Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABUBUWAN DA ZA KU IYA YIN NAZARI A KAI

Masu So Su Gamshi Jehobah Sukan Yanke Shawarwari Masu Kyau

Masu So Su Gamshi Jehobah Sukan Yanke Shawarwari Masu Kyau

Ku karanta Farawa 25:​29-34 don ku ga ko Isuwa da Yakub sun yanke shawarwari masu kyau.

Ku bincika labarin sosai. Mene ne ya faru da farko? (Far. 25:​20-28) Mene ne ya faru daga baya?—Far. 27:​1-46.

Ku nemi ƙarin bayani. A zamanin, wane gata da kuma hakki ne ɗan fari yake da su?—Far. 18:​18, 19; w10-E 5/1 13.

  • Shin, sai mutum ya zama ɗan fari ne Almasihu zai fito daga zuriyarsa? (w17.12 14-15)

Ku yi tunani a kan abubuwan da kuka koya kuma ku yi amfani da su. Me ya sa Yakub ya daraja gatan da ɗan fari yake da shi fiye da Isuwa? (Ibran. 12:​16, 17; w13 5/15 28 sakin layi na 10-11) Yaya Jehobah ya ji game da shawarar da Yakub da Isuwa suka yanke, kuma me ya sa? (Mal. 1:​2, 3) Mene ne ya kamata Isuwa ya yi don ya yanke shawarwari masu kyau?

  • Kowa ya tambayi kansa: ‘Ta yaya zan nuna cewa ina so in faranta wa Jehobah rai a yadda nake amfani da lokacina kowane mako, kuma in tabbata cewa ina da lokacin yin ibada ta iyali?’