HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Maris 2019

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 6 ga Mayu zuwa 2 ga Yuni, 2019

Mene ne Yake Hana Ni Yin Baftisma?

Wasu da sun riga sun koya game da Jehobah suna jinkirin yin baftisma. Mene ne zai taimaka musu su magance wannan matsala da ke sa su jinkirin yin baftisma?

Ku Saurari Jehobah

Ta wace hanya ce Jehobah yake yi mana magana a yau? Ta yaya za mu amfana daga saurarar Allah?

Ku Nuna Kun Damu da Mutane

A wadanne hanyoyi ne Jehobah da Yesu suka nuna sun damu da mutane, kuma ta yaya za mu bi misalinsu?

Ku Nuna Kun Damu da Mutane a Wa’azi

A wadanne hanyoyi guda hudu ne za mu iya nuna tausayi sa’ad da muke wa’azi?

Nagarta​—Ta Yaya Za Mu Koyi Nuna Wannan Halin?

Mece ce nagarta? Me ya sa muke bukatar mu koyi nuna wannan halin?

Jehobah Yana Daraja “Amin” da Muka Furta

Mutane da yawa suna furta ‘amin’ bayan an kammala addu’a. Mene ne wannan kalmar take nufi kuma ta yaya aka yi amfani da ita a Littafi Mai Tsarki?