Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 25

WAƘA TA 7 Jehobah Ne Ƙarfinmu

Ka Tuna Cewa Jehobah “Allah Mai Rai” Ne

Ka Tuna Cewa Jehobah “Allah Mai Rai” Ne

“Yahweh mai rai ne!”ZAB. 18:46.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda sanin cewa Jehobah Allah “mai rai ne” yake amfanar mu.

1. Me yake taimaka wa bayin Jehobah su ci-gaba da bauta masa duk da matsalolin da suke fuskanta?

 LITTAFI MAI TSARKI ya ce a zamaninmu “za a sha wahala sosai.” (2 Tim. 3:1) Shaidun Jehobah ma suna fuskantar matsalolin da kowa yake fuskanta. Amma ban da haka, ana tsananta mana domin muna bauta ma Jehobah. Me yake taimaka mana mu ci-gaba da bauta ma Jehobah duk da matsalolin nan? Wani muhimmin abu da ke taimaka mana shi ne sanin cewa Jehobah “Allah Mai Rai” ne.—Irm. 10:10; 2 Tim. 1:12.

2. Mene ne muka sani game da Jehobah da zai iya ƙarfafa mu?

2 Jehobah yana ganin dukan wahaloli da muke sha, kuma a kullum yana so ya taimaka mana. (2 Tar. 16:9; Zab. 23:4) Idan muka tuna cewa Allah yana nan kuma ya damu da mu, hakan zai taimaka mana mu jimre kowanne irin matsala da muke fuskanta. Bari mu ga yadda Dauda ya amfana daga yin hakan.

3. Mene ne Dauda yake nufi saꞌad da ya ce “Yahweh mai rai ne”?

3 Dauda ya san Jehobah kuma ya dogara gare Shi. Saꞌad da Sarki Shawulu da wasu mutane suke ƙoƙarin kashe Dauda, ya roƙi Jehobah ya taimaka masa. (Zab. 18:6) Da Jehobah ya cece shi, Dauda ya ce: “Yahweh mai rai ne!” (Zab. 18:46) Mene ne Dauda yake nufi da ya ce Allah mai rai ne? Wani littafi da ke bayyana Littafi Mai Tsarki ya ce Dauda yana nufin cewa Jehobah Allah ne na gaskiya da ke taimaka wa bayinsa a kullum. Abubuwan da suka faru a rayuwar Dauda sun tabbatar masa da cewa Allahnsa mai rai ne. Hakan ya sa ya ci-gaba da bauta ma Allah da kuma yabon sa.—Zab. 18:28, 29, 49.

4. Ta yaya za mu amfana idan muka tuna cewa Jehobah Allah mai rai ne?

4 Idan muna da tabbacin cewa Jehobah Allah ne mai rai, hakan zai taimaka mana mu ci-gaba da bauta masa da ƙwazo. Zai kuma ba mu ƙarfin jimre matsalolin da muke fuskanta kuma ya sa mu yi niyyar ci-gaba da bauta ma Jehobah da ƙwazo. Ƙari ga haka, ba za mu bar wani abu ya sa mu yi nisa da Jehobah ba.

ALLAHNMU MAI RAI ZAI ƘARFAFA KA

5. Me zai taimaka mana kar mu ji tsoro in muka fuskanci matsaloli? (2 Korintiyawa 4:7)

5 Idan muka tuna cewa Jehobah Allah ne mai rai kuma yana marmarin taimaka mana a kullum, hakan zai sa mu jimre matsalolinmu komen girmansu. Domin ko da yaya matsalar da muke fuskanta, ba ta fi ƙarfin Jehobah ba. Shi ne mai iko duka kuma zai iya ba mu ƙarfin jimrewa. (Karanta 2 Korintiyawa 4:7.) Don haka, bai kamata mu ji tsoron matsaloli da za mu fuskanta ba. Idan muka ga yadda Jehobah yake taimaka mana mu jimre ƙananan matsaloli, hakan zai tabbatar mana da cewa zai taimaka mana idan muka fuskanci manyan matsaloli a gaba.

6. Waɗanne abubuwa ne suka faru da Dauda da suka sa ya ƙara dogara ga Jehobah?

6 Bari mu ga abubuwa biyu da suka faru da Dauda da suka sa ya ƙara dogara ga Jehobah. Saꞌad da Dauda yake matashi kuma yake kiwon tumakin babansa, ya taɓa gamuwa da zaki da kuma beyar, kowannensu ya ɗauki tunkiyar babansa. A lokuta biyun nan, Dauda ya bi dabbar dajin kuma ya ceci tunkiyar. Duk da haka, bai buga ƙirji cewa da ƙarfinsa ne ya yi hakan ba. Ya san cewa Jehobah ne ya taimaka masa. (1 Sam. 17:34-37) Dauda bai manta da abin da ya faru ba. Da ya yi tunani a kan abin da ya faru, ya ƙara kasancewa da tabbacin cewa Jehobah zai taimaka masa a nan gaba.

7. Mene ne Dauda ya mai da hankali a kai, kuma ta yaya hakan ya taimaka masa ya yi faɗa da Goliyat?

7 Daga baya, Dauda ya je inda sojojin Israꞌila suka yi zango, kuma a lokacin bai kai shekara 20 ba. Da ya kai wurin, ya ga cewa wani jibgegen sojan Filisti mai suna Goliyat yana “rena dukan sojojin Israꞌila,” kuma hakan ya sa sojojin tsoro ba kaɗan ba. (1 Sam. 17:10, 11) Sojojin sun mai da hankali ga girman sojan da kuma abin da yake faɗa, shi ya sa suka ji tsoro. (1 Sam. 17:24, 25) Amma ba abin da Dauda ya mai da hankali a kai ke nan ba. A ganin Dauda, ba sojojin Israꞌila ne sojan ya rena ba, amma “sojojin Allah Mai Rai” ne ya rena. (1 Sam. 17:26) Dauda ya mai da hankali a kan yadda abin ya shafi Jehobah. Kuma ya ba da gaskiya cewa yadda Jehobah ya taimaka masa saꞌad da yake kiwon tumaki, zai taimaka masa a wannan karon ma. Da yake ya san Allah yana tare da shi, ya yi faɗa da Goliyat kuma ya yi nasara!—1 Sam. 17:45-51.

8. Idan muna fuskantar matsaloli, mene ne zai sa mu gaskata cewa Jehobah zai taimaka mana? (Ka kuma duba hoton.)

8 Mu ma za mu iya jimre matsalolin da muke fuskanta idan muka tuna cewa Allahnmu mai rai yana a shirye ya taimaka mana. (Zab. 118:6) Idan muka yi laꞌakari da abubuwan da Allah ya yi a dā, za mu ƙara gaskata cewa zai taimaka mana. Za ka iya yin hakan ta wajen karanta labaran Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda Jehobah ya ceci bayinsa a dā. (Isha. 37:17, 33-37) Ka kuma bincika labaran ꞌyanꞌuwa a dandalin jw.org da suka nuna yadda Jehobah yake taimaka wa bayinsa a zamaninmu. Ƙari ga haka, ka tuna lokutan da Jehobah ya taimaka maka. Mai yiwuwa ka yi tunanin cewa Jehobah bai taɓa taimaka maka a hanya mai ban mamaki kamar yadda ya ceci Dauda daga zaki da kuma beyar ba. Amma gaskiyar ita ce, Jehobah ya taimaka maka a hanyoyi da yawa. Alal misali, shi ne ya jawo ka ka zama abokinsa. (Yoh. 6:44) Kuma don taimakonsa ne har yanzu kana bauta masa. Don haka, ka roƙe shi ya tuna maka da lokutan da ya amsa adduꞌoꞌinka, da lokutan da ya ba ka daidai abin da kake bukata, da kuma lokutan da ya taimaka maka ka jimre matsaloli. Yin hakan zai sa ka ƙara gaskata cewa Jehobah ba zai fasa taimaka maka ba.

Abin da muke yi saꞌad da muke fuskantar matsaloli zai iya sa Jehobah farin ciki ko ya sa shi baƙin ciki (Ka duba sakin layi na 8-9)


9. Yaya ya kamata mu ɗauki wahalolin da muke sha? (Karin Magana 27:11)

9 Idan muna fuskantar matsaloli, mu mai da hankali ga batu da ya fi muhimmanci. Ta yaya? Shaiɗan ya yi zargi cewa idan muna fuskantar matsaloli za mu daina bauta ma Jehobah. Don haka, abin da muke yi saꞌad da muke fuskantar matsaloli zai iya sa Jehobah farin ciki ko kuma ya sa shi baƙin ciki. (Ayu. 1:10, 11; karanta Karin Magana 27:11.) Amma idan muka ci-gaba da bauta ma Jehobah duk da matsalolin da muke fuskanta, za mu nuna wa Jehobah cewa muna ƙaunar sa kuma za mu nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Mai yiwuwa gwamnati a yankin da kake tana tsananta wa Shaidun Jehobah, ko kana fama da rashin kuɗi, ko mutane a yankinku ba sa saurarar waꞌazi, ko kuma kana fuskantar wasu matsaloli dabam, ka tuna cewa hakan zarafi ne mai kyau na sa Jehobah farin ciki. Ka kuma tuna cewa Jehobah ba zai bar ka ka fuskanci jarrabawa da ya fi ƙarfin ka ba. (1 Kor. 10:13) Zai ba ka ƙarfin jimrewa.

ALLAHNMU MAI RAI ZAI BA KA LADA

10. Mene ne Allahnmu mai rai zai yi ma waɗanda suke bauta masa?

10 Jehobah yana ba da lada ga waɗanda suke bauta masa. (Ibran. 11:6) A yanzu, yana ba mu kwanciyar hankali kuma yana sa mu gamsu da abin da muke da shi. A nan gaba kuma, zai ba mu rai na har abada. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana so ya ba mu lada kuma yana da ikon yin hakan. Hakan yana sa mu ci-gaba da bauta masa da ƙwazo kamar yadda bayinsa a dā suka yi. Abin da Timoti ya yi ke nan.—Ibran. 6:10-12.

11. Me ya sa Timoti ya yi ayyuka da ƙwazo a ikilisiya? (1 Timoti 4:10)

11 Karanta 1 Timoti 4:10. Timoti ya ba da gaskiya cewa Allah zai ba shi lada. Shi ya sa ya yi ayyuka da ƙwazo domin Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Waɗanne ayyuka ne ya yi? Manzo Bulus ya gaya masa cewa ya ci-gaba da kyautata yadda yake koyar da jamaꞌa. Ya kuma gaya masa ya zama misali mai kyau ga masu bi, manya da ƙanana. An kuma gaya masa ya gargaɗi wasu ꞌyanꞌuwa. Kuma an ce ya gaya musu gaskiya ba tare da ɓoye-ɓoye ba, amma ya yi hakan cikin ƙauna. Wannan aikin bai da sauƙi. (1 Tim. 4:11-16; 2 Tim. 4:1-5) Akwai lokutan da mutane ba su lura da ayyukan da Timoti ya yi ba, wasu kuma ba su yi godiya ba, amma Timoti ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ba shi lada.—Rom. 2:6, 7.

12. Me ya sa dattawa suke yin ayyuka da ƙwazo a ikilisiya? (Ka kuma duba hoton.)

12 A yau ma, dattawa za su iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana ganin ayyukan da suke yi kuma hakan yana sa shi farin ciki. Dattawa suna yin waꞌazi, da koyarwa, da kuma kai wa ꞌyanꞌuwa ziyarar ƙarfafa. Ban da haka, akwai dattawa da yawa da suke taimakawa a ayyukan gine-gine da ƙungiyarmu take yi, wasu kuma suna yin aikin agaji. Ƙari ga haka, wasu dattawa suna Kwamitin Hulɗa da Asibitoci ko kuma Rukunin Ziyartar Majiyyata. Dattawa da suke taimakawa a hanyoyin nan sun san cewa Jehobah ne yake da ƙungiyarmu ba ɗan Adam ba. Don haka, suna yin aikin da dukan zuciyarsu, kuma suna da tabbacin cewa Jehobah zai ba su lada.—Kol. 3:23, 24.

Allahnmu mai rai zai ba ka lada yayin da kake yin aiki da ƙwazo don ƙungiyarsa (Ka duba sakin layi na 12-13)


13. Yaya Jehobah yake ji game da ƙoƙarin da muke yi don mu bauta masa?

13 Ba kowa ne zai iya zama dattijo ba. Amma dukanmu za mu iya ba wa Jehobah wani abu. Allahnmu yana farin ciki idan muka bauta masa da iya ƙarfinmu. Yana ganin gudummawar da muke bayarwa domin ayyuka da ake yi a faɗin duniya, ko da gudummawarmu ƙarami ne. Idan muka ɗaga hannu muka yi kalami duk da cewa muna jin kunya, ko kuma muka gafarta ma ꞌyanꞌuwa da suka yi mana laifi, hakan yana sa Jehobah farin ciki. Ko da kana ganin abin da za ka iya yi kaɗan ne, ka kasance da tabbaci cewa abin da ka iya yi yana sa Jehobah farin ciki. Yana ƙaunar ka don abin da kake yi kuma zai ba ka lada.—Luk. 21:1-4.

KA CI-GABA DA YIN KUSA DA ALLAHNMU MAI RAI

14. Mene ne zai taimaka mana mu guji yin abin da zai ɓata ma Jehobah rai? (Ka kuma duba hoton.)

14 Idan mun tuna cewa Jehobah Allah ne mai rai, zai yi mana sauƙi mu ci-gaba da bauta masa da aminci. Abin da ya taimaka wa Yusufu ke nan. Ya ƙi yin zina. Yusufu yana ƙaunar Jehobah kuma ba ya so ya ɓata masa rai. (Far. 39:9) Idan muna so mu zama aminan Jehobah, muna bukatar mu keɓe lokaci da za mu riƙa yin adduꞌa da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki. Hakan zai sa mu ƙara yin kusa da shi. Idan muka zama aminan Jehobah kuma muna ƙaunar sa, kamar Yusufu, ba za mu so mu yi abin da zai ɓata Masa rai ba.—Yak. 4:8.

Yin kusa da Allahnmu mai rai zai taimaka maka ka ci-gaba da bauta masa da aminci (Ka duba sakin layi na 14-15)


15. Wane darasi ne za mu iya koya daga abin da ya faru da Israꞌilawa saꞌad da suke daji? (Ibraniyawa 3:12)

15 Idan mutum ya manta cewa Jehobah Allah ne mai rai, zai yi masa sauƙi ya yi rashin aminci. Abin da ya faru da Israꞌilawa saꞌad da suke daji ke nan. Sun san cewa akwai Allah, amma sun soma shakka cewa zai iya tanada musu abubuwan da suke bukata. Har suna cewa: “Yahweh yana tare da mu ko babu?” (Fit. 17:2, 7) A sakamakon haka, sun yi wa Allah tawaye. Hakika, ba ma so mu yi irin rashin biyayya da suka yi, domin an rubuta labarin ne don ya zama gargaɗi a gare mu.—Karanta Ibraniyawa 3:12.

16. Mene ne zai iya gwada bangaskiyarmu?

16 Mutanen da ba sa bauta ma Jehobah suna sa ya yi mana wuya mu ci-gaba da kasancewa kusa da shi. Mutane da yawa ba su yarda cewa akwai Allah ba. Kuma kamar dai waɗanda ba sa bauta ma Jehobah suna jin daɗin rayuwa. Idan muka lura da hakan, za mu iya soma yin shakka. Ko da yake ba za mu yi shakka cewa akwai Allah ba, amma za mu iya soma shakka ko zai taimaka mana. Marubucin Zabura sura 73 ma ya yi wannan tunanin. Ya lura cewa waɗanda ba sa bin dokokin Allah suna jin daɗin rayuwa. Hakan ya sa ya soma shakka ko bauta ma Jehobah yana da amfani.—Zab. 73:11-13.

17. Me zai taimaka mana mu ci-gaba da yin kusa da Jehobah?

17 Mene ne ya taimaka wa marubucin zaburar ya canja raꞌayinsa? Ya yi tunani a kan abin da zai faru da waɗanda suka daina bauta ma Jehobah. (Zab. 73:18, 19, 27) Ya kuma yi tunani a kan albarkar da yake samuwa don yana bauta ma Jehobah. (Zab. 73:24) Mu ma za mu iya yin tunani a kan albarkun da Jehobah ya yi mana. Bayan haka, sai mu yi tunani a kan yadda rayuwarmu za ta kasance da a ce ba ma bauta ma Jehobah. Idan muka yi tunani a kan yadda muke amfana don muna bauta ma Jehobah, hakan zai taimaka mana mu ci-gaba da bauta masa da aminci, kuma kamar marubucin zaburar, kowannenmu zai ce: “A gare ni, yana da kyau a yi kusa da Allah.”—Zab. 73:28.

18. Me ya sa bai kamata mu ji tsoron abin da zai iya faruwa da mu a nan gaba ba?

18 Za mu iya jimre kowace irin matsala a wannan kwanakin ƙarshe domin muna “bauta wa Allah na gaskiya kuma mai rai.” (1 Tas. 1:9) Allahnmu mai rai ne, kuma yana taimaka ma waɗanda suke bauta masa. Ya kasance da bayinsa a dā, kuma yana tare da mu a yau. Nan ba da jimawa ba, za mu fuskanci ƙunci da ba a taɓa yin irinsa ba a nan duniya. Amma Jehobah zai kasance tare da mu a wannan lokacin. (Isha. 41:10) Don haka, “ba tare da shakka ba, muna iya cewa, ‘Ubangiji mai taimakona ne, ba zan ji tsoro ba.’”—Ibran. 13:5, 6.

WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu