Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da yadda Jehobah yake sanin abin da zai faru a nan gaba?

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah zai iya faɗin abin da zai faru a nan gaba. (Isha. 45:21) Amma bai gaya mana kome-da-kome game da yadda Jehobah yake hakan da kuma lokacin da yake hakan ba. Kuma bai gaya mana ko Jehobah yakan so ya san duk wani abin da zai faru ba. Don haka, ba kome ne muka sani game da yadda Jehobah yake faɗin abin da zai faru a nan gaba ba. Amma, ga wasu abubuwan da muka gano.

Ba abin da zai gagari Jehobah, sai dai in ba ya so ya yi shi. Da yake hikimar Jehobah ba ta da iyaka, zai iya faɗin abin da zai faru a nan gaba in ya ga dama. (Rom. 11:33) Amma da yake Jehobah yana iya kame kansa a ko da yaushe, zai iya zaɓan ya ƙi sanin abin da zai faru a nan gaba.—Ka duba Ishaya 42:14.

Jehobah yakan sa abin da yake so ya faru. Ta yaya hakan zai taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake faɗan abin da zai faru a nan gaba? Ishaya 46:10 ta ce: ‘Ina bayyana ƙarshen abu tun daga farkonsa, tun daga kwanakin dā, abin da bai faru ba, ina cewa, “Nufina zai cika, zan aikata duk abin da na yi niyyar yi.”’

Don haka, wani abin da ya sa Jehobah yake iya faɗin abin da zai faru a nan gaba shi ne, yana da ikon sa kome ya faru. Idan mutum yana kallon fim, zai iya tsallake ya je ya kalli ƙarshen don ya san yadda labarin zai ƙare. Amma ba abin da Jehobah yake yi don ya san abin da zai faru a nan gaba ke nan ba. A maimako, Jehobah zai iya ce wani abu zai faru a lokaci kaza, kuma idan lokacin ya kai sai ya sa abin ya faru.—Fit. 9:​5, 6; Mat. 24:36; A. M. 17:31.

Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce, wani lokaci Jehobah yakan “shirya” abin da zai faru a nan gaba. (2 Sar. 19:25; Isha. 46:11) A Ibrananci, kalmar nan “shirya,” tana da alaƙa da wata kalma da take nufin ‘mai ginin tukwane.’ (Irm. 18:​3, 4) Mai ginin tukwane zai iya sarrafa laka ta zama tukunya mai kyau, haka ma Jehobah zai iya sa abubuwa su faru yadda nufinsa zai cika.—Afis. 1:11.

Jehobah yana barin mutane su zaɓi abin da za su yi. Ba ya ƙaddara yadda rayuwar kowa za ta kasance. Kuma ba ya sa mutanen kirki su yi abin da zai kai su ga hallaka. Jehobah yakan koya mana yadda za mu yi rayuwa mai kyau, amma yakan bar kowa ya zaɓi irin rayuwar da zai yi.

Ga wasu misalai biyu. Na farko shi ne yadda Jehobah ya yi da mutanen Nineba. Jehobah ya ce zai hallaka su don muguntarsu. Amma da mutanen birnin suka tuba, sai Jehobah “ya canja niyyarsa, bai halaka su kamar yadda ya shirya zai yi ba.” (Yona 3:​1-10) Jehobah ya canja abin da ya yi niyyar yi, don ya ga cewa mutanen Nineba sun ji gargaɗin kuma su da kansu ne suka zaɓi su canja halinsu.

Misali na biyun kuma shi ne, annabcin da Jehobah ya yi game da Sarki Sairus. Jehobah ya ce Sairus zai ba Yahudawa ꞌyanci kuma zai ba da umurni a sake gina haikalin Jehobah. (Isha. 44:26–45:4) Sarki Sairus ya yi daidai abin da Jehobah ya faɗa. (Ezra 1:​1-4) Jehobah ya yi amfani da Sairus ya cika nufinsa. Amma ya bar Sairus ya zaɓa ko zai bauta masa ko ba zai bauta masa ba.—K. Mag. 21:1.

Waɗannan kalila ne daga cikin abubuwan da Jehobah yake dubawa kafin ya faɗi abin da zai faru a nan gaba. Gaskiyar ita ce, babu ɗan Adam da zai iya gama fahimtar yadda Jehobah yake tunani da ayyukansa. (Isha. 55:​8, 9) Amma, abubuwan nan da muka gano game da Jehobah sun tabbatar mana da cewa, a kullum Jehobah yakan yi abin da ya dace, kuma yana haka idan zai faɗi abin da zai faru a nan gaba.