Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

An shirya wannan littafin ne don ta taimaka maka ka san abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da batutuwa da yawa, kamar dalilin da ya sa muke shan wahala, abin da ke faruwa da mu sa’ad da muka mutu, yadda za mu sa rayuwar iyalinmu ta kasance da farin ciki da dai sauransu.

Abin da Allah Ya Nufa Ke Nan?

Za ka iya yin mamakin dalilin da ya sa muke fama da matsaloli da yawa a yau.Ka san cewa Littafi Mai Tsarki ya ce abubuwa za su gyaru kuma kai ma za ka amfana?

BABI NA 1

Mece ce Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah?

Kana ganin Allah ya damu da kai kuwa da gaske? Ka koyi halayensa da yadda za ka iya kusantar sa.

BABI NA 2

Littafi Mai Tsarki—Littafi Ne Daga Allah

Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka bi da matsaloli na yau da kullum? Me ya sa za ka gaskata da annabcin Littafi Mai Tsarki?

BABI NA 3

Menene Allah ya Nufa ga Duniya?

Nufin Allah na mai da duniya aljanna zai tabbata kuwa? Idan haka ne, yaushe?

BABI NA 4

Wanene Yesu Kristi?

Ka bincika dalilin da ya sa aka kira Yesu Almasihun da inda ya fito da kuma dalilin da ya sa aka kira shi Dan fari na Jehobah.

BABI NA 5

Fansa—Kyauta Mafi Girma Daga Allah

Mece ce fansa? Ta yaya za ka amfana daga fansar?

BABI NA 6

Ina Matattu Suke?

Ka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da inda matattu suke da kuma dalilin da ya sa mutane suke mutuwa.

BABI NA 7

Bege na Gaskiya ga Ƙaunatattunka da Suka Mutu

An taba mana rasuwa ne? Zai yiwu ka gan su kuma? Ka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da tashin matattu.

BABI NA 8

Menene Mulkin Allah?

Mutane da yawa sun da addu’ar Ubangiji. Mene ne ma’anar furucin nan: “Mulkinka shi zo”?

BABI NA 9

Muna Rayuwa ne a “Kwanaki na Karshe”?

Ka bincika yadda yanayin mutane da kuma halayensu zai zama a “kwanaki na karshe” kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta.

BABI NA 10

Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu

Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mala’iku da kuma aljannu. Shin wadannan halittun ruhun suna wanzuwa kuwa? Za su iya shafan rayuwarka?

BABI NA 11

Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Wahala?

Mutane da yawa suna gani cewa Allah ne yake da alhakin wahala da muke sha a duniya. Me kake tsammani? Ka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da wahala da muke sha.

BABI NA 12

Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai

Zai yiwu mu yi rayuwa a hanyar da take faranta wa Jehobah rai. Hakika, za ka iya zama abokinsa.

BABI NA 13

Ra’ayin Allah Game da Rai

Yaya Allah yake daukan zub da ciki da karban karin jin da kuma ran dabba?

BABI NA 14

Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki

Yesu ya kafa misalin kauna ga maza da mata da iyaye da kuma yara. Me muka koya daga wurinsa?

BABI NA 15

Bauta da Allah Ya Amince da Ita

Ka yi la’akari da abubuwa shida da za a gane addini na gaskiya da shi, wato irin bautar da Allah ya amince da ita.

BABI NA 16

Ka Dage Domin Bauta ta Gaskiya

Wadanne kalubale za ka fuskanta sa’ad da ka soma gaya wa mutane abin da ka yi imani da shi? Ta yaya za ka yi hakan ba tare da bata musu rai ba?

BABI NA 17

Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a

Allah yana sauraronka sa’ad da kake masa addu’a? Don ka ba da amsa ga wannan tambayar kana bukata ka fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da addu’a.

BABI NA18

Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah

Mene ne muke bukatar yi don mu cancanci yin baftisma a matsayin Kirista? Ka koya abin da hakan yake nufi kuma yadda ya kamata mu yi hakan.

BABI NA 19

Ka Tsare Kanka Cikin Kaunar Allah

Ta yaya za mu nuna kauna da kuma godiya don dukan abubuwan da Allah ya yi mana?

RATAYE

Ma’anar Sunan Allah da Yadda Ake Amfani da Shi

An cire sunan Allah daga juyin Littafi Mai Tsarki da yawa. Me ya sa? Shin yin amfani da sunan Allah yana da muhimmanci?

RATAYE

Yadda Annabcin Daniel ya Bayyana Zuwan Almasihu

Allah ya nuna daidai lokacin da Almasihun zai bayyana shekaru fiye da 500 kafin lokacin. Ka bincika wannan annabci mai ban mamaki!

RATAYE

Yesu Kristi—Almasihu da Aka Yi Alkawarinsa

Yesu ya cika duk wani annabci da aka yi game da Almasihu a cikin Littafi Mai Tsarki. Ka bincika Littafi Mai Tsarki don ka tabbata cewa wadannan annabce-annabcen sun cika.

RATAYE

Gaskiya Game da Uba, Ɗa, da Kuma Ruhu Mai Tsarki

Mutane da yawa sun dauka cewa koyarwar Dunkulin-Alloli-Uku koyarwar Littafi Mai Tsarki ce. Hakan gaskiya ce?

RATAYE

Abin da Ya Sa Kiristoci na Gaskiya ba Sa Amfani da Gicciye Wajen Bauta

Da gaske ne Yesu ya mutu a kan gicciye? Ka karanta amsar a cikin Littafi Mai Tsarki.

RATAYE

Jibin Maraice na Ubangiji—Farilla da Ke Daraja Allah

An umurci Kiristoci su rika tunawa da mutuwar Kristi. Yaushe ne ya kamata mu tuna da mutuwar Yesu kuma yaya ya kamata mu yi hakan?

RATAYE

“Kurwa” da Kuma “Ruhu”—Menene Ainihi Ma’anar Waɗannan Kalmomi?

Mutane suna gani cewa idan mutum ya mutu wani abu yana fita kuma ya ci gaba da rayuwa. Mece ce Kalmar ta ce?

RATAYE

Menene Sheol da kuma Hades?

Wasu masu fassara Littafi Mai Tsarki sun yi mafani da kalaman nan “kabari” ko “hell” a madadin Sheol da Hades. Menene ma’anar wadannan kalmomin?

RATAYE

Mecece Ranar Shari’a?

Ka bincika yadda ranar Shari’a za ta kawo albarka ga dukan mutane masu aminci.

RATAYE

1914—Shekara Mai Muhimmanci a Annabcin Littafi Mai Tsarki

Mene ne ya nuna cewa 1914 shekara ce mai muhimmanci a Littafi Mai Tsarki?

RATAYE

Wanene Mika’ilu Shugaban Mala’iku?

Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da wannan mala’ika mai iko. Ka sami karin bayani game da shi da kuma abin da yake yi yanzu.

RATAYE

Gano “Babila Babba”

Littafin Ru’ya ta Yohanna ya yi magana game da wata karuwa mai suna Babila Babba. Ita ainihin mace ce? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da ita?

RATAYE

A Watan Disamba ne Aka Haifi Yesu?

Ka bincika yadda yanayin wuri yake a shekarar da aka haifi Yesu. Mene ne hakan ya koya mana?

RATAYE

Ya Kamata Ne Mu Kiyaye Ranaku Masu Tsarki?

Mene ne tushen yawancin ranaku masu tsarki da mutane suke kiyayewa a yankinku? Amsar da za ka samu zai ba ka mamaki sosai.