Koma ka ga abin da ke ciki

Na Amince da Ra’ayin Allah Game da Jini

Na Amince da Ra’ayin Allah Game da Jini

Na Amince da Ra’ayin Allah Game da Jini

WANI LIKITA YA BA MU LABARINSA

AKWAI ranar da nake gaban rukunin likitoci a babban dakin taro a asibiti don in yi bayani akan abin da ya kai ga rasuwar wani mutum a asibitin. Mutumin kafin ya rasu ya yi fama da cutar kansa. Na ce: “Bincike ya nuna cewa abin da ya jawo mutuwarsa shi ne, jajjayen kwayoyin jininsa sun mutu kuma kodarsa ta daina aiki. Kuma abin da ya jawo hakan shi ne yawan jini da aka ba shi.”

Da jin haka sai wani farfesa ya tashi da fushi ya ce: “Kana nufin mun ba shi jinin da bai dace da shi ba ke nan?” Sai na ce: “Ba abin da nake nufi ba ke nan.” Sai na nuna musu wasu hotunan kodar mutumin kuma na ce: “Hotunan nan sun nuna cewa mutuwar jajjayen kwayoyin jininsa ne ya sa kodarsa ta daina aiki.” * Ransu ya baci sosai, ni kuma hankalina ya tashi. Ko da yake ni matashi ne a lokacin kuma shi farfesa ne, ban ji tsoronsa ba domin na san abin da na fada gaskiya ne.

A lokacin da muka yi gardamar nan, ni ba Mashaidin Jehobah ba ne. A shekara ta 1943 aka haife ni a wani birni mai suna Sendai a arewacin kasar Japan. Da yake mahaifina likita ne, ni ma na zaba in zama likita. A 1970 da nake shekarata ta biyu a jami’a na auri wata mai suna Masuko.

Yadda Na Soma Nazarin Cututtuka

Matata Masuko ta yi aiki don ta tallafa wa iyalinmu yayin da nake makaranta. Aikin likita ya burge ni sosai. Na yi mamaki sosai da na ga yadda aka tsara jikin dan Adam. Amma ban taba tunanin cewa akwai Mahalicci ba. Na dauka cewa yin bincike da ya shafi aikin likita zai sa in yi rayuwa mai kyau. Don haka, bayan da na zama likita, sai na soma nazarin cututtuka (pathology), wato nazarin alamomin cututtuka da abin da ke jawo su da kuma illolinsu.

Da nake yin bincike akan wadanda suka mutu sanadiyyar cutar kansa, shi ne na soma yin shakkar ko karin jini da ake musu yana taimaka wa. Wadanda cutar kansa ta shiga jikinsu sosai za su iya yin karancin jini domin jinin da ke zuba daga ciwon. Jinyar da ake musu kuma tana kara hakan. Shi ya sa a yawancin lokaci, likitoci suna cewa a musu karin jini. Amma na soma ganin alamar cewa karin jinin yana sa kansar ta dada yaduwa. A yau likitoci sun san cewa karin jini yana rage karfin garkuwar jikin mutum. Yana sa kansar ta sake dawowa kuma yana kara sa ya yi wa masu cutar wuya su rayu. *

A 1975 ne abin da na fada a farkon labarin nan ya faru. Farfesan kwararre ne a fannin cututtukan da suka shafi jinin mutum, kuma a hannunsa ne marar lafiyar nan ya rasu. Shi ya sa ya ji fushi sosai da ya ji cewa jinin da aka sa wa mutumin ya kashe shi. Amma na ci gaba da yin bayani kuma daga baya, ya kwantar da hankalinsa.

Karshen Rashin Lafiya da Mutuwa

A kwanakin ne wata tsohuwa Mashaidiyar Jehobah ta ziyarci matata. Da Mashaidiyar take magana, ta yi ta ambatar sunan “Jehobah.” Don haka, matata ta tambaye ta ko waye ne Jehobah. Sai Mashaidiyar ta ce “Jehobah shi ne sunan Allah Madaukaki.” Matata Masuko ta saba karanta Littafi Mai Tsarki tun tana karama. Amma ba ta taba ganin kalmar nan Jehobah ba domin an cire ta kuma an saka “UBANGIJI.” Yanzu ta san cewa akwai Allah kuma yana da suna.

Nan da nan matata ta yarda Mashaidiyar ta soma nazari da ita. Ina dawowa daga asibiti da dare wajen karfe daya, sai matata ta zo ta same ni tana farin ciki kuma ta ce, “Littafi Mai Tsarki ya ce za a kawar da ciwo da mutuwa.” Sai na ce, “Da gaske?” Sai ta kara da cewa, “Tun da sabuwar duniya ta yi kusa, ba na son ka ci gaba da bata lokacinka.” Da na ji hakan, sai na dauka cewa tana son in daina aikin likita ne, don haka raina ya bace kuma mun yi ta samun sabani.

Duk da haka, matata ba ta gaji ba. Ta ci gaba da rokon Allah ya taimaka mata ta sami nasossin da za su ratsa zuciyata. In ta sami wani nassi, sai ta karanta min. Abin da Mai-Wa’azi 2:​22, 23 sun fada ya sa ni tunani. Wurin ya ce: “Mene ne ’yan Adam suke samuwa daga dukan aikin da suke yi, da irin wahalar da suke sha cikin aikinsu a rayuwar duniyar nan? . . . Har ma da dare zuciyarsu ba ta hutawa. Wannan ma banza ne.” Na ga cewa abin da ke faruwa da ni ne ke nan. Domin na dukufa yin aiki da bincike dare da rana amma ba na farin ciki.

Ana nan wata ranar Lahadi, a watan Yuli 1975, matata ta yi shiri kuma ta tafi taron Shaidun Jehobah. Ni ma sai na ce zan bi ta. Matata tana zaune, sai ga ni, ta yi mamaki sosai. Sauran Shaidun Jehobah da ke wurin kuma sun marabce ni sosai. Tun daga ranar, na soma zuwa taronsu kowace ranar Lahadi. Bayan wajen wata guda, sai wani Mashaidin Jehobah ya soma nazari da ni. Watanni uku bayan matata ta hadu da tsohuwar nan, an mata baftisma.

Yadda Na Amince da Ra’ayin Allah Game da Jini

Da na soma nazari, ban jima ba sai na ga abin da Littafi Mai Tsarki ya fada cewa Kiristoci su ‘kiyaye kansu daga jini.’ (Ayyukan Manzanni 15:​28, 29; Farawa 9:⁠4) Da yake tun dā can ina shakkar amfanin sa wa mutum jini, ya yi min sauki in amince da ra’ayin Allah game da jini. * Kuma na ce, ‘Idan har akwai Allah kuma abin da ya ce ke nan, to lallai hakan gaskiya ne.’

A nazarin, na kuma gano cewa zunubin Adamu ne ya janyo rashin lafiya da mutuwa. (Romawa 5:12) Lokacin ina kan nazari a kan wata cutar jijiyoyin jini da ake kira arteriosclerosis. Cutar takan sami mutum ne yayin da yake tsufa, jijiyoyin jinin mutum sukan soma yin tauri, kuma fadin inda jinin ke bi ya soma raguwa. Hakan na jawo wa mutum cututtuka masu tsanani. Ban ga abin da zai sa hakan ya dinga faruwa in ba ajizanci ba. Da na ga hakan, sai marmarin yin bincike a kan cututtuka ya bi ya fita min a kai. Domin na gane cewa Jehobah ne kadai zai iya sa a daina rashin lafiya da mutuwa!

A watan Maris 1976, na daina binciken da nake yi a wani asibitin koyarwa. Watanni bakwai ke nan da na soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Na dauka ba zan sake samun aikin likita ba, amma sai na sami aiki a wani asibiti. A watan Mayu 1976 kuma, sai aka yi min baftisma. Na tsai da shawara cewa zan zama mai yin bishara na cikakken lokaci, wato majagaba, don na ga cewa abu mafi kyau da zan yi da rayuwata ke nan. Na soma hidimar a watan Yuli 1977.

Bayyana Ra’ayin Allah Game da Jini

A watan Nuwamba 1979, ni da matata Masuko mun kaura zuwa yankin wata ikilisiya da ke bukatar masu shela. A wurin na sami aiki na ’yan kwanaki a mako a wani asibiti. Ranar da na soma aiki, wasu likitoci sun zo sun kewaye ni suna cewa, ‘Kai Mashaidin Jehobah ne ko? To me za ka yi idan aka kawo marar lafiya da ke bukatar a yi masa karin jini?’

Sai na natsu kuma na gaya musu cewa zan bi abin da Allah ya ce game da amfani da jini. Kari ga haka, na gaya musu cewa akwai abubuwan da mutum zai iya yi don ya taimaka ma wanda yake fama da karancin jini ba tare da sa masa jini ba, kuma cewa zan yi iya kokarina in taimaka wa duk marar lafiya da ya zo wurina. Bayan mun yi wajen awa guda muna tattaunawa, sai shugaban masu yin fida a asibitin ya ce min, “Na fahimce ka. Amma idan aka kawo marar lafiya da ya yi hasarar jini sosai, za mu yi aikin ban da kai.” An san mutumin nan da wuyar sha’ani, amma bayan tattaunawar nan, sai ni da shi muka zama abokai. A kullum yana daraja ni don imanina.

Ban Daina Bin Ra’ayin Allah Game da Jini Ba

A lokacin Shaidun Jehobah suna gina ofishinsu da ake kira Bethel a Japan. Ni da matata mukan je wurin sau daya kowace mako don mu kula da lafiyar wadanda suke taimakawa a aikin ginin. Bayan ’yan watanni sai aka ce mu koma yin aiki a Bethel. Don haka a watan Maris 1981, mun kaura zuwa inda Shaidun Jehobah da suke aikin suke zama. Su fiye da dari biyar ne suke zama a wurin. Kowane safe, aikina shi ne in tsabtace wuraren wanka da ba haya. Da rana kuma sai in yi aikin likita.

Akwai wata mai wa’azi a kasashen waje mai suna Ilma Iszlaub, da ta zo daga kasar Ostireliya a 1949. A lokacin tana fama da kansar jini da ake kira leukemia kuma likitoci sun gaya mata cewa bayan ’yan watanni za ta mutu. Likitocin sun ce karin jini ne zai taimaka mata, amma Ilma ta ki. Kuma ta zabi ta karasa rayuwarta a Bethel. Akwai wani jan sinadari da ke jinin mutum da ake kira hemoglobin. Kowane mutum yana bukatar tsakanin giram 12 zuwa 15 na wannan sinadari a cikin jininsa. Amma yawan sinadarin nan a jinin Ilma yakan sauka zuwa giram 4 har giram 3, don a lokacin ba mu da irin magungunan da muke da su a yau. Duk da haka, na yi iya kokarina wajen yi mata jinya. Ilma ta ci-gaba da rike imaninta har lokacin da ta mutu, bayan wajen shekaru bakwai!

A shekarun da na yi ina hidima a ofishin Shaidun Jehobah da ke Japan, an sami ’yan’uwa da yawa da suka bukaci a yi musu fida. Kuma an sami likitoci a asibitocin da ke kusa da suka yarda su yi wa ’yan’uwanmu aiki ba tare da yin karin jini ba. Muna musu godiya. Sau da yawa likitocin sukan kira ni in zo in kalli yadda suke aikin. Har ma a wasu lokuta, ni ma na taimaka wajen yi ma wasu ’yan’uwa fida. A gaskiya, na gode wa likitocin nan da suka daraja zabin Shaidun Jehobah na kin karbar jini. Aikin da muka yi ta yi da su, ya sa na iya gaya wa mutane game da imanina sau da yawa. Kwanan nan, daya daga cikin likitocin ya zama Mashaidin Jehobah.

Abin farin cikin shi ne, kokarin da likitoci suka yi don su yi wa Shaidun Jehobah jinya ba tare da yi musu karin jini ba, ya kyautata aikin likita sosai, don ya taimaka wa marasa lafiya da yawa. Yanzu an gano cewa wadanda aka musu fida sun fi saurin warkewa idan ba a yi musu karin jini ba.

Na Ci-gaba da Koyo Daga Wurin Likitan da Babu na Biyunsa

Na ci-gaba da koyan sabbin abubuwan da ake kirkirowa a fannin aikin likita. Kuma na ci-gaba da koyo game da Jehobah wanda shi ne likitan da babu na biyunsa. Ba yadda mutum yake a waje ne kawai Jehobah yake gani ba, amma yana lura da tunanin zuciyar mutum. (1 Sama’ila 16:⁠7) Ni ma yayin da nake aikina na likita, ba rashin lafiyar da ke damun mutum kawai nake mai da wa hankali ba, nakan kuma lura da abin da marar lafiyan yake tunani. Yin hakan yana taimaka min in ba su kulawa mai kyau.

Na ci-gaba da yin hidima a Bethel kuma ina taimaka wa mutane su san game da Jehobah da ra’ayinsa game da jini, domin daya daga cikin abubuwan da suka fi sa ni farin ciki ke nan. Nan ba da dadewa ba, Jehobah wanda shi ne likitan da babu na biyunsa, zai kawo karshen rashin lafiya da mutuwa, ina marmarin ganin wannan ranar, kuma ina rokon Allah ya kawo ta.​​—⁠Yasushi Aizawa ne ya ba da labarin.

[Footnotes]

^ sakin layi na 4 A littafin nan Modern Blood Banking and Transfusion Practices da Dr.  Denise M. Harmening ya wallafa, wani masani ya ce: “Marasa lafiya da suke da ciki da wadanda aka taba musu dashe za su iya samun matsala sosai da zai kai ga mutuwar jajjayen kwayoyin jininsu idan aka musu karin jini. Haka ma wadanda aka taba musu karin jini kuma aka sake musu.” Idan mutum yana wannan yanayin, gwaje-gwajen jinin da ake yi kafin a sa wa mutum jini ba sa iya nuna ko za a sami matsala daga baya ko a’a ba. Wani littafi da ya yi bayani akan jini ya ce, “Ko da jinin da aka saka wa mutum da ya bambanta da nasa dan kadan ne, zai iya hallakar da jajjayen kwayoyin jininsa. Hakan zai sa kodar mutumin ta daina aiki. Kuma idan koda ta daina tsabtacce jini, datti yakan taru ya zama kamar guba a jikin mutumin.”

^ sakin layi na 8 Wata mujallar da aka wallafa a 1988 game da jinyar cutar kansa ta ce: “Wadanda aka musu karin jini don tiyata da aka musu ya yi musu wuya su warke fiye da wadanda ba a musu karin jini ba.”

^ sakin layi na 16 Don karin bayani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da jini, ka karanta kasidar nan How Can Blood Save Your Life? Shaidun Jehobah ne suka wallafa ta.

[Bayani]

“Na gaya musu cewa akwai abubuwan da mutum zai iya yi don ya taimaka wa wanda yake fama da karancin jini ba tare da sa masa jini ba, kuma cewa zan yi iya kokarina in taimaka wa duk marar lafiya da ya zo wurina

[Bayani]

Yin jinya ba tare da yin karin jini ba ya taimaka wa marasa lafiya da yawa

[Hotuna]

Hoto na sama: Ina yin jawabi daga Littafi Mai Tsarki

Na dama: Ni da matata, Masuko