIYARMU DON TARON TUNAWA DA MUTUWAR YESU?

5. (a) Me ya sa ya kamata mu yi tunani mai zurfi a kan muhimmancin fansar? (Zabura 49:​7, 8) (b) Me ka koya daga bidiyon nan, Me Ya Sa Yesu Ya Mutu?

5 Ɗaya daga cikin hanyoyi mafi muhimmanci da za mu shirya zuciyarmu don Taron Tunawa da Mutuwar Yesu ita ce, ta wajen yin tunani a kan muhimmancin fansar da Yesu ya bayar. Idan aka bar mu da kanmu, ba za mu taɓa iya ceci kanmu daga zunubi da mutuwa ba. (Karanta Zabura 49:​7, 8; ka kuma duba bidiyon nan, Me Ya Sa Yesu Ya Mutu?) a Shi ya sa Jehobah ya ba da Yesu ya mutu don ya cece mu. Jehobah da Yesu ne suka yi wannan babbar sadaukarwa. (Rom. 6:23) Idan muka yi ta yin tunani mai zurfi a kan irin sadaukarwar da Jehobah da Yesu suka yi domin mu, za mu ƙara yin godiya don wannan fansar. Za mu bincika kalila daga cikin abubuwa masu wuya da Jehobah da Yesu suka yarda su yi mana. Amma kafin nan, me ake nufi da fansa? Kuma ta yaya aka fanshe mu?

6. Me ake nufi da fansa, kuma me ya sa Yesu ya ba da fansar?

6 Fansa tana nufin abin da ake bayarwa don a sake samun abin da aka rasa. A lokacin da aka halicci Adamu, ba shi da zunubi. Da Adamu ya yi zunubi, ya rasa damar yin rayuwa har abada kuma wannan hasarar ta shafi ꞌyaꞌyansa ma. Yesu ya ba da kamiltaccen ransa don a sake samun abin da Adamu ya rasa. Yesu ya yi rayuwa a duniya amma “bai taɓa yin laifi ba ko kaɗan. Bai taɓa yin ƙarya ba.” (1 Bit. 2:22) A lokacin da ya mutu shi ma bai da zunubi kamar Adamu, shi ya sa ransa da ya bayar ya yi daidai da wanda Adamu ya rasa.—1 Kor. 15:45; 1 Tim. 2:6.

7. Ka ambaci wasu jarabobi da Yesu ya fuskanta saꞌad da yake duniya.

7 Duk da jarabobin da Yesu ya fuskanta saꞌad da yake duniya, ya ci-gaba da yin biyayya ga Allah. Da aka haife shi a duniya shi marar zunubi ne, iyayensa kuma masu zunubi ne, duk da haka ya yi musu biyayya. (Luk. 2:51) Saꞌad da yake matashi, Yesu ya yi iya ƙoƙarinsa don kar mutane su sa ya yi rashin biyayya. Da ya yi girma ma, sai da Yesu ya dage sosai don Shaiɗan ya yi ta ƙoƙarin sa shi ya yi zunubi. Shaiɗan ya takura ma Yesu, har ya ce ma Yesu ya yi masa sujada. (Mat. 4:​1-11) Burinsa shi ne ya sa Yesu ya yi zunubi don ya kasa biyan fansar.

8. Waɗanne abubuwa ne kuma Yesu ya yi fama da su?

8 A lokacin da Yesu yake hidimarsa a duniya, ya kuma yi fama da wasu matsaloli. An tsananta masa kuma sau da yawa an yi ƙoƙarin kashe shi. (Luk. 4:​28, 29; 13:31) Mabiyansa ma sun yi ta yin abubuwa da ba su dace ba amma ya yi haƙuri da su. (Mar. 9:​33, 34) A lokacin da ake yi masa shariꞌa, an zalunce shi kuma an yi masa baꞌa. Bayan haka, an zarge shi da aikata laifi kuma an rataye shi har ya mutu. (Ibran. 12:​1-3) Ƙari ga haka, saꞌad da yake kan gungumen azaba ya sha wahala sosai shi kaɗai, Jehobah bai kāre shi ba. bMat. 27:46.

9. Yaya kake ji game da sadaukarwar da Yesu ya yi? (1 Bitrus 1:8)

9 Ba shakka Yesu ya sha wahala sosai yayin da yake ba da wannan fansar. Tunanin irin sadaukarwar da Yesu ya yi saboda mu, yana sa mu ƙaunace shi sosai.—Karanta 1 Bitrus 1:8.

10. Wane sadaukarwa ne Jehobah ya yi don ya fanshe mu?

10 Jehobah kuma fa? Mene ne ya sadaukar don ya yi mana tanadin wannan fansar? Irin ƙaunar da Jehobah yake ma Yesu yana kama da ƙaunar da uba yake wa ɗansa. (K. Mag. 8:30) Don haka, ka yi tunanin yadda Jehobah ya ji da ya ga Yesu yana shan wahala. Ba shakka, Jehobah ya ji zafi sosai a ransa da ya ga ana wulaƙanta ɗansa, da kuma yadda mutane suka ƙi ɗansa.

11. Wane misali ne ya nuna yadda Jehobah ya ji saꞌad da aka kashe ɗansa?

11 Duk wani mahaifin da ya taɓa rasa ɗansa ya san cewa hakan yana da zafi sosai. Mun san za a ta da matattu, amma duk da haka muna baƙin ciki sosai idan wanda muke ƙauna ya rasu. Wannan misalin zai taimaka mana mu san irin zafin da Jehobah ya ji a ransa, saꞌad da ya ga ɗansa yana shan wahala har ya mutu a ranar 14 ga Nisan na shekara ta 33. cMat. 3:17.

12. Me zai dace mu yi kafin ranar Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

12 Kafin ranar Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, ka yi ƙoƙari ka yi nazari game da fansar Yesu. Idan kana da iyali, ku yi shi a ibada ta iyalinku. Ka yi amfani da Littafin Bincike don Shaidun Jehobah ko wata hanyar bincike da muke da ita don ka bincika wannan batun. d Kuma ka tabbata ka bi tsarin karatun Littafi Mai Tsarki don Tunawa da Mutuwar Yesu da ke Littafin Taro Don—Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. Ƙari ga haka, a ranar tunawa da mutuwar Yesu, kar ka manta ka kalli Ibadar Safiya ta musamman da za a yi. Idan muka shirya zuciyarmu don Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, za mu iya taimaka wa mutane sosai don su ma su amfana daga taron.—Ezra 7:10.

KA TAIMAKA WA MUTANE SU AMFANA DAGA TARON

13. Mece ce hanya ta farko da za mu taimaka wa mutane su amfana daga Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

13 Ta yaya za mu taimaka wa mutane su ma su amfana daga Taron Tunawa da Mutuwar Yesu? Hanya ta farko ita ce, mu gayyace su. Ya kamata mu gayyaci mutane idan muka fita waꞌazi. Ban da haka, zai dace mu rubuta sunayen wasu da za mu so mu gayyata. Za mu iya haɗa da sunayen danginmu da abokan aikinmu da abokan makarantarmu da dai sauransu. Ko da ba mu da littafin gayyata da aka buga da yawa, za mu iya tura wa mutum mahaɗi, wato link, don ya iya duba gayyatar da naꞌurarsa. Idan muka yi hakan, mai yiwuwa za mu yi mamakin yawan mutane da za su zo taron.—M. Wa. 11:6.

14. Ka ba da misalin da ya nuna amfanin gayyatar wanda ka sani ya zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu.

14 Idan ka gayyaci mutum ya zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, hakan zai iya sa ya ɗauki taron da muhimmanci sosai. Wata ꞌyarꞌuwa da maigidanta ba Mashaidi ba ne ta yi mamaki sosai da ya gaya mata cewa zai bi ta zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Me ya sa ta yi mamaki? Dalilin shi ne, ta saba gayyatar sa zuwa wannan taron sau da yawa amma bai taɓa zuwa ba. Me ya sa ya canja raꞌayinsa a karon nan? Da aka tambaye shi, ya ce wani dattijo da ya waye shi ne ya ba shi takardar gayyata na taron. Maigidan wannan ꞌyarꞌuwar ya kuma ci-gaba da zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu.

15. Idan muna gayyatar mutane zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, me ya kamata mu tuna?

15 Ka tuna cewa idan ka gayyaci mutum zuwa taron nan, mai yiwuwa zai so ya yi maka wasu tambayoyi, musamman idan bai taɓa zuwa taronmu ba. Don haka, zai dace mu yi tunanin tambayoyin da za su iya yi mana da amsar da za mu ba su. (Kol. 4:6) Alal misali, wasu za su iya tambayar mu cewa: ‘Me da me za a yi a taron?’ ‘Yaya tsawon lokaci da taron zai ci?’ ‘Akwai irin kayan da ake so mutum ya saka ne?’ ‘Ana biyan kuɗi kafin a shiga?’ ‘Za a ce a yi baiko?’ Don haka, idan ka gayyaci mutum ya zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu za ka iya tambayar sa, “Akwai abin da za ka so ka sani game da taron?” Sai ka bayyana masa duk abin da yake so ya sani. Ƙari ga haka, za mu iya yin amfani da bidiyoyin nan, Ka Tuna da Mutuwar Yesu da kuma Me Ake Yi a Majamiꞌar Mulki? don mu taimaka masa ya san yadda muke yin taronmu. Akwai kuma abubuwa masu kyau da za mu iya gaya wa mutumin a darasi na 28 na littafin nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!

16. Waɗanne tambayoyi ne kuma waɗanda suka zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu za su iya yi mana?

16 Waɗanda suka zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu za su iya yi mana wasu tambayoyi kuma bayan taron. Don ƙila sun yi mamakin abin da ya sa mutane kalila ne kawai suka ci burodin kuma suka sha ruwan inabin, mai yiwuwa ma babu wanda ya ci. Za su kuma iya tambayar mu ko sau nawa ne muke yin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, kuma za su so su san ko haka muke yin dukan tarurrukanmu. Ko da an bayyana abubuwan nan a jawabin da aka yi a Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, mai yiwuwa waɗanda suka zo taron a karon farko za su bukaci ƙarin bayani. Talifin nan mai jigo, “Me Ya Sa Yadda Shaidun Jehobah Suke Yin Jibin Ubangiji Ya Bambanta da Na Sauran Addinai?” da ke jw.org/ha zai iya taimaka mana mu amsa wasu tambayoyin mutane. Hakika, kafin ranar taron, a lokacin taron, da kuma bayan taron, zai dace mu yi duk wani abin da za mu iya don mu taimaka wa masu “zuciya ta samun rai na har abada” su amfana daga wannan taron.—A. M. 13:​48, New World Translation.

KA TAIMAKA WA WAƊANDA SUKA DAINA ZUWA TARO

17. Ta yaya dattawa za su iya taimaka ma waɗanda suka daina zuwa taro? (Ezekiyel 34:​12, 16)

17 Mene ne dattawa za su iya yi a lokacin tunawa da mutuwar Yesu don su taimaka ma waɗanda suka daina zuwa taro? Ku nuna musu cewa kun damu da su. (Karanta Ezekiyel 34:​12, 16.) Ku yi ƙoƙari ku ziyarci dukansu in zai yiwu. Ku tabbatar musu da cewa kuna ƙaunarsu kuma kuna so ku taimaka musu iya gwargwadon ƙarfinku. Ku gayyace su su zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu kuma idan suka zo, ku karɓe su hannu bi-biyu. Bayan taron, ku ci-gaba da tuntuɓar waɗannan ꞌyanꞌuwanmu kuma ku ba su duk taimakon da suke bukata don su iya komowa ga Jehobah.—1 Bit. 2:25.

18. Ta yaya dukanmu za mu iya taimaka ma waɗanda suka daina zuwa taro? (Romawa 12:10)

18 Kowa a ikilisiya zai iya taimaka ma ꞌyanꞌuwa da suka halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu bayan sun daɗe ba su zo taro ba. Ta yaya? Ta wurin marabtarsu cikin ƙauna da yin musu alheri da kuma daraja su. (Karanta Romawa 12:10.) Ku tuna cewa mai yiwuwa bai yi musu sauƙi su halarci taron ba. Mai yiwuwa sun ji tsoro don ba su san abin da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya za su faɗa game da su ba. e Don haka, kada ka yi musu tambayoyin da za su kunyantar da su ko kuma ka faɗi abin da zai sa su baƙin ciki. (1 Tas. 5:11) Su ꞌyanꞌuwanmu ne kuma muna farin cikin sake bauta wa Jehobah tare da su.—Zab. 119:176; A. M. 20:35.

19. Wane amfani muke samu daga tunawa da mutuwar Yesu?

19 Muna godiya domin Yesu ya umurce mu mu tuna da mutuwarsa kowace shekara kuma mun san muhimmancin yin hakan. Idan muka halarci taron, za mu amfana kuma mutane ma za su amfana a hanyoyi da yawa. (Isha. 48:​17, 18) Zai sa mu ƙara ƙaunar Jehobah da kuma Yesu. Zai nuna cewa muna godiya don abin da suka yi mana. Zai kyautata dangantaka da ke tsakaninmu da ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci. Za mu kuma taimaka ma mutane su san yadda su ma za su amfana daga fansar Yesu Kristi. Bari dukanmu mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi shiri don Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na wannan shekara, wato ranar da ta fi muhimmanci a shekara!

TA YAYA ZA MU . . .

  • shirya zuciyarmu don Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

  • taimaka wa mutane su ma su amfana daga taron?

  • taimaka ma ꞌyanꞌuwa da suka daina zuwa taro?

WAƘA TA 18 Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

a Don ka ga talifofi da kuma bidiyoyin da aka ambata a wannan talifin, ka je dandalin jw.org/ha kuma ka rubuta jigon a inda aka ce “Bincika.”

b Ka duba talifin nan, Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu, da ke Hasumiyar Tsaro ta Afrilu, 2021.

d Ka duba akwatin nan, “ Abubuwan da Za Mu Iya Yin Bincike a Kansu.”

e Ka duba hotunan da akwatin nan, “ Yadda ꞌYanꞌuwa Suka Marabce Su” Wani ɗanꞌuwa da ya daɗe bai zo taro ba, yana masa wuya ya shiga Majamiꞌar Mulki, amma daga baya ya yi ƙoƙari ya shiga. ꞌyanꞌuwa sun marabce shi hannu bi-biyu kuma ya ji daɗin bauta ma Jehobah tare da su.

f BAYANI A KAN HOTUNA: Yayin da Shaidun Jehobah suke yin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu a wasu ƙasashe, wasu kuma a wasu ƙasashe suna shirin yin taron.