Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 24

WAƘA TA 24 Ku Zo Tudun Jehobah

Ka Ci-gaba da Zama a Tentin Jehobah Har Abada!

Ka Ci-gaba da Zama a Tentin Jehobah Har Abada!

“Yahweh, wa ya isa ya zauna a Tentinka?”ZAB. 15:1.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da ya zama dole mu yi don mu ci-gaba da zama aminan Jehobah, da kuma yadda yake so mu yi shaꞌani da abokansa.

1. Ta yaya za mu amfana idan muka bincika Zabura 15:1-5?

 A TALIFIN da ya gabata, mun koyi cewa waɗanda suka yi alkawarin bauta ma Jehobah kuma suka zama aminansa su ne za su iya shigowa tentinsa. Amma me za mu yi don mu cancanci zama a tentin Jehobah? Zabura ta 15 ta yi bayani a kan wannan batun. (Karanta Zabura 15:1-5.) Wannan zaburar ta nuna abubuwan da za mu yi don mu ƙara kusantar Jehobah.

2. Da Dauda ya yi zancen tentin Jehobah, mene ne wataƙila yake tunani a kai?

2 Zabura ta 15 ta soma da cewa: “Yahweh, wa ya isa ya zauna a Tentinka? Wa ya isa ya yi sujada a Sihiyona, Tudunka Mai Tsarki?” (Zab. 15:1) Saꞌad da Dauda ya ambaci tentin Jehobah a ayar nan, mai yiwuwa yana tunani a kan tentin saduwa ne. Akwai lokacin da aka ajiye tentin a Gibiyon. Dauda ya kuma ce, “Tudunka Mai Tsarki,” wataƙila tudun Sihiyona da ke Urushalima ne yake nufi. Sihiyona yana wajen kilomita 10 daga kudancin Gibiyon, kuma a wurin ne Dauda ya kafa wani tenti don a ajiye akwatin yarjejeniyar Yahweh har sai lokacin da za a gina haikalin Jehobah.—2 Sam. 6:17.

3. Me ya sa ya kamata mu bincika Zabura ta 15? (Ka kuma duba hoton.)

3 Yawancin Israꞌilawa ba su yi hidima a tentin saduwa ba, kuma kaɗan daga cikinsu ne kawai suka taɓa shiga tentin Jehobah inda ake ajiye akwatin yarjejeniyar. Amma kamar yadda Zabura ta 15 ta nuna, dukan bayin Jehobah masu aminci za su iya zama a tentinsa idan suka ci-gaba da zama aminansa. Abin da kowannenmu yake so ke nan, ko ba haka ba? Zabura ta 15, ta bayyana wasu halaye da muke bukatar mu koya kuma mu nuna su idan muna so mu ci-gaba da zama aminan Jehobah.

Israꞌilawa a zamanin Dauda sun fahimci abin da ake nufi da shigowa tentin Jehobah (Ka duba sakin layi na 3)


KA YI TAFIYA CIKIN GASKIYA KUMA KA AIKATA ABIN DA KE DAIDAI

4. Me ya nuna cewa ba yin baftisma ne kawai Jehobah yake bukata a gare mu ba? (Ishaya 48:1)

4 Zabura 15:2 ta ce aminin Allah shi ne wanda “yake tafiya cikin gaskiya” da kuma “aikata abin da yake daidai.” Kalmomin nan “tafiya,” da kuma “aikata,” sun nuna cewa abu ne da mutum yake bukatar ya ci-gaba da yi. Amma za mu iya yin “tafiya cikin gaskiya” kuwa? Ƙwarai! Dukanmu ajizai ne kam, amma idan muna yin iya ƙoƙarinmu mu bi abin da Jehobah ya ce, Jehobah zai ɗauke mu a matsayin masu tafiya cikin gaskiya. A lokacin da muka yi alkawarin bauta ma Jehobah kuma muka yi baftisma ne muka soma zama aminan Jehobah. Amma ko da yake alꞌummar Israꞌila ta yi alkawarin bauta ma Jehobah, ba kowannensu ne ya cancanci shigowa tentin Jehobah ba, domin wasunsu suna kiran sunan Jehobah “amma ba a cikin gaskiya ko adalci ba.” (Karanta Ishaya 48:1.) Waɗanda suke so su shiga tentin Jehobah suna bukatar su san abin da yake bukata a gare su kuma su yi shi. Mu ma a yau, idan muna so mu zama aminan Jehobah, muna bukatar mu yi baftisma kuma mu zama Shaidun Jehobah. Amma ba shi ke nan ba. Muna bukatar mu ci-gaba da “aikata abin da yake daidai.” Ta yaya za mu yi hakan?

5. Ta yaya za mu yi wa Jehobah biyayya a dukan kome?

5 A gun Jehobah, yin “tafiya cikin gaskiya” da kuma “aikata abin da yake daidai” ya wuci yin wasu ayyukan ibada kawai. (1 Sam. 15:22) Muna bukatar mu yi wa Jehobah biyayya a kowane fanni na rayuwarmu, har a lokacin da muke mu kaɗai. (K. Mag. 3:6; M. Wa. 12:13, 14) Yana da muhimmanci mu bi abin da Jehobah ya faɗa ko a ƙananan abubuwa. Abin da zai nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da gaske ke nan, kuma zai sa shi ma ya ƙaunace mu sosai.—Yoh. 14:23; 1 Yoh. 5:3.

6. Bisa ga Ibraniyawa 6:10-12, mene ne ya fi ayyukan kirki da muka yi a dā muhimmanci?

6 Abubuwan da muka yi wa Jehobah a dā suna sa shi farin ciki. Amma ba abubuwan da muka yi a dā ne kawai za su sa mu cancanci zama a tentin Jehobah ba. Ibraniyawa 6:10-12 sun nuna hakan. (Karanta.) Hakika Jehobah ba ya manta da abubuwa masu kyau da muka yi a dā. Amma yana so mu ci-gaba da bauta masa da dukan zuciyarmu “har zuwa ƙarshe.” Kuma “idan ba mu gaji muka bar ƙoƙari ba,” za mu ci-gaba da zama aminansa har abada.—Gal. 6:9.

KA RIƘA FAƊIN GASKIYA DAGA ZUCIYARKA

7. Me ake nufi da faɗin gaskiya daga zuciyarmu?

7 Idan mutum yana so ya zauna a tentin Jehobah, dole ne ya riƙa “faɗin gaskiya daga zuciyarsa.” (Zab. 15:2) Hakan yana nufin cewa ba zai yi ƙarya ba. Amma ba shi ke nan ba. Jehobah yana so mu riƙa yin gaskiya ko da me muke yi. (Ibran. 13:18) Wannan yana da muhimmanci sosai domin “Yahweh yana ƙyamar mai halin ruɗu, amma yana amincewa da mai gaskiya a zuci.”—K. Mag. 3:32.

8. Wane hali ne ya zama dole mu kiyaye shi?

8 Waɗanda suke faɗin gaskiya daga zuciyarsu ba sa yi kamar su masu biyayya ne a idon mutane, alhali suna taka dokokin Jehobah a ɓoye. (Isha. 29:13) Ƙari ga haka, ba sa wayo-wayo idan ya zo ga bin dokokin Jehobah. Mutumin da yake ganin yana da wayo, zai iya ganin kamar bin dokokin Jehobah a wasu lokuta ba zai amfane shi ba. (Yak. 1:5-8) Zai iya taka dokar Jehobah a batun da yake ganin ba shi da muhimmanci. Kuma idan ya ga cewa ba abin da ya same shi, mai yiwuwa ya soma yin abubuwan da suka fi wanda ya yi a baya muni. Irin wannan mutumin ko da yana tsammanin cewa yana bauta ma Jehobah, Jehobah ba zai amince da ibadarsa ba. (M. Wa. 8:11) Ba shakka mu kam muna so mu yi gaskiya a kome da muke yi.

9. Mene ne abin da ya faru saꞌad da Yesu ya ga Nataniyel ya koya mana? (Ka kuma duba hoton.)

9 Abin da ya faru saꞌad da Filibus ya kawo abokinsa Nataniyel wurin Yesu, ya nuna cewa yana da muhimmanci sosai mutum ya zama mai faɗin gaskiya daga zuciyarsa. Ko da yake Yesu bai taɓa haɗuwa da Nataniyel ba, da ganin sa Yesu ya ce: “Ku ga mutumin Israꞌila na gaske, wanda ba shi da ƙarya a cikinsa.” (Yoh. 1:47) Yesu ya san cewa sauran almajiransa suna faɗin gaskiya, amma ya lura cewa Nataniyel yana faɗin gaskiya ba kaɗan ba. Ko da yake Nataniyel ajizi ne kamar mu, ba ya munafunci, yana yin gaskiya a kome da yake yi. Halinsa ya burge Yesu kuma Yesu ya yaba masa. Ba shakka dukanmu za mu so a ce Yesu ya yaba mana don muna yin gaskiya a kome da muke yi!

Filibus ya kawo abokinsa Nataniyel wurin Yesu, kuma da ganin Nataniyel Yesu ya ce ba shi da ƙarya a cikinsa. Mu ma za a iya faɗin hakan game da mu? (Ka duba sakin layi na 9)


10. Me ya sa ya kamata mu yi hankali da irin maganganu da muke yi? (Yakub 1:26)

10 Yawancin umurnan da ke Zabura ta 15 game da yadda ya kamata mu yi shaꞌani da mutane ne. Zabura 15:3 ta ce baƙo da ya shigo tentin Jehobah “ba ya ɓata sunan wani, . . . ba ya yi wa abokansa mugunta, ko ya baza jita-jita game da maƙwabtansa.” Irin waɗannan maganganun za su iya cutar da mutane sosai, kuma idan muna yin su, Jehobah ba zai bar mu mu ci-gaba da zama a tentinsa ba.—Karanta Yakub 1:26.

11. Wane mataki ne za a ɗauka a kan wanda yake ɓata sunan mutane kuma ya ƙi tuba?

11 A Zabura ta 15, Dauda ya ambaci ɓata suna. Mene ne hakan yake nufi? Yana nufin mutum ya yi ƙarya a kan wani kuma hakan ya sa a daina ganinsa da mutunci. Idan mutum yana ɓata sunan mutane kuma ya ƙi tuba, ba za a bar shi ya ci-gaba da zama Mashaidin Jehobah ba.—Irm. 17:10.

12-13. A waɗanne yanayoyi ne idan ba mu yi hankali ba, za mu zub da mutuncin ꞌyanꞌuwanmu? (Ka kuma duba hoton.)

12 Zabura 15:3 ta kuma ce waɗanda suke zama a tentin Jehobah ba sa yi wa abokansu mugunta, kuma ba sa baza jita-jita game da maƙwabtansu. Ta yaya za mu iya yin hakan?

13 Idan ba mu yi hankali ba, za mu iya zub da mutuncin mutum ta wajen yaɗa jita-jita game da shi. Alal misali, a ce: (1) wata ꞌyarꞌuwa ta daina yin hidimar majagaba, (2) wani ɗanꞌuwa da matarsa sun bar Bethel, ko kuma (3) an dakatar da wani ɗanꞌuwa daga hidimar dattijo ko bawa mai hidima. Zai dace mu soma tunanin dalilan da wataƙila su ne suka sa hakan ya faru, kuma mu soma gaya wa mutane abin da muke tunani? Aꞌa. Wataƙila hakan ya faru ne domin wasu dalilai da ba mu sani ba. Ƙari ga haka, mu tuna cewa wanda yake zama a tentin Jehobah “ba ya yi wa abokansa mugunta, ko ya baza jita-jita game da maƙwabtansa.”

Bai da wuya mu fara baza jita-jita game da mutane, kuma irin maganganun nan za su iya ɓata sunan mutum (Ka duba sakin layi na 12-13)


KA GIRMAMA MASU TSORON YAHWEH

14. Ka bayyana yadda za mu ƙi “wanda Yahweh ya ƙi.”

14 Zabura 15:4 ta ce aminin Allah “ba ya darajarta wanda Yahweh ya ƙi.” Ta yaya za mu san wanda Yahweh ya ƙi? Idan muka bi raꞌayinmu kawai, ba za mu iya sanin wanda Yahweh ya ƙi ba. Me ya sa? Domin mu ajizai ne. A wasu lokuta mukan so mutane domin muna son halinsu, ko mu ƙi su don yadda suke yin abubuwa yana ɓata mana rai. Saboda haka, waɗanda Jehobah ya “ƙi” ne kaɗai ya kamata mu ƙi. (1 Kor. 5:11) Wato waɗanda suke yin abubuwa marasa kyau kuma suka ƙi tuba, da waɗanda ba sa mutunta imaninmu, da kuma waɗanda suke ƙoƙarin ɓata abokantakarmu da Jehobah da makamantansu.—K. Mag. 13:20.

15. Me za mu yi don mu “girmama masu tsoron Yahweh”?

15 Zabura 15:4 ta kuma ce mu “girmama masu tsoron Yahweh.” Don haka, zai dace mu yi tunanin hanyoyin da za mu girmama aminan Jehobah, kuma mu yi musu alheri. (Rom. 12:10) Ayar ta gaya mana hanya ɗaya da za mu yi haka. Ta ce wanda yake a tentin Jehobah “yakan cika alkawarinsa ko da ma zai zafe shi.” Idan muka yi wa mutum alkawari kuma ba mu cika ba, mutumin ba zai ji daɗi ba. (Mat. 5:37) Alal misali, Jehobah yana bukatar mata da miji su cika alkawari da suka yi wa juna. Kuma yakan ji daɗi idan ya ga iyaye suna iya ƙoƙarinsu don su cika alkawari da suka yi wa yaransu. Idan muna ƙaunar Allah da maƙwabtanmu, za mu yi iya ƙoƙarinmu mu cika duk wani alkawari da muka yi.

16. Mene ne kuma za mu yi don mu nuna cewa muna girmama aminan Jehobah?

16 Wani abu kuma da za mu yi don mu girmama aminan Allah shi ne mu zama masu karɓan baƙi da kuma masu bayarwa. (Rom. 12:13) Idan muna kasancewa tare da ꞌyanꞌuwanmu kuma muna shakatawa tare da su, hakan zai sa mu ƙara kusantar su kuma mu kusaci Jehobah. Ƙari ga haka, idan muna karɓan ꞌyanꞌuwanmu hannu bibbiyu, muna bin halin Jehobah ke nan.

KADA KA ZAMA MAI SON KUƊI

17. Me ya sa aka yi zancen kuɗi a Zabura ta 15?

17 Zaburar ta kuma ce aminin Jehobah “ba ya ba da bashi don riba, ba ya karɓar cin hanci domin ya ba da shaidar ƙarya a kan marar laifi.” (Zab. 15:5) Me ya sa marubucin zaburar ya yi zancen kuɗi? Domin idan mun cika son kuɗi, hakan zai iya sa mu yi abin da zai ɓata wa mutane rai, har ya ɓata dangantakarmu da Jehobah. (1 Tim. 6:10) A zamanin dā, wasu Israꞌilawa sukan wulaƙanta ꞌyanꞌuwansu ta wajen sa su su biya bashin da suka ci da riɓa a kai. Ban da haka, wasu alƙalai suna karɓan cin hanci, saꞌan nan su yi wa mutane rashin adalci. Jehobah ya tsani irin abubuwan nan.—Ezek. 22:12.

18. Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka wa kowannenmu ya bincika raꞌayinsa game da kuɗi? (Ibraniyawa 13:5)

18 Ya kamata kowannenmu ya bincika raꞌayinsa game da kuɗi. Ka yi wa kanka tambayoyin nan: ‘Na cika yin tunani a kan kuɗi ko abin da zan iya saya da kuɗi? Idan na ci bashi kuma lokacin biya ya yi, nakan yi jinkirin biya domin ina ganin cewa mutumin ba ya bukatar kuɗin? Idan na samu kuɗi, nakan ji kamar na fi wasu? Yakan yi min wuya in yi wa mutum kyauta? Idan na ga ꞌyanꞌuwa masu kuɗi, nakan ɗauka cewa sun cika son abin duniya? Na fi son yin abokantaka da masu kuɗi, saꞌan nan in rena waɗanda ba su da shi?’ Yana da muhimmanci mu bincika raꞌayinmu game da kuɗi don Jehobah ya ba mu gatan kasancewa a tentinsa. Da yake son kuɗi zai iya sa mu rasa wannan gatan, ya kamata mu kiyaye shi. Idan muka yi hakan, Jehobah ba zai taɓa yashe mu ba!—Karanta Ibraniyawa 13:5.

JEHOBAH YANA ƘAUNAR AMINANSA

19. Me ya sa Jehobah yake so mu yi dukan abubuwan da ya gaya mana a Zabura ta 15?

19 An kammala Zabura ta 15 da cewa: “Mai yin waɗannan ba ya taɓa jijjiguwa.” (Zab. 15:5) Wannan ayar ta nuna dalilin da ya sa Jehobah yake so mu yi dukan abubuwan da ya ce a Zabura 15. Dalilin shi ne, Jehobah yana so mu yi farin ciki. Idan muka yi abubuwan da Jehobah ya ce mu yi, za mu ji daɗin rayuwa kuma Jehobah zai tsare mu.—Isha. 48:17.

20. Wane lada ne waɗanda suke zama a tentin Jehobah za su samu?

20 Waɗanda Jehobah ya amince musu su zauna a tentinsa za su sami lada mai ban shaꞌawa a nan gaba. Shafaffun Kiristoci da suka riƙe amincinsu, za su yi rayuwa a inda Yesu ya shirya musu a sama. (Yoh. 14:2) Waɗanda za su yi rayuwa a duniyar nan kuma, za su mori abubuwan da Allah ya yi musu alkawari a Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3. Hakika, Jehobah ya mutunta mu sosai da ya gayyace mu zama aminansa kuma mu kasance a tentinsa har abada!

WAƘA TA 39 Mu Yi Suna Mai Kyau a Wurin Allah