Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

An kawo duwatsun da aka nika da ya fi kilo 27,500 a wurin daukan sauti da bidiyo da ke Mt. Ebo, don wannan wasan kwaikwayon

YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKA

Yadda Aka Shirya Bidiyoyin Taron Yanki na 2020 Mai Jigo, Ku Rika Farin Ciki!

Yadda Aka Shirya Bidiyoyin Taron Yanki na 2020 Mai Jigo, Ku Rika Farin Ciki!

10 GA AGUSTA, 2020

 Bidiyoyin da ake nunawa a taron yankinmu suna ratsa zukatanmu kuma suna taimaka mana mu gane koyarwar Littafi Mai Tsarki da kyau. Bidiyoyin da aka yi don Taron Yanki na 2020 mai jigo, Ku Rika Farin Ciki! sun kai 114, hade da jawabai 43 da membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu da mataimakansu suka yi. Ka taba tunanin yawan aiki da kuma kudin da aka kashe don shirya wadannan bidiyoyin?

 ’Yan’uwanmu kusan 900 daga wurare da dama a duniya ne suka yi amfani da lokacinsu da kuma kwarewarsu wajen shirya wadannan bidiyoyin. Duka-duka sun yi awoyi kusan 100,000 cikin shekaru biyu a kan wannan aikin. Hakan ya hada da awoyi 70,000 da aka yi ana shirya wasan kwaikwayo daga Littafi Mai Tsarki mai jigo, Nehemiya: “Farin Cikin da Jehobah Yake Bayarwa Shi Ne Ƙarfinku,” wanda yake da tsawon minti 76.

 Hakika an kashe kudi sosai wajen kula da wadannan ma’aikatan da suka ba da kansu don yin aikin, da sayan kayan aiki da kuma shirya wuraren da aka yi aikin.

 Dan’uwa Jared Gossman da ke aiki a Sashen Bidiyo da Sauti ya ce: “Kwamitin Koyarwa na Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu yana so a rika nuna al’adu da kuma yankuna dabam-dabam a bidiyoyinmu. Ana hakan ne domin muna da ’yan’uwa a fadin duniya kuma muna so bidiyoyinmu su nuna hakan.” Ya kara da cewa: “Don a cim ma hakan, rukunoni 24 a kasashe 11 ne suka hada hannu wajen yin wannan aikin. Sai da kudi da kuma shirye-shirye sosai ne za a iya yin irin wannan gagarumin aikin.”

 Da yawa daga cikin bidiyoyinmu suna bukatar a yi amfani da kayan aiki na musamman kuma a shirya wurin da za a dauka wasan da kyau. Alal misali, an gina wuraren da aka dauki bidiyon Nehemiya: “Farin Cikin da Jehobah Yake Bayarwa Shi Ne Ƙarfinku” a wurin daukan sauti da bidiyo da ke Mt. Ebo, kusa da Patterson, New York, U.S.A. Don a yi amfani da gudummawar da ake bayarwa a hanyar da ta dace kuma a nuna gine-ginen da ke bidiyon kamar yadda suke a dā, ’yan’uwa sun gina katangar da wasu abubuwa marasa nauyi kuma sun yi su yadda za su yi kama da katangar Urushalima ta dā. An yi katangar ne da katakai masu tsawon mita shida (kafa 20) kuma an rufe su da dunlop da aka yi musu fenti don su yi kama da duwatsu. An yi katangar yadda za a iya raba ta kuma a sake shirya ta bisa ga wurin da ake so a dauka bidiyon. Hakan ya sa ba a bukaci a gina irinta da yawa ba. Duk da haka, an kashe kusan dala 100,000 wajen gina dukan abubuwan da aka yi amfani da su a wasan kwaikwayon. a

 Yanzu da muka san yadda aka shirya taron yanki na wannan shekarar, muna fatan hakan zai sa mu dada godiya don aikin da aka yi. Mun tabbata cewa kokarce-kokarcen da aka yi wajen shirya taron yankin nan zai sa a yabi Jehobah a ko’ina a duniya. Mun gode muku da gudummawar da kuka yi hannu sake ta donate.pr418.com da kuma wasu hanyoyi.

a An yi bidiyon Nehemiya: “Farin Cikin da Jehobah Yake Bayarwa Shi Ne Ƙarfinku,” kafin bullowar annobar COVID-19 wato, koronabairas. Ba a bukatar a ba da tazara tsakanin mutane a lokacin.