HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Oktoba 2019
Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 2-29 ga Disamba, 2019.
1919—Shekara Dari da Suka Shige
A shekara ta 1919, Jehobah ya karfafa mutanensa su yi irin wa’azin da ba a taba yi ba. Amma Daliban Littafi Mai Tsarki suna bukatar yin canje-canje.
Hukuncin Allah—Yana Ba da Isashen Gargadi Kuwa?
Jehobah yana gargadar da mutane game da guguwar da ke nan tafe da ta fi kowace irin guguwa hadari. A wace hanya ce yake yin hakan?
Ka Ci Gaba da Kwazo a Karshen “Kwanaki na Karshe”
Wadanne abubuwa ne za su faru a karshen “kwanaki na karshe”? Kuma mene ne Jehobah yake so mu yi yayin da muke jiran abubuwan nan su faru?
Ku Kasance da Aminci a Lokacin Kunci Mai Girma
Mene ne Jehobah zai so mu yi a lokacin “kunci mai girma”? Ta yaya za mu yi shiri yanzu don mu kasance da aminci a lokacin?
Mene ne Jehobah Zai Sa Ka Zama?
A zamanin dā, Jehobah ya ba bayinsa marmari da kuma karfin yin nufinsa. Ta yaya Jehobah yake shirya mu mu bauta masa a yau?
Mu Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciyarmu
Ka yi la’akari da abubuwa biyu da za su iya hana mu bauta wa Jehobah shi kadai.