Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SHAWARA A KAN YIN NAZARI

Ku Nemi Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah da Za Su Amfane Ku

Ku Nemi Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah da Za Su Amfane Ku

Idan muka karanta Littafi Mai Tsarki kuma muka yi bincike, za mu iya samun abubuwa masu daraja. Amma me zai sa mu amfana sosai?

Ka lura da ƙananan bayanai da suka shafi labarin. Alal misali, ka san wanda ya rubuta labarin, don wa ya rubuta, kuma a wane lokaci ne ya yi rubutun? Me ke faruwa a lokacin? Me ya faru kafin hakan, kuma me ya faru bayan hakan?

Ka yi ƙoƙari ka ga darussa da ke labarin ta wurin tambayar kanka: ‘Yaya waɗanda suke labarin suka ji? Wane hali ne suka nuna? Me ya sa zai dace in bi halinsu, ko kuma in guji bin halinsu?’

Ka bi abin da ka koya saꞌad da kake shaꞌani da mutane ko saꞌad da kake waꞌazi. Idan ka yi hakan, za ka amfana sosai. Yesu ya ce: “Yanzu da kun san waɗannan abubuwa za ku zama masu albarka idan kun yi su.”—Yoh. 13:17.

  • Shawara: Ka ga yadda sashen Darussa Daga Kalmar Allah da ke taron tsakiyar mako yake taimaka mana mu san yadda da za mu bi abin da muke koya. A sashen nan, akwai tambayoyi da za mu iya yi wa kanmu, da abubuwa da za mu iya yin tunani a kai, da kuma hotuna da za su taimaka mana.