HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Janairu 2019

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 4 ga Maris zuwa 7 ga Afrilu, 2019

‘Kada Ka Damu, Domin Ni Ne Allahnka’

Ka yi la’akari da dalilai uku da za su sa mu kasance da kwanciyar rai sa’ad da muke fuskantar matsaloli.

Mu Yabi Jehobah a Cikin Ikilisiya

Yana yi maka wuya ka yi kalami a taro? Talifin nan zai taimaka maka ka san abin da ya sa kake jin tsoro da kuma yadda za ka daina yin hakan.

Ta Yaya Za Ka Iya Kiyaye Zuciyarka?

Ta yaya Shaidan yake kokari ya gurbata zuciyarmu kuma ta yaya za mu kiyaye ta

Abin da Taron Tunawa Ya Koya Mana Game da Sarkinmu

Mene ne taron Tuna da Mutuwar Yesu ya koya mana game da tawali’unsa da karfin halinsa da kuma kauna da ya nuna?

Abin da Halartan Taro Yake Nunawa Game da Mu

Ta yaya halartan taro yake nuna cewa muna da kauna da tawali’u da kuma karfin hali?

Sabon Memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu

Ka koyi wasu abubuwa game da yadda dan’uwa Kenneth Cook ya girma.