Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ruhu Mai Tsarki Yana Shaida Mana

Ruhu Mai Tsarki Yana Shaida Mana

“Ruhu da kansa tare da namu ruhu yana shaida, mu ‘ya’yan Allah ne.”—ROMAWA 8:16.

WAƘOƘI: 109, 108

1-3. Mene ne ya faru a Fentakos da ya sa ranar ta kasance da muhimmanci, kuma ta yaya hakan ya cika annabcin da aka yi a cikin Littafi Mai Tsarki? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.)

RANAR Lahadi ta Fentakos na shekara ta 33 rana ce ta musamman. Mutane suna bikin Fentakos. Wannan biki ne da ake yi sa’ad da aka soma girbin hatsi. Babban firist yakan yi hadaya a cikin haikali kamar yadda aka saba yi. Bayan haka, sai ya yi hadayar gurasa guda biyu na hatsi da aka soma girbinsa, sai ya kaɗa hadayar kuma ya miƙa ta ga Jehobah.—Levitikus 23:​15-20.

2 Ɗarurruwan firistoci suna yin wannan hadaya ta kaɗawa kowace shekara. Wannan hadayar tana da alaƙa da wani abu mai muhimmanci da ya faru a Fentakos na shekara ta 33. Wannan abin ya faru ga almajiran Yesu guda 120 da ke yin addu’a a wani ɗaki da ke gidan sama a Urushalima. (Ayyukan Manzanni 1:​13-15) Shekaru ɗari takwas kafin wannan lokacin, annabi Joel ya yi annabci game da wannan abin da ya faru. (Joel 2:​28-32; Ayyukan Manzanni 2:16-21) Mene ne ya faru da ke da muhimmanci haka?

3 Karanta Ayyukan Manzanni 2:​2-4. Allah ya ba wa waɗannan Kiristoci ruhu mai tsarki a Fentakos ta shekara ta 33 kuma ya shafe su. (Ayyukan Manzanni 1:⁠8) Bayan haka, sai mutane suka soma taruwa a inda suke kuma almajiran suka soma magana a kan abubuwa masu ban al’ajabi da suka gani da kuma ji. Manzo Bitrus ya bayyana abin da ya faru da kuma yadda hakan yake da muhimmanci. Sai ya gaya wa mutanen da suka taru cewa: ‘Ku tuba, a yi wa kowane ɗaya daga cikinku baftisma cikin sunan Yesu Kristi zuwa gafarar zunubanku; za ku karɓi Ruhu Mai-tsarki kyauta.’ A ranar, mutane wajen 3,000 ne suka yi baftisma kuma suka karɓi ruhu mai tsarki.​—⁠Ayyukan Manzanni 2:​37, 38, 41.

4. (a) Me ya sa ya kamata mu tattauna abin da ya faru a Fentakos? (b) Wane abu mai muhimmanci ne ya taɓa faruwa shekaru da yawa kafin wannan lokacin? (Ka duba ƙarin bayani.)

4 Mene ne babban firist da kuma hadayar da ake yi a kowace ranar Fenkatos suke wakilta? Babban firist yana wakiltar Yesu. Gurasa guda biyun suna wakitar shafaffun almajiran Yesu. Allah ya zaɓi waɗannan almajirai daga cikin ‘yan Adam ajizai kuma ya mai da su “ ’ya’yan fari.” (Yaƙub 1:18) Allah ya ɗauke su a matsayin ‘ya’yansa kuma ya zaɓe su su yi sarauta tare da Yesu a Mulkin Allah a sama. (1 Bitrus 2:⁠9) Jehobah zai yi amfani da mulkin ya albarkaci dukan ‘yan Adam masu biyayya. Saboda haka, wannan ranar ta Fentakos ta shekara ta 33 tana da muhimmanci a gare mu ko da za mu je sama, ko kuma za mu zauna a aljanna a duniya. [1]​—⁠Ka duba ƙarin bayani.

MENE NE YAKE FARUWA SA’AD DA AKA SHAFE WANI?

5. Ta yaya muka san cewa yanayin da aka shafe Kiristoci ya bambanta?

5 Almajiran da suka taru a wannan ɗaki da ke gidan sama ba za su manta da abin da ya faru a ranar ba. Wani abu kamar wuta ta sauko a kan kowannen su. Jehobah ya ba su baiwar yin wani yare. Hakika, hakan ya nuna cewa an shafe su da ruhu mai tsarki. (Ayyukan Manzanni 2:​6-12) Amma, ba dukan Kiristoci ba ne suka shaida wannan abin al’ajabi sa’ad da aka shafe su da ruhu mai tsarki. Alal misali, Littafi Mai Tsarki bai ce wani abu kamar wuta ya sauko a kan dubban mutanen da aka yi musu baftisma kuma aka shafe su a Urushalima a ranar ba. (Ayyukan Manzanni 2:38) Ƙari ga haka, ba dukan Kiristoci ba ne aka shafe su a lokacin da aka yi musu baftisma. Wasu Samariyawa sun zama shafaffu ne jim kaɗan bayan an yi musu baftisma. (Ayyukan Manzanni 8:​14-17) Wani abin mamaki kuma, an shafe Karniliyus da waɗanda suke gidansa kafin a yi musu baftisma.​—⁠Ayyukan Manzanni 10:​44-48.

6. Mene ne dukan shafaffu suka samu, kuma ta yaya hakan yake shafan su?

6 Kiristoci sun gane cewa yadda Allah ya shafe su ya bambanta sosai. Wasu sun gane nan da nan cewa Jehobah ya shafe su. Wasu kuma sun fahimci hakan ne daga baya. Amma kowannen su ya shaida abin da manzo Bulus ya bayyana sa’ad da ya ce: ‘Sa’anda kuka ba da gaskiya kuma, aka hatimce ku da Ruhu Mai-tsarki na alkawari, wanda shi ne tabbacin gādonmu.’ (Afisawa 1:​13, 14) Saboda haka, Jehobah yana amfani da ruhu mai tsarki don ya tabbata wa waɗannan Kiristoci cewa ya zaɓe su su je sama. Ruhu mai tsarki shi ne “tabbacin” da ya nuna cewa a nan gaba, za su yi rayuwa a sama, ba a duniya ba.​—⁠Karanta 2 Korintiyawa 1:​21, 22; 5:⁠5.

Kada kowane shafaffen Kirista ya yarda wani abu ya hana shi bauta wa Jehobah

7. Mene ne ya wajaba kowane shafaffen Kirista ya yi don ya sami ladarsa na zuwa sama?

7 Sa’ad da aka shafe Kirista, hakan yana nufin cewa tabbas zai sami ladarsa ne? A’a. Hakika, ya tabbata cewa Allah ya zaɓe shi ya je sama. Amma, zai sami ladarsa ne kawai idan ya kasance da aminci ga Jehobah. Bitrus ya bayyana cewa: ‘Domin wannan fa, ‘yan’uwa, ku daɗa ba da anniya garin ku tabbatar da kiranku da zaɓenku: gama idan kun yi waɗannan abu, ba za ku yi tuntuɓe ba daɗai: gama haka nan za a ba ku shigowa mai-yalwa zuwa cikin madawwamin mulki na Ubangijinmu da Mai-cetonmu Yesu Kristi.’ (2 Bitrus 1:​10, 11) Saboda haka, kada kowane shafaffen Kirista ya yarda wani abu ya hana shi bauta wa Jehobah. Gaskiya ne cewa Allah ya zaɓe shi ya je sama, amma idan bai kasance da aminci ba, ba zai sami ladarsa ba.​—⁠Ibraniyawa 3:1; Ru’ya ta Yohanna 2:⁠10.

TA YAYA MUTUM ZAI SANI?

8, 9. (a) Me ya sa yawancin mutane ba za su iya fahimtar abin da ke faruwa sa’ad da aka shafe wani da ruhu mai tsarki ba? (b) Ta yaya mutum yake sanin cewa Allah ya zaɓe shi ya je sama?

8 Yawancin bayin Jehobah a yau ba za su iya fahimtar abin da ke faruwa da mutum sa’ad da Allah ya shafe shi da ruhu mai tsarki ba. Hakan ba abin mamaki ba ne don ba a shafa su da ruhu mai tsarki ba. Allah ya halicci ‘yan Adam don su yi rayuwa har abada a duniya ne ba a sama ba. (Farawa 1:28; Zabura 37:29) Amma Jehobah ya zaɓi wasu su zama sarakuna da firistoci a sama. Saboda haka, sa’ad da Allah ya shafe su, hakan yana canja begensu da tunaninsu kuma su soma marmarin yin rayuwa a sama.​—⁠Karanta Afisawa 1:⁠18.

9 Amma ta yaya mutum yake sani cewa an shafe shi ya je sama? Ka yi la’akari da abin da manzo Bulus ya gaya wa ‘yan’uwa shafaffu da ke Roma da aka zaɓe su ‘su zama tsarkakku.’ Ya ce musu: ‘Ba ku karɓi ruhun bauta da za ku sake jin tsoro ba; amma kuka karɓi ruhun ɗiyanci, inda muke kira, Abba, Uba. Ruhu da kansa tare da namu ruhu yana shaida, mu ‘ya’yan Allah ne.’ (Romawa 1:7; 8:​15, 16) Allah yana amfani da ruhu mai tsarki don ya tabbatar wa ɗan’uwa ko ‘yar’uwa cewa ya zaɓe su su yi sarauta tare da Yesu a sama.​—⁠1 Tasalonikawa 2:⁠12.

10. Mene ne 1 Yohanna 2:27 yake nufi sa’ad da ya ce Kirista shafaffe ba ya bukatar wani ya koyar da shi?

10 Waɗanda Allah ya zaɓe su su je sama ba sa bukatar wani ya gaya musu cewa an shafe su. Jehobah ne yake sa su tabbata da kansu cewa an shafe su. Manzo Yohanna ya gaya wa shafaffun Kiristoci cewa: “Mai Tsarkin nan ya shafe ku, dukanku kuma kun san gaskiya.” Ya daɗa cewa: “Ku kam, shafan nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafan nan tasa ke koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna cikinsa.” (1 Yohanna 2:​20, 27, Littafi Mai Tsarki.) Shafaffun Kiristoci suna bukatar Jehobah ya koyar da su kamar sauran Kiristoci. Amma, ba sa bukatar wani ya tabbatar musu cewa an shafe su. Jehobah ya riga ya yi amfani da ikonsa, wato ruhu mai tsarki, don ya nuna musu dalla-dalla cewa su shafaffu ne!

TA YAYA AKE SAKE HAIFAR MUTUM?

11, 12. Wane irin tunani ne Kirista da aka shafe shi zai iya yi, amma wane tabbaci ne yake da shi?

11 Sa’ad da aka shafe Kiristoci da ruhu mai tsarki, hakan yana canja yanayinsu sosai. Shi ya sa Yesu ya ce, an haife su “daga bisa.” (Yohanna 3:​3, 5) Sai ya bayyana cewa: “Kada ka yi mamaki domin na ce maka, dole a haife ku daga bisa. Iska yakan hura wajen da yake nufa, kana jin motsinsa kuma, amma ba ka sani wajen da yake fitowa, da inda za shi ba: Haka nan ne dukan wanda an haife shi daga cikin ruhu.” (Yohanna 3:​7, 8) Hakika, yana da wuya shafaffe ya iya bayyana yanayinsa ga wanda ba a shafe shi da ruhu mai tsarki ba. [2]—Ka duba ƙarin bayani.

Wanda aka shafe shi ya tabbata cewa Jehobah ya zaɓe shi kuma ba ya shakka

12 Wanda Allah ya shafe shi da ruhu mai tsarki zai iya yin wannan tunanin, ‘Me ya sa Jehobah ya zaɓe ni maimakon ya zaɓi wani?’ Har ma zai ɗauka cewa bai cancanta ya sami wannan gatan ba. Amma ya tabbata cewa Jehobah ya zaɓe shi kuma ba ya shakka. Yana farin ciki da kuma godiya saboda wannan gatan. Ra’ayin shafaffu ɗaya ne da na Bitrus sa’ad da ya ce: “Albarka ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, wanda ya maya haihuwarmu bisa ga jinƙansa mai-girma zuwa bege mai-rai ta wurin tashin Yesu Kristi daga matattu, zuwa gādo marar-ruɓewa, marar-ƙazantuwa, wanda ba shi yanƙwanewa, ajiyayye a sama dominku.” (1 Bitrus 1:​3, 4) Sa’ad da shafaffu suka karanta waɗannan kalaman, sun tabbata cewa Ubansu wanda ke sama ne yake yi musu magana kai tsaye.

13. Ta yaya ra’ayin mutum yakan canja sa’ad da aka shafe shi da ruhu mai tsarki, kuma mene ne yake sa mutumin ya canja ra’ayinsa?

13 Kafin Jehobah ya zaɓi waɗannan shafaffu su je sama, sun kasance da begen yin rayuwa har abada a duniya. Sun yi ɗokin lokacin da Jehobah zai kawar da dukan mugunta kuma ya mai da duniya aljanna. Wataƙila sun yi tunani cewa za su marabci ɗan’uwansu ko abokinsu da za a tayar daga mutuwa. Ƙari ga haka, sun yi ɗokin lokacin da za su gina gida su zauna a ciki ko kuma su dasa itatuwa kuma su ci ‘ya’yan. (Ishaya 65:​21-23) Me ya sa suka canja ra’ayinsu? Shin sun yin hakan saboda baƙin ciki ko kuma wahala da suka sha ne? Sun soma tunani cewa yin rayuwa har abada a duniya ba zai yi daɗi ba kuma ba za su kasance da farin ciki a duniya ba ne? Ko kuma suna so su shaida yadda rayuwa take a sama ne? A’a. A maimakon haka, Allah ne ya yanke musu wannan shawarar. Sa’ad da ya zaɓe su, ya yi amfani da ikonsa, wato ruhu mai tsarki don ya canja ra’ayinsu da kuma begen da suke da shi.

14. Yaya shafaffu suke ji game da rayuwar da suke yi a duniya?

14 Shin hakan yana nufin cewa shafaffu suna so su mutu ne? Bulus ya bayyana ra’ayin shafaffu sa’ad da ya kwatanta jikinsu da ‘mazauni’ kuma ya ce: ‘Gama hakika mu da ke cikin wannan mazaunin jiki muna nishi, mun nauwaita; ba cewa muna so a kware mana sutura ba, amma a ƙara bisanta, domin abin da ke na mutuwa rai shi haɗiye.’ (2 Korintiyawa 5:⁠4) Waɗannan Kiristoci shafaffu ba sa so su mutu. Suna jin daɗin rayuwa kuma suna so su riƙa bauta wa Jehobah kullum tare da iyalinsu da abokansu. Amma a dukan al’amuransu, ba sa manta da abin da Allah ya yi musu alkawarinsa a nan gaba ba.​—⁠1 Korintiyawa 15:53; 2 Bitrus 1:4; 1 Yohanna 3:​2, 3; Ru’ya ta Yohanna 20:⁠6.

JEHOBAH YA ZAƁE KA NE?

15. Mene ne yake nuna cewa ba a shafe mutum da ruhu mai tsarki ba?

15 Wataƙila kana tunani ko Jehobah ya zaɓe ka ka je sama. Idan kana ganin cewa ya yi hakan, ka yi la’akari da waɗannan tambayoyi masu muhimmanci: Kana gani cewa kana da himma sosai a wa’azin bishara? Kana jin daɗin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma koyan al’amura masu zurfi na Allah? (1 Korintiyawa 2:10) Kana gani cewa Jehobah ya sa ka sami sakamako mai kyau a wa’azin bishara? Kana marmarin yin nufin Allah fiye da kome? Kana ƙaunar mutane daga zuciyarka kuma kana ganin hakkinka ne ka taimaka musu su bauta wa Jehobah? Akwai abubuwan da suka faru a rayuwarka da suka nuna maka cewa Jehobah ya taimake ka? Idan amsarka e ne ga dukan waɗannan tambayoyin, shin hakan yana nufin cewa Jehobah ya zaɓe ka ka je sama ne? A’a. Me ya sa? Domin dukan bayin Jehobah za su iya shaida waɗannan abubuwan, ko da an shafe su ko ba a shafe su ba. Ƙari ga haka, Jehobah zai iya ba wa kowane bawansa ruhu mai tsarki ya cim ma wasu abubuwa a bautarsa ko da an zaɓe shi ya je sama ko a’a. Gaskiyar ita ce, idan har kana tunani ko Jehobah ya zaɓe ka, hakan yana nufin cewa ba a zaɓe ka ba. Waɗanda Jehobah ya zaɓe su sun san cewa an zaɓe su kuma ba sa shakka ko kaɗan!

16. Ta yaya muka san cewa ba dukan waɗanda aka ba wa ruhu mai tsarki ba ne aka zaɓe su su je sama?

16 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalan amintattun bayin Allah da yawa da suka sami ruhu mai tsarki amma ba su je sama ba. Ɗaya daga cikinsu shi ne Yohanna Mai Baftisma. Yesu ya ce babu mutumin da ya fi Yohanna, amma kuma ya ce Yohanna ba zai yi sarauta a sama ba. (Matta 11:​10, 11) Dauda wani ne da ruhu mai tsarki ya ja-gorance shi. (1 Sama’ila 16:13) Ruhu mai tsarki ya taimaka masa ya fahimci abubuwa masu muhimmanci game da Jehobah. Ƙari ga haka, ta wajen ja-gorar ruhu mai tsarki, ya rubuta sassan Littafi Mai Tsarki. (Markus 12:36) Duk da haka, manzo Bulus ya ce: “Dawuda bai hau zuwa cikin sammai ba.” (Ayyukan Manzanni 2:34) Jehobah ya ba wa waɗannan bayin ruhu mai tsarki don su cim ma wasu abubuwa masu ban al’ajabi, amma bai shafe su da shi don su je sama ba. Shin hakan yana nufin bangaskiyarsu bai kai wanda zai sa su cancanci zuwa sama ba ne? A’a. Abin da yake nufi shi ne, Jehobah zai ta da su don su yi rayuwa a Aljanna a duniya.​—⁠Yohanna 5:​28, 29; Ayyukan Manzanni 24:⁠15.

17, 18. (a) Wane bege ne yawancin bayin Jehobah suke da shi a yau? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Yawancin bayin Allah a yau ba za su je sama ba. Kamar Ibrahim da Dauda da Yohanna Mai Baftisma, da kuma maza da mata da yawa da suka yi rayuwa a dā, suna ɗokin yin rayuwa a duniya sa’ad da Mulkin Allah ya soma sarauta a duniya. (Ibraniyawa 11:10) Yesu zai yi sarauta tare da shafaffu 144,000 a sama. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa da ‘sauran zuriyar’ ko kuma shafaffu da suka rage a duniya a wannan ƙarshen zamani. (Ru’ya ta Yohanna 12:17) Amma yawancinsu sun riga sun mutu kuma sun tafi sama.

18 Amma idan wani ya ce an shafe shi fa, yaya ya kamata waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya su ɗauke shi? Idan wani a ikilisiyarku ya soma cin gurasa da kuma shan ruwa inabi a taron tuna mutuwar Yesu fa, yaya ya kamata ku bi da shi? Ƙari ga haka, idan adadin shafaffu yana ƙaruwa fa, ya kamata mu damu ne? Za mu amsa waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.

^ [1] (sakin layi na 4) Wataƙila ana yin Idin Fentakos a daidai lokacin da Allah ya ba wa Musa Dokoki a dutsen Sinai. (Fitowa 19:⁠1) Idan haka ne, kamar yadda Allah ya yi amfani da Musa wajen ƙulla yarjejeniya da al’ummar Isra’ila a wannan ranar a shekara ta 1513 kafin haihuwar Yesu, haka ma ya yi amfani da Yesu wajen yin alkawari da shafaffun almajiran Yesu a wannan ranar a shekara ta 33.

^ [2] (sakin layi na 11) Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 2009, shafuffuka na 3-11 don ƙarin bayani a kan abin da sake haifar mutum yake nufi.