HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Disamba 2020
Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 1-28 ga Fabrairu, 2021.
Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Furucin manzo Bulus da ke 1 Korintiyawa 15:29 yana nufin cewa wasu Kiristoci a zamanin dā sun yi baftisma ne a madadin matattu?
Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Littafin Karin Magana 24:16, ta ce: “Ko da mai adalci ya fāɗi sau bakwai, zai tashi.” Shin wannan furucin yana magana ne game da mutum da ya yi zunubi a kai a kai, kuma Allah ya gafarta masa?