Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KU ZAUNA A SHIRYE!

Miliyoyin Mutane Suna Gudun Hijira Daga Yukiren

Miliyoyin Mutane Suna Gudun Hijira Daga Yukiren

 Rasha ta kai wa Yukiren hari a ranar 24 ga Fabrairu, 2022. Hakan ya jefa rayukan miliyoyin mutane cikin hadari kuma ya sa da yawa suna kokarin barin kasar. a

 Wata mai suna Nataliia daga Kharkiv a kasar Yukiren ta ce: “Bama-bamai suna ta tashi. Abin tsoro ne sosai, ba zan iya kwatanta yadda na ji ba. Da muka ji cewa akwai jirgin kasa da ke kwasan mutane, sai muka yanke shawara mu gudu. Mun gudu mun bar komai domin dan karamin jakar baya ne kawai kowannenmu ya dauka. A cikin jakar, mun saka magunguna da ruwa da dan abinci da kuma takardunmu. Haka muka gudu muka je tashar jirgin kasar yayin da bama-bamai suke tashi a ko’ina.”

 Wata mai suna Nadija daga Kharkiv a kasar Yukiren ta ce: “Har aka soma yakin, muna ganin kamar ba za a taba yin yakin ba. Na ji bama-bamai suna ta tashi a wasu wurare kuma wundunanmu suna ta jijjiga. Sai na yanke shawara zan gudu kuma na dauki dan abubuwan da nake bukata. Na bar gida da karfe takwas na safe na shiga jirgi zuwa Lviv, daga nan na shiga bas zuwa Polan.”

A wannan talifin, za mu tattauna tambayoyin nan

 Wadanne abubuwa ne suke sa mutane gudun hijira?

 Ana gudun hijira daga Yukiren ne domin sojojin Rasha sun kai wa kasar Yukiren hari. Amma ga wasu dalilai da Littafi Mai Tsarki ya bayar da suke sa mutane gudun hijira:

  •   Gwamnatin ’yan Adam sun kasa biyan bukatun talakawansu. A yawancin lokuta, masu mulki sukan yi amfani da ikonsu don su wulakanta mutane.​—Mai-Wa’azi 4:1; 8:9.

  •   Shaidan ne “mai mulkin duniyar nan.” Kuma shi ne yake zuga mutane su rika yin mugunta, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duniya duka tana a hannun mugun nan.”​—Yohanna 14:30; 1 Yohanna 5:19.

  •   Ban da cewa ’yan Adam sun yi daruruwan shekaru suna fama da matsaloli, yanzu muna rayuwa ne a lokacin da aka yi annabci a Littafi Mai Tsarki cewa: “A kwanakin karshe za a sha wahala sosai.” (2 Timoti 3:1) Kari ga haka, a kwanakin nan za a yi yake-yake da bala’i iri-iri da yunwa da cututtuka. Kuma irin matsalolin nan ne suke sa mutane su gudu daga gidajensu.​—Luka 21:​10, 11.

 Waye ne zai iya taimaka wa ’yan gudun hijira?

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Mahaliccinmu, wato Jehobah, b Allah ne mai kauna kuma yana tausaya wa ’yan gudun hijira da wadanda suka bar gidajensu. (Maimaitawar Shari’a 10:18) Ya yi alkawari cewa ba za a sami ’yan gudun hijira a gwamnatinsa da zai kafa a sama ba. Wannan gwamnatin ce ake kira Mulkin Allah kuma ita ce za ta sauya gwamnatocin ’yar Adam. (Daniyel 2:44; Matiyu 6:10) Jehobah zai halaka Shaidan ta wurin Mulkinsa. (Romawa 16:20) Mulkin nan zai yi sarauta a duk fadin duniya, hakan zai sa ba za a sami iyakokin kasashe ba. Dukan ’yan Adam za su zama iyali daya kuma ba za a rika nuna bambanci ba. Ba wanda zai sake gudu daga gidansa, domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane mutum zai zauna cikin salama a karkashin itacen inabinsa da na baurensa. Ba wanda zai tsoratar da shi, gama Yahweh Mai Runduna ne ya fada.”​—Mika 4:4.

 Mulkin Allah ne kadai zai iya magance matsalar gudun hijira da muke fuskanta a yau. Ta wurin Mulkinsa, Jehobah zai kawar da matsalolin da suke sa mutane su bar gidajensu. Ga wasu daga cikin matsalolin:

  •   Yaki. Jehobah zai “tsai da yake-yake.” (Zabura 46:9) Don samun karin bayani game da yadda Allah zai kawar da yake-yake, ka karanta talifin nan “Salama a Duniya​—Ta Yaya Za a Same Ta?

  •   Wulakanci da mugunta. “Daga masu danniya da masu tā da hankali” Jehobah yakan cece su. (Zabura 72:14) Don ka ga yadda mutane za su iya canja ra’ayin da bai dace ba, ka karanta talifofin da ke mujallar nan mai jigo, “Yadda Za A Magance Kiyayya.”

  •   Talauci. “[Jehobah] yakan kubutar da masu bukata yayin da suka yi kira.” (Zabura 72:12) Don ka ga yadda Allah zai magance matsalar talauci, ka karanta talifin nan “Is a Fair Economic System Possible?”

  •   Karancin abinci. Za “a sami hatsi a yalwace a ƙasar.” (Zabura 72:16) Don ka ga yadda Allah ya tabbatar mana cewa ba wanda zai yi fama da matsalar yunwa, ka karanta talifin nan “A World Without Hunger?”

 Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka wa ’yan gudun hijira a yau kuwa?

 E. Ba kawai kasancewa da bege Littafi Mai Tsarki yake sa ’yan gudun hijira su yi ba, amma zai iya taimaka musu da shawarwari game da yadda za su bi da matsalolin da suke fama da su a yanzu.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Marar tunani yakan gaskata kome, amma mai hankali yakan yi tunani kafin ya fara wani abu.”​—Karin Magana 14:15.

 Abin da hakan yake nufi: Ka yi tunani game da matsalolin da za ka iya fuskanta da kuma matakin da za ka dauka don ka kāre kanka. Zai dace ka lura don kar ka fada a hannun masu mugunta da suke kokarin su cuci masu gudun hijira, domin mutanen sun san a yawancin lokuta, masu gudun hijira ba su san abin da za su yi ba.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Idan dai muna da abinci da rigunan sawa, wannan ma ya isa.”​—1 Timoti 6:8.

 Abin da hakan yake nufi: Kada ka mai da hankali a kan kayan duniya. Idan ka hakura da dan abin da kake da shi, za ka fi farin ciki.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Duk abin da kuke so mutane su yi muku sai ku ma ku yi musu.”​—Matiyu 7:12.

 Abin da hakan yake nufi: Ka zama mai hakuri da kuma kirki. Halayen nan ne za su sa mutane su karbe ka da hannu biyu, su kuma ga mutuncinka a inda kake hijira.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Idan wani ya yi muku mugunta, kada ku saka masa da mugunta.”​—Romawa 12:17.

 Abin da hakan yake nufi: Idan wani ya wulakanta ka, kada ka rama ko da hakan ya bata maka rai. Don ramawa zai sa abubuwa su dada muni.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Zan iya yin kome ta wurin . . . wanda yake ƙarfafa ni.”​—Filibiyawa 4:13.

 Abin da hakan yake nufi: Ibadarka ta zama farko a rayuwarka kuma ka ci gaba da yin addu’a. Allah zai taimaka maka ka jimre.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kada ku damu da kome, sai dai a cikin kome ku fada wa Allah bukatunku ta wurin addu’a da roko, tare da godiya. Ta haka kuwa Allah zai ba ku salama iri wadda ta wuce dukan ganewar dan Adam, za ta kuma tsare zukatanku da tunaninku.”​—Filibiyawa 4:​6, 7.

 Abin da hakan yake nufi: Ka roki Allah ya ba ka kwanciyar hankali a duk yanayin da kake ciki. Don karin bayani, ka duba talifin nan “Philippians 4:​6, 7​—‘Do Not Be Anxious About Anything.’ ”

a Kwana daya bayan sojojin Rasha sun shiga Yukiren, Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR ta ce, abin da ya faru a Yukiren na da tsanani sosai kuma ana bukatar taimakon gaggawa. A cikin kwana sha biyu, fiye da mutane miliyan biyu ne suka yi gudun hijira zuwa kasashe kusa da Yukiren, wajen miliyan daya kuma sun gudu daga gidajensu zuwa wasu bangarori a kasar Yukiren.

b Jehobah ko kuma Yahweh shi ne sunan Allah. (Zabura 83:18) Don karin bayani, ka duba talifin nan “Wane ne Jehovah?