Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 8

WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah

Ku Ci-gaba da Bin Ja-gorancin Jehobah

Ku Ci-gaba da Bin Ja-gorancin Jehobah

‘Ni ne Yahweh . . . wanda yake nuna muku hanyar da za ku bi.’ISHA. 48:17.

ABIN DA ZA MU KOYA

Wannan talifin zai taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake yi wa mutanensa ja-goranci a yau, da kuma amfanin da za mu samu idan muka bi ja-gorancinsa.

1. Wane kwatanci ne ya nuna muhimmancin bin ja-gorancin Jehobah?

 A CE ka ɓata a wani daji. Ka ji tsoro sosai domin dajin yana da haɗari, kuma akwai dabbobin daji, da ƙwari da shuke-shuke masu haɗari da kuma ramuka da za ka iya faɗawa ciki. Za ka ji daɗi idan kana tare da wanda ya san dajin sosai, kuma zai taimaka maka kada ka shiga wuraren da ke da haɗari. Duniyar nan kamar wannan dajin take. Akwai abubuwa da yawa a duniyar nan da za su iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Amma Jehobah yana mana ja-goranci, yana taimaka mana mu guji waɗannan haɗarurrukan, kuma mu sami rai na har abada a sabuwar duniya.

2. Ta yaya Jehobah yake mana ja-goranci?

2 Ta yaya Jehobah yake mana ja-goranci? Da farko, yana yin hakan ta Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. Ban da haka, yana amfani da ꞌyan Adam don ya yi mana ja-goranci. Alal misali, yana amfani da “bawan nan mai aminci, mai hikima” don ya tanada mana abubuwan da za su taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau. (Mat. 24:45) Akwai wasu mutane kuma da Jehobah yake amfani da su don ya yi mana ja-goranci. Alal misali, masu kula da daꞌira da dattawa a ikilisiya suna ƙarfafa mu kuma suna ba mu shawarwari da za su taimaka mana saꞌad da muke yanayi mai wuya. Muna godiya sosai don yadda Jehobah yake mana ja-goranci a wannan lokaci mai wuya. Shawarwari da muke samu suna taimaka mana mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah, kuma mu sami rai na har abada.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Amma a wasu lokuta yana iya mana wuya mu bi ja-gorancin Jehobah, musamman ma in ya yi hakan ta wurin ꞌyan Adam. Me ya sa? Wataƙila saboda ba ma son abin da suka faɗa. Ko muna ganin cewa shawarar da suka bayar ba ta dace ba, don haka muna ganin cewa shawarar ba daga wurin Jehobah ba ne. A wannan yanayin, muna bukatar mu ƙara gaskata cewa Jehobah ne yake yi mana ja-goranci ta wurin ꞌyanꞌuwan nan. Kuma za mu amfana idan muka bi ja-gorancin. Don mu ƙara gaskata da hakan, talifin nan zai tattauna (1) yadda Jehobah ya yi wa mutanensa ja-goranci a dā, (2) yadda yake mana ja-goranci a yau, da kuma (3) yadda za mu amfana idan muka ci-gaba da bin ja-gorancinsa.

Daga zamanin dā har zuwa yanzu, Jehobah ya yi amfani da ꞌyan Adam don ya yi wa mutanensa ja-goranci (Ka duba sakin layi na 3)

YADDA JEHOBAH YA YI WA ALꞌUMMAR ISRAꞌILA JA-GORANCI

4-5. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana amfani da Musa don ya yi wa Israꞌilawa ja-goranci? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

4 Jehobah ya naɗa Musa ya ja-goranci alꞌummar Israꞌila saꞌad da suke barin ƙasar Masar. Jehobah ya ba wa Israꞌilawan tabbacin cewa Shi ne yake amfani da Musa don ya yi musu ja-goranci. Alal misali, ya tanada musu ƙunshin girgije da rana da kuma ƙunshin wuta da dare. (Fit. 13:21) Musa ya bi wannan ƙunshin girgije, kuma girgijen ya ja-gorance shi da Israꞌilawan zuwa Jar Teku. Mutanen sun ji tsoro sosai da suka ga cewa babu hanyar da za su bi, kuma ga sojojin Masar a bayansu. A ganinsu Musa ya yi kuskure da ya kawo su Jar Teku. Amma hakan ba kuskure ba ne. Domin Jehobah da kansa ne ya yi amfani da Musa don ya ja-goranci mutanensa zuwa Jar Tekun. (Fit. 14:2) Sai Allah ya cece su a hanya mai ban alꞌajibi.—Fit. 14:​26-28.

Musa ya bi kunshin girgijen don ya ja-goranci alꞌummar Israꞌila saꞌad da suke tafiya a cikin daji (Ka duba sakin layi na 4-5)

5 Musa ya yi shekaru 40 yana bin girgijen nan don ya ja-goranci alꞌummar Israꞌila saꞌad da suke tafiya a cikin daji. a Akwai ma lokacin da Jehobah ya saka ƙunshin girgijen a kan tentin Musa don dukan Israꞌilawa su gani. (Fit. 33:​7, 9, 10) Jehobah yakan yi magana da Musa daga ƙunshin girgijen, sai Musa kuma ya gaya wa mutanen abin da Jehobah ya faɗa. (Zab. 99:7) Akwai abubuwa da yawa da ya kamata su tabbatar wa Israꞌilawan cewa Jehobah ne yake amfani da Musa ya yi musu ja-goranci.

Musa da magājinsa Joshua (Ka duba sakin layi na 5, 7)

6. Mene ne Israꞌilawan suka yi game da ja-gorancin da Jehobah ya yi musu ta Musa? (Littafin Ƙidaya 14:​2, 10, 11)

6 Abin baƙin ciki shi ne, yawancin Israꞌilawa ba su yarda cewa Jehobah yana amfani da Musa ba. (Karanta Littafin Ƙidaya 14:​2, 10, 11.) Sun yi ta ƙin amincewa da ja-gorancin da Musa yake musu. Saboda haka, Jehobah bai bar su su shiga Ƙasar Alkawari ba.—L. Ƙid. 14:30.

7. Ka ba da misalin mutanen da suka bi ja-gorancin Jehobah. (Littafin Ƙidaya 14:24) (Ka kuma duba hoton.)

7 Amma akwai wasu Israꞌilawa da suka bi ja-gorancin Jehobah. Alal misali, Jehobah ya ce, “Kaleb . . . ya kuma bi ni da dukan zuciyarsa.” (Karanta Littafin Ƙidaya 14:24.) Jehobah ya albarkaci Kaleb, har ma ya bar shi ya zaɓi wurin da ya fi so a ƙasar Kanꞌana. (Yosh. 14:​12-14) Israꞌilawan da aka bar su su shiga Ƙasar Alkawari, su ma sun bi ja-gorancin Jehobah. Da Joshua ya soma ja-goranci bayan mutuwar Musa, mutanen sun “yi ta girmama shi dukan kwanakin ransa.” (Yosh. 4:14) Shi ya sa Jehobah ya albarkace su kuma ya kawo su ƙasar da ya yi musu alkawari.—Yosh. 21:​43, 44.

8. Ka bayyana yadda Jehobah ya yi wa Israꞌilawa ja-goranci saꞌad da suka soma samun sarakuna. (Ka kuma duba hoton.)

8 Shekaru da yawa bayan haka, Jehobah ya naɗa alƙalai su ja-goranci mutanensa. Da Israꞌilawan suka soma samun sarakuna, Jehobah ya naɗa annabawa da za su riƙa yi musu ja-goranci. Sarakuna masu aminci sun bi ja-gorancin annabawan. Alal misali, Sarki Dauda ya bi gargaɗin da annabi Nathan ya yi masa. (2 Sam. 12:​7, 13; 1 Tar. 17:​3, 4) Sarki Yehoshafat ya bi shawarar da annabi Yahaziyel ya ba shi, kuma ya ƙarfafa mutanen su “gaskata da annabawan [Allah].” (2 Tar. 20:​14, 15, 20) Da Sarki Hezekiya yake cikin yanayi mai wuya, ya nemi shawarar annabi Ishaya. (Isha. 37:​1-6) A duk lokacin da sarakunan suka bi ja-gorancin Jehobah, suna samun albarka kuma hakan na kāre alꞌummar. (2 Tar. 20:​29, 30; 32:22) Ya kamata waɗannan alamu su sa mutanen su gaskata cewa Jehobah yana amfani da annabawa don ya yi musu ja-goranci. Amma yawancin sarakuna da mutanen Israꞌila sun ƙi amincewa da ja-gorancin da Jehobah yake musu ta annabawa.—Irm. 35:​12-15.

Sarki Hezekiya da annabi Ishaya (Ka duba sakin layi na 8)

YADDA JEHOBAH YA YI WA KIRISTOCI A ƘARNI NA FARKO JA-GORANCI

9. Su wane ne Jehobah ya yi amfani da su don ya yi ja-goranci a ƙarni na farko? (Ka kuma duba hoton.)

9 A ƙarni na farko, Jehobah ya kafa ikilisiyar Kirista. Ta yaya ya yi ma Kiristocin ja-goranci? Ya naɗa Yesu ya zama shugaban dukan ikilisiya. (Afis. 5:23) Amma Yesu bai yi wa kowanne Kirista ja-goranci da kansa ba. Ya yi musu ja-goranci ne ta wurin manzanni da dattawan da ke Urushalima. (A. M. 15:​1, 2) Ƙari ga haka, an naɗa dattawa a ikilisiya don su yi ja-goranci.—1 Tas. 5:12; Tit. 1:5.

Manzanni da kuma dattawa a Urushalima (Ka duba sakin layi na 9)

10. (a) Mene ne yawancin Kiristoci a ƙarni na farko suka yi game da ja-gorancin da aka yi musu? (Ayyukan Manzanni 15:​30, 31) (b) Me ya sa wasu a dā suka ƙi amincewa da waɗanda Jehobah ya yi amfani da su don ya yi ja-goranci? (Ka duba akwatin nan “ Abin da Ya Sa Wasu Suka Ƙi Yarda.”)

10 Shin Kiristoci a ƙarni na farko sun bi ja-gorancin waɗannan ꞌyanꞌuwan? Yawancin su sun bi ja-gorancin nan da farin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce sun “yi farin ciki saboda ƙarfafawar da suka samu.” (Karanta Ayyukan Manzanni 15:​30, 31.) Amma ta yaya Jehobah yake yi wa mutanensa ja-goranci a yau?

YADDA JEHOBAH YAKE MANA JA-GORANCI A YAU

11. Ka ba da misalin da ya nuna cewa Jehobah ne yake ja-gorantar ꞌyanꞌuwan da suke ja-goranci a zamaninmu.

11 Jehobah ya ci-gaba da yi wa mutanensa ja-goranci a yau. Yana yin hakan ta Kalmarsa da Ɗansa, wanda shi ne shugaban ikilisiya. Shin akwai abubuwan da suka tabbatar mana cewa Jehobah ya ci-gaba da amfani da mutane don ya yi mana ja-goranci? Ƙwarai kuwa. Alal misali, ku yi laꞌakari da abin da ya faru bayan shekara ta 1870. A shekarar ce Ɗanꞌuwa Charles Taze Russell da abokansa suka soma fahimtar cewa, shekara ta 1914 za ta zama shekara mai muhimmanci, domin a shekarar ce za a kafa Mulkin Allah a sama. (Dan. 4:​25, 26) Sun san da hakan ne domin sun bincika Littafi Mai Tsarki, kuma sun gaskata cewa za su ga cikar sa. Shin Jehobah ne ya ja-gorance su? Ƙwarai kuwa. A 1914, abubuwan da suka faru a duniya sun nuna cewa Mulkin Allah ya soma sarauta. An soma Yaƙin Duniya na Ɗaya, bayan haka cututtuka suka yaɗu koꞌina, sai girgizar ƙasa da kuma rashin abinci. (Luk. 21:​10, 11) Tabbas, Jehobah ya yi amfani da waɗannan ꞌyanꞌuwa maza don ya taimaka wa mutanensa.

12-13. Waɗanne abubuwa ne ƙungiyar Jehobah ta yi saꞌad da ake Yaƙin Duniya na Biyu don ta faɗaɗa aikin waꞌazinmu?

12 Wani misali kuma shi ne abin da ya faru a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu. Bayan ꞌyanꞌuwa a hedkwatarmu sun yi nazarin littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​8, sai suka gano cewa Yaƙin Duniya na Biyu ba zai kai ga yaƙin Armageddon ba. Za a sami salama bayan yaƙin, kuma Shaidun Jehobah za su samu damar yi wa mutane da yawa waꞌazi. Don haka, ꞌyanꞌuwan sun buɗe wata sabuwar makaranta da ake kira Makarantar Gilead, don su horar da ꞌyanꞌuwa su yi waꞌazi a ƙasashen waje. A lokacin da suka yanke shawarar nan, wasu suna ganin cewa shawarar ba ta dace ba. Har a lokacin yaƙin ma, an yi ta aikan ꞌyanꞌuwa su je yin waꞌazi a ƙasashen waje. Ƙari ga haka, bawan nan mai aminci mai hikima ya shirya wata sabuwar makaranta ta musamman b don ya koyar da dukan masu shela a ikilisiya su iya yin waꞌazi da kyau. Ta waɗannan hanyoyin ne Jehobah ya shirya mutanensa don aikin da za su yi a nan gaba.

13 A yau, muna ganin cewa Jehobah ne ya yi wa mutanensa ja-goranci a waɗannan lokuta masu wuya sosai. Tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu, Shaidun Jehobah sun yi waꞌazi a ƙasashe da yawa ba tare da taƙura ba. Mutane da yawa a faɗin duniya sun ji game da Jehobah kuma sun soma bauta masa.

14. Me ya sa za mu iya gaskata umurnan da dattawa da kuma ƙungiyar Jehobah suke ba mu? (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 2:1) (Ka kuma duba hoton.)

14 A yau, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta ci-gaba da neman ja-gorancin Yesu Kristi. Tana son umurnin da take ba wa ꞌyanꞌuwa ya yi daidai da raꞌayin Jehobah da na Kristi. Tana kuma ba da umurni ta wurin masu kula da daꞌira da kuma dattawa. c Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dattawa suna ‘hannun daman’ Kristi. (Karanta Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 2:1.) Hakika, dattawa ajizai ne, haka ma yake da Kiristoci shafaffu, kuma sukan yi kuskure. Musa da Joshua sun yi kurakurai, haka ma yake da manzanni a ƙarni na farko. (L. Ƙid. 20:12; Yosh. 9:​14, 15; Rom. 3:23) Har yanzu, Kristi yana yi wa bawan nan mai aminci mai hikima da dattawa ja-goranci, kuma zai ci-gaba da yin hakan “har ƙarshen zamani.” (Mat. 28:20) Don haka, muna da dalilai da yawa da ya kamata su sa mu gaskata umurnan da ꞌyanꞌuwan nan suke ba mu.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu a yau (Ka duba sakin layi na 14)

MUNA AMFANA SOSAI IDAN MUKA CI-GABA DA BIN JA-GORANCIN JEHOBAH

15-16. Mene ne ka koya daga labaran waɗanda suka bi ja-gorancin Jehobah?

15 Idan muka ci-gaba da bin ja-gorancin Jehobah, za mu amfana ko a yanzu. Alal misali, Andy da Robyn sun bi shawarar da aka bayar game da sauƙaƙa rayuwarmu. (Ibran. 13:5) Hakan ya sa sun iya taimakawa a aikin gine-ginenmu. Robyn ta ce: “A wasu lokuta, mukan kwana a ƙaramin gida da babu wurin dafa abinci. Ina son ɗaukan hoto sosai, amma saboda muna bukutar kuɗi, na sayar da kayan ɗaukan hoton. Na yi kuka lokacin da na sayar da su. Amma kamar Saratu, na yanke shawara cewa zan ci-gaba da mai da hankali a kan abubuwan da ke gabana ba abubuwan da na bari a baya ba.” (Ibran. 11:15) Waɗanne albarku ne waɗannan maꞌauratan suka samu? Robyn ta ce: “Mun yi farin ciki sosai domin mun san cewa muna ba wa Jehobah dukan abin da muke da shi. A duk lokacin da muke aikin da aka ba mu, muna ganin yadda rayuwa za ta kasance a sabuwar duniya.” Andy ma ya ce: “Mun yi farin ciki sosai domin mun yi amfani da dukan ƙarfinmu da lokacinmu a hidimarmu ga Jehobah.”

16 Ta yaya kuma muke amfana idan muka bi ja-gorancin Jehobah? Da aka shawarci wata mai suna Marcia ta soma hidimar majagaba, sai ta yanke shawarar yin hidimar idan ta gama makaranta. (Mat. 6:33; Rom. 12:11) Ta ce: “An ba ni damar yin karatu a wata jamiꞌa na shekara huɗu kyauta. Amma ina so in ƙara ƙwazo a hidimata ga Jehobah. Don haka, ban je jamiꞌar ba, a maimako, na koyi sanaꞌar da za ta ba ni damar yin hidimar majagaba. Wannan yana cikin shawara mafi kyau da na yanke. Yanzu ina jin daɗin hidimar majagaba kuma aikin da nake yi yana ba ni damar taimakawa a Bethel da kuma yin wasu ayyuka a ƙungiyar Jehobah.”

17. Waɗanne ƙarin albarku ne za mu samu idan muna bin ja-gorancin Jehobah? (Ishaya 48:​17, 18)

17 A wasu lokuta, akan yi mana gargaɗi game da abubuwa kamar son abin duniya, da abubuwan da za su sa mu taka dokokin Allah. Idan muka bi waɗannan umurnai, za mu amfana sosai. Zai sa mu kasance da zuciya mai tsabta kuma zai taimaka mana mu guji matsaloli da yawa. (1 Tim. 6:​9, 10) Ban da haka, zai sa mu bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu, kuma babu abin da zai sa mu farin ciki ko ya ba mu salama kamar haka.—Karanta Ishaya 48:​17, 18.

18. Me ya sa kake so ka ci-gaba da bin ja-gorancin Jehobah?

18 Babu shakka, Jehobah zai ci-gaba da yin amfani da ꞌyan Adam don ya yi mana ja-goranci a lokacin ƙunci mai girma, har zuwa lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu. (Zab. 45:16) Shin za mu ci-gaba da bin umurnin da za su bayar ko da ba abin da muke so ba ne? Yin hakan zai yi mana sauƙi idan muna bin ja-gorancinsu yanzu. Saboda haka, bari mu ci-gaba da bin ja-gorancin Jehobah har da na waɗanda ya naɗa su kula da mu. (Isha. 32:​1, 2; Ibran. 13:17) Yayin da muke hakan, mu ci-gaba da gaskata da Jehobah, wanda yake mana ja-goranci. Hakan zai sa mu guji abubuwan da za su ɓata dangantakarmu da shi, kuma zai sa mu sami rai na har abada a sabuwar duniya.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya Jehobah ya yi wa alꞌummar Israꞌila ja-goranci?

  • Ta yaya Jehobah ya yi wa Kiristoci a ƙarni na farko ja-goranci?

  • Ta yaya muke amfana idan muka bi ja-gorancin Jehobah a yau?

WAƘA TA 48 Mu Riƙa Bauta wa Jehobah Kullum

a Jehobah ya naɗa wani malaꞌika, wanda “yake tafiya a gaban ƙungiya-ƙungiyar jamaꞌar Israꞌila” saꞌad da suke zuwa Ƙasar Alkawari. Da alama cewa wannan malaꞌika Mikaꞌilu ne, wato Yesu Kristi kafin ya zo duniya.—Fit. 14:19; 32:34.

b Daga baya an kira wannan makarantar, Makarantar Hidima ta Allah. A yau, wannan makarantar tana cikin taronmu na tsakiyar mako.

c Ka duba akwatin nan “Hakkin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu” da ke Hasumiyar Tsaro ta Fabrairu 2021, shafi na 18.