HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Maris 2020

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 4-31 ga Mayu, 2020.

Kauna ga Jehobah Za Ta Sa Mu Yi Baftisma

Kauna ga Jehobah za ta sa mu yi baftisma. Amma mene ne zai iya hana ka yin hakan?

Ka Shirya Yin Baftisma Kuwa?

Tambayoyin da aka tattauna a wannan talifin za su taimaka maka ka san ko ka cancanci yin baftisma.

TARIHI

“Ga Mu Nan Ka Aike Mu!”

Jack da Marie-Line sun bayyana abin da ya sa suka soma hidima ta cikakken lokaci da kuma abin da ya taimaka musu su saba da wurare dabam-dabam da suka je hidima.

A Wane Lokaci Ne Ya Dace Ka Yi Magana?

Ka yi la’akari da wasu misalai a Littafi Mai Tsarki da za su taimaka maka ka san lokacin da ya kamata ka yi magana kuma shiru.

Ku Rika Kaunar Juna da Zuciya Daya

Yesu ya ce kauna ce za ta nuna cewa mu Kiristoci ne na gaskiya. Ta yaya kauna za ta taimaka mana mu zama masu zaman lafiya da kin nuna son kai da kuma karimci?

Ka Sani?

Ban da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, mene ne kuma ya nuna cewa a dā, Isra’ilawa bayi ne a Masar?

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Su waye ne ’yan sandan haikalin Yahudawa? Mene ne aikinsu?