Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Yi Farin Ciki Yayin da Kake Jiran Jehobah

Ka Yi Farin Ciki Yayin da Kake Jiran Jehobah

SHIN kana marmarin lokacin da Jehobah zai kawar da dukan mugunta, kuma ya mai da kome sabo? (R. Yar. 21:​1-5) Ba shakka kana hakan! Amma idan muna fuskantar matsaloli, yin hakan bai da sauƙi. Idan muna sa rai a kan wani abu, amma abin bai faru ba, hakan zai sa mu baƙin ciki.—K. Mag. 13:12.

Duk da haka, Jehobah yana so mu jira shi ya ɗau mataki a lokacin da ya kamata. Me ya sa yake so mu jira? Kuma me zai taimaka mana mu yi farin ciki yayin da muke jira?

ME YA SA JEHOBAH YAKE SO MU JIRA?

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai. Gama Yahweh Allah ne mai yin gaskiya. Masu albarka ne masu jiransa.” (Isha. 30:18) Ainihi dai Ishaya yana magana ne ga Yahudawa masu taurin kai. (Isha. 30:1) Amma akwai wasu Yahudawa masu aminci da wannan saƙon ya ba su bege. A yau ma, kalmomin nan suna sa bayin Jehobah masu aminci su kasance da bege.

Jehobah yana haƙuri yayin da yake jira. Don haka, dole ne mu ma mu jira da haƙuri. Jehobah ya riga ya shirya lokacin da zai kawo ƙarshen muguwar duniyar nan, kuma yana jiran lokacin ya kai. (Mat. 24:36) A lokacin, kowa zai ga cewa zargin da Shaiɗan ya yi a kan Jehobah da kuma mutanensa ƙarya ne. Jehobah zai halaka Shaiɗan da magoya bayansa, amma zai “yi [mana] jinƙai.”

A yanzu dai, wataƙila Jehobah ba zai cire matsalolin da muke fuskanta ba, amma ya ba mu tabbacin cewa za mu iya yin farin ciki yayin da muke jira. Kamar yadda Ishaya ya faɗa, za mu iya yin farin ciki idan muna jiran wani abu mai kyau ya faru. (Isha. 30:18) a Ta yaya za mu yi farin ciki? Ga abubuwa huɗu da za su taimaka mana.

YADDA ZA KA YI FARIN CIKI YAYIN DA KAKE JIRA

Ka riƙa tunanin abubuwa masu kyau da suke faruwa da kai. A dukan rayuwar Dauda, ya ga yadda mutane suke yin mugunta. (Zab. 37:35) Duk da haka, ya rubuta cewa: “Ka natsu a gaban Yahweh, yi haƙuri kana sa zuciya a kansa, kada ka damu game da ci gaban wani, ko a kan mai nasara cikin mugayen shirye-shiryensa.” (Zab. 37:7) Dauda da kansa ma ya bi shawarar da ya rubuta saꞌad da ya mai da hankali a kan alkawarin da Jehobah ya yi cewa zai taimaka masa. Ban da haka ma, Dauda ya yi godiya don dukan alherin da Allah ya yi masa. (Zab. 40:5) Mu ma idan mun yi ta yin tunani a kan abubuwa masu kyau da suke faruwa da mu, maimakon matsaloli ko kuma munanan abubuwa da suke faruwa, zai yi mana sauƙi mu jira lokacin Jehobah.

Ka yi amfani da kowane zarafi don ka yabi Jehobah. Marubucin Zabura sura 71, wanda wataƙila Dauda ne, ya ce ma Jehobah: “Ni dai, zan dinga sa zuciya a gare ka, zan yabe ka a kai a kai.” (Zab. 71:14) Ta yaya Dauda ya yabi Jehobah? Ya gaya wa mutane game da Jehobah kuma ya rera waƙoƙin yabo ga Jehobah. (Zab. 71:​16, 23) Kamar Dauda, za mu iya yin farin ciki yayin da muke jiran Jehobah. Za mu iya yabon Jehobah saꞌad da muke waꞌazi, saꞌad da muke hira da mutane, da kuma saꞌad da muke rera waƙoƙinmu. Idan kana rera waƙarmu, ka yi tunani sosai a kan kalmomin waƙar, da yadda kalmomin suke sa ka farin ciki.

Ka riƙa kasancewa da ꞌyanꞌuwanka Kiristoci don su ƙarfafa ka. Saꞌad da Dauda ya fuskanci matsaloli, ya ce ma Jehobah: “Zan yi shelar Sunanka a gaban masu hali iri naka.” (Zab. 52:9) Mu ma za mu iya samun ƙarfafa daga ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. Ba a taro da waꞌazi ne kawai za mu iya yin hakan ba, amma za mu iya yin hakan saꞌad da muke yin liyafa tare da su.—Rom. 1:​11, 12.

Ka ƙara kasancewa da bege. Zabura 62:5 ta ce: “Raina, ka yi sauraro ga Allah kaɗai; Gama daga gareshi begena yake.” (Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Yana da muhimmanci sosai mu ƙara kasancewa da bege musamman ma idan ƙarshen bai zo a lokacin da muke tsammani ba. Dole ne mu kasance da tabbaci cewa alkawuran Jehobah za su cika, kome yawan lokacin da za mu ɗauka muna jira. Za mu iya ƙara kasance da bege ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, za mu iya yin tunani a kan annabcin Littafi Mai Tsarki da sun riga sun cika, da yadda abubuwan da marubutan Littafi Mai Tsarki dabam-dabam suka rubuta sun jitu da juna, da kuma abubuwan da Jehobah ya bayyana mana game da kansa. (Zab. 1:​2, 3) Ƙari ga haka, ya kamata mu riƙa ‘yin adduꞌa ta wurin ikon ruhu mai tsarki’ don mu ci-gaba da zama abokan Jehobah, yayin da muke jiran cikar alkawarin da ya yi mana cewa zai ba mu rai na har abada.—Yahu. 20, 21.

Kamar Dauda, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana lura da waɗanda suke jiran sa kuma yana nuna musu ƙaunarsa marar canjawa. (Zab. 33:​18, 22) Ka ci-gaba da jiran Jehobah ta wajen yin tunani a kan abubuwa masu kyau da suke faruwa da kai, ta wajen yabon Jehobah, ta wajen samun ƙarfafa daga wurin ꞌyanꞌuwanka Kiristoci da kuma ta wajen yin abubuwa da za su sa ka ƙara kasancewa da bege.

a Kalmar nan “jira” a Ibrananci, tana iya nufin “marmari ko kuma begen wani abu.” Hakan ya nuna cewa ba laifi ba ne mu yi marmarin lokacin da Jehobah zai kawo ƙarshen dukan wahalolin da muke sha.