HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Agusta 2017

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari na 25 ga Satumba zuwa 22 ga Oktoba, 2017.

Kana Shirye Ka Jira Jehobah da Hakuri?

Bayin Jehobah masu aminci a zamanin dā sun yi tambaya cewa har yaushe za su ci gaba da jimre da jarabobbi, duk da haka, Allah bai yi fushi da su ba.

“Salama ta Allah ta Fi Ganewar Dan Adam”

Ka yi tunanin abin da ya sa Allah ya kyale ka kana fuskantar wasu jarabobbi? Idan haka ne, mene ne zai iya taimaka maka ka jimre kuma ka dogara ga Jehobah?

TARIHI

Na Sami Albarka Sosai don Na Jimre da Tsanantawa

Me ya sa wadanda aka kai zaman bauta a Saberiya za su yi tambayar shanu kuma da gaske suna neman tumaki? Za a iya samun amsar a labari mai kayatarwa na Pavel da Maria Sivulsky.

Yadda Za Mu Kawar da Halin Banza

Mu kawar da halin banza kuma mu ci gaba da kasancewa da hali mai kyau. Ta yaya za mu yi nasara a yin hakan ko da zunubin da muka yi yana da muni sosai?

Ka Dauki Sabon Hali kuma Ka Ci gaba da Hakan

Jehobah zai taimaka maka ka yi nasara wajen kasancewa da sabon hali. Ka yi tunanin hanyoyin da za ka iya kasancewa da tausayi da nagarta da alheri da tawali’u a rayuwarka na yau da kullum.

Kauna​—Hali ne Mai Muhimmanci

Nassosi sun nuna cewa kauna ce ke sa ruhu mai tsarki yake aiki. Mece ce kauna? Ta yaya za mu kasance da wannan halin? Kuma ta yaya za rika nuna shi a kowace rana?

DAGA TARIHINMU

“Yaushe Za Mu Yi Wani Babban Taro Kuma?”

Me ya sa karamin taro da aka yi a babban birnin Meziko a shekara ta 1932 yake da muhimmanci sosai?

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Me ya sa labarin Matta game da lokacin da Yesu yake karami da iyalin da ya fito ya yi dabam da na Luka?