Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 16

WAƘA TA 64 Mu Riƙa Yin Waꞌazi da Farin Ciki

Yadda Za Ka Ƙara Jin Daɗin Yin Waꞌazi

Yadda Za Ka Ƙara Jin Daɗin Yin Waꞌazi

“Ku yi wa Yahweh hidima da murna!”ZAB. 100:2.

ABIN DA ZA MU KOYA

A wannan talifin za mu tattauna abubuwa da za su taimaka mana mu ƙara jin daɗin yin waꞌazi.

1. Yaya wasu suke ji game da yi wa mutane waꞌazi? (Ka kuma duba hoton.)

 MU BAYIN Jehobah muna waꞌazi domin muna ƙaunar Ubanmu na sama kuma muna so mu taimaka wa mutane su san shi. ꞌYanꞌuwa da yawa suna jin daɗin yin waꞌazi sosai. Amma wasu ba sa jin daɗin yin sa. Me ya sa? Domin wasunsu suna jin kunya sosai. Wasu kuma suna ganin ba su ƙware sosai wajen koyar da mutane ba. Wasu ba sa jin daɗin zuwa gidajen mutane ba tare da an gayyace su ba. Wasu suna tsoro cewa mutane za su yi fushi da su. Wasu kuma an koya musu cewa kar su yi abin da zai ɓata wa mutane rai. Ko da yake ꞌyanꞌuwan nan suna ƙaunar Jehobah sosai, yana yi musu wuya su yi waꞌazi ga waɗanda ba su taɓa haɗuwa da su ba. Amma, sun san cewa yin waꞌazi aiki ne mai muhimmanci sosai kuma suna yin hakan a-kai-a-kai. Ba shakka, Jehobah yana farin ciki da su.

Shin kana jin daɗin yin waꞌazi? (Ka duba sakin layi na 1)


2. Me ya sa bai kamata ka yi sanyin gwiwa ba idan ba ka jin daɗin yin waꞌazi?

2 Shin kai ma ba ka jin daɗin yin waꞌazi a wasu lokuta saboda dalilan da muka ambata? Idan haka ne, kada ka yi sanyin gwiwa. Mai yiwuwa yadda kake ji ya nuna cewa kai mai sauƙin kai ne kuma ba ka so ka jawo hankalin mutane ga kanka. Ya kuma nuna cewa, ba ka so ka yi gardama da mutane. Hakika, ba wanda yake so wani ya yi fushi da shi, musamman ma idan yana ƙoƙarin taimaka wa mutumin. Ubanmu na sama ya san yadda kake ji kuma yana so ya taimaka maka. (Isha. 41:13) A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa guda biyar da za su taimaka maka kuma su sa ka ƙara jin daɗin yin waꞌazi.

KA SAMI ƘARFAFA DAGA KALMAR ALLAH

3. Mene ne ya taimaka ma annabi Irmiya ya yi waꞌazi?

3 A zamanin dā ma, bayin Allah sun sami ƙarfafa daga Kalmarsa saꞌad da aka ba su aiki mai wuya. Abin da ya faru da annabi Irmiya ke nan. Ya ji tsoro a lokacin da Jehobah ya ba shi aikin yin waꞌazi. Ya ce: “Ga shi, ni yaro ne, ban san yadda zan yi magana ba.” (Irm. 1:6) Mene ne ya taimaka masa ya yi waꞌazi da ƙarfin zuciya? Ya samu ƙarfafa daga Kalmar Allah. Game da Kalmar Allah, Irmiya ya ce: “Ta zama kamar wutar da take ci a zuciyata, kamar wutar da take cikin ƙasusuwana. Na gaji da riƙe ta.” (Irm. 20:​8, 9) Duk da cewa mutanen da aka ce Irmiya ya yi musu waꞌazi masu taurin kai ne, saƙon da ya yi waꞌazin sa ya ƙarfafa shi.

4. Idan muka karanta Littafi Mai Tsarki kuma muka yi tunani mai zurfi a kansa, ta yaya hakan zai taimaka mana? (Kolosiyawa 1:​9, 10)

4 Kalmar Allah tana ƙarfafa Kiristoci a yau. A wasiƙar da manzo Bulus ya rubuta wa ikilisiyar da ke Kolosi, ya gaya musu cewa fahimtar gaskiyar da ke Kalmar Allah za ta taimaka musu su “yi tafiyar da ta cancanta da masu bin Ubangiji” yayin da suke yin “rayuwa mai kyau cikin kowane irin aiki.” (Karanta Kolosiyawa 1:​9, 10.) Yin waꞌazi yana cikin aikin da manzo Bulus ya yi magana a kai. Idan muna karanta Littafi Mai Tsarki kuma muna yin tunani mai zurfi a kansa, zai taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Kuma zai taimaka mana mu ƙara fahimtar muhimmancin yi wa mutane waꞌazi.

5. Ta yaya za mu amfana sosai idan muna karanta Kalmar Allah kuma muna nazarin ta?

5 Idan muna so mu amfana sosai daga Kalmar Allah, ba za mu yi karatu ko nazari ko kuma mu yi tunani a kanta cikin hanzari ba. Amma za mu ɗau lokaci sosai mu yi hakan. Idan ka karanta wani nassi da ba ka gane ba, kada ka tsallake shi ka wuce. A maimako, ka yi amfani da Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah ko kuma Watch Tower Publications Index, don ka samu bayani game da ayar. Idan ka ɗau lokaci sosai ka yi nazari, za ka ƙara kasancewa da tabbaci cewa abin da Kalmar Allah ta faɗa gaskiya ne. (1 Tas. 5:21) Kuma idan kana da wannan tabbacin, za ka ji daɗin gaya wa mutane abin da ka koya.

KA YI SHIRI SOSAI KAFIN KA FITA YIN WAꞌAZI

6. Me ya sa ya kamata mu yi shiri sosai kafin mu fita waꞌazi?

6 Idan ka yi shiri kafin ka fita waꞌazi ba za ka ji tsoro sosai saꞌad da kake yi wa mutane magana ba. Yesu ya shirya almajiransa kafin ya aike su su yi waꞌazi. (Luk. 10:​1-11) Almajiran Yesu sun bi abin da ya koya musu, shi ya sa suka yi abubuwa masu kyau da yawa, kuma hakan ya sa su farin ciki.—Luk. 10:17.

7. Ta yaya za mu yi shiri kafin mu fita waꞌazi? (Ka kuma duba hoton.)

7 Ta yaya za mu yi shiri kafin mu fita waꞌazi? Ya kamata mu yi tunani sosai a kan abin da muke so mu faɗa. Hakan zai taimaka mana mu yi magana daga zuciyarmu. Zai dace kuma mu yi tunani a kan abubuwa biyu ko uku da mutanen za su iya gaya mana, saꞌan nan mu yi tunani a kan amsar da za mu ba su. Saꞌad da muke magana da mutane, mu yi ƙoƙari mu sake jiki kuma mu yi murmushi.

Ka yi shiri sosai kafin ka fita waꞌazi (Ka duba sakin layi na 7)


8. Ta yaya Kiristoci suke kama da tukwane na ƙasa da manzo Bulus ya ambata a kwatancinsa?

8 Ga yadda manzo Bulus ya kwatanta waꞌazin da muke yi. Ya ce: “Muna da wannan kaya mai-daraja cikin tukwane na ƙasa.” (2 Kor. 4:​7, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Mene ne wannan kaya mai daraja? Yana nufin waꞌazin Mulkin Allah da ke ceton rayukan mutane. (2 Kor. 4:1) Mene ne tukwane na ƙasa suke nufi? Suna nufin bayin Allah da suke gaya wa mutane labari mai daɗi. A lokacin manzo Bulus, ꞌyan kasuwa sukan yi amfani da tukwane na ƙasa don su kai abubuwa masu daraja kamar abinci, da ruwan inabi, da kuɗi zuwa inda ake bukatar su. Haka ma, Jehobah yana amfani da mu wajen kai wa mutane bisharar nan mai daraja. Da yake Jehobah yana tare da mu, zai ba mu ƙarfin da muke bukata don mu ci-gaba da yin waꞌazi.

KA ROƘI ALLAH YA BA KA ƘARFIN ZUCIYA

9. Me zai taimaka mana mu daina jin tsoron tsanantawa ko tsoron cewa mutane ba za su so su ji mu ba? (Ka kuma duba hoton.)

9 A wasu lokuta, za mu ji tsoro cewa mutane ba za su so su ji waꞌazinmu ba, ko kuma za su tsananta mana. Ta yaya za mu shawo kan irin wannan tsoron? Ka yi laꞌakari da adduꞌar da manzanni suka yi saꞌad da aka ce su daina yin waꞌazi. Ba su daina yin waꞌazi saboda tsoro ba, amma sun roƙi Jehobah ya ba su ‘ƙarfin halin faɗin kalmarsa babu tsoro.’ Nan-da-nan Jehobah ya amsa adduꞌarsu. (A. M. 4:​18, 29, 31) Idan a wasu lokuta muna jin irin wannan tsoro, mu roƙi Jehobah ya taimaka mana. Ka roƙi Jehobah ya sa ka ƙara ƙaunar mutane don ka iya shawo kan tsoron da kake ji.

Ka yi adduꞌa Jehobah ya ba ka ƙarfin zuciya (Ka duba sakin layi na 9)


10. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu yi waꞌazi game da shi? (Ishaya 43:​10-12)

10 Jehobah ya ce mu Shaidunsa ne, kuma ya ce zai ba mu ƙarfin zuciya. (Karanta Ishaya 43:​10-12.) Bari mu ga hanyoyi huɗu da yake yin haka. Da farko, Yesu yana tare da mu a duk lokacin da muke waꞌazi. (Mat. 28:​18-20) Na biyu, Jehobah ya ba mu malaꞌiku da suke taimaka mana. (R. Yar. 14:6) Na uku, Jehobah ya ba mu ruhunsa mai tsarki wanda yake sa mu tuna da abubuwa da muke koya. (Yoh. 14:​25, 26) Na huɗu, Jehobah ya ba mu ꞌyanꞌuwanmu da suke taimaka mana. Da yake Jehobah yana taimaka mana kuma muna da ꞌyanꞌuwa a faɗin duniya, za mu iya kasancewa da ƙarfin zuciya kuma mu ci-gaba da yin waꞌazi.

KA YI CANJI IDAN DA BUKATA KUMA KA KASANCE DA RAꞌAYI DA YA DACE

11. Ta yaya za ka fi samun mutane a waꞌazi? (Ka kuma duba hoton.)

11 Shin kana sanyin gwiwa idan ba ka yawan samun mutane a gida? Idan haka ne, ka tambayi kanka: ‘A ina ne zan iya samun su?’ (A. M. 16:13) ‘Suna wurin aiki ne ko sun je yin sayayya a kasuwa?’ Idan haka ne, za ka iya yi wa mutane waꞌazi a hanya. Wani ɗanꞌuwa mai suna Joshua ya ce: “Na samu damar yi wa mutane waꞌazi saꞌad da nake wucewa a wuraren da akwai shaguna da inda ake faka motoci.” Ƙari ga haka, shi da matarsa suna samun mutane da yawa a gida idan suka je waꞌazi da yamma ko kuma ran Lahadi da rana.—Afis. 5:​15, 16.

Ka canja lokaci da kuma wurin da za ka riƙa yin waꞌazi (Ka duba sakin layi na 11)


12. Ta yaya za mu san abin da mutane suka yi imani da shi ko abin da ya fi damun su?

12 Idan ka lura cewa mutane ba sa marmarin saƙon Littafi Mai Tsarki sosai, ka yi ƙoƙari ka san abin da suka yi imani da shi ko kuma abin da ya fi damun su. Ɗanꞌuwa Joshua da matarsa da muka ambata a baya sukan yi amfani da tambaya da ke gaban warƙarmu don su fara magana da mutane. Yayin da suke amfani da warƙar nan, Mene Ne Raꞌayinka Game da Littafi Mai Tsarki?, sukan yi tambaya cewa: “Wasu suna ganin Littafi Mai Tsarki littafi ne daga Allah, wasu kuma ba su yarda da hakan ba. Mene ne raꞌayinka?” Hakan yana sa mutane su yarda su tattauna da su.

13. Me ya sa za mu iya ce mun yi nasara ko da mutane ba su saurari waꞌazinmu ba? (Karin Magana 27:11)

13 Idan mun yi waꞌazi kuma mutane ba su saurare mu ba, hakan ba ya nufin cewa ba mu yi nasara ba. Me ya sa muke ce hakan? Domin mun yi aikin da Jehobah da kuma Ɗansa Yesu suke so mu yi, wato yin waꞌazi ga mutane. (A. M. 10:42) Ko da ba mu samu waɗanda za mu yi musu waꞌazi ba, ko kuma mutane ba su saurare mu ba, muna farin ciki don mun san muna faranta wa Jehobah rai.—Karanta Karin Magana 27:11.

14. Me ya sa ya kamata mu yi farin ciki idan wani ɗanꞌuwa ya samu wanda yake son waꞌazinmu?

14 Za mu iya yin farin ciki idan wani ɗanꞌuwa ko wata ꞌyarꞌuwa ta sami wanda yake son waꞌazinmu. Hasumiyar Tsaro ta ce waꞌazin da muke yi yana kama da neman yaro da ya ɓata. Idan yaro ya ɓata, mutane da yawa ne suke nemansa kuma za su dudduba koꞌina. Idan an ga yaron, kowa zai yi farin ciki. Haka ma, muna bukatar taimakon kowa a ikilisiya don mu iya yi wa dukan mutane waꞌazi a yankinmu. Kuma idan wani ya soma halartan taro, kowa ne zai yi farin ciki.

KA ƘARA ƘAUNAR JEHOBAH DA MUTANE

15. Ta yaya bin shawara da ke Matiyu 22:​37-39 za ta taimaka mana mu ƙara yin waꞌazi da ƙwazo? (Ka kuma duba hoton.)

15 Idan muna ƙaunar Jehobah da maƙwabtanmu sosai, hakan zai sa mu ƙara yin ƙwazo a yin waꞌazi. (Karanta Matiyu 22:​37-39.) Ka yi tunanin yadda Jehobah yake farin ciki idan ya ga muna yin waꞌazi, da yadda mutane za su yi farin ciki idan suka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki! Ka riƙa tuna cewa dukan waɗanda suka saurari waꞌazinmu kuma suka soma bauta wa Jehobah za su yi rayuwa har abada.—Yoh. 6:40; 1 Tim. 4:16.

Idan kana ƙaunar Jehobah da mutane sosai, hakan zai sa ka ƙara jin daɗin yin waꞌazi (Ka duba sakin layi na 15)


16. Ta yaya za mu ji daɗin yin waꞌazi ko da yanayinmu ya hana mu barin gida? Ka ba da misali.

16 Idan ba ka iya barin gida saboda yanayin da kake ciki kuma fa, me za ka yi? Ka riƙa yin abubuwa da za su nuna cewa kana ƙaunar Jehobah da mutane. A lokacin korona, Samuel da matarsa Dania ba su iya barin gida ba. Duk da haka sun yi ta yin waꞌazi ga mutane ta waya, sun rubuta wasiƙu, kuma sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane ta waya. Samuel ya kuma yi wa mutane da ya haɗu da su a asibiti waꞌazi saꞌad da yake zuwa jinyar cutar kansa. Samuel ya ce: “Idan mun samu kanmu a cikin yanayi mai wuya, hakan yana iya sa mu ji tsoro kuma mu gaji. Kuma hakan yana iya gwada bangaskiyarmu. Don haka, ya kamata mu yi abubuwa da za su sa mu ji daɗin bautarmu ga Jehobah.” Yayin da Samuel yake fama da nashi rashin lafiya, sai Dania ta faɗi, kuma ta yi watanni uku ba ta iya tashiwa daga kan gado. Daga baya, ta soma amfani da keken guragu har na watanni shida. Dania ta ce: “Na yi ƙoƙari in yi waꞌazi iya ƙarfina. Na yi ma nas da take kula da ni waꞌazi, kuma na yi waꞌazi ga waɗanda suke kawo mana abubuwa a gida. Na kuma yi waꞌazi ga wata wakiliyar kamfani da ke sayar da kayan kiwon lafiya.” Duk da cewa Samuel da Dania ba sa iya yin abubuwan da suke yi a dā saboda yanayinsu, sun yi waꞌazi iya ƙarfinsu kuma sun ji daɗin yin haka.

17. Me za ka yi don ka amfana sosai daga shawarwarin da aka bayar a talifin nan?

17 Ka yi ƙoƙari ka bi shawarwari guda biyar da aka ambata a wannan talifin. Kowanne cikin shawarwari biyar nan, yana kama da kayan haɗi a abinci. Idan ka yi amfani da dukan kayan haɗin, abincin zai yi daɗi sosai. Idan muka bi dukan shawarwarin da aka bayar a talifin nan, za mu iya shawo kan tsoron da muke ji kuma za mu ƙara jin daɗin yin waꞌazi.

TA YAYA ZA KA ƘARA JIN DAƊIN YIN WAꞌAZI . . .

  • idan kana yin shiri sosai kafin ka fita waꞌazi?

  • idan kana roƙon Jehobah ya ba ka ƙarfin zuciya?

  • idan kana ƙaunar Jehobah da kuma mutane sosai?

WAƘA TA 80 ‘Mu Ɗanɗana, Mu Gani, Jehobah Nagari Ne’